Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Idi Ya Faɗo A Ranar Juma'a Za A Bar Sallar Juma'a?

Idan idin ƙaramar sallah ko babba ya faɗo ranar Jumu'a to akwai maganganun malamai guda uku:

1• Zaiyi idi kuma Juma'a ba za ta faɗi a kansa ba, saboda Juma'a wajibi ce a kan kowa don haka ba za ta faɗi saboda idi ba, wannan ita ce maganar Malikiyya da Hanafiyya.

2• Ya halatta ga waɗanda suke '‘yan ƙauye subar Juma'a, idan sun yi idi sai su koma gida, Ba dole sai sun halarci Juma'a ba, saboda hakan zai wahalar da su, tunda ba a gari suke

ba, ga shi kuma babu ƙuntatawa a cikin musulunci.

3• Wanda ya yi idi zai iya barin Juma'a, saboda Ibnu Majah ya rawaito hadisi daga Ibnu Umar a lamba ta: 1312 cewa:

Manzon ALLAH {s.a.w} ya yi rangwame idan Juma'a ta haɗu da idi a ƙyale sallar juma'a.

Zance na uku yafi inganci saboda hadisi yana goya masa baya, tare da cewa, ya wajaba ga wanda baije Juma'a ba ya yi Azahar, tunda anyi rangwame a kan barin Juma'a ne saboda wahalarwa a cikin haɗa biyun, hakan kuma babu shi a Azahar .

 Wanda yake Liman ne zaiyi Juma'a saboda waɗanda zasu halarta, saboda faɗin Annabi {s.a.w} Lokacin da ya yi sauƙi game da Juma'a.

Don neman ƙarin bayani duba:

Mudawwanah 6/153 da kuma Al-mugni 2/105

ALLAH shi ne mafi sani.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments