Ticker

6/recent/ticker-posts

Taubasantakar Bazamfare Da Badakkare (5)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Taubasantakar Bazamfare Da Badakkare (5)

NA

ABDULRAHMAN BALA

 

Taubasantaka

                                                    BABI NA HUƊU

TASIRIN TAUBASANTAKAR BAZAMFARE DA BADAKKARE

4.0 GABATARWA

Haƙiƙa wannan taubasantaka da ke tsakanin Zamfarawa da Dakkarawa ta yi tasiri sosai a tsakanin waɗannan al’ummomi guda biyu, inda ta haifar da muhimman abubuwa waanda za su ƙara sa wannan alaƙa ko taubasantakar ta ƙara ƙarfi sosai a tsakaninsu. Daga cikin waɗannan abubuwa akwai, ƙarfafa zumunci, akwai kuma auratayya da dama a tsakanin waɗannan al’ummomi. Bayan haka kuma sun fahimci al’adun juna, hasali ma, sun kasance masu taimakon juna, tare da haƙuri da girmama juna. Waɗannan su ne tasirin da taubasantakar ta haifar a tsakaninsu.

4.1 ƘARFAFA ZUMUNCI

Mene ne zumunci?: Zumunci shi ne zamantakewa irinta ‘yan uwantaka, wadda take ƙulla mu’amuloli daban-daban a takanin al’ummomi, da suka haɗa da ziyartar juna, da taimakon juna ta fannona mabambanta. Ta hanyar zumunci ake samun taimakekeniya, wurin hidimomi na yau da kullum. Misali hidimar aure, hidimar suna da sauransu.

 

Tabbas in dai haka ne zumunci, to wannan taubasantakar da ke tsakanin Zamfarawa da Dakkarawa ta ƙarfafa zumunci sosai a tsakaninsu, domin baya ga yan uwantakar da ke tsaianinsu, su kan ziyarci junansu akai-akai, inda Zamfarawa sukan samu wasu lokutta, sukai ziyara ga ‘yan uwansu Dakarkari. Su kan ziyarci yan uwansu Zamfarawa, a duk lokacin da ɗaya daga cikinsu zai ziyarci ɗaya, to yakan yi ‘yar sayayya wadda zai tafi da ita a matsayin gudunmawa, ko tsaraba don ya ba ‘yan uwansa wanda hakan ma taimako ne da ke ƙara ƙarfafa zumunci.

 

 

4.2 AURATAYYA TSAKANIN ZAMFARAWA DA DAKKARAWA

Mene ne Aure?. Aure alaƙa ce ta ƙulla yarjejeniyar zamantakewa a tsakanin Namiji da mace. Wannan alaƙa ta auratayya tana wanzuwa a tsakanin al’ummar Zamfarawa da Dakkarawa wadda za a iya samun Badakkare (namiji) ya auri mace yar ƙasar Zamfara, kuma a kai ta ƙasar Zuru ko kuma a samu Bazamfare ya auri mace yar ƙasar Dakarkari, kuma a kawo ta ƙasar Zamfara don ta yi zaman aure. Misali, akwai ɗiyar Sarkin Zuru na yanzu wadda take aure a garin Kwatarkwashi ta ƙaar Zamfara, haka kuma akwai wata mata mai suna Fatima mai kitso, ita ma asalinta Badakkara ce. Amma ta dalilin aure ya sa take zaune a ƙasar Zamfara, wato tana auren Bazamfare. Sannan kuma mata yan ƙasar Zamfara da suke aure a ƙasar Dakarkari; misali akwai Hajiya Salima mai abinci yar asalin kauyen Gamji ce ta ƙasar Zuru, wadda take aure a garin Gummi da dai sauran makamantan haka (Fira da Fatima).

 

Wannan dai alaƙa ta auratayya ta mai da waɗannan al’ummomi ‘yan ‘uwan juna, tare da ƙarfafa zumunci a tsakaninsu. Kuma hakan duk ta faru ne ta dalilin taubasantakar da ke tsakaninsu.

 

4.3 FAHIMTAR AL’ADUN JUNA

Mece ce al’ada? Al’ada ita ce hanyar gudanar da rayuwar kowace al’umma; Al’ummar Zamfarawa da Dakkarawa kowa ne daga cikinsu yana da tashi ko nashi al’adun da suka keɓanta a kanshi. Amma wannan bai hana su fahimtar al’adun juna ba. Bayan fahimtar al’adun juna akwai tasirin da al’adunsu suka yi a tsakaninsu, ma’ana akwai al’adun Zamfarawa da suka yi tasiri akan al’adun Dakkarawa. Misali kasancewar cigaba na zumunci, akwai al’adar barantaka ta noma har na shekara bakwai (7) mai suna “Gwalmo” kafin a bai wa mutum auren Badakkara, yanzu babu ita, dalili shi ne yanzu Zamfarawa sukan shiga neman auren Dakkarawa, kuma a ba su, ba tare da sun bi waccan al’adar ba ta noma. Hakan na nufin al’adar ko al’adun Zamfarawa na neman aure, sun yi tasiri a kan wasu daga cikin al’adun Dakarkari na neman aure. Don haka za mu iya cewa sun fahimci al’adun juna domin samun mu’amula mai ɗorewa.

 

4.4 TAIMAKON JUNA

Mene ne taimako? Taimako wata hanya ce ta musamman da take sauƙaƙa ma wani wanda ke gudanar da wani abun da ya shafi rayuwa. Tabbas akwai taimakekeniya a tsakanin waɗannan al’ummomi domin sun kasance maƙwabtan juna. Ma’ana, ƙasar Zamfara tana makwabtaka da ƙasar Dakkarawa, wannan makwabtaka, da kuma zamansu taubasan juna ya sa idan an samu huɗɗoɗi waɗanda kan haifar da taimakekeniya a tsakaninsu, sukan taimaka ma junansu. Misali akwai abubuwan da suka shafi aikin daji kamar noma, shuka, girbi da sauransu. Ta ɓangaren sha’anin rayuwa na yau da kullum, a nan ma sukan taimaka ma junansu, kamar wajen hidimar aure, zanen suna, gini, abinci, sutura da sauransu. Waɗannan abubuwan duk suna cikin tasirin da taubasantakar ta haifar.

 

4.5 HAƘURI DA GIRMAMA JUNA

Masu iya magana na cewa “Duk wanda ya ce zo mu zauna to ya ce zo mu saɓa,” kasancewar huɗɗa daban-daban na kasancewa a tsakanin Zamfarawa da Dakkarawa, kuma babban abun da ya sa huɗɗar ko taubasantakar ta ɗore shi ne haƙuri da juna. Ta hanyoyi daban-daban. Misali kamar haƙuri a cikin al’amurran auratayya, ko huɗɗar kasuwanci da sauransu. Dukkansu haƙuri shi ne abin da ke dauwamar da su.

 

Bayan haka akan samu girmama juna a tsakanin Zamfarawa da Dakkarawa ta hanyoyi mabambanta da suka haɗa da girmama Dattijai (tsofaffi) girmama surukai, da malamai da shuwagabanni da suka haɗa da na siyasa da kuma sarakuna da sauransu.

 

4.6 NAƊEWA

A kammale, wannan babi ya yi tsokaci ne a kan mu’amulolin da ke tsakanin Zamfarawa da Dakkarawa. Dangane da abubuwan da suka shafi, zumunci gami da huɗɗar aurataya, tare da fahimtar juna ta hanyar al’adu. Sai kuma yadda suke taimakon junansu, bugu da kari, akwai girmamawa da kuma haƙuri da juna a kan sha’anin rayuwa na yau da kullum.

Post a Comment

0 Comments