Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma'aurata // 22: Don Me Na Ƙaunace Ki?


"Anya wannan mutumin ba zai bi ta ba kuwa?" Don wasu matan da dama ba sa iya tsawon rai bayan rasuwar maigidan da suka ƙwallafa rai a kansa. Na san matan da suka bi mazansu da 'yan kwanaki kaɗan. Akwai ma wata da yanzu take gidan mijin, uwayenta sun yi faɗa har sun gaji ta ce....

Kundin Ma'aurata // 22:  Don Me Na Ƙaunace Ki?

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah


Ina ganin akwai zubar da ƙima ba kadan ba mace ta yi tsammanin don zaman gida da harkokin shimfida kawai aka auro ta kuma iya abin da za ta yi kenan, akwai mata barjak a duniya, kuma kowa na da wannan halitta ta matantaka, me zai sa na watsar da kowa sai ke, har na riƙa jin in ba ki rayuwata ba za ta kammala kamar yadda nake buƙata ba? Ba shimfida ce ba kadai Hajia, akwai wasu abubuwan ƙari a kan haka:-

1) Zan danƙa miki komai ne na rayuwata a hannunki, ina sa rai za ki kula da duk abin da zai sa raina ya yi haske, ki sa a yi nesa da duk abin da zai baƙanta min rai, za ki sa wata kadada tsakanina da abin da yake so ya wargaza min gida ko zumuntata, za ki yi ƙoƙarin ganin farin cikina a kullum yana hannunki, za ki dauki ragamar kawar min da baƙin ciki a duk lokacin da kika ga yana ƙoƙarin kawo min farmaki.
.
2) Duk wani abin da zanci kuma a cikin gida zabinki ne, ke ce za ki rarrabe abin da nake so da wanda nake buƙata, gwargwadonsa da dandanonsa, da yanayin dafuwarsa har ma da abubuwan da aka zuba a ciki, gami da sanin lokacin da za a ci din, kin san abin da in na ci zai bata min ciki da wanda zai kwanta lafiya, kin kiyaye irin abincin da ba na buƙata da daddare saboda kauce wa matsalolin shimfida, kamar zobo mai sanyin gaske ko cin ganyen latas mai dama a lokacin kwanciya, kiyaye waɗannan abubuwa ne na tsayayyiyar mace.
.
3) Idan rashin lafiya ya kama ni ke ce ta farkon da zan nema, ba don kina ba da magani ko waraka ba, yanayin kularki da tausayinki, da kawo min duk abin da nake buƙata, har ki mai da ni tamkar danki, wajen rarrashi da sauransu, ba ki ƙyamar wani abu a wurina kasancewar ban da lafiya, da haka ko ciwon kai nake yi sai na gaya miki, don kin san irin magungunan da nake buƙata, duk abubuwan da likita ya yi bayani kina wurin kuma kin haddace su gaba daya, lokutan shan maganina na zuwa kin dauko min ga ruwa kin kawo min, ko na ƙi sha za ki matsamin ta wajen gaya min dadadan maganganunki, za ki yi iya ƙoƙarinki wajen ganin yara ba su dame ni sun hana ni barci ba, za ki tantance irin maganganun da za a iya gaya min a lokacin, da waɗanda ba na buƙatarsu.
.
4) Dukiyata kina ganin naki ne da duk waɗanda suke cikin gidan, amma ba ke ce kike da haƙƙin taba su ko juya su ba, don haka ba kya sanya ido ko kadan a ciki in ba wanda aka ba ki a hannu kuma aka nuna miki ga abin da ake buƙatar ki yi da su ba, sannan za ki yi iya ƙoƙarinki wajen ganin ba a yi almubazzaranci da su ba, in buƙatun yau sun biya sai a adana sauran don gobe, kina iya bakin ƙoƙarinki wajen asusunta abubuwan dake shiga hannunki don magance ranar da za a rasa wani abin, akwai daɗi a ce komai ake buƙata kuna da shi amma almubazzaranci saboda wadata ba dabi'ar mace ta ƙwarai ba ne, takan dafa ko ta sa a dafa abin da suke da buƙata ne kawai, ba wai a ci a bar shi ya lalace a zubar ba.
.
5) Ina sa rai da komai na gida yana hannunki ne, in bananan kamar inanan ne, don kin wuce mataimakiyata, gidan kacokan dinsa naki ne, 'yan uwana ba za su ji wani bambanci tsakanina da ke ba, to bare kuma mahaifiyata, har 'yan uwana mata su gummace su yi magana dake sama da ni don ke ce 'yar uwarsu mace za ki fi fahimtar abin da suke nufi cikin sauƙi, 'yan uwanki in sun zo sun san darajar nawa, sun kuma san iyakarsu, don haka akan hadu cikin mutunci a rabu ba tare da matsala ba, duk wani abin da zai bata sunan gidana kin taka masa burki ko ma kin kawar da shi, mata masu gulma da tsugudidi kin yi musu iyaka da gidanki don neman zaman lafiya da maigidanki, idonki a bude yake ga duk abin da yake faruwa a cikin gidan.
.
6) Ba wani abu a dakinki wanda zan kalla ban yi sha'awa ba, komai an gyara shi kuma an ajiye shi a inda ya dace, wurin da yake buƙatar guga da tsaftacewa tuni kin gyara, haka kicin dinki da ban-daki kamar tsakar gida ne, ke kanki suturarki tsaftatacciya ce, in ina ɗaki daga ni sai ke ƙamshinki kawai yake tashi sai jan hankalina kike yi da halittarki da kwalliyarki da adonki, maganarki mai daɗi cikin kwanciyar hankali, a tsawon zamanki da ni, in zan shugo sau dubu ba abin da nake gani sama da wanda zai faranta rai, sam ba ki yarda kin girma ba bare a yi maganar tsufa, a kullun kina jin cewa jin daɗina yana hannunki ne kuma ke din ce dai za ki ba ni, ƙamshinki sai tashi yake ta ko'ina, ɗaki ga kayayyakin ado a inda na juya, kin yi shafe-shafe ga tozali rambadadau, lallen dake hannunki kuwa ko ke kanki kin san yana jan kankali, suturar jikinki ko diyarki ce ta cikinki za ta shugo dakin sai kin ɗan gyara, ta ya ba za ki mallake zuciyata ba?
.
6) 'Ya'yana da kika haifa da wanda wasu suka haifa min duk kin mayar da su 'ya'yanki na cikinki, kin ba su tarbiyya ta ƙwarai don gyaran sunan gidan da ke kanki gaba daya, ba ki taba rarrabe cewa waɗannan ke kika haifa ba a baki bare ki raba abincinsu ko suturarsu ko tarbiyarsu, duk abin da za su yi tare suke yi, hatta maganganunsu kina lura da irin furucin da suke yi, kin ƙi ba su damar kishi ya shiga tsakaninsu bare wani ya ware daya daga cikinsu da tunanin cewa ɗan dakinsu ne ko ɗan wani daki, kin yi ƙoƙarin hada kansu tun suna ƙanana, ta yadda kowa zai yi wani abu gidan gaba dayansa yake kallo, kowa a cikinsu yana ƙaunar ɗan uwansa ba tare da jin cewa a dakinsu yake ko a wani ɗaki ba, duk wannan kina yi ne don kin sani cewa wajibinki ne da ya zama dole ki kiyaye ba don mijinki ya yaba miki ko don jama'a su ce kin yi ƙoƙari ba, shi ya sa ma yaran ko kadan ba su san cewa ke ce mahaifiyarsu ko ba ke ce ba, in mahaifiyarsu na tare da su duk daya suke ji, in ma ba tanan ko an hure musu kunne sun san abin da yake wakana.
.
Wannan ba ƙaramin aiki ba ne, kin ga in kika yi tsammanin jikinki kawai namiji yake buƙata kin zubar da ƙimarki, kina da abubuwa da dama waɗanda ba za su samu ba sai a wurinki, in ma rasuwa kika yi zai dade bai manta ki ba, kwanannan ba a jima ba wani mutum da ya rasa matarsa na je yi masa ta'aziyya, a maganganunsa na ce a zuciyata "Anya wannan mutumin ba zai bi ta ba kuwa?" Don wasu matan da dama ba sa iya tsawon rai bayan rasuwar maigidan da suka ƙwallafa rai a kansa. Na san matan da suka bi mazansu da 'yan kwanaki kaɗan. Akwai ma wata da yanzu take gidan mijin, uwayenta sun yi faɗa har sun gaji ta ce ba za ta yi aure ba sai ta aurar da duk 'ya'yanta maza da mata, ta dena fita waje gaba dayanta in ba wasu sha'anunnuka na addini ba, madalla da matar da ta san ƙimar namiji, ta san cikakken abin da ake kira aure, Hajiya don waɗannan na auro ki ba don jima'i kadai ko zama a gida ba.

Post a Comment

0 Comments