Sakkwato Ce Tushen “Hausa” In Ji Narambad’a: Laluben gudunmuwar mawak’a a kan asalin Bahaushe da harshensa

 Amsoshi

Daga


 


Aliyu Muhammad Bunza


Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,


Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina


Waya: 0803 431 6508 K’ibd’au: mabunza @yahoo.com


 


 


Takardar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani a Tsangayar Fasahar ‘Dan’adam Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina a babban d’akin taron Tsangayar Fasahar ‘Dan’adam, k’ark’ashin Jagorancin shugaban Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Dr. Atiku Ahmad Dumfawa, ranar Alhamis 05/05/2011 da k’arfe goma na safe


 


 

TSAKURE


 

Irin matsayin harshen Hausa da Hausawa a duniya ya kyautu a ce, an kakka’be buzun karatun binciken tarihin asalinsu da harshensu tuni. Matsalolin da suka yi wa binciken asalin Bahaushe tarnak’i sun had’a da; shigan sharo ba shanu da wasu masana fannoni ke yi wa karatun. Haka kuma, k’arancin masu bincike, da kasa daidaita akalar bincike, da k’in aminta a yi taron dangi ga abin da ake bincike cikas ne babba. Babbar matsala duk ba ta fi saki zari kama tozon da aka sha yi wajen assasa tushen bincike ba. Ga maciji ana gani a dinga biyar shayinsa da sanda wai don nuna k’warewa, a k’arshe, ya tsere, a yi ‘batan ‘bak’atantan. Wannan takarda ta himmatu ga tauraro d’aya Ibrahim Maidangwale Abdulk’adir (Narambad’a) ga irin gudunmuwarsa a wannan fagen. An tsinto d’iyan wak’ok’insa ashirin da hud’u (24) daga cikin shahararrun wak’ok’insa goma (10) da ya yi da kansa da muryar bakinsa domin kwakkwahe hujjojin nazari. An gayyato shahararrun mawak’a biyar (5) a fannonin wak’ok’in sarauta, sana’a, maza, sha’awa, yak’i, da suka raka shi a fahinta. An yi amfani da d’iyan wak’ok’insu tara (9) domin a daddage hukuncinsa. An d’auraye hujjojin da tulu bakwai, aka rataye sakamakon a itace biyu nagartattu domin manazarta su harare su sosai. Makad’a Narambad’a sun ga jiya, sun ga yau, gobe ba ta zaunuwa lafiya idan aka yi watsi da batunsu. Narambad’a ya yarda da cewa, mawak’in fadar Fulani (Torankawa) ne amma mazauna k’asar Hausa. Don haka ya yanke hukuncin Sakkwato ce k’asar Hausa, wanda duk ke cikinta da bazar Bahaushe yake rawa. Bahaushen da duk ke wajenta cibiyarsa na Sakkwato in an bi diddign tarihi.Gabatarwa:


Manazarta da masana da dama sun yi bayanai muhimmai na fayyace asalin Hausawa da harshensu da al’adunsu. Asalin Hausawa da harshen Hausa ya samu kyakkyawar gudunmuwa daga bakunan masana ‘yan k’asa da na waje. Muhawarori da sa-in-sa da tak’addama a kan wane ne Bahaushe? Ina ya fito? Yaya harshensa da al’adunsa suke? An sha yin su a tarukan k’ara wa juna sani da gidajen rediyo da telebijin na cikin k’asa da waje musamman gidan rediyon BBC, VOA, Radio Kaduna da kafofin yad’a labarai na janhuriyyar Nijer da Ghana. Wad’annan abubuwan duk sun tiamaka wa karatu da masu neman karatu a kan yadda ya kyautu a tunkari biyar diddidin asalin Bahaushe. Da gangan na za’bi tauraro d’aya domin mu kalli yadda ya kalli ‘Hausa’, ‘Bahaushe’, da ‘K’asar Hausa’. Na za’bi in karkata akalar nazarina kan zantukan malamin wak’a Ibrahim Maidangwale Abdulk’adir (Narambad’a) domin cancantarsa a wannan bagiren.

Wane ne Narambad’a?


Narambad’a mutumin k’asar Isa ne da aka haifa a garin Tubali. Ya rayu bayan jihadin k’arni na goma sha tara. Ya rayu gabanin mulkin mallaka. Allah Ya k’addare shi da ganin bayana. Turawa da shimfid’a mulkinsu har ya zuwa jamhuriyya ta farko a Nijeriya. Bai gaji wak’a ba wajen uba ga uwa ya gaji wak’a. Kid’in kokuwa ya fara daga nan ya shiga kid’in noma da likafa ta ci gaba ya shiga kid’in sarauta. Babban uban gidansa da ya yi wa bakandamiya shi ne Sarkin Gobir Amadu Bawa, kuma shi ne sarkin Gobir na k’arshe da ya yi wa wak’a. Wannan d’an tsakuren nuni ne kawai da ba da haske kan cewa, tauraronmu ya cancanci a saurare shi. Domin samun cikakken bayanin Narambad’a a dubi, Gusau, 1988, Furniss, 1996, Bunza, 2009, Yaro Sodangi 1979, Mazawaje, 1985.

 

https://www.amsoshi.com/2017/11/06/noma-igiya-madura-kaya-yi-ba-da-kai-ba-su-watse/

Bagiren Nazari:


Burina a wannan takarda shi ne, tabbatar da zancen Bahaushe da ke cewa, da tsohon zuma ake magani. Hak’ik’a gaskiyar Bahaushe da yake cewa, komi zafin Larba tana barin Talata ta wuce. Na hangi malamanmu da magabatanmu da wasu daga cikin takwarorinmu suna yi wa tarihin asalin Bahaushe kwasan karan mahankaciya. Da haka sai karan ya yi yawa a kasa d’aukarsa a ka, a rasa mai taimaka maka ka d’ora a ka, da k’arshe sai a bar kowa da kayansa babu mai taya wani d’auka. Idan bincike ya kasance an bar kowa da ra’ayinsa abin nema bai samu ba. Kyawon bincike shi ne, a taru, a had’u wuri d’aya a rairaye ra’ayoyi da hasashe-hasashen kowa a samu wata magana mai kauri da za a yi gora da ita domin dukan kan duk wani mai ra’ayin a ware kowa ya bi hanyarsa. Daga cikin abubuwan da na gani na cikas garemu mu d’aliban Hausa da tarihi su ne:

 1. Rashin tsayar da daidaitacciyar magana a kan cewa, ina ne k’asar Hausa take?

 2. Rashin tantance wurin da Bahaushe ya fito ko ya tsira da yadda ya samu kansa a yau. • Kasawarmu ta fito da wasu matakan bincike na k’wararru da za a bari masana su bi har sai sun kai ga sin-wau-raa-takuri su ba mu bayani. 1. Rashin ke’be darasi na musamman a kowane matakin digiri (1-3) da zai himmatu ga biyar diddigin tarihin Bahaushe, asalinsa da al’adunsa.

 2. Babban kurenmu shi ne, sake wa masana tarihin akalar binciken asalin Bahaushe mu tsura musu ido muna jiran sakamako. Rashin sani ya sa karen gwauro ya kori bazaura, su kansu masana tarihi da bazar masana al’ada da adabi da harshen Bahaushe suke rawa. A k’arshe, aka yi haihuwar guzuma, d’a kwance, uwa kwance.


 

 1. Kasawarmu ta rashin kiran gagarumin taro na musamman a kan asalin Hausawa da harshensu ba k’aramin kure ba ne. Lallai sai an kira taron masana Hausa a yi wankin d’ankanoma mashaya, kana a nemi gudunmuwar masana na fannoni daban-daban domin a kakka’be buzun karatu.


Idan muka dubi wad’annan abubuwa shida da idon nazari, za mu ga cewa, masana da malamai da d’aliban Hausa ba su da wani muhimmin abu a gabansu face na tantance tarihin Bahaushe sahihi tare da fayyace tantagayyar asalin harshensa. Duk wani digiri, da babban digiri, da rawanin Farfesa, da za a nad’a wa wani d’alibi ko malamin Hausa a yau, Hausa da Hausawa na bin sa bashi idan bai ba da gudunmuwarsa a wannan fanni ba. Abubuwan da suka mamaye littattafan nazari da kundayen binciken k’anana da manyan digiri da tarkardun shimfid’a buzun karatu na wasu fitattun masana a kan asalin Bahaushe da harshensa cike suke da tarihihi da tatsuniya da jita-jita hadisin Bamaguje. Tunkararsu gaba d’aya a takarda d’aya ko littafi d’aya ba zai yi wu ba, don haka na ga ya kyautu in d’an tsakuro kad’an da fatar k’iliu ta tono balau. A tak’aice, nazarce-nazarcen da suka gabace mu za a ga sun karkata zuwa ga:

 1. Tarihihin Bayajida da asalin Daura.

 2. Kwararowar bak’i daga gabas da samuwar Bahaushe da k’asar Hausa. • Matsalolin Habasha da Misra da Sudan a kan ginuwar k’asar Hausa. 1. Rigingimun tantance daidaitacciyar Hausa tsakanin Kano da Sakkwato da Zazzau da Katsina da Saharar Nijar.

 2. K’ok’arce-k’ok’arce tantance addinin Bahaushe da al’adunsa na asali da wad’anda ya aro da wad’anda aka ara daga gare shi.

 3. Tarihihin Hausa Bakwai da Banza Bakwai ya dad’a dagula al’amarin aka bar Bahaushe cikin k’ila-wa-k’ala.


Hangen wad’annan abubuwa bakwai suka ba ni k’arfin gwiwan tunkarar wani gwarzo daga cikin gwarajen k’asar Hausa, domin in isar da sak’onsa da irin gudunmuwarsa tun gabanin rikice-rikicen da masana suka shiga a yau na tantance ina ne k’asar Hausa. Gabanin yin haka, ya kyauttu mu d’an yi waiwayen fitattun masanan da suka yi rawar gani a wannan bagire.

Waiwaye:


Ban ga laifin magabata da suka yi binciken asalin Bahaushe da harshensa ba, sai dai ina son in yi ya’bi ne a kan katangarsu. Bayan na yi ya’bi, in bud’a wata k’ofa mafi kusa ga a kai ga buk’ata mu jarraba ta mu gani. Da na yi waiwayen ayyukan magabata na hangi akwai cikas a wasu wurare da ya kyautu a agaza musu. Daga cikin masanan da suka yi fice a bincike-bincken asalin Hausawa akwai: M.G Smith da Murray, Last, da Hisket, da Abdullahi Smith da Lange da Smith da Lavers da Shea da dai sauransu. Daga cikin matsalolin da za a ci karo da su a cikin ayyukansu sun had’a da:

 1. Masana tarihi ne suna kallon abubuwan ta fannin tarihi da dogara da bincike-binciken da ya gabace su a tarihance. Wannan babban cikas ne, domin ba makami d’aya za a yi amfani da shi a irin wannan yak’i ba.

 2. Babban abin ban tausayi shi ne su ba Hausawa ba ne. Rashin kasancewarsu ba Hausawa ba, ba k’aramin cikas ba ne domin wanda ya san dad’in sure ke yi wa fadama shinge. Manufarsu a koyaushe ita ce, da sun ji abu za su rubuta shi, su d’ora shi a kan mizanin tunanninsu. Da yawa tunane-tunanensu na takin sak’a da Bahaushen tunani, su yi tsaye su mak’ala wa Bahaushe shi, bai ji ba bai gani ba. • Akwai mamaki k’warai a ga wad’annan fitattun masana ba sa jin Hausa bale karance-karancen abubuwan da aka rubuta da Hausa ko su yi nazarin adabi da harshe da al’adun Bahaushe a rubuce-rubucensu. Rashin jin Hausa, da iya rubuta ta, da iya karanta ta, wata babbar hujja ce ta sa ayar tambaya ga rubuce-rubucensu da suka shafi asalin Hausawa da harshensu. 1. Makamin farautar asalin Bahaushe na cikin harshensa da adabinsa da al’adunsa. Wad’annan abubuwa kuwa wasu masana da suka gabace su sun ce wani abu cikin Larabci da Ajamin Hausa da Zabarmanci da Azbinanci da Fulatanci. Ga alama, wad’annan wasanan ba sa jin kowane daga cikin wad’annan harsuna bale su karanci abubuwan da aka rubuta cikinsu. Don haka, k’olin hujjojinsu su ne, abubuwan da suka sani a harshen Turanci da wad’anda aka yi fassarar (ba ni bak’i in ba ka fassara) daga harshen aslai zuwa Turanci ko Faransanci. Da haka dai sakamakon bincikensu zai koma, ba ni na kashe zomo ba rataya aka ba ni.


Abdullahi Smith ya fara hango daular Bahaushe da k’asar Hausa. Wad’annan abubuwa da muka lisafa suka yi wa ayyukansa tarnak’i. M.G Smith ya wallafa shahararrun ayyuka biyar da ba irinsu ga zamaninsa (watau Daular Zazzau, Kano, Sakkwato, Daura da Katsina). A ayyukkan tarihi ne aka ba amana aka manta da gudummuwar adabi da harshe da al’ada. Hisket, ya yi abin a zo a gani cikin wak’ok’in Hausa da rubuce-rubucen ajami, sai dai rashin jin Hausa, da iya karanta ta, da rubuta ta, ya yi wa tunaninsa cikas. Murray Last, da Lange da Lavers duk wannan matsala ta ci su. Philip Shea, ya ku’buta ga jin Hausa da iya magana da ita, sai dai tarihi ya karanta ba Hausa ba, ga shi kuma ba Bahaushe ba ne bale ya san adabin Hausa yadda ya kamata.

Ayyukan masana da suka ku’buta ga wannan tarnak’in sun had’a da Mahdi Adamu, Garba Nadama, Abdullahi Rafi Augi, Bala Usman, Hambali Jinju da sauran d’alibansu. Ayyukansu suna hararar fannonin da suka k’ware ne kawai kuma wasunsu ba su yi wa adabin Hausa da al’adun Bahaushe karatun Fatiha ba. Da dai sun sami wani wuri d’aya sun la’be su tusa shi gaba suna daddaga da basirar fannoninsu da yanzu su ya kai gurbi ga tantance asalin Bahaushe da harshensa. Da wannan zan ce, ga d’an abin da na hango a cikin wak’ok’in Narambad’a:

K’asar Hausa:


Babu mai musanta kasancewar Bahaushe mutum daga cikin mutanen da ke rayuwa a bangon duniya. Wasu masana na hasashen k’aura Hausawa suka yi daga wani wuri suka zo k’asar da suke a yau. Wasu na ganin a nan k’asar da suke aka halacce su. Ga iyakan bangon k’asar Hausa in ji makad’a Narambad’a:

Jagora  :Ai dag ga Kaduna har Gusau k’arewar Hausa,

Yara     :Kowace shawara ta labarin Turawa

:Amadu ba a yin sa sai ya sa hannunai,

:Zamakin k’ok’ari garai ga sanin hujjoji.

Gindi          :Gwarzon shamaki na Malam toron giwa,

:Baban Dodo ba a tammai da batun banza,

 

A ganin Narambad’a, iyakan k’asar Hausa ya k’are daga Zamfara a babban birninsu “Gusau”. An samu ka-ce-na-ce da yawa a kan wannan d’an wak’a na Narambad’a. Daga cikin abubuwan hasashe a wannan d’an wak’a akwai:

 1. i) Daga Gusau zuwa Kaduna ne k’asar Hausa?

 2. ii) Daga Sakkwato zuwa Gusau ne k’asar Hausa?


Hasashe na biyu shi ne ya fi daidaituwa da ra’ayin Narambad’a. A ganin makad’a Narambad’a da’irar k’asar Hausa daga Zamfara (Gusau) ne zuwa Sakkwato. Tun gabanin haihuwar Narambad’a da bayan haihuwarsa haka nan ake kiran farfajiyar k’asar duka da suna “Hausa” ba k’asar “Hausa” ba. Watak’ila sauran daulolin k’asar Hausa duk haka nan ake kiransu gaya ba tare da sa kalmar “k’asa” ba, kamar a ce: Katsina, Zazzau, Zamfara, Kabi, Gobir da dai sauransu.

Farfajiyar K’asar Hausa:


Idan aka ce “Hausa” Sakkwato za a zo in ji Narambad’a. Idan aka ce iyakokin cibiyar k’asar Hausa Narambad’a cewa ya yi:

Jagora         :An gamu Hausa kulluhun jama’a duk an zo

:Kamfunnan ga arba’in da bakwai duk sun zo

:Kowane kamfani shi na tsaye bakin garka,

Yara:           Maiduka yah hito da shi da su Gatau

:Amadu duk magana wadda kay yi

:An ka ji daidai kay yi

:Tun ran nan Amiru yak’ k’ara ma girma,

:Kuma ran nan Waziri yak’ k’ara ma girma

:Amadu bai hito ga dattijon banza ba.

Gindi :         Gwarzon shamaki na Malam toron giwa

:Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

Kalmar “Hausa” a nan tana nufin “birnin Sakkwato” kai tsaye. Zancen da ya yi na kamfuna arba’in da bakwai yana nufin gundumomi (Districts) arba’in da bakwai (47) na jahar Sakkwato da Kabi. Kabi ta k’unshi Argungu da Gwandu da Yawuri da Zuru. Sakkwato da Zamfara kuwa kamar yadda suke a da. A tarihi ba a ci Yawuri da Zuru da yak’i ba k’asashe ne ko Dauloli masu zaman kansu. Zamansu k’ark’ashin Sakkwato ba ya rasa nasaba da kariya ta yak’i bayan k’are jihadi.

A nan, Narambad’a ya k’ara fad’ad’a yawan iyakokin Hausa wanda ya had’a da gundumomi (47) da ke k’ark’ashin Sakkwato. Abin kulawa a nan shi ne, mutanen k’asar Yawuri da Zuru, idan za su je Birnin Kabi ko Sakkwato sukan ce, za mu je “Hausa”. Ba su cewa, za mu je “k’asar Hausa ba” sai dai za mu je “Hausa”. Yanzu haka, akwai wani zana da suke yi mai kauri su gewaye gidajensu da shi, a Zuru da Yawuri duk sunansa “Ba-ka-zuwa-Hausa”. Makad’a ya k’ara yi wa maganarsa daddage a wani d’an wak’a da yake cewa:

 

Jagora:        Na tuna wata shekara

:Da an ka yi taro Hausa

Yara:           Kamfunan ga arba’in da bakwai duk sun zo

:Ni ba ya ga Isa ban ji labarin kowa ba.

Gindi:           Gwarzon shamaki na Malam toron giwa

:Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

Wani taro na da gundumomi arba’in da bakwai da aka yi na Daular Sakkwato, ya ambace shi da cewa: “an ka yi taro Hausa”. Abin nufi, an ka yi taro a Sakkwato. Ya k’i ya ambace ta da sunanta Sakkwato ya ce “Hausa” sunan da aka fi saninta da shi a tarihance. Wannan ya nuna gabanin a nad’a wa Sakkwato sunan Sakkwato “Hausa”ake ce wa farfajiyar k’asar duka. A taron, Narambad’a yake cewa, bayan labarin gundumar Isa bai ji wata gunduma da ta yi fice ba.

Mutanen K’asar Hausa:


Makad’an bai manta da yawan mutane su ne kasuwa ba. Don haka, a cikin wak’ok’insa akan yi tsintuwar dami a kala na tantance mutanen da ke k’asar Hausa. A cikin wani habaici da yake yi wa magabtan Sarkin Gobir Amadu yana cewa:

Jagora         : Yau mai ashararu ya kad’e

:Dunya ta yi mai hwashi

: Babu zama garai

:Zama fitina yar tayas

Yara            :Ya san ba a k’warijini

:Ga mutanen Hausa

:Kowac ce shina iyawa

:Ga fili nan

:Sai ya k’etare gidanai

:Ba ban kwana

Gindi:           Gwarzon shamaki na Malam toron giwa

:Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

A nan, ana magana ne kan magabtan sarkin Gobir na Isa aka nuna ba a nuna iyawa “k’warjini” ga mutanen Hausa. Hasashen Narambad’a a nan shi ne, Amadu Batoranke (Fulani) ne, amma mutanen k’asarsa Hausawa ne. Don haka, mutanen k’asar Isa, Gobirawansu da Zamfarawansu Hausawa ne, kuma mutanen Hausa aka ce musu. Domin k’ara tabbatar da wannan da’awa yana cewa:

Jagora         :Uban Malami ka kai

:Wurin da Ibrahim duk yak kai,

:Zamakin an kira shi

:Sarkin Gobir Hausa

:Kai ko an kira ka

:Sarkin Gobir Hausa

Gindi           :Gwarzon shamaki na Malam toron giwa

:Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

A kaikaice, Narambad’a na gaya muna gabanin jihadi k’asar Isa da Gobir Hausa ake kiransu. Ana kira kakansa Ibrahim Sarkin Gobir na Hausa, shi ko an kira shi Sarkin Gobir na Hausa. Da sarkin Gobir na Sabon Birni da Sarkin Gobir na Isa sarakunan Hausawa ne mutanen da suke sarauta Hausawa ne, sunan k’asar, “Hausa”.

Harshen Mutanen Hausa:


‘Dan’adam na da ‘yanci sa k’afarsa duk wurin da ya so ya rayu. Duk da haka, idan aka samu cinkoson mutanen da suka mamaye wuri da yawansu da al’adunsu da harshensu ya zama na d’aya bisa ga sauran k’abilun da ke zaune da su. Ga tsarin adalcin zamantakewa su za su kar’bi jagorancin siyasar k’asar ta fuskar tattalin arzikinta da tsaronta. Mutanen da ke zaune a farfajiyar da Narambad’a ya kira “Hausa” wurare daban-daban a wak’ok’insa su ne Hausawa, sunan harshensu “Hausa” don haka suke da mawak’a Hausawa kamar yadda ya tabbatar da cewa:

Jagora          :Amadu bana Hausa ka yi rinjaya ni na yi

:In an ce Isa ba ka jin an ce wani sarki

:Ni ko duk Hausa ba ka jin wak’a bayan tau.

Gindi:           Gwarzon shamaki na Malam toron giwa

:Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

Da harshen Hausa Narambad’a yake rera wak’a, mawak’in k’asar Hausa ne na basarake Batoranke (Bafulatani). Ga dukkanin hasashe ‘Hausa’ a nan yana nufin Daular Sakkwato, wanda yake ganin ita ce “Hausa”. Narambad’a bisa hanya yake domin bayan rusa daulolin k’asar Hausa na Gobir, Zamfara da Kabi da Katsina da Kano da Gimbana da dai sauransu sai aka kafa sabuwar daula ta masu jihadi duk da haka k’asar ba ta sauya suna ba tana nan zamanta “Hausa” tattare da sanin Fulani suka mamaye gurabun sarautar Hausawa. Komai k’asaitar sarautar Bafulatani ko Batoranke, dole ya aminta, k’asar wasu suka kafa ta gabaninsa, kuma sunansu ya mamaye sunan kowane irin mai mulki da zai mulke ta. Narambad’a ya tabbatar da haka a gindin wak’ar da ya yi wa Amadu yana cewa:

Gidin :         Gogarman Tudu jikan Sanda

:Maza su ji tsoron d’an mai “Hausa”.

 

Ana son a nuna dole maza su ji tsoron sarkin Amadu domin d’an Sarkin Musulmi ne, shi ko sarkin Musulmi shi ne mai k’asar Hausa. Ai Narambad’a ya furta wani d’an wak’a da zai fayyace wannan gindi kamar haka:

Yara: Sun san Garba d’an Hasan

: Shi yah hau gadon Hassan

:Shi as shugabansu

:Kai ab babban d’anai

: Komi kay yi ba a cewa ba daidai ba

:Nasabas Shehu ba ta d’ai

:Da ta kakan kowa.

Gindi: Gwarzon shamaki na Malam toron giwa

:Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

Garba d’an Hassan a nan, shi ne, Sarkin Musulmi Abubakar III. Hassan shi ne sarkin Musulmi Hassan d’an Mu’azu, wanda Abubakar III ya gada (mahaifinsa). Wad’annan d’iyan wak’ar tagwaye ne, na biyun na k’ara tabbatar da na d’aya. “‘Dan mai Hausa” na nufin d’an Sarkin Musulmi domin shi ne sabon Sarkin k’asar Hausa bayan da aka ci Hausawa da jihadi. Hausa a nan, tana nufin Sakkwato, don haka muke hasashen tushen Hausawa Sakkwato. Harshen da Sakkwatawa ke magana da shi, shi ne Hausa da kare-karen harsunan da ya haifar.

Cibiyar Hausa:


Ba ni musun zaman Kano Jalla babbar Hausa kamar yadda Kanawa ke yi mata kirari. Buk’atata a nan shi ne, in d’an binciko ko Narambad’a na da wannan labari? In ba ya da labarin wane labari yake da shi game da Kano? Zancen da Narambad’a zai fad’a ba zai zama wata tabbatacciyar hujja ba ga mai bincike. Duk da haka, wata babbar fitila ce mai dogon haske ga mai son yin magartaccen bincike. Narambad’a cewa ya yi:

Jagora:Da Kano sa Kaduna sa Jos

:Su duk wad’anga

:Babbar aiki Hausa

Yara  :Kul dotti’be sun had’e

:Kowace shawara a kai

:Sai ya sa hannu

:Sai ka ji dariya ana ta hwad’a daidai

Gindi :Kai bajinin Namoda

:Gagara Gago na zagi.

:Iya gaba na Rwahi

:Baban Yarin K’aura.

 

A zamanin da Narambad’a ke wak’a, Kaduna da Jos da Kano da Sakkwato su ne duniyar Nijeriya ta Arewa. To, makad’a ya nuna da Kano da Kaduna da Jos manya ne amma babbar cibiya tana “Hausa”. A fad’arsa ya ce:

Jagora: Su duk wad’anga

:Babbar aiki Hausa”.

 

A fahintarsa Hausa ce cibiyarsu, Hausa kuwa a wajensa ita ce “Sakkwato” ko cibiyar da masarautar Sakkwato take da fadar mulkinta.

Ina Ne Hausawan Suke?


Makad’a Narambad’a bai k’uk’unta bayaninsa ga birnin Sakkwato na yau ba, a kan amfanin da yake yi da kalmar “Hausa”. Yana sane da kyau cewa, Hausawa ‘yan dangi ne, kuma sun kasu dangi-dangi, zuriya-zuriya wanda shi ne  musabbabin kasuwarsu daula-daula. A ko’ina aka samun wata zuriya ta Bahaushe Hausawa ne, in sun yi k’asa tasu ce, amma ‘Hausa’ na nan wurin da take “Sakwkato”. Ga d’an misali:

https://www.amsoshi.com/2017/06/29/kutsen-zamani-cikin-makadan-fada-5/

 

Zazzau:

Narambad’a ya yi wa fadar Zazzau wak’a sosai amma bai ta’ba kiranta Hausa ba ya kuma san tana cikin k’asar Hausa domin da Hausa ya yi wa masarautarta wak’a. Dubi yadda yake cewa:

Jagora:Sardaunan Kaduna ya yi jawabi

:Duk ga Zage-zagi zaune

:Yac ce ku bar hushi da danginku,

:Sarauta tana ga Allah

:Kun ga gidan Alu gidan sarauta na,

:Gidan Yaro gidan sarauta na

Yara: Shi wannan da kun ka so a nad’a

:Allah bai yi mai sarauta ba.

Gindi:Mijin Nana Yelwa d’an sanda

:Gulbi ka wuce kwalhewa.

 

Narambad’a ya ambaci wata zuriya daga cikin zuriyar Bahaushe Zage-zagi a wak’ar yana cewa:

Jagora:Jikan Shehu mai k’asar Zazzau

Yara: Gogarman Makama d’an Kwasau

 

A gindin wata wak’ar masarautar Zazzau cewa yake yi:

 

Gindi:Gaskiya to yi halinta

:Sai mu koma Zazzau

:Mui ta kid’an murna

:Ga Muhammada ya zan sarki.

 

Ya tabbatar da kasancewar Zazzau k’asa daga cikin k’asashen Hausa amma bai kira ta Hausa ba. Domin a ganinsa cibiyar Hausa na Sakkwato.

Katsina:

Narambad’a ya san Katsina da fadarta sosai domin ya yi wa sarki ‘Dankulodo na Marad’i wak’a. Haka kuma, an neme shi da ya je Katsina ya yi wak’a har yake neman iznin Uban gidansa da cewa:

Jagora:Bisa yarda na Garba

:In ya sa min hannu

Yara: Bana yawo nikai

:Zaman dangina sun yi

Jagora:Katsinawa suna bid’a ta

:Ban je can ba

Yara: Dan nan in yi Buza

:In zarce Madawa.

Gindi:Gwarzon shamaki na Malam toron giwa

:Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

Ya ambaci Katsina da zuriyarta duka wato “Katsinawa”, ya kuma yi wa sarkin Katsina Marad’i Dankulodo wak’a amma bai ambace su da sunan “Hausa” ba.

Zamfara:

Makad’a cikin k’asar Zamfara yake amma bai ce mata Hausa ba. Ya ambace ta da sunan da aka taras na tarihinta. A nan cewa ya yi:

Jagora:Zamfara ba makad’in da ka ja mini

Yara  :Baya ga Jankid’i

:Sai ko ‘Dandawo

:Sai d’an Dodo Alu mai taushi

:Amma ba makad’in gayya ba

Gindi:Gogarman Tudu jihan Sanda

:Maza su ji tsoron d’an mai Hausa.

 

Narambad’a ya za’bi wasu fitattun k’asashen Zamfara ya yi wa sarakunansu wak’a. Haka kuma, a cikin bakandamiya ya yi wani darzaje na nuna sanin Zamfara da Zamfarawa kamar haka:

Jagora:Moriki K’aura da Zurmi

:Dut maganar ta zan d’ai

Yara  :Bungud’u sa Gusau,

:Kwatarkashi ga ‘Yandoto

-        -        -        -        -

Gindi:Gwarzon shamaki na Malam toron giwa

:Babban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

Dukkanin zuriyar Zamfara da za a iya lisafawa masu magana da harshen Hausa za a same su a nan, watau: Moriki da K’aura da Zurmi da Bungud’u da Gusau da Kwatarkashi da Tsafe (garin ‘Yandoto). Makad’a bai ta’ba ambatunsu da sunan “Hausa” ba, duk da kasancewarsu Hausawa masu magana da harshen Hausa da al’adu na Hausawa.

‘Daurayar Zantukan Narambad’a:


Narambad’a ya tabbatar da cewa, ba a samun harshe ba tare da samun masu magana da shi ba. Haka kuma, samun cunkason masu harshe wuri d’aya ya tababtar da samuwar k’asar da suka rayu wadda za a ce ita ce k’asarsu. A ganin Narambad’a, idan wasu mazauna suka zauna k’asar, suka shimfid’a mulkinsu, suka kafa daula, ta zama k’asarsu. Narambad’a na ba mu labarin cewa, duk da kasancewar an ci Hausawa da yak’in jihadi k’asarsu tana nan tare da sunansu da sarautu irin nasu kamar dai yadda yake ce wa sarki Amadu:

Jagora:Gawurtacce na Magajin Rafin Hausa.

Gindi:Gwarzon shamaki na malam Doron giwa,

:Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

A ganin Narambad’a, kowace sarauta aka nad’a k’asar Hausa, kowane irin aiki ake yi cikinta tana nan da sunan “Hausa” daidai yadda yake ce wa wani ma’aikacin hukuma:

Jagora:Malam Jelani malamin shanu

:Ya yi k’ok’ari

Yara: Na ji ana hwad’in

:Irin aikinai Hausa.

Gindi:Gwarzon shamaki na malam toron giwa

:Baban dodo ba a tamma da batun banza.

 

Haka kuma, a wak’ar da ya yi wa Alk’alin Alk’alai ya k’ara tabbatar da bayanan da ya sha yi da cewa:

Jagora         :Alk’alin Alk’alai na Hausa

Yara            :Ko wai kaura da kai

:Kana turmuje shi.

Gindi          :Alk’ali shiri nai da kyawo

: Shi yai zaune daidai wa daidai.

 

A da, idan aka ba ma’aikaci muk’ami a Lardin Sakkwato (wadda ta had’a da Kabi da Zamfara). Za a ce shi ne, wane a Hausa. Yadda Narambad’a ya ambaci Alk’alin Alk’alai na Hausa, haka kowane muk’ami ke tafiya. Muk’aman da ke wajen Lardin Sakkwato kamar Kano da Zazzau da Katsina ba a kiran su yadda aka kira a Sakkwato wato “Hausa”.

Gudammuwar da makad’a Narambad’a ya ba mu ita ce:

 • K’asar Hausa d’aya ce wadda ke da cibiya Sakkwato.

 • Idan an ce Hausa Sakkwato ake nufi daga cikin garuruwan Hausawa.

 • Ba birnin Sakkwato ne Hausa ba, fad’in gundumar duka shi ne Hausa.

 • Babu wata gunduma da ake ce wa Hausa bayan ita a duniya.

 • Sarakunan daular Sakkwato sarakunan k’asar Hausa ake ce musu, bayan su babu sarakunan da ake kira haka a zamaninsu. Me ya sa haka?

 • Wanda duk ke rik’e da cibiyar Daular Sakkwato a ko’ina aka sauya ta, shi ne mai Hausa. K’asarsa ita ce Hausa. Mutanenta su ne mutanen Hausa.

 • Duk zuriyoyin Bahaushe da suka kafa daulolinsu wajen Hausa, Hausawa ne amma tushensu na Hausa a farfajiyar Sakkwato.


Taron Dangi:

Na za’bi ni yi amfani da Ibrahim Narambad’a domin fito da irin tsintuwar dami kala da za a iya yi a cikin adabinmu a kan tarihin asalinmu. Babu wai, da za a bi diddigin fitattun tsofafin mawak’a da yawa, za a samu abin cewa a kan asalin Hausawa da wane ne Bahaushe? Takwarorin Narambad’a da yawa sun ba da irin gudunmuwar da ya bayar a kaikaice.

Aliyu ‘Dandawo:

Yana daga cikin shahararrun mawak’an sarauta na k’asar Hausa. Ya yi wa fadar Shuni wak’a da fadar Sakkwato da fadar Isa da fadar Augi da fadar Argungu da fadar Zabarkana ta Nijar (daular Shonghai) a k’arshe ya k’are a fadar Yawuri ga gindin bakandamiyarsa ta sarki Abdullahi:

Gindi: Mai Yawuri bangon duniya

:         Abdullahi sadaukin maza

:         Allah Ya yi ma d’aukakar

:         Da kowa ba shi da ita Hausa dut.

 

A halin da yake wak’ar, mawak’in daular Yawuri ne. Da masarautar Sakkwato ta sa a kore shi, ya bar k’asar ya koma daular Kabi. Daga nan aka sa masarautar ta kore shi. Wannan ne dalilin k’arshen zamansa Yauri. “Hausa” a nan yana nufi Sakkwato da gundumominta. Ai fadar Sakkwato ba ta yi na’am da wak’ar ba. Aliyu ‘Dandawo fahintarsa a kan k’asar Hausa ya yi canjaras da Narambad’a ka ce dai game baki suka yi. Dalilin wannan shi ne, a zamanin da suka rayu da wanda ya gabace ce su, da an ce “Hausa” Sakkwato ake nufi kai tsaye.

‘Dan’anace:

Bari in had’a ku da makad’a Dan’anace mutumin Gandi ta Sakkwato da yake yi wa Shagon Mafara wak’a na ‘Yarkahoji ta k’asar Zamfara. Bayan da ya yi yawo da Shago ko’ina aka rasa mazan da za su fito a yi adashin k’ulli yana cewa:

Jagora       :Na koma Kano da ‘yar gangata

:Ban dai iske kai kad’ai gayya ba

:An ce Hausa na da runjin dambe

:(Bakandamiyar shago)

 

Da ya zo ambaton Sakkwato cewa ya yi, “an ce Hausa”, duk da k’asancewarsa Basakkwace yana yi wa Bazamfare wak’a ya ambaci Sakwato da sunan Hausa amma bai ambaci Kano da Katsina da sunan ba domin cewa ya yi:

Jagora       :An ce Katsinan Dikko

:Na da manyan fama.

 

Da ‘Dan’anace na ambaton mazajen da ke iya dambe da Shago ya tuna da wani goga mutumin k’asar Sakkwato ga abin da makad’a ya ce:

Jagora:        Sai ko Yari wanda ab bisa Hausa,

 

Marigayi Bawa ‘Dan’anace ya kwakkwahe jawabinsa na cewa, Lardin Sakkwato ne “Hausa” a cikin wak’ar Nadelu da yake cewa:

Jagora         :’Yan makad’a ku na nan arewa,

:Masu lak’a d’an abin kid’i

:’Yan wak’ok’i k’ire-k’ire

:Makid’a ku dai ka hassadanmu.

:To mu dai ba mu hassadakku.

:Hwad’a musu ko sun yi hassadanmu

:Ga banza an nan

:Makid’a sai dai ku dangana

:Wani mai roko ba a....

Yara            :Ba a sake mai da kamata Hausa,

Gindi          :Kai maza suka shakku ko can

:Kiro Nadelu kutunkun ‘bauna.

 

Cikin salon bugun gaban wannan d’an wak’a ‘Dan’anace ya nuna ba za a sake samun kamarsa a k’asar Hausa ba, wato Sakkwato.

Muhammadu Gambo:

Muhammadu Gambo ya k’ara wa Borno dawaki domin ya tabbatar mana da cewa duk k’asar da ke k’ark’ashin mulki ko sarautar Sakkwato Hausa ake ce mata. Gambo Bagimbane ne mutumin Fagada ta k’asar Jega rik’on Gwandu amma ya ce:

Jagora       :An d’au na maraye an mik’a min

:Abin mabaraci an mik’a min,

:Mun ci na Alk’ali uzurce

:Mun canye na malam mai karatu

:Balenta na boka d’an gaton uwa

:Bale mai kud’d’i bawanmu wannan,

:Mun canye na limami la’bin nan

:Gambo ga ni da raina lahiya Hausa

:Ban ta’ba ko ciwon ido ba,

:Komi adadinai na tahowa

:Gambo da sauran gargarenai.

 

Mutumin k’asar Jega, yana zaune Jega cikin Gimbanawa, amma bai ce ga shi k’asar Gimbanawa ba sai ya ce “Hausa”. Gaskiyar Gambo, idan mutumin Zuru zai je Birnin Kabi ko Jega, cewa yake yi, zai je “Hausa”.

Garba Maitandu Shinkafi:

Marigayi Garba Maitandu Shinkafi da kunama ta yi masa halinta ya wak’e ta. Maitandu mutumin Shinkafi ne amma ga irin sunayen wuraren da ya lisafo na ma’boyar kunama:

Jagora        :Marad’awa na hwad’in

:Ga tankan d’aki tare

:Hillani na hwad’in

:Cikin d’an rame tare

:Kanawa na hwad’in

:A gindin dutse take

Yara:         Su ko ‘yan Hausa

:Suka ka ce ga ciyawa take

:Buzu ya ce Galif talif a bakakamba

:Ko’ina dai dakinta ne.

Gindi:                Kunama zan wa kid’i

:Zama ciwo ag gare ta

:Ta halban na fiya.

 

Maitandu ya k’ara tabbatar da hasashen Narambad’a, ya kuma k’ara ba da fatawar cewa, babban birninmu Kano ba garin Hausawa ba ne. Haka kuma, da an ce, Hausa ko ‘yan Hausa a fad’ar Maitandu Sakkwatowa ake nufi da gundumominta arba’in da bakwai:

Makad’an Yak’in Kabi:

Gangunan Kabawa da suke kad’awa na bukin cin daular Sakkwato da yak’i ya isa ya yi wa zantukan wad’annan mawak’a kwakkwahe. Idan ana bukin cin Fulani da yak’i a k’asar Kabi ga sak’on da turayen Kabawa ke cewa:

Jagora:       Kabi ta ci Hausa

Makad’a:    Da mi tac ci Hausa?

Jama’a:      Da k’arhi da yaji

 

Idan Kabawan Argungu na ganin Sakkwato “Hausa”, kuma ba su da fitaccen harshe a lokacin wak’ar sai Hausa. Haka kuma, da Hausa suke isar da sak’onsu na gwazangwari (cin nasara). Wannan zai nuna muna Sakkwato ce Hausa, ita ce cibiyar Hausa, Hausawan da ke gewaye da da garin da wajen k’asarta Hausawa ne, amma tushensu Sakkwato a ko’ina suke. Kasancewarsu wajen rik’on Sakkwato ya ba su damar kafa daulolinsu da sarautunsu kamar yadda ‘Dantanoma makad’in Kabawa ke cewa:

Jagora:       Mu sarkinmu bai biyan wani sarki

:In ba Allah na ba.

:Sama in bi ka kai

:Fito bi Nasara

:In san manya kab bi

 

Ya rera wannan wak’a ga Sarkin Kabin Argungu da aka ce ya je ya tarbo sarkin Musulmi a Fak’on Sarki. Ashe gaskiyar Narambad’a da yake zargin Argungu da ta yi dabar dawaki da ta yi wa Sakkwato (Hausa) barazana yake cewa:

Jagora:       Ai wani rincimi

:Da Argungun tak kawo

:Ga dokinmu ya iso

:Su kau nasu ya iso

Yara:           Kuma ga Bubakar cikin mota ya kawo

Jagora:       Yac ce Amadun Muhammadu

Yara:         Allah Ya bar ma kowa babban d’anai

:Sarkin Gobir na Isa

:Kak ka ji tsoron komi

Gindi:                Gwarzon shamaki na malam toron giwa

:Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

Narambad’a ya k’ara tabbatar da zancen Kabawa cewa Argungu ba k’ark’ashin Hausa take ba. Tana cin gashin kanta, don haka ya kira ta Argungu.

 

 

https://www.amsoshi.com/2017/06/29/kutsen-zamani-cikin-makadan-fada-4/

Sakamakon Bincike:


Kalmar Hausa bayan ma’anar ta, ta fasaha, da azanci, da basira, a wajen Bahaushe tana da ma’anoni na daban. Mak’wabtan cibiyar Daular Sakkwato duka, kamar Zamfara da Yauri da Zuru da Kabi da Dandi suna kiran Sakkwato da gundumominta “Hausa”. Mutanen k’asar Nupe da Kwara idan sun ce, “Hausa” Sakkwato suke nufi. Mutanen k’asar Ghana da Saliyo da Togo da Benin, da Libya da Sudan, idan suka ce “Hausa”, Sakkwato suke nufi. Fitattun garuruwanmu na tarihi irin Kano da Katsina da Zariya da Gobir idan ana zancensu a rubuce-rubucen magabata na tarihi akan ambace su da sunansu ba “Hausa” ake ambato su da shi ba. Rubuce-rubucen masu jihadi duk wurin da suka ambaci “Hausa” Sakkwato da gundumominta na yanzu zai shafa. Idan za su yi magana kan fitattun biranen da na ambata sukan ambace su da sunayensu da aka san su da su ba sa ce wa “Hausa”. Hasashen Narambad’a na kiran k’asar Sakkwato Hausa, ba shege ba ne, da ubansa. Rashin kasancewarsa a rubuce bai cuta wa gaskiyar da ke ciki ba. Ba garin Sakkwato ba ne Hausa duk da kasancewarsa Hausawa suka kafa shi, masarautar dai ce “Hausa”. Ai an ce masarautar ta yi zama Wurno da Cimmaula da Sifawa gabanin a kafa birni a Sakkwato. Tun fil azal masu k’asar na asali “Hausa” suke kiran ta.

Idan dai mun tabbatar da cewa, ba Nrambad’a d’ai ke da wannan hasashe ba, takwarorinsa mawak’a na da shi. Marubuta tarihi masu ziyarce-ziyarce suna da ra’ayin. Daulolin k’asar Hausa na Hausawa sun yarda da Sakkwato ce Hausa. Masu jihadi da suka tum’buke daular Hausawa, sun yarda da Sakkwato ce Hausa, labudda a mik’a kai bori ya hau. A ko’ina Bahaushe ya fito a duniya ba ya da wurin da ake kira Hausa bayan Sakkwato bisa ga abubuwan da d’an bincikenmu ya k’yallaro. Yanzu mun ji Sakkwato ce Hausa, binciken da ya kyautu a duk’ufa shi ne, me ya sa ake kiranta “Hausa”?. Da d’aliban Hausa da Tarihi sun mayar da akalar bincikensu ga ire-iren wad’annan tussa na adabi, da ‘yan kallo ba su yi muna katsalandan su ‘bata muna asali da tarihi bisa karkataccen bincike da aka gina a kan k’ila-wa-k’ala.

Gurbin Sakkwato a Tarihin Bahaushe:


Hasashen Narambad’a idan aka d’ora shi a gadon fed’e al’ada da adabi da harshen Hausa akwai d’imin gaskiya ciki sosai. Sakkwato a matsayinta na gari Hausawa suka sare ta shi. Mutanen da ke karkarar su ne Sakkwatawa. Da sunan garin da mutanen k’asar duk Narambad’a ya ambace su, a wurare da dama kamar haka:

Jagora         :Ka gama lafiya uban Ajiya

Yara            :In ji Sakkwatawa na Amiru

:Ko Amiru munai ma hwata

Gindi          :Gwarzon shamaki na Malam toron Giwa

:Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

 

Da Amadu ya je Sakkwato garin Sakkwatawa su na yi masa addu’ar gamawa lafiya. A nan, ana ce wa Sakwkato “Hausa” kasancewarta cibiyar daular Hausa, jama’ar da ke cikin su ne Sakkwatawa kamar yadda jama’ar garin Isa Gobirawa ne amma a ce wa Isa “Hausa” zaman ta a farfajiyar k’asar Hausa. Narambad’a ya ambaci garin da sanannen sunansa wurare daban-daban kamar yadda yake cewa:

Jagora:        A runguma uban Yari

Yara  :         Mazan gabas ga Sakkwato

Gindi:           Yai halin mazan jiya

:         ‘Dan sanda mai Kwatarkwashi.

 

Kasancewar Sakkwato cibiyar Hausa take da sarautun yanki-yanki, irin su: Sarkin Yamma, Sarkin Kudu, Sarkin Gabas, Sarkin Sudan da dai sauransu domin a samu had’a k’asa d’aya bayan jihadi. An ci nasarar jihadi a addinance, a siyasance k’asa na nan daram da sunanta “Hausa”.

Idan za a yi wa tunanin Narambad’a adalci, za a ga ba shi ya fara kira ta “Hausa” ba. Ya tarar ana kiranta haka, ba shi ya kashe zomo ba rataya aka ba shi. Babu shakka, batun Narambad’a zai sa d’aliban adabi da al’ada da harshen Hausa tunanin cewa:

 1. Fitattun makad’an sarautar k’asar Hausa duk a Sakwkato ake samunsu. Daga cikinsu akwai: Salihu Jankid’i, Dandodo Alu mai Taushi, Narambad’a, Aliyu ‘Dandawo, ‘Dank’wairo, Kurna, Dantanoma, ‘Dankyana, Sa’idu Faru, Alhaji Muhammadu Shata.

 2. Fitattun makad’an sana’ar Bahaushe duk a Sakkwato ake samun su, daga cikinsu akwai: Makad’an noma, makad’an k’ira (zari), makad’an farauta, kamar su: Yaro Hore, Bawa ‘Dan’anace, Amali Subugu, Kassu Zurmi, Ladan Tuji, Bawa mai Zari, Namata Mai Zari, Garba ‘Danwasa Gumi, ‘Danbuga na Sabon Sara, Bala Lahodu, da dai makamantansu. • Fitattun mawak’an sha’awa da holewa na k’asar Hausa a Sakkwato suka tattara. Daga cikinsu akwai: ‘Danmaraya Jos, Garba Maitandu Shinkafi, Kaka Dawa. 1. Fitattun makad’an miyagun d’abi’u da suka yi wa k’asar Hausa shigon kutse irin su; Sata, Caca, Shaye-Shaye, Zina, da dai sauransu, duk a k’asar Sakkwato suke cure, irinsu; Alhaji Gambo Fagada, Kassu Zurmi, Bala Karhe, Faru, Yahayya, Golok’o.

 2. Fitattun makad’an wasannin k’asar Hausa, dambe da kokuwa Sakkwatawa ne ga abin da aka tabbatar. Daga cikin su akwai: Bawa ‘Dan’anace, Alh. Muhammadu Narayau, Sagwalo, Naramabad’a, da sauransu.


A iya bincikena, fitattun wasannin Bahaushe Narambad’a ya ambace su a cikin wak’e-wak’ensa. Dubi wad’annan d’iyan wak’a sosai:

Jagora: Bamin Kokawa bai iya ba

: Shi aka shammata kodayaushe

Yara  : Ga wata kokawwa an wuce da shi

: Karsanai kakka’be mishi k’asa.

Gindi : Ibrahimu na Guraguri

: Mai Shinkafi bajinin zagi

: Mu dai Allah Ya bar muna kaya.

Jagora: An ce mini an yi kokuwa

: Ban san kan ta ba

: Da na dac ciki

: Da na daw wuri

Yara  : Amfana ta na dac cikin ga

: Ya kada na daw wuri

Gindi: Jikan Mamman Tukur

: Maza ba mata ba ne

: ‘Dan namijin duniya

: A gai she ka Guraguri.

Yara: Uban zakara mugun madambaci

Gindi: ya ci maza ya kwan shina shire

: Gamda’aran Sarkin Tudu Alu,

 

Dalilina ke nan na ganin Narambad’a ya san Bahaushe sanin hatsi, ya san al’adun Hausawa gwargwado, ya san k’asar Hausa sani, ya san siyasa da sarautar Hausa sosai. Don haka, ya cancanci ya ce wani abu cikin tarihin Bahaushe. Daga cikin abubuwan da za su k’ara wa jawaban Narambad’a amo a kan asalin Bahaushe akwai:

 1. Ire-iren kare-karen harshe na Hausa na cikin kamfanunan Sakkwato arba’in da bakwai babu wata alk’arya daga cikin alk’aryun k’asar Hausa da ta tara su. Kad’an daga cikin akwai: Gobarci, Gimbananci, Arabci, Kabanci, Sakkwatanci, da dai sauransu.

 2. Ga alama, cuukoson tsofaffin kalmomin Hausa da ake iya tsinta cikin Sakkwato da karin harshen Sakkwatanci ba a samunsu a wasu sassa na k’asar Hausa. Don haka Sakkwato tafi yawan mawak’a da babu mai masantawa. A nazarci wad’annan kad’an a gani:


-        Cissawai      - ratsen hasken rana cikin inwa

-        Kushuli       - liwad’i

-        Lantago       - busasshen rogo da ake tuwo da shi ko d’an wake

-        Dibilwa       - wayon wayo

-        Kasherek’e  - namijin bubuk’uwa

-        Accakwama - matattu da raunannun yak’i da aka kwaso.

-        Sambari       - Adon da mata ke yi a le’be na katambiri (mai bak’i)

-        Kashindo    - ragowar kayan sata (la’bo)

-        Dak’walwa  - budurwa

Nad’ewa


Yayin da nake fafitikar neman kayan aikin wannan takarda na tattauna da jama’a da yawa. Wasu na ganin, a ce wa Sakkwato “Hausa” ba za a rasa amon siyasa ba. Wasu na ganin, Hausawa kawai ne ke ce mata “Hausa” domin tabbatar da martabarsu. Wa su na ganin masarautun ne suka aminta da haka domin samun kar’buwa da yayyafa wa turnuk’un siyasa ruwa. Ga abin da ya tabbata da Hausawa da Fulani da masu sarauta da talakawa da makad’ansu duk an aminta da amfani da kalmar “Hausa” ga Sakkwato kad’ai koma bayan kowace k’asa daga cikin k’asashen Hausa. Da dai an d’auki adabin Bahaushe da al’adunsa a matsayin makaman gano asalinsa da harshensa da an rarrabe zare da abawan tarihin Bahaushe ba da wata wahala ba. Hausawa kan ce gaskiya ta yi halinta; ana cikin gina ga wutsiya. Wani d’an jaridar Jahar Zamfara mai suna Ibrahim Aliyu Mayanci ya rubuta tarhin Gwamnan Jihar Zamfara mai ci yanzu, Muhammadu Aliyu Shinkafi sunan littafin: Wane ne Dalhatu? A cikin hirar da ya yi da yayan Gwamna Muhamamdu Namoriki. Da ya tambaye shi tarihin iyayensu, ya fara da mahaifiyarsu sai ya ce: “Ita tsohuwarmu asalinsu mutanen k’asar Hausa ne daga Ra’ba” (2011). Ashe mutanen zamani su suka cancanci su ba da labarin zamanin da ya gabace su. Wannan ita ce hujjata ta gayato Narambad’a da takwarorinsa su ba mu labarin abin da suka ji daga magabatansu. Na gode Narmabad’a, Allah Ya gafarta maka.

 

 

MANAZARTA


 

Adamu, M. (1976) “The Spread of Hausa Culture in West Africa” Savanna 5, 3-

13.

 

Bunza, A.M. (2008) Religion and The Emergence of Hausa Identity: An Enquiry

into the Early Traditional Religion in Hausaland, paper presented at International Conference titled: Hausa Identity: Religion and History, Organized by AHRC and ESRL held at University of East Anglia (Norwich) U.K, Friday 11- Saturday, 12 July 2008.

 

Bunza, A.M. (2009) Narambad’a, Wallafar IBRASH, Lagos.

 

Bunza, A.M. (2010) “Fashin Bak’in Wak’ar Mai Yawuri Bangon Duniya ta Aliyu

‘Dandawo”, takardar da aka gabatar a bukin k’addamar littafin Mai Yawuri Bangon Duniya da d’aliban Jami’ar Sakkwato suka yi a Fadar Masarautar Yawuri, a k’ark’ashin Jagoranci mai Martaba Sarkin Yawuri Alhaji Zayyanu Abdullahi, PhD.

 

Fisher, H.I (1975) “Leo Africanus and the Shonghai Conquers of Hausaland”,

African Historical Studies 11, 86-112.

 

Fuglast ed, F. (1978) “A Consideration of Hausa History Before the Jihad”,

Journal of African History, 19, 319-339.

 

Gusau, S.M. (2009) Diwanin Wak’ok’in Baka: Za’ba’b’bun Matanoni na Wak’ok’in

Baka Na Hausa.

 

Haour, A and Rossi, B. (ed) (2010) Being and Becoming Hausa, Interdisciplinary

Perspectives, Africna Social Studies Series, Brill, Leiden-Boston.

 

Hill, R. (1972) Rural Hausa a Village and Setting, Cambridge, Cambridge

University, Press.

 

Johnston H.A.S. (1967), The Fulani Empire of Sokoto London, London Oxford

University Press.

 

Last, D.M (1967) The Sokoto Caliphate, Ibadan and London Longman.

 

Lauge, D. (1987b) The evaluation of the Hausaland story: From Bawo to

Bayajida”, Africa und Ubersee 70, 195-209.

 

Meck, C.K. (1926) The Northern Tribes of Nigeria, Oxford University Press.

 

 

 

Muhammad A. (1972), “Individual Talent in the Hausa Poetic Tradition: A study

of Ak’ilu Aliyu and his Art”, PhD Thesis University of London.

 

Muhammad, D. (1981), Bakandamiya: “Towards a characteriazation of the poets

master piece in Hausa”. In Oral poetry in Nigeria (eds) By Abologun and others Lagos; Nigeria Magazine.

 

Muhammadou, K. (2006) “Asalin Hausawa da Rubutun Hausa na Ainihi”,

Takardar da aka gabatar a k’ark’ashin Inwar Kwamitin k’asa Nijeriya kan Nazarin Haruffan Hausa, Kaduna, Litinin 24 ga Yuli, 2006.

 

Philips, J.E. (1989), “A History of the Hausa Language”. In Barkind’o B.M. (ed)

Kano and some of her Neighbours. Kano/Zaria, Ahmadu Bello University Press 37-58.

 

Schuh, R.G. (1982), “The Hausa Languges and its nearest relatives”, Hausa

Nijeriya 17, 1-24.

 

Smith, A. (H.F.C) (1970) “Some Consideration to the formation of state in

Hausland, Journal of the Historical Society of Nigeria, 329-346.

 

Smith, M.G. (1960), Government in Zazzau: A study of governemnt in the Hausa

Chiefdom of Zaria in Northern Nigeria from 1800 to 1950 Oxford, Oxford University Press.

 

Smith, M.G. (1960) Government in Kano. 1350-1950, Westview Press.

 

Smith, M.G. (1978) The Affairs of Daura. History and Changes in Hausa States,

1800-1958 Barkeley and Los Angeles: University of California Press.

 

Sutton, J.E.G. (1979) “Towards a less Orthodox history of Hausaland”, Journal of

the African History 20, 179-201.

 

Vansina, J. (1985) Oral Tradition as History, James Currey Ltd 73 Botley Road

Oxford OX2 OBJ.

 

Westley, D. (1986), “The Oral Tadition and the Begining of Hausa Fiction”, PhD

Thesis University of Wisconsin- Madison.

 

Yaro Sodangi B.A. (1979) “Narambad’a da Wak’ok’insa” Kundin digirin BA         Jami’ar Bayero, Kano.

 

 

 

No comments