Gulma da Tsegumi a Tunanin Bahaushe: Nazari Daga Habarcen Hausa

    Cite this article as: Tahir, M.R. & Lawal, N. (2023). Gulma da Tsegumi a Tunanin Bahaushe: Nazari Daga Habarcen Hausa. Zamfara International Journal of Humanities, (2)2, 111-116. www.doi.org/10.36349/zamijoh.2023.v02i02.013.

    Gulma da Tsegumi a Tunanin Bahaushe: Nazari Daga Habarcen Hausa

    Muhammad Rabiu Tahir,
    Sashen Harsuna Da Aladun Afirka,
    Jamiar Ahmadu Bello Zariya
    07031340632
    mrtahir@abu.edu.ng

    da

    Nura Lawal
    nlawal.hau@buk.edu.ng
    Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
    Jami’ar Bayero, Kano

    Tsakure

    Al’ummar Hausawa, al’umma ce da take da hanyoyi mabambanta na tantance abubuwa masu ɗimbin yawa, waɗanda suke abin koyi da kuma munana waɗanda Hausawa suke ɗaukar su a matsayin abin ƙyama. Gulma da tsegumi suna ɗaya daga cikin munanan halaye da ɗabi’un da Hausawa sukan yi hani da aikata su. Gulma da tsegumi ɗabi’u ne marasa kyau da suka daɗe a cikin al’umma. Kamar yadda ba a san ranar da aka fare su ba, haka kuma ba a san ranar barin su ba. Duk da an san ƙarshen mai yin su shi ne jin kunya. Wannan takardar ta kalli ɗabi’ar daga gulma da tsegumi ne daga adabin baka na habarce da tatsuniya ta hanyar fito da gulma da tsegumin da kuma matsayinsu a al’adun Hausawa da ma dalilan yin gulma da tsegumin. Gulma da tsegumi abubuwa biyu ne masu makusanciyar ma’ana, amma da an ambaci gulma da abu mara kyau aka fi danganta shi. Shi kuwa tsegumi ba lallai ba ne ya zama abu mara kyau. Ana iya tsegunta wani alheri ga wani kamar yadda aka ga tsuntsuwa ta je ta tsegunta wa sarki labarin narkewar Ta-kitse.Wannan bincike ya gano dalilan da yake sanyawa ana gulma ko tsegumi da suka haɗa da: Hassada wato burin wani ya rasa wani abin da yake da shi da ƙyashi da kishi da son faɗar albarkacin baki. Kamar a tatsuniyar ta-kitse, a lokacin da gizo ya kai tsegumin cewa akwai wani tirkekken bajimin sa a gidan tsohuwa aka kuma je aka raba ta da wannan bajimin san. Haka kuma ya sake komawa ya sanya aka ɗauko wannan yarinyar a wurinta. A kuma labarin Shaihu Umar an ga yadda aka yi wa Makau hassada aka kai gulmarsa aka sa ya rasa komai har sai da aka kore shi a gari.

    Muhimman Kalmomi: Gulma, Tsugumi, Tunani da Habarce

    Gabatarwa

    Gulma da tsegumi kalmomi ne na Hausawa waɗanda suke da makusanciyar ma’ana da juna. Haka kuma, ma’anonin kalmomin sun zama iri ɗaya da na kalmomin munafurci da annamimanci waɗanda su kuma asalinsu daga harshen Larabci ne. Idan aka ce gulma ana nufin ɗaukar zancen wani a kai ma wani da nufin haɗa husuma. Tsegumi kuma shi ne ƙoƙarin jin wani labari da bai shafe ka ba, ka baza labaran da ba a tambaye ka ba. A yayin da annamimanci da munafunci a tunanin Bahaushe ke nufin haɗa ƙullalliya tsakanin mutane don haɗa husuma.

    A wannan takarda an yi amfani da ma’aunin da Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos ya yi amfani da shi wurin fayyace magulmaci a waƙarsa ta “Zancen Magulmaci” sai kuma a ƙara da abubuwan da Hausawa suke faɗa dangane da gulma da tsegumi da annamimanci da munafurci a karin maganarsu. A aikin za a duba tatsuniyar Gizo da Tsohuwa (Tatsuniyar ta-kiste) da labarin Ɗantsatsube da namun daji a littafin nuni cikin nishaɗi. Dukkan waɗannan an yi amfani da su a matsayin misalan da aka samu ba don wani fifiko ba a kan sauran tatsuniyoyin.

    Tatsuniya

    Tatsuniya labari ce mai ɗauke da hikimomin sarrafa rayuwa da ake labarta su ga al’umma, amma daga bisani ana danganta tatsuniya ga yara da kuma cewa ana koyar da su domin su fahimci makamar rayuwa. Galadanci, da wasu (1990:sh-59) sun bayyana tatsuniya da cewa, labari ne da Hausawa ke ƙagowa saboda su koyar da yara wani darasi. Junaidu, da Yaraduwa, (2007:sh-75) sun ƙara da cewa, tatsuniya labari ne na ƙarya wanda ba alamar gaskiya a cikinta da Hausawa ke amfani da shi domin hira da annashuwa. Junaidu, da wasu, (2008:sh-20) suka ce, akan ƙirƙira a kuma faɗa wa yara tatsuniya da dare bayan cin abincin almuru kuma babu gaskiya a cikinta. Su zarruƙ, (1986:sh-58) sun bayyana cewa, tatsuniya ta ƙunshi maganganu da ayyukan mutane da dabbobi da aljanu kuma sau da yawa tana ƙarewa da farin ciki. Yahaya, da wasu, (1992:sh-7) suka ce, tatsuniya takan ɗan yi tsawo kuma akwai hikima da nuna ƙwarewa a cikinga har ma da nishaɗantarwa. Galadanci, da wasu (1990:sh-60) sun musa, sun nuna cewa tatsuniyar labari ta ƙunshi labarai da wani lokaci su yi tsawo wani lokaci kuma gajeru ne ake yin su saboda a koyar da wani darasi na tarbiya.

    Ciroma, (1999:sh-ii) ya bayyana cewa yara masu sauraron tatsuniya sukan natsu sosai ta yadda ba sa so wani abu ya ɗauki hankalinsu balle a faɗi wani abin da zai kasance ba su ji shi ba ko su kasa fahimta. Haka kuma idan an gama tatsuniya yaro yakan riƙa riya abin a zuciyarsa kamar dai abin ya faru ne a gabansa. Kuma daga bisani sai an sami wani yaron da ya yi koyi da wani darasi muhimmi daga wannan tatsuniya. Malamin ya ƙara da cewa, a yanzu adabin tatsuniya ya sami tasgaro saboda tasirin zamani da ya zo da su talabijin da gidajen silima da finafinai da sauran kayan zamani da suka daƙile tafiyar tatsuniya, ya kuma nuna cewa tasirin zamananci bai tsaya a birane ba har ƙauyuka ya bi ya rage tafiyar tatsuniyoyi.

    Mai yin tatsuniya yakan fara ta da, ga ta nan ga ta nan ku Masu saurare kan amsa da ta zo mu ji ta.” Akan ƙare tatsuniya da ƙurungus kan kusu. Ko wasu kalmomi masu kama da haka. Ba a yin tatsuniya da rana, saboda akwai camfin cewa za a yi ɗemuwa (makuwa). In kuma ta kama za a yi ta dole, to, akan ɗaure gizo wanda idan an yi hakan sai ya zama ba za a yi ɗemuwar ba ba. Duk da cewa tatsuniya kayan yara ne, amma kuma manya kan shiga cikin shaanin saboda wani lokaci manya ne ke yi wa yaran tatsuniya da dare bayan sun dawo daga wuraren aiki ko a sami wata tsohuwa ko wata amarya da yara za su hallara a ɗakinta suna ɗauke masu kewa su kuma suna yi musu tatsuniyoyi. A wasu lokutan akan haɗa tatsuniya da wasu ’yan aikace-aikace kamar su kaɗi ko ƙananan sanaoi na mata. Zarruƙ, (1986:sh-59).

    Masana irin su Zarruƙ da wasu (1986) da Galadanci, da wasu (1990) da su Yahaya, da wasu, (1992) da kuma Tahir, (2021) sun nuna a kan sami tatsuniyar da ta ƙunshi mutane zalla ko dabbobi da aljanu zalla ko ta zama hatsin bara, wato a yamutsa dabbobi da aljanu da mutane a cikinta. Haka kuma, akan yi amfani da wurare kamar garuruwa ko dazuka ko rafuka a cikin tatsuniya. Sannan sifofi da ake bayarwa a cikin tatsuniyoyin masu kyau ne. Akan nuna na kyawun ne sosai, haka shi ma muni akan nuna ya kai maƙura. Akan kuma sami kowane irin hali a cikin tatsuniya ko mai kyau ko kuma marar kyau waɗanda suka saɓa kamar su gulma da tsegumi da annamimanci da munafunci da makamantansu.

     

    Gulma/Tsegumi

    CNHN (2006:sh 173) ya bayyana kalmar gulma da: (1) ɗaukar zance daga wani zuwa wani yadda zai kawo saɓani a tsakaninsu. (2) faɗin ƙarya. Magulmaci/magulmaciya: sunan mutum ne namiji/mace wanɗanda aikinsu shi ne gulma. Magulmata kuma: jam’i ne na mutane masu yin gulma. Bayan wannan sanance na ƙamusu akwai zantuttukan hikima na Hausawa game da batun gulma da suke ƙara bayani a kan gulma. Misali:

    Ba ni shiga gidan yara, tsohuwa ta so gulma.

    Da wannan misali na karin magana a iya fahimtar cewa a tunanin Bahaushe na dauri, yana hararo yawan kai-komo- a tsakanin gidajen surikai hakan yana iya haddasa zantuttuka waɗanda suna iya zamowa tsegumi. Ko kuma hakan na ƙoƙarin nuna cewa a alada ta Hausawa iyaye ko tsofoffi, musamman mata ba daidai ba ne su riƙa zuwa gidan yara, domin hakan ba abu ba ne mai kyau. Saboda ko ba komai sai sun ga wani abu da ya zama ba daidai ba kuma sai sun yi magana. Yawan magana kuma, yana iya zama tsegumi ko haɗin faɗa. Wannan ne ya sa tsohuwa da ta so yin gulma sai ta ce ita ba ta zuwa gidan yara wato gulma ce aka kawo mata.

    Haka kuma akwai karin maganganu masu yawa bayan wannan masu nuna gulma – misali da aka so a nuna irin mutanen nan da gulma ta zame musu jiki sai aka yi musu habaici da cewa;

     Gulma ajali in ba a yi ba a mutu.

    Domin a nuna yadda abin ya kama jikinsu kuma ba su da wani tsoro don an same su sun yi gulma kuma ko waye za su iya kai gulmarsa. Da kuma aka so bambance tsakanin gulma da tsegumi sai Hausawa suke cewa, Gulma ta riga tsegumi wato tsegumi madakin gulma ne. Duk inda ake yawan samun tsegume gulma na nan zuwa. Da kuma aka so a nuna ɓacin rana ga mai gulma sai aka ce;

     “Gulma ta yi kai.”

    Wato an yi gulma kuma asiri ya tonu. Kuma da irin wannan ne ake yin ba’a ga mai gulmar da asiri ya tonu da “Kai da gulma kai da jin haushi.” Sannan aka nuna rashin kamun kan budurwa mai gaida uwar saurayi da cewa “Ƙaƙalen gulma, gai da uwar saurayi a kasuwa.

    CNHN (2006:sh 455) ya ce, tsegumi shi ne: ƙoƙarin jin abin da bai shafi mutum ba ko baza labari. Tsegunguma/tsegume-tsegume shi ne jami ne na tsegumi. Kalmar tsegunta kuma shi ne baza labarin wani a bayan idonsa. Tsegumi abu ne mai sauƙi wanda a wasu lokuta mutum na iya yin sa bai sani ba, shi ya sa Hausawa suke cewa, “Abin ba wuya kamar tsegumi.” Haka kuma da aka kama mai gida ya yi tsegumi sai yake cewa;Ba ni da ta cewa, mai gida ya yi tsegumi.Wanda yake nuna azarɓaɓi da rashin iya yi wa baki linzami. Da kuma Hausawa suka tashi fallasa waɗanda za a fi zargi da aikin tsegumi sai ya nuna masu kwaɗayi da yawo gidajen mutane yake cewa, Bayan ci, zama tsegumi; kwanciya lalaci; tafiya rashin kunya. Shi kuma makaho duk da cewa ba shi da ido kuma tsegumi abin zargi ne don ba ya so a kama shi yana yi kamar yadda aka kama mai gida sai yake cewa, Duba mani hanya, makaho ya so tsegumi. Wai a duba masa hanya ko ba kowa don akwai labarin da yake so ya bayar.

    Haka kuma, Hausawa sun yarda cewa, duk mai tsegumi yana da yawan magana shi ya sa yake cewa, Furen yawan tsegumi, magana. Sannan ya ƙara da cewa, In kana kashi ka hangi mai tsegumi, zauna kan kashinka. Wato in kana aikata wani abu musamman na laifi ko na ɗebe wa kai takaici idan ka ga mai yawan magana to ka yi kurum ka nuna ba ka aikata komai. Zantuttukan Hausawa game da tsegumi ko mai tsegumi suna da yawa ga kuma wasu nan ma biye:

    a.      Ina zan zauna, mai tsegumi ya je kasuwa.

    b.      Komai tsegumin mutum, ya bari a tambaye shi.

    c.       Kurum maganin mai tsegumi.

    d.     Mai tsegumi, ba shi rabuwa da waiwaye.

    e.      Mai tsegumi, ba ya rabo da tsugunni.

    f.        Tsegumi da daɗi in ya fito da kunya.

    g.      Tsegumi sana’ar gado, kowa ya ƙware da kai in bai gada ga tsoho ba, to, ga tsohuwa.

    h.      Wai-wai shuru ’yar mai tsegumi ta yi cikin shege. (Gwammaja, 2018)

     

    Bayan gulma da tsegumi akwai wasu kalmomi kamar yadda aka ambata a gabatarwa da suke da dangantaka da waɗanda su kuma asalinsu kalmomi ne na Larabci wato annamimanci da kuma munafunci. Waɗannan kalmomi ga yadda Hausawa suke kallon su:

    a.      Annamini: mai haɗin husuma ko munafuki ko magulmaci.

    b.      Annamimiya: mai haɗin husuma ko munafuka ko magulmaciya.

    c.       Annamimai: masu haɗin husuma ko munafukai ko magulmata.

    d.     Annamimanci: (1) ɗaukar maganar wani a kai ma wani don haɗa su husuma (2) gulma ko munafunci.

    e.      Munafuki: mutum mai ƙulle-ƙulle tsakanin mutane don ta da husuma.

    f.        Munafuka: mace mai ƙulle-ƙulle tsakanin mutane don ta da husuma.

    g.      Munafukai: jam’in munafuki/munafuka

    h.      Munafunci: ƙulle-ƙulle tsakanin mutane

    i.        Munafunta: ha’inta/ yin munafunci. Abdurrahman, (1981)

    Alhaji Adamu Ɗanmaraya mai waƙa ya yi ƙoƙarin fayyace wannan ɗabi’a ta gulma a waƙarsa ta zancen magulmaci. Kusan duk hasashen Hausawa game da gulma ko tsegumi ya tabbatar da su a cikin waƙar ya kuma nemi Allah da ya kare kowa daga sharrin magulmaci. Da ya tashi nuna yadda magulmaci yake sai yake cewa:

     

    Jagora: To kun ji zancen magulmaci,

    : Sannan kau za i zo wajan wannan,

    : Sanan kau ai wane ya ce ma,

    : Ba ka da kirki sam!

     

    Sannan idan ya yi haka ba ya ƙyale ke nan ba; rugawa zai yi wajen ɗayan shi ma ya kai suka kamar yadda mawaƙin ya faɗa:

     

    Jagora: Zai gangara kau wajan wancan,

    : Abun haƙun ke nan,

    : Yau wane kau shi ne ka ɓata ka; oh!

    : Amma abun ai da mamaki,

    : Kamar wane shi ne ka ɓata ka.

     

    A ƙarshe mawaƙin ya fito da manufar magulmaci kamar haka:

     

    Jagora: Muddin idan dai ya zana ma,

    : In ka ɗau zancen magulmaci,

    : Matakka ma sai ta raina ka,

    : Danginka ma sai ku ɓara sam,

    : Wajen aiki sai a raina ka,

    : ’Ya’yanka ma sai su raina ka,

    : In ka bi zancen magulmaci,

    : Yikan ɓata halin zaman da can,

    : Yikan ɓata halin zaman yanzu,

    : Yakan ɓata halin zaman gobe,

    : Allahu ya Wahidun mai ni,

    : Raba mu da sharrin magulmaci...

    Wato, shi burinsa shi ne duk gulmar da ya kawo a ɗauka a yi aiki da ita; daga ya haɗa husuma shi ke nan burinsa ya cika.

    Idan aka lura da abin da ya gabata za a fahimci cewa magulmaci shi ne duk mutumin da ke ɗaukar zancen wani ya kai ma wani da niyyar ya ɓata tsakaninsu. Amma dangane da tsegumi kuma shi madaki ne na gulma kuma ana iya tsegunta labari da nufin albishir ba da nufin haɗa husuma ba. Kuma tsegumi a taƙaice yake amma gulma za a iya zuwa fiye da sau ɗaya kafin a haɗa husuma. Haka kuma idan tsegumi ya yi yawa yakan zama gulma.

    Gulma da Tsegumi A Habarcen Hausa

    A tatsuniyar “Ruwan Ido”, “Zaɓen Tumun Dare” an fahimce cewa tsegumi labari ɗan kaɗan da za a bayar da shi na wani abu wanda ke iya sa duk wanda ya ji wannan labarin ya nemi kandaminsa wato cikakken labari:

    to ana nan, sai ta isa aure, sai sarki ya ce mata, sai ta faɗi wanda take so, don ya fito a ɗaura musu aure, don kuwa ta cika Kwalbar Ƙwayan, kowa ya ji ya kawo caffa, sai ta dube shi, yatsine ta ce bai yi mata ba. Hassan, (1980:sh 6)

    A wannan wuri an nuna tsegumi da kuma dalilin da ya sa tsegumi ya yaɗu cikin jama’a. Sannan kasancewar tsegumin bai zama cikakken labari ba shi ne ya sanya kowa ya ji sai ya taho neman wannan yarinya wato “Kwalbar Ƙwaya”.

    A wannan wuri tsegumi da ya ba na haɗa husuma ba ne tsakanin mutane, na a zo ko za a dace a ƙulla dangantaka ta auratayya a tsakanin wanda ya dace da ’yar sarki ne.

    Haka kuma, da abin ya girmama sai tsegumi ya zama gulma wato gamin husuma tsakanin mutane don an sami waɗanda suka kai gulma ga wata aljana wadda rabinta mutum, rabinta kuma kifi:

    To, ana cikin wannan hali ake har ran nan wata aljanar ruwa ta sami labari, mai gida a tsakiyar teku.

    Wannan turin jeka ka mutu ne magulmatar nan suke ƙoƙarin yi ma wannan yarinya. Da nufi aka kai ma wannan aljanna labarinta saboda an san takan tsare fatake kuma takan yi kisa.

    Tatsuniyar “Sarki da Kaho” wadda Salihu wanzami ya ga wani asiri na sarki a yayin da ya zo yi masa aski. Sarki ya cire rawaninsa sai ya ga ƙaho ya fito masa a ka, aka yi aski aka gama. Bai ce da Salihu komai ba amma da ya tafi sai labari ya riƙa cin sa ya rasa inda zai je ya faɗa saboda yana tsoron in ya faɗi a bakin ransa, sarki zai sa a yanka shi. A ƙarshe da gulmar ta ci shi sai ya je daji ya tona rami ya faɗi wannan magana a ciki ya huta da gulmar da ke cin sa. Amma da ruwan damina ya zo sai karan dawa ta fito Bafulatani kuma ya zo ya ɗiba ya yi sarewa sai ya zama sarewar idan aka busa ta sai ta riƙa amon zance da Salihu ya faɗi wato, “Turu tururu, turururururu!” ma’ana sarki da ƙaho, inji Salihu wanzami. Ko da aka ji sarki ya bincika ya sa kuma aka yanka Salihu wanzami. (Edger, 1911.) Wannan habarcen ya fito da tsegumi da gulmar da Salihu wanzami ya yi, da kuma yadda asirinsa ya tonu, wanda daga ƙarshe sarki ya sa aka yanka shi.

    Tatsuniyar marainiya Mai Icen Ƙosai ita ma shaida ce a kan yadda mahaifiyar marainiya ta bar mata ƙosai da nufin in ta mutu ta je daji ta shuka shi. Bayan mutuwarta kuwa da marainiya ta ga yadda kishiyar mahaifiyarta take matsa mata da aiki kuma ba abinci sai ta je daji da wannan ƙosai ta shuka shi. Nan da nan itace ya girma ita kuma in ta zo sai ta rera waƙa itace kuma ya yi ƙasa-ƙasa sai ta tsinki ƙosai ta ci sai ta ƙoshi ta nemi ruwa ta sha. A ƙarshi kishiyar mahaifiyarta ta gani ta kuma kai tsegumi da gulma wurin sarki saboda a muzanta yarinyar ko ma a kashe ta amma abin bai yiwu ba sai ya ƙare a kansu. Soboda rera waƙa da ta yi sauko sai sarki da fadawa da kishiya suka hau itace kuma ya tafi da su.

    Wannan tatsuniya ita ma ta nuna gulma da kuma illarsa da ma sakamakon mai yin ta; sannan ta nuna dalilin da ya sa aka yi gulmar wato a tozarta yarinya marainiya.

    A littafin Shaihu Umar an nuna cewa bayan Makau ya sami karɓuwa a wurin sarki sauran fadawa sun ji haushin haka, don haka, sai suka yi ta fata Allah ya kawo wata rana da za su shiga tsakanin sarki da Makau. Ana nan, ran nan sai sarki ya aika su Makau samame don su samo masa bayi. Ko da suka je Makau bayi biyu ya samu ko da suka dawo gida sai Makau ya ce bari ya biya ta gida ya kimtsa kafin ya je fada. Da sauran fadawa suka sami ’yar wannan kafa sai suka ce wa sarki bayi huɗu, suka dai ɓata shi a wurin sarki. Ko da Makau ya zo sarki ya tambaye shi, shi kuma ya bayyana abin da ya samo na bayi sai ran sarki ya ɓaci ya yi tambaya sai aka ce masa bayi huɗu ya kamo ya ce ka ji ba. Daga nan sarki ya sa aka washe gidan makau aka kore shi a gari.

    Da wannan an ga yadda fadawa suka ƙullaci Makau amma kuma ba su sami damar kai tsegumi ba sai da suka sami inda ya yi kuskure kafin suka kai sukarsa wurin sarki. Su a wurinsu buƙatarsu ta biya don an kori Makau daga gari, an yi masa wulaƙanci an washe masa gida.

    A tatsuniyar Ta-kiste, an ga yadda Gizo ya je bara gidan tsohuwa daga nan kuma sai ya ga saniyarta da ta tirke. Daga nan Gizo ya je ya kai tsegumi da gulma wurin sarki. Gizo bai rabu da wurin sarki ba sai da aka haɗa shi da fadawa domin a je a duba in da gaske ne a zo da saniya. Haka Gizo ya sa aka yi ta dukar tsohuwa har aka raba ta da saniyarta aka yanka. Bayan an yi kaso aka ba ta kayan ciki ita kuma ta zo gida ta ajiye ƙarshe suka zame yan mata. Wata rana kuma Gizo ya ƙara zuwa neman tsegumi ya ga waɗannan ’yan mata ya kuma ƙara zuwa ya tsegunta wa sarki nan ma aka ƙara zuwa aka raba ta da Ta-kishe amma sai ta gindaya musu sharaɗi cewa kar a bar ta yi kusa da wuta. A ƙarshe ƙyashi da hassada ta sa sauran matan sarki suka sa ta yin girki bayan sun ga sarki ya je wajen yaƙi. Ta-kitse ta narke aka rasa yadda za a yi a tsegunta wa sarki; sai da ƙyar tsuntsuwa ta je ta tsegunta wa sarki. Sarki ya dawo gida ya ga abin da ya faru ya sa aka kashe waɗannan mata da suka shirya wannan makirci tsohuwa kuma aka yi mata ɗaki a gidan sarki ta ci gaba da kula da ta kitse.

    A wannan tatsuniya an ga yadda gizo yake fita yawon neman tsegumi don ya kai shi ga sarki domin ya sami lada. A ƙarshe an ga sakamakon gizo saboda tsohuwa ta ci gaba ta koma gidan sarki da zama. Haka kuma an ga sakamakon waɗanda suka cutae da ta kiste, su ma a sakamakon tsegumin da tsuntsuwa ta kai wa sarki a wurin yaƙi.

    Kammalawa

    Gulma da tsegumi abubuwa biyu ne masu makusanciyar ma’ana. Amma da an ambaci gulma da abu mara kyau aka fi danganta ta. Shi kuwa tsegumi ba lallai ba ne ya zama abu mara kyau, ana iya tsegunta wani alheri ga wani kamar yadda aka ga tsuntsuwa ta je ta tsegunta wa sarki labarin narkewar ta kitse. Wannan bincike ya gano dalilan da yake sanyawa ana gulma ko tsegumi da suka haɗa da: hassada wato burin wani ya rasa wani abin da yake da shi da ƙyashi da kishi da son faɗar albarkacin baki. Kamar a tatsuniyar ta kitse da gizo ya kai tsegumin cewa akwai wani tirkekken saniya a gidan tsohuwa aka kuma je aka raba ta da wannan saniya. Haka kuma ya sake komawa ya sanya aka amshe ta kiste a wurinta. A kuma labarin Shaihu Umar an ga yadda aka yi wa Makau hassada aka kai gulmarsa aka sa ya rasa komai har sai da aka kore shi a gari. A kuma labarin sarki da ƙaho an ga yadda son tsegumi ya kasance da har Salihu wanzami ya rasa wanda zai faɗa wa tsegumi ƙarshe sai da ya je daji ya haƙa rami ya faɗi wannan tsegumin a ciki. Haka kuma binciken ya gano sakamakon mai Gulma ko Tsegumi su ma kamar haka: jin kunya ko kunyata da mummunan ƙarshe da zubewar mutunci ko tozarta. A tatsuniyar marainiya an ga yadda gulma da tsegumi ya halaka sarki da fadawansa da kuma kishiya mai kai gulma. Sannan a tatsuniyar ta kiste an ga yadda gulmar gizo ta zama saniyar ɗaukakar tsohuwa da ta kiste.

    Manazarta

    1.      Abdurrahman, A.A. (1981). Akhbaru Al-ahad Fil Al-hadith Al-nabawiy: Azhar Cairo. Darul Al- Fikir.

    2.      Ahmad, S.B. ( 1997). Narrator as Interpreter: Stability and Variation in Hausa Tales Rudiger Koppe Verlag Koln .

    3.      Gwammaja, K.D. (2018). Jagoran Nazarin Karin Magana. Kano: K.D.G. Publishers

    4.      Edgar, f. (1911), Littafi na Tatsuniyoyi na Hausa Littafi na Biyu. Belfast.

    5.      Galadanci, M.K.M. Da wasu, (1990). Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare. Ibadan: Longman Nigeria.

    6.      Gusau, S.M. (2000). Tatsuniya a Rubuce. Kano: Century Research and Publishing Company.

    7.      Gusau, S.M. (2006). Tatsuniya (gatanan): Sigoginta da Hikimominta. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies; Kano: Department of Nigerian Languages, Bayero University.

    8.      Junaidu, I. da Wasu, (2007). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandare. Ibadan: Spectrum Books Limited.

    9.      Junaidu, I. da wasu, (2008). Darussan Hausa a Kammale. Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. Ibadan: hebn.

    10.  Ƙaraye, M. (1979). Structural Characteristic of Gizo in Huasa Folktales, Unpublished M.A. Thesis, University of Khartoum.

    11.  Ƙaraye, M. (1982). The Structural Study of African Oral Narrative: Evidence From Hausa. Journal Harsunan Nijeriya, vii, Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    12.  Skinner, N. (1980) Anthology of Hausa Literature: Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

    13.  Umar, M.H. (1980). Nuni Cikin Nishaɗi. Zariya: Northern Nigerian Publishing Company.

    14.  Usman, B. (2005). Jarumin Sarki da Wasu Labarai. Kano: Gidan Dabino Publishers.

    15.  Usman, B. (2013). Folklore and the History the Twin Rivers of World Heritage. Abuja: Klamidas Communication Limited.

    16.  Yahaya, I.Y. (1979). Labarun Gargajiya 1. Ibadan: University Press plc.

    17.  Yahaya, I.Y. (1979). Labarun gargajiya 2. Ibadan: University Press plc.

    18.  Yahaya, I.Y. Da Wasu, (1992). Darussan Hausa 1 Don Manyan Makarantun Sakandare. Ibadan: University Press plc.

    19.  Zarruƙ, M.R. Da Wasu, (1986). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Ɗaya. Ibadan: University Press.

    Download the article:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.