Takardar da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ɗaliban Babban Digiri na Uku da na Biyu (Ph.D & M.A) a Babban Ɗakin Taron Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato Ranar Lahadi, 03/09/2023 da Misalin Ƙarfe 11: 00 na Safe.
RA’IN
GAME-DUNIYACIKIN KARATUN BAHAUSHEN KARIN MAGANA:
(Duba
Cikin “Komai Ya Cika Zai Batse” a Tunanin Bahaushe)
Daga
Aliyu
Muhammad Bunza
Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sokoto
Email: mabunza@yahoo.com
Phone Number: 08034316508
Tsakure
Ra’in Game-Duniya cikin karatun Bahaushen karin magana
wani yunƙuri ne na tsakuro karin
maganan da suka game duniya ga karatunsu. An ɗora wannan bincike a kan tunanin
Bahaushe da ke cewa: “Hantsi leƙa gidan kowa” domin karuruwan
maganan duniya suka game. An bi salon rangadin kayan aiki na binciken ayyukan da aka wallafa da waɗanda ba a wallafa ba. An dogara ga
tattaunawa da masana da ɗaliban ilmi da duniyar intanet. Kayan aikin binciken an ɗora su a fasula ashirin da ɗaya (21). Goshin aiki ya mamaye fasula tara (9). Fashin baƙin gabatar da ƙwaryar bincike faslai shida (6) tatarniyar tabbatar da
hujjojin bincike faslai shida (6). An ci nasarar fito da matakai bakwai (7) na
tantance karin magana game-duniya, da matakai biyar (5) na tantance cika da
batsewa. An gano karin magana game-duniya na hawa matakai biyar na gamsasshen
ra’i yardajje ga masana ra’i don haka aka nemi a daidaita sahu. An ci
nasarar samo karin magana ɗari (100) an ɗora saba’in da biyar a faifan
nazarin game-duniya ba su goce ba.
Gabatarwa
Tunanin magabata da ke ƙunshe cikin adabi ba ƙaramin makami ba ne ga na baya a kowace fuska ta rayuwar duniya. Idan aka
ji Bahaushe ya ce: “Bari inyi na babban mahaukaci”. Yana nufin wai ya game
duniya da sani, kamar ya ce: “duk duniya babu kamar wane adalci”. Faɗar “duk duniya” babbar magana ce da
ke nuna kamar an kewaye komai da ilmi. To, ƙudurina a wannan takarda fito da
wasu fitattun karin magana domin assasa ko ƙirƙiro wani ra’i da yi wa suna “Ra’in
Game-Duniya”. Na ɗora wannan ra’in da nake hasashe a kan karatun karin maganan da ke cewa:
“Komi ya cika zai batse”. Wannan tunanin Bahaushe idan aka ɗora shi kan gadon nazari na rayuwar
duniya jiya da yau, za a ga ruwan dare ne game duniya. Burina in gayyato karin
maganan da suka yi canjaras da jigonsa tare da wasu sassan adabi da al’adu na
dahir da suka tabbatar da ƙunshiyarsa da zai ba mu damar ƙirƙiro Ra’in “Game-Duniya” cikin karatun Hausa.
Shimfiɗa
Da duniya, duniya ce a yau ta koma kamar ɗaki ɗaya komai ya wakana cikin sassanta
kowa na gani, kowa na ji. Kimiyyar cigaban rayuwa ta haifar da wannan. Idan an
ce “kimiyya” gajeren tunanin makaftaccen ɗan boko ita ce ƙere-ƙeren na’urorin ƙarnukannu da ilmin ƙwanƙwanto ya kawo. To! Saɓanin haka, sai ga shi a ƙunshiyar adabinmu na baka ana tsintuwar abubuwan da suka shafi kimiyyar ƙere-Ƙere tun ba a kai ga samuwarsu ba. Haka kuma,
ana samun abubuwan da suka kewaye duniyar mutane da ba su musantuwa a ko’ina ta
kowace fuska, a addinance, ko kimiyance, ko al’adance, babu binciken mai
bincike da zai ƙure su, bale ya musanta su. Na hango tunanin wasu sassan
karin maganan Bahaushe ya kakkamo su. Su nake son mu ɗan tsakuro domin a fara gwada su a
ga tsawonsu da faɗinsu.
Dabarar Bincike
Ƙudurin bincike shi zai ba da haske kan hanyoyin da za a
bi a tattaro kayan aikinsa. Dabara ta farko da aka bi ita ce, tattaunawa da
masana da ɗaliban ilmi da suka gogu kan adabi. Ta bakinsu an samu ayyukan da aka yi
kan karin magana da yawa. An samu kundayen bincike da takardun ilmi da aka
gabatar wurare daban-daban, wallafaffau da waɗanda ba a wallafa ba. An ziyarci ɗakunan karatu daban-daban domin kai
hannu ga ayyukan da aka yi. Haka kuma, an lalubo duniyar intanet da ƙibɗau da Wasap da Kafofin sadarwa na Hausa da yawo gidajen rediyo da Talabijin da
jaridu da mujallu sun agaza. Yunƙurin da aka yi ya sa aka samu
nasarar tattaro karin magana fiye da hamsin (50) da ke da saƙon game-duniya. An ci karo da sassan adabin baka fiye da hamsin (50) da
suka dace da tunanin karin maganan da aka samo. Daga nan aka bi dabarar yunƙurin karkasa karuruwan maganan bisa ƙunshiyarsu domin daidaita su a kan sikelin game duniya bisa ga tunanin
Bahaushe.
Hanyar Ɗora Bincike
Da gangan na kauce wa amfani da kalmar “ra’i" domin
ra’in ne muke son hawa matakan ƙago shi a farfajiyar karatun Hausa.
Da yake burina fito da shirin game duniya, watau nazarin gaskiyar ƙunshiyar karin maganan da suka yi wa duniya bugun goro a tunaninsu muna
son mu ga fassarar da ta dace da tunaninsu. Na yanke shawarar ɗora wannan bincike a kan fitaccen
karin magana da ke cewa: “Hantsi leƙa gidan kowa”. Na san akwai yankin
duniyar da sukan ɗauki watanni ba su ga rana ba, amma duk da haka, ranar da ta ɓullo wajensu gidan kowa ana
ganinta. Bahaushe ya ɗauki mafitar rana da faɗuwarta nan ne farko da ƙarshen duniyar mutane. Don haka
kowa ke zaune ƙarƙashin giragizai sai hasken rana ya ratse shi kuma sai ya
ratsi gidansa. A nan kalmar “kowa” ta cikin karin maganar ta haɗe duniya gaba ɗaya domin ba ta ba da tazarar rage
wani yanki nata ba. Haka nan ne karuruwan da ke kan gadon game-duniya suke
tafiya. Bisa wannan tunanin na ɗora tunanin nazarinsu, domin gano shin sun leƙa gidan kowa ko akwai gidan da ba su leƙa ba?
Fashin Baƙin Kalmomin Game-Duniya
Tunanin bincikena gano karin magana da ya game duniya a
karatun fasaharsa. Na farko na fara duba kalmar “komai/komi” da ta kasance
fitila cikin karin maganan: “Komi ya cika yana batsewa”. A nan kalmar “komai”
ba ta toge komai ba, don haka gama-gari ce ko mu kira ta game-duniya. Abin nufi
dai duk wani abu ya kai ga matuƙarsa, to ya gama yayinsa, abin da ya rage batsewarsa ya shiga kwandon tarihi. Kalmar “kowane” na da
irin wannan sigar idan muka dubi, “kowane gauta ja ne sai in bai ji rana ba”,
togiyar da aka yi kawai ita ce, wanda rana ba ta wa aiki ba. kalmar “kowane” ta
haɗe dukkanin gauta, kuma a ko’ina yake bangon duniya. Haka kuma kalmar
“kowa” ta cikin: “Kowa ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake”, ta game
dukkanin mutanen duniya. Bugu da ƙari, kalmar togiya ko koriya ta
“ba” ko “babu” suna wakiltar duniya cikin karin maganan: Babu mai nunin gidansu
da hannun hagu, da kuma “ba a mugun sarki sai mugun bafade”. Waɗannan kalmomin game-duniya suna
zuwa a:
a.
Farkon karin magana
b.
Tsakiyar karin magana
c.
Ƙarshen karin magana.
Abin nufi shi ne, in dai su sa karatunsu gaba su bayyana
a farko batu. In ko sun sa karatu tsaka su bayyana a
tsakiyar jimlar karin magana. In ko sun zo a ƙarshen bayani a yanke wa karatun da ya gabace su hukunci ya tabbatar na
game-duniya ne.
Mene ne Game-Duniya a
Fagen Nazari?
Duniyar ƙarninmu ta fito da shiri na
musamman da ake cewa: “Shirin Game-Duniya” har an yi digirin MA a kansa a
Jami’ar Bayero, (Chamo: ). Shiri ne da ya yi zurfi cikin
ilmin tattalin arziki da siyasa da al’ada, shi ya sa a Ingilishi suka ce manyan
rassa uku na shirin game-duniya su ne: Economic globalization, Political globalization
da Cultural globalization. A taƙaice “globalization” shi ne
“game-duniya”. A fassararsa sun ce:
Inglishi: Globalizationis the process by which ideas,
knoweldge
information, goods and services spread around the world.
www.techlitarget.com?definition>g...
Hausa: Shirin game-duniya shi ne wani
tsari na ɗora tunanin mutane, ko ilminsu,
ko wasu dabarun sadarwa ko ƙadarorin kasuwancinsu ko wasu
ayyukan hidimominsu za su bazu uwa duniya su game ta.
Fashin baƙin shirin game-duniya na farko
tunani da ra’ayoyin jama’a ya kawo. Abin ban sha’awa na biyu ya kawo “ilmi”, ya
ƙara mara masa baya da dabarun sadarwa. To! A nan kaɗai ya isa a ɗora karatun karin magana a faifan
nazari. Karin magana ingataccen tunanin ƙwararrun magabata ne da suka kwana
suka tashi cikin abubuwa da suka adana a karin magana. Ɗora tunaninsu ko ilmin da suka ƙunshe cikin karin magana, ko
fasahar da suka sadar da na baya da ita, da ba ta keɓanta ga mamaya gurbinsu kawai ba, a’a ta haɗe duniyar kowane ƙarni, muke son mu takuro mu ga yadda suka karɓi sunansu “globalization”
(game-duniya).
Mene ne Ra’i?
Ra’ai wasu taƙaitattun kalmomin masana ƙwararru ne da suka tsakuro bisa ga ƙwarewarsu da nacewarsu da
goggewarsu da ficensu cikin fannin da suka shahara. A taƙaice kalmar “Ra’i” a luga ita ce:
Ingilishi:
A brief policy, or procedure proposed or followed as the
basis of action. www.merriamwebsite.com.
Hausa:
Ra’i wata ‘yar ƙa’ida ce, ko wata hanya da aka zaɓa ko aka
bi a matsayin wata shimfiɗa ko hujjar da za a ɗora wani ƙuduri a kai”.
A wata taƙaitacciyar fassara an ce:
Ingilishi:
An idea or set of ideas that is intended to explain faces or
event (count) a widerly accepted scientific
theory.
www.britanica.com> dictionary.
Hausa:
Wani tunani ko tsarin wasu hasashe-hasashen tunani daban-
daban da aka ƙago bisa ga niyyar bayyana wasu
hujjojin ilmi ko wasu ayyuka. Ya kasance ya samu karɓuwa gama-gari bisa ga kimiyyar ƙunshiyarsa.
Waɗannan gajerun bayanai suna ƙoƙarin fayyace mana cewa, ra’i na da fassarori biyu: akwai fassarar luga wadda waɗannan fassarori biyu suka bayar. Da
an ambace su ko na bayan fage na hangen abin da aka nufa. A fagen nazarin
binciken ilmi ra’i na ɗaukar fassarar:
Ingilishi:
Theories are formulated to explain, predict and understand
phenomena and in many cases to challenge and extend
existing knowledge within the limits of critical boundign assumptions. The
theoretical framework in the strucure that can hold or support a theory of a
research study. libguides.usc.edu>writingguides.
Hausa:
Ra’o’i ƙirƙiro su ake yi domin yin bayanin wani abu, ko a yi
hasashensa kuma domin a fahimci wani tsari ko ƙuduri. Da yawa ana amfani da ra’i domin a ƙalubalanci wani abu ko a faɗaɗa ilmin da ake da shi bisa ga
tsarin tuƙewar nagartaccen hasashen da aka yi. Daidaita aiki a kan
ra’i shi ne tsarin da zai jagoranci ko ƙarfafa guiwar ra’in da aka ɗora bincike a kai.
Ra’i a ko’ina ƙirƙiro shi ake yi. Haka kuma da yawa
za a taras mutum ɗaya ya ƙirƙiro shi ba taron dangin masana fannin ba ne. Sai dai,
daidaitarsa ke sa masana fannin su mara masa baya domin cigaba, wasu
kuma su fanɗare. Masana sun ce ana son ra’i nagartacce ya ƙunshi abubuwa guda biyar tare da shi:
Ingilishi:
A good theory should be testable, be coherent, be economical,
be generalizable and explain known findings they serve
as primary fucntion of theory to be generative of new ideas and new
discoveries.
Hausa:
Nagartaccen ra’i dole ya kasance an yi an gani ya dace,
dogaggen abu, ya kasance taƙaitacce ko mai taƙaituwa ga bayaninsa, ya zamo gama-gari ga abin da yake
bayani. Haka kuma ya bayyana sanannun sakamakon da aka samu na sababbin
fahintoci da abubuwan cigaba sababbi da aka gano a ciki.
A taƙaice, ƙwararru ke ƙirƙiro ra’i. Haka kuma a koyaushe ana iya a ƙirƙiro shi daga cikin binciken da ake gudanarwa. Ba taron
dangi ake yi wajen ƙirƙiro shi ba, masanan da suka fara aiki da shi sun san
masanin da ya gabace su da shi tare da sanin irin ƙwarewarsa a kai. Duk da haka, sai an ɗora shi kan sikelin awon nauyinsa
da dacewarsa guda biyar. Idan ya kasa yin tangam! Kodaram! A kansu dole a
sake lale. A nan mun fahimci ra’i na tsufa, yana lali, ana wuce shi, ana kuma
jingine shi idan kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba. Ya kyautu ɗaliban ilmi su kula da wannan a
wajen sama wa ayukan bincikensu ra’i.
Laluben “Cika” da
“Batsewa” a Game-Duniyan Tunani
A nan ne zuciyar wannan bincike take domin duk karin
maganan da za a zaɓo dole yana da mafari ga abin da
Bahaushe ya sani, ya gani, ya karanta, ya ƙware da sanin cewa ga cikarsa ga
batsewarsa. Cikar da batsewar ana son ta kasance ta game-duniya, yadda take ga
Bahaushe haka nan take ga kowane mutum ko al’umma da ke doron ƙasa. Abin buƙata, shi ne, a samu cikarsa a kuma samu batsewarsa na haƙiƙa da bai musantuwa ƙarƙashin kowane ilmi ko bincike.
Laluben yadda aka ƙirƙiro tunanin da karin magana komi ya cika zai batse
tunanin ba na yau ba ne, ya fi ƙarfin na jiya, wataƙila ya zarce na shekaranjiya ban da jiya, ya tunkari zamanin halittar
Bahaushen farko a duniya. Don haka za mu fara laluben.
Matakan Raywuar
Bahaushe
Matakan raywuar Bahaushe “uku” ne, kuma kowanensu yana
kan ma’aunin karin maganan cika da batsewa. Matakan su ne: Aure, haihuwa, da
mutuwa. Daga cikin taƙaddamar masana al’ada na cewa, aure aka fara yi ko
haihuwa? Ni na goyu bayan aure aka fara yi don haka zan fara da aure in ɗora shi kan sikelin cika da
batsewa:
1)
Neman aure da bayar da shi da bukukuwansa duk suna ƙarƙashin inuwar kalmar “komai”.
2)
Tarewa gidan miji da aiwatar da hulɗoɗin aure su ne “cika” buri ya cika
an ɗaura an tare, an san juna, me ya rage?
3)
Samun saɓani da kace-na-ce alamomin batsewa
ne domin gabanin ƙulla auren ba su.
4)
Tsufa da zai rage ko kore ko hana
cigaba da hulɗar ƙurya batsewa ne.
5)
Mutuwar aure a rabu batsewa ne.
6)
Mutuwar miji ko mata batsewar cikar
aure ne.
Waɗannan abubuwa gama gari ne a duniyar mutane kuma auren kowace nahiya a
duniya yana tare da su ko da kuwa na tsuntsaye ne, da dabobbi, da itace. Ashe
karatun Bahaushen karin magana da ke cewa:
1)
Komai ke da farko yana da ƙarshe
2)
Komai adadinsa na tahowa
3)
Kowa ya ce, zo mu zauna,
ya ce, “zo mu saɓa”
4)
Ko tsakanin harshe da haƙora akan samu saɓani
5)
Yau da gobe ba ta bar komai
ba.
6)
Komai aka sa gaba ana ganin ƙarshensa
7)
Komai da lokacinsa.
Ga alama, waɗannan karuruwan magana da
makamantansu ba daga bakin ‘yan dagaji suka fito ba. Hausawa sun jarraba
aikinsu sun ga sun yi canjaras nashin ƙasa babu kure musamman a farfajiyar
zamantakewar aure. Wannan tunanin na Bahaushe game-dunya ne, babu ƙasar da ba haka nan suke ba.
Haihuwa
Ba zama ɗaya ake haihuwa ba, sai an tare an yarda da juna za a ɗauki ciki:
1)
Idan aka ɗauki ciki abin da ya cika ya fara
batsewa.
2)
Idan an haihu lafiya ya batse,
batsewar farko.
3)
Da jinjiran taka har zuwa
sadaukantaka batsewa ta biyu ke nan.
4)
Da an shiga matakin tsufa batsewar haƙiƙa ta bayyana.
Tunanin Bahaushe na cewa:
1)
Komai ya ruɓa yana wari
2)
Komai wayo ya ɓoye hankali na gano shi
3)
Komai nisan jifa ƙasa ta yi.
4)
Babu mai rai da ke tabbata a bangon ƙasa
5)
Yau da gobe sai Allah
6)
Babu mai wuce lokacinsa
7)
Kowa ya cin ma iyaka bai wucewa.
Duk
wani tunani na ƙage karin maganan game-duniya an same shi bayan da aka zo duniya, aka hau matakan rayuwa aka nazarci yadda
suke kasancewa. Ashe tunanin game-duniya a adabi ba gajeren tarihi gare shi ba.
Bayan da aka faɗo duniya aka zaune ta abubuwan da aka fara hulɗa da su ne yanayin sararin subhana
da halittun da ke tare da su, da farfajiyar ƙasar da ake kanta. Don haka, mataki
na biyu shi ne:
Duniyar Mutane
Duniyar da Bahaushe ya taras ya karance ta sosai a
karatun karin magana, kuma ya dace da wasu ababe da yake ganin sun gama duniyar
ko’ina. Daga cikin su akwai rana, wata, taurari, gizagizai, bakan gizo, tsawa,
ruwa, iska, sanyi, zafi, haske da duhu, ƙasa, tsirran da ke birbishinta da
sauran halittu.
i)
Fitowar rana ta kai tsakiya cikarta ne, faɗuwarta batsewa.
ii)
Fitar jinjirin wata zuwa tsakiyarsa cikarsa, ƙarshen batsewarsa.
iii)
Maƙurar rani watan bakwai bayyanar
damina batsewarsa.
iv)
Cikar damina malka (sarfa)
batsewarta ɗaukewar ruwan sama.
v)
Koguna da sun cika ga damina su yi
ambaliya sun batse
vi)
Tsirrai da sun yi fure sun cika, in ya kakkaɓe sun batse.
vii)
Itace da sun yi ‘ya’ya sun cika, in sun nuna sun faɗo sun batse.
Karatun ire-iren waɗannan halayyar abubuwan da ake rayuwa cikinsu yau da gobe ana tare da su juddadun
zawarcin jaka ya ba shi damar yin tunani a kansu. Da tunanin ya kasance na yau
da gobe, sai ya haifar da zantukan hikiman da za su taskace su, a matsayin
hikimomin game-duniya. Nazarci waɗannan karuruwan magana ka gani:
1)
Komi nisan dare gari zai waye
2)
Babu irin daren da jemage bai gani ba.
3)
Kowa ya ce, “duhu” bai ji zawo ba.
4)
Kowa ya ce, “duhu” ba a ɗaure shi ya kucce ba.
5)
Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta yi ƙarya.
6)
Hantsi leƙa gidan kowa.
7)
Kowa ya rena tsayuwar wata ya hau sama ya gyara.
8)
Nashin ƙasa babu kure.
9)
Ko Kwara tana da tsibiri
10)
Komai ya nutse ruwa a nemai ganga.
11)
Maras gaksiya ko cikin ruwa
ya yi jiɓi.
12)
Ruwan dare game duniya.
13)
Rana mai raba wa kowa aiki.
14)
In rana ta fito tafin hannu ba
ya kare ta.
15)
Ruwa ba sa tsamin banza.
16)
Ruwa suna gudu ake shan su, kowa ya sha na kwance ya sha gumɓa.
17)
Kowa ya samu rana ya shanya garinsa.
18)
Ƙarya fure take ba ta ‘ya’ya.
Batsewa a Halayen
Game-Duniya
Matakan rayuwar ɗan Adam zai fuskanci farfajiyar duniyar da zai rayu ciki a hau matakin ƙarshe “mutuwa”. Gaɓɓan jikin ɗan Adam a nan ne yake fara karatunsa na karin maganan game-duniya. Dalili
kuwa shi ne, za a ga:
i.
Ƙarfin jiki a koyaushe raguwa yake har sai an kai a
kwantas a tayar ko da babu wani rashin lafiya.
ii.
Ƙwazon gaɓɓan jiki na aiki musamman hannu da ƙafafu da gadon baya tun ana rarafe har a kai ga jan gindin.
iii.
Gaɓɓan sadarwa (baki), da na gani
(idanu), da na ji (kunnuwa), da na shaƙe (hanci), za su kai ga batsewar ba sa ayyukansu.
iv.
Kaifin hankali da wayo su fara
batsewa wauta da taɓuwar hankali su kusato.
v.
Ficen da aka yi na suna da ɗaukaka ya batse a yi kamar ba a yi
mutum ba a duniya.
Waɗannan arkane da rayuwar ɗan Adam ke fuskanta suke haifar da wasu fitattun
karuruwan magana daga ƙwararrun da suka ga jiya da yau, tunaninsu ya game
duniyar zamaninsu da wadda ta gabace su, suka yi wa waɗanda ke tafe kashedi. Daga cikin
karatun da waɗannan halayen game-duniya suka bayar akwai:
1)
Komai na jiran lokacinsa.
2)
Komai ya cika zai batse
3)
A kwana a tashi ba ta bar komai ba.
4)
Duniya budurwar wawa
5)
Komai ya ba ka tsoro sai ya ba ka
tausai
6)
Komai ke da lokaci ya ƙare.
7)
Ƙarshen tika-tika tik!
8)
Ba a tsohon banza sai da ƙuruciyar banza.
9)
Ta yaro kyau take ba ta ƙarko.
10)
Abin da babba ya hango a zaune, yaro ko ya daka tsalle ba zai hango ba.
11)
Wanda duk ya riga ka barci yana
rigayarka hanzari (binsheri)
Tunanin da ke ƙunshe cikin ire-iren waɗannan karin magana na batsewa ga ƙirar halitta aka fara karatunsu. Kowace halitta lokacin cika da batsewa
gare ta. Lura da cewa a rasa wani yau, gobe a rasa wani, jibi a rasa wasu, ya
sa aka gane a kwana a tashi ba ta bar kowa ba. A tunanin Bahaushe wawa kaɗai ne bai san halin duniya na ɗauka da ajewa ba. Komai ɗaukakar mutum a bangon ƙasa akwai zamanin da ba irin tasu ake yi, an wuce su, lokacinsu ya riga ya
cika ya batse. Kowa a halin yaranta ya fara irin tasa rayuwa, batsewarsa tsufa.
Makaɗa Bawa Ɗan’anace ‘Yartsakuwa ya yi fashin baƙin wannan fasali haka:
Jagora : Wada duk duniyag ga tai mini daɗi,
: Sai duniyar ga
tai mini ɗwaci,
: Wallai watan wata rana,
: Waɗansu ne ba mu ba,
: Walau mun mace, walau tsohewa.
: Kai ko akwai mu, ba mu da ƙarhi.
Yara : Wallai watan rana
: Sai a rarrabe muna kaya.
(Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Waƙar Shago).
Diddigin Ma’aunin
Cika da Batsewa a Al’adance
Ma’auni a wajen Bahaushe yana da fassarori da yawa. Na
farko akwai ma’aunin hankali wanda za a auna abu da yadda aka san wasu abubuwa
makamantansa. Na biyu, akwai ma’aunin zaɓi da Bahaushe ke cewa kama da wane
ba wane ba ne. Wannan ma’aunin ya ƙunshi awo, da ƙima, na tsawo, da faɗi, da rinjaye, da jimiri, da dacewa da akasinsa. Na uku, akwai ma’aunin
Bahaushe na mazubi na zahiri da yake aune-aunen abincinsa da abin shansa da kuma kayan aikinsa irin su:
-
Tulu
-
Randa
-
Masaki
-
Zakka
-
Taiki
-
Lato
-
Buhu
-
Ƙwarya
-
Salka
-
Tukunya
-
Gora
-
Mangala
-
Wasaki
-
Ƙoƙo
-
Gidauniya
-
Kumbu
-
Kasko
-
Shantali
-
Jigo
-
Moɗa
-
Ludayi
-
Kuyafa
-
Akushi
Ga alama, waɗannan ma’aunai na gargajiya su suka
yi tasiri wajen ƙago “komai ya cika zai batse”. Abin sani shi ne,
ma’aunai ne na ruwa da tsaba. Duk abin da yake ruwa-ruwa ko tsaba ko ƙwara idan aka cika shi ya yi soro zai batse ya darje ya fara zuba ƙasa. Zuban da zai yi a ƙasa shi ne batsewarsa. A ganin
Bahaushe, ruwa da ruwa-ruwa kaɗai za a auna a ma’auni ba su yi
soro ba. Don haka, su, ba sa batsewa. Wannan shi ya sa Bahaushe ya kasa awo
gida biyu. Akwai awon ruwa da awon gurori. Waɗannan abubuwa su suka assasa
hikimomin:
Komi ya cika zai
batse.
Ido mudu ne ko bai ci ba ya san abin da ke cika
masa tumbi.
Tilas mai awon ruwa ya yi babban masaki.
Rabe-Raben Lafuzan Karin
Maganan Game-Duniya
A tsarin nahawun karin maganan Game-duniya akwai
kalmomin da ke bayyana a ciki da ke ba da haske ga kadadar da suka dosa. Za a
ga kalmomin da suka shahara ga bayyana ciki akwai:
i.
Komai: Ta haɗe komai da komai na duniyar da ake
zance.
ii.
Kowanne: Tana nuni ga ɗaiɗaikun abubuwan da ake zance.
iii.
Kowa: Tana zance ga mutum ɗaya da masu kama da shi a ko’ina
suke duniya.
iv.
Duk: Ta haɗa komai babu ragi ga abin da ta ƙunsa
v.
Babu: Koriya ce, ta nuna kaɗaici ga jigon da take zance.
vi.
Ko: Togiya ce mai keɓance wani abu na game-duniya.
vii.
Ko’ina: Babu zaɓi ga bagire kan abin da ake zance a duniya.
Nazarin da na yi wa ƙirar kalmomin karin magana
game-duniya, ya nuna akwai buƙatar a fayyace da me suka game
duniya? Gano haka ba ta kasance ba, sai an shiga fiɗar irin lafazin kalmomin da ke ƙunshe cikinsu. Ga yadda tsarin ya kasance:
Komai
Komai ya haɗa da komai da komai kuma bai bar
komai waje ba. Wannan sigar ta fi shafuwar al’amurran duniya gaba ɗaya da Bahaushe ya nazarta cikin
tsanaki ya ilmantu da su sosai ya yanke musu hukuncin game-duniya.
1)
Komai nisan dare gari zai waye
2)
Komai nisan jifa ƙasa tay yo
3)
Komai ya ruɓa zai yi wari
4)
Komai ya nutse ruwa a tarbe shi ganga.
5)
Komai saurin Larba tana barin Talata ta wuce
6)
Komai ake yi da jaki sai ya ci kara
7)
Komai da lokacinsa
8)
In an ce Allah ba a cewa komai.
9)
Abin da bai zo don rai ba, ba ya wa rai komai
10)
Haƙuri na ganin ƙarshen komai
11)
Yau da gobe ba ta bar komai
ba.
Waɗannan misalai sun game duniyar mutane gaba ɗaya. Haka kuma, tantagaryar gaskiya
suka feɗe a saƙonsu ba ya musantuwa ko ƙaryatuwa ko’ina. Fitattun karin
magana ne da Hausawa suka yi tarayya a ƙunshiyarsu. Bayyanar “komai” a farkonsu yana tabbatar da abin da zai biyo bayansa.
Kasancewar kalmar “komai” a ƙarshen saƙon kwakkwafe bayanin saƙon yake yi. Babu saɓani waɗannan karin magana suna magana da
duniyar mutane gaba ɗaya, ƙunshiyarsu tana tabbatuwa a ko’ina duniya.
Kowanne
Shi ma game-duniya ne amma yana tsittsinto wasu abubuwan
da yake son ya ware su ko ya yi garkuwa domin shi tsintso karan gwajin dahinsa
ya yi, ya kuma nuna su, aka gan su ƙuru-ƙuru. Ga yadda yake cewa:
1)
Kowane bakin wuta da irin nasa hayaƙi
2)
Kowane gauta ja ne, sai in bai ji rana ba.
3)
Kowane Fir’auna da nasa Musa
4)
Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi
5)
Kowace ƙwarya da abokiyar ɓurminta
6)
Kowane allazi da nasa amanu
Ga alama wannan rukunin a farkon saƙon kalmar “kowanne/ kowace” ke bayyana ya sa saƙo gaba ya tabbatar da shi a game-duniya. Wannan rukunin ya fi kula da
abubuwan rayuwa da sassauyawarsu. Ya tsakuro abubuwan da yake son ya game
duniya da su, su kaɗai. Idan muka nazarce su za mu ga gaskiya ce, domin haka suke a al’adance
a duniyar mutane.
Kowa
Tana zance ga mutum ɗaya. zancenta ba a kanshi kawai ta
tsaya ba, na zance ne ga duk wani irinsa a bangon duniya don haka ta kasance,
game-duniya. Daga cikin karatun akwai:
1)
Kowa am mutum mutane ne shi
2)
Kowa ya ce: “Ya ce”, sai ya ce: “Bai ce ba”.
3)
Kowa da bukin zuciyarsa maƙwabcin mai akuya ya sai kura
4)
Kowa ya ɗebo da zafi bakinsa.
5)
Kowa ya ce: “bai iya kuka ba”, uwarsa ce ba ta mutu ba.
6)
Kowa ya yi zagi a kasuwa, ya san da wanda yake
7)
Kowa ya ci zomo ya ci gudu
8)
Kowa ya yi ƙarya ana samun ɗan garinsu.
9)
Kowa ya ƙi noma yana awo
10)
Kowa ab bai ji bari ba, ya ji hoho
11)
Kowa ya faɗi kansa yake yi wa nishi
12)
Bashi hanji ne yana cikin cikin kowa.
13)
Gidan kowa ba a rasa ɓara gurbi
14)
Amshi ba ta bar kowa ba.
15)
Rana mai raba wa kowa aiki.
16)
Hantsi leƙa gidan kowa.
17)
Shege kowa ya yi.
A kowane sashen na saƙon “kowa” na zuwa. Ana samunta a
farko, ko tsakiya, ko ƙarshe. In ta zo a farko ta sa saƙon gaba ta tabbatar da shi. In ta zo a tsakiya ta girgije saƙon ya tabbata kan kowa. In ta zo ƙarshe ta tababta saƙon da ta goyo. Za a ga tana kula da ɗaiɗaikun mutane kawai amma ta game
jinsinsu a duniyar zamanin da take magana. Haka kuma saƙon za a taras babu ƙarya a ciki sai dai can ba a rasa ba a samu masu buƙatar ƙarin bayani kamar na (17).
Duk
Kalma ce da ke nufin tarsashin abu dukkaninsa ba a toge
komai ba. Tana aiki irin aikin “komai” cikin karin maganan game-duniya. Ga ɗan misali:
1.
Mai rai duk na duniya yana son daɗi.
2.
Duk wurin da aka hau icce nan ake
sauka.
3.
Mutum duk ɗan tara ne
4.
Duk ɗaya makafi sun yi dare
5.
Ba a taruwa duk a zama iri ɗaya.
6.
Duk wurin da ka sha furar shinkafa
nan ne kabi gare ka.
7.
Duk duniya in ji babban mahaukaci.
8.
Duk ɗai ga baba in ji agola.
Kalmar “duk” ba ta rage komai ba, don haka, da duniya take magana dole a saurara mata. A matsayin goma na turken
ƙidayar Bahaushe kuma cika cicciccif babu mutumin da za a
ce, ya tara dukkanin kamala da ake so ga ɗan Adam, dole a sami wani ɗan cikas na kasawa. Haka ce ta sa aka ce, “mutum duk ɗan tara ne bai cika goma ba” kalmar
“duk” a nan ta game duniya. Don haka karin
magana da ke ɗauke da kalmar “duk” game-duniya ne, ga abin da yake magana a kai.
Babu
Kore abu ne gaba ɗaya. Idan ta bayyana a karin magana
takan zo gaba ɗaya da “babu” ko “ba” ko “ba a” ko “ba ta” duk ɗaya ne cikin ƙumshiyar karin maganan game-duniya. Idan aka dubi waɗannan zantuka za a ga hasken abin
da ake son bayyanawa:
1)
Babu mai nunin gidansu da hannun hagu.
2)
Babu irin daren da jemage bai gani ba.
3)
Babu maraya sai raggo.
4)
Baya ba ta da kaɗan.
5)
Tusa ba ta hura wuta.
6)
Gaskiya ba ta neman ado.
7)
Waƙa ɗaya ba ta kai safe.
8)
Shure-shure ba ya hana mutuwa.
9)
Na shiga ban ɗauka ba, ba ta fid da ɓarawo.
10)
Yaro bai yi kamar babba ba.
11)
Maɗi bai kai ga zuma ba.
12)
Ba ta da filin gyara, mai neman beli ya mari uwar Alƙali.
13)
Ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare.
14)
Lokaci ba ya jira.
15)
Ba a magaji da yaro ba a yi da tsohon banza.
16)
Ba a gudu da susar baya.
17)
Taura biyu ba su haɗuwa a baki ɗaya.
18)
Sannu ba ta hana zuwa, sai
dai a daɗe ba a je ba.
19)
Barewa ba ta gudu ɗanta ya yi rarahe.
Nazarin waɗannan zantuka cikin natsuwa zai
lurar da mu cewa, maƙagan karin magana ƙwararru ne kuma gogaggu ga maganganun da suke ƙagawa. A taƙaice karin maganan nan guda (19) suna kore wasu abubuwa
da duniyar mutane ta tabbata korarru ne, kuma suka tabbatar da abin da duniya
ta tabbatar a bayyane ko a kaikaice. Da za a kalli karin maganan farko za a ga
yana ƙoƙarin ya:
-
Jaddada kishin ƙasa.
-
Kishin kai.
-
Soyayyar zumunci.
-
Girmama iyaye.
-
Naka shi ne naka, na wani ba naka
ba ne.
-
Babu kamar gida ga mutum.
-
Girmama mafari/tushe dole ne.
Don haka karin maganan ya kama hankulan mutuanen duniya
wanda ya ba shi matsayin game duniya. Kowannensu aka yi wa fasalin kansa za a
same shi haka nan. Dalili kuwa babu ƙasar duniya da ake hura wuta da
tusa. Ba mu taɓa jin adabin wasu mutane da ya kira yaro babba ba. Wa lokaci ya taɓa jira a tarihi? Yadda ‘ya’yan
taura ba sa haɗuwa a baki ɗaya a ci su, haka in lalurar gudu da susan baya suka riski mutum
dole ya tsaya ya yi wani abu mai zaƙi baya ga zuma yake.
Ko
A nahawu wasu lokuta tana nuna ƙololuwar abu, a wasu lokuta ta nuna zaɓi, a wasu lokuta ta zo da shawara
ga su nan dai. Duk yadda makaɗa Dr. Ibrahim Narambaɗa ya sarrafa “ko” a matsayin “ƙololuwar abu/tuƙe shi” a waƙar Dokin Iska yana cewa:
Jagora: Sa akawal sa hurde sa Didi
Yara : Ba a gama su da Ɗanhilinge
Jagora: Ko alsan bai kai kamatai ba
Yara : Don ya samu jiki fari fes!
Gindi: Ɗan Malam ci ƙwallo sarkin gudu
: Na yarda da Ɗanhilinge.
(Dr. Ibrahim Narambaɗa: Waƙar Doki Ɗanhilinge)
Alsan shi ne ƙoli ga tunanin kamancen dawakin
duniya ƙasar Hausa, don haka ya zo da zancen “ko”. A duniyar
jaruntaka “soja” ne na ƙarshe, makaɗa Gambo Fagada ya auna tauraronsa
Manu Dahi da cewa ya fi ƙarfin fuskantar bataliyarsu ya ce:
Jagora: Ko bataliyas soja tas shiga daji
: In gaya maka
Manu Dahi na ɗan taya ta.
(Gambo Fagada: Waƙar Manu Dahi).
Wasu sassan karin magana masu zuwa da kalmar “ko” da ke
nuna kasancewarsu game duniya sun haɗa da:
1)
Ko ba a gwada ba linzami ya fi
bakin kaza.
2)
Ko ba magana a tsura ido ya ishi
mai hankali.
3)
Ko an ci birnin kura, ba a ba kare
hakimci.
4)
Ko baba da babansa.
5)
Ko masa ta lalace ta fi kashin
shanu.
6)
Ko akuya aka matsa wa tana cizo.
7)
Ko ba a faɗa ba, sunan mijin iya baba.
8)
Ko ba lagwani fitilar sharri na kai
safe.
9)
Ko da ganin kan kura ya ci mutum.
10)
Ko Kwara tana da tsibiri.
Kasancewar abu gama gari shi zai ba shi darajar game
duniyar mutane. A ko’ina ake da dawakai da kaji an san ba a ɗora linzami ga bakin kaza domin ya fi ƙarfinta. A duniya babu kazar da
bakinta ke iya ɗaukar linzami. Kowa aka tsura wa ido zugum! Ba ce masa uffan ba, ko harshe
da launin fata ba iri ɗaya ba ne dole mutum ya shiga taitayinsa. Cin birnin kura da yaƙi ba ya ba kare natsuwar leƙa garin bale a ba shi sarautar hakimcin garin ya karɓa. Wada duk aka ce wa baba a ko’ina
duniya, shi ma yana da baban da ya haife shi. Gaskiyar da ke bayyana a waɗannan karuruwan magana da game
duniya da ilminsu ya yi shi ya ɗora su a martabar game duniya.
Ko’ina
Ko’ina ba ta rage komai ba kamar kowa” ce da “komai”, sai
dai ita bagire da muhalli da wuri da sarari take tunkara. Fitattu daga cikin
ire-iren waɗanan karin amgana akwai:
1)
Ko’ina aka ga hanya gida ta nufa.
2)
Ko’ina ga homa (koma) ƙulli.
3)
Ko’ina ka sha furar shinkafa nan ne Kabi gare ka.
4)
Ko’ina ta faɗi rataya.
5)
Mugu ko’ina ana saunar ka.
6)
Ruɗani ba ka ko’ina, amma ko’ina da labarin ka.
Cika da Batsewa a
Tunanin Karin Magana Game-Duniya
Cika da batsewa a tunanin Bahaushe ya game komai da ke a
birbishin bangon ƙasa. Yadda Bahaushe ya karanci duniyar da ya samu kansa
ciki da matakan rayuwarsa nan ne tunanin ya tsira aka taskace shi cikin karin
magana. Abubuwan da muka yi nazari a ƙunshiyar karin maganan game-duniya
idan muka auna karatunsu da tunanin: “Komai ya cika zai batse” za mu ga suna da
alaƙa ta ƙuƙut. Idan muka kalle su sosai za mu
ga:
i.
Suna zance ne kan duniyar mutane
gaba ɗaya face abin da suka toge.
ii.
Na biyu, game-duniya da suka yi ga
karatunsu za a ga kai ƙololuwar abin da suke zance ne wanda daga nan sai
“batsewa”.
iii.
Na uku, abin ban sha’awa za a ga
abubuwan da suka tuƙe gaskiyar abin ke nan, wanda duk ya san shi ko ya
karance shi, ko ya kasance cikinsa ba zai musanta shi ba.
iv.
Na huɗu za mu ga, sun hau gadon feɗe fassarar game-duniya domin:
a)
Fitattua ne a ko’ina.
b)
Gaskiya ce tantagaryarta.
c)
An jarraba sun yi.
d)
Sun taƙaitu ga bagiren da ko’ina aka rawaya haka yake.
Nazari
Bari mu ɗauki karan gwajin dahinmu “komai ya cika zai batse”. Za
mu ga a karatunsa abubuwa da yawa za a tsinta da za su tabbatar da hasashen
wannan bincike. Na farko, kalmar “komai” ba ta rage komai ba. Haka kuma ba ta
rage wani bagire a bangon duniya ba. Nazarin karin maganan zai kasance:
1)
Cika na ɗaukar fassarori biyu. Fassara ta
farko wadda al’ada ta tababtar na awon abu ruwa-ruwa ko tsaba ko waninsu. Da
zarar ma’aunin da ake awonsu ya cika batsewa zai yi ya dinga zuba ƙasa. Duk abin da ake awo a duniyar mutane in dai cikin mazubin ma’auni
yake, haka yake kasancewa.
2)
Abin lura na biyu shi ne, komai na
da ma’auninsa. Ma’aunin abu shi ne tuƙewarsa. Ke nan abin da ba da
ma’auni ake awonsa ba, lokaci ko yanayi ke awonsa hankali na gane cika da
batsewarsa. To, wannan ita ce doguwar fassara ƙungiyar karin magana, idan yaranci
ne akwai tsufa, idan tsufa ne akwai mutuwa, idan mulki ne akwai ƙarshe, idan samu ne akwai matuƙa, ga su nan dai.
3)
Abu na uku shi ne kalmar “komai” ta
faɗaɗa karatun da yawa. Ta kewaye abin da ake ciki, da mai zuwa, wanda aka sani
da wanda ba a sani ba, wanda ya taɓa faruwa da wanda bai taɓa faruwa ba. Ashe idan haka ne ƙofar gina “RA’I” ta samu sai dogewa da bincike domin a samu nagartacciyar matsaya da sunan da ya dace a raɗa mata.
4)
Zance komai ya cika yana batsewa,
sananne ne a duniyar adabin Hausa. Haka kuma jarrababbe
ne a matakan rayuwar Bahaushe da abubuwan da ke bayyana a zahiri jiya da yau.
Zancen musu ko gardama da karatunsa bai taso ba. Haka nan yake kuma tabbatacce
ne haka.
5)
An taƙaita ƙunshiyar karatun cikin kalmomi uku
kacal: “komai”, “cika” da “batse”. Ya samu turke daga cikin turakun gina ra’i
ga masu da’awar ra’i cewa ya kasance mai “taƙaitattun” kalmomi.
Ma’aunin Cika da
Batsewa a Mizanin Kairn Magana
A tsarin rayuwar mutanen duniya babu abin da ba ya da
lokaci don haka karin magana game-duniya ke cewa, “komai na da lokacinsa”.
Ma’aunin cika da batsewar abubuwan duniya huɗu ne a al’adance:
i.
Farkon abu: Assasa tubalinsa
ii.
Tsakiya abu: Daidaitarsa
iii.
Ƙarshen abu: Kai matuƙarsa
iv.
Batsewarsa: Rugujewarsa na ƙarewar lokacinsa.
v.
Mayar da gami: Ga abubuwan da ke da
lokacin sake yunƙuri.
Waɗannan abubuwa biyar idan aka nazarce su sosai za a ga sun fassara “komai ya cika zai batse”. Abin lura, “batsewa” ba ta rufe ƙofar sake yunƙuri ba ga abin da ya batse in ba na kan ma’auni ba ne. Na kan ma’auni ne
idan ya zuba ba za ai tunanin sake mayar da shi cikin
ma’auninsa ya tsaya ba. Karin maganan cewa ya yi “komai” don haka ya hakkamo
abubuwa da yawa. Ma’aunin da za a kula da shi na fassarar “komai”
ya kasance game-duniya shi ne:
i.
Halittar ɗan Adam rayuwarsa zuwa mutuwarsa.
ii.
Abin da, ko abubuwan da ɗan Adam zai samu ko za su same shi.
iii.
Halittun sararin Subhana da ke
aikin da muke kallo dare da rana.
iv.
Yanayin duniyar da muke ciki huɗu: Bazara, hunturu, rani da damina.
v.
Halittun da muke rayuwa a duniya
tare da su na dabbobi da ƙwari da tsuntsaye da tsirrai.
Waɗannan abubuwa biyar su ne ƙididdigar abubuwan da duniyar mutane ta ƙunsa, a karatun karin magana su ne
“komai”. Haka kuma, su ne ke cika da batsewa. Dalili kuwa, duk abin da ke ƙarƙashin giragizai daga abin da aka halitta sai abin da
halittu suka ƙago. Abubuwan da ke sararin Subhana hulɗar nesa da nesa ce tsakaninsu da
‘yan Adam, don haka karatun halayyarsu da ake hange ya sa suka hau
doron komai ya cika yana batsewa. Mu ɗauki misalin itace masu ‘ya’ya
kamar ɗunya:
a)
Za ta tsiro : Farkonta.
b)
Ta girma ta tsayu : Bunƙasarta.
c)
Ta yi fure : Tsakiyarta.
d)
Ta yi ‘ya’ya : Cikarta.
e)
Su nuna su faɗo ƙasa : Batsewarta.
f)
Ta sufa ta rushe : Batsewarta.
g)
‘Ya’yanta su sake tsirowa : Mayar da gami.
Duba zuwa ga waɗannan matakai ga ɗan Adam da tsirrai da sauran
halittu da muke raye tare da su, za mu ga ashe zance ne karin maganan Bahaushe da ke cewa:
Komi ke da farko yana da ƙarshe.
Yau da gobe ba ta bar komai ba.
Komai na jiran lokacinsa.
Da dai makamantansu da aka yanke wa hukuncin game
duniya, duk wani al’amari na duniya aka ɗora kansu za su zauna daram ba da
musu ba.
Sakamakon Bincike
Sanin cewa, Bahaushe bai yarda a ce, an game duniya da sani
ba, ya sa, idan zai yi zancen da yake ganin ya kusa ya zama game duniya sai ya ce, bari in yi na babban
mahaukaci, wato ba ko ƙaramin mahaukaci ba. Saɓanin haka, sai ga shi a cikin karuruwan magana fitattu, gama gari, amintattu, jarrababbu
a ƙunshiyar saƙonsu Bahaushe na game duniya a
cikinsu. Idan aka nazarci game-duniyan da ke cikinsu sai a ga lallai sun game
duniya a ilmance da hankalce. Wannan ya tabbatar da cewa, komai ya cika zai batse, tunanin Bahaushe ne ba a game duniya ga magana
ya tsufa, ya cika, ya kuma batse da samuwar waɗannan karuruwan magana da suka daɗe a bakunan magabata. Wannan bincike ya ci nasarar sama wa karin magana
game duniya gadon feɗe shi da tace shi da tantance shi. Cikin haka ya tabbatar da ingancin
karin maganan “komai ya cika zai batse”. Daga cikin nasarorin
da nake ganin wannan bincike ya ci, shi ne gano karin maganan game-duniya sun hau matakai biyar da masana suka ce su ne, sifofin
ingataccen ra’i dole duk ra’i ya hau su cif-da-cif. To samun wannan dacewa da
bincike ya yi yake neman ku kira da cewa:
Babu cigaban da ya fi mutane su dinga auna cigabansu da
cigaban waɗanda aka ce sun ci gaba da burin cikawa da su. In dai sassan wasu fitattun
karuruwna magananmu sun yi kunnen doki da ƙa’idojin da masana ra’i suka ɗaura ra’i, to babu laifi mu fara
tunanin inganta su da faɗaɗa su da yi musu zaman kansu na yiyuwar ɗora ayyukanmu na ilmi a kansu.
Naɗewa
Wannan bincike yunƙuri ne na gabatar da ƙorafi domin a taru a ga mafitar al’amari. Takensa na “Ra’in Game-duniya” ƙuduri ne na ƙyallaro ire-iren karatun karin magana da suka game
duniya ga saƙonsu. Buri shi ne, a tabbatar da cewa, shin saƙon nasu ya gama duniya ga gaskiyar karatunsa? Shin karuruwan fitattu ne a
duniyar masu harshe? Ko ƙunshiyar karatun ya game duniya a haƙiƙa? Samun tabbacin haka ya sa ake son a sake mayar da
hankali ga adabin karin magana domin an bar tazarar bincike mai yawa da ke son
a sake nazari. Ɗan yunƙurin da binciken ya yi na samar da
sunan “karin magana game-duniya” yana son a sake bitar sa ko akwai wani sunan
da ya fi shi dacewa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.