Ticker

6/recent/ticker-posts

Salo Asirin Waka na Farfesa Abdullahi Bayero Yahya [05 - Shafukan Babi Na Huɗu]

 Salo Asirin Waƙa

Salo Asirin Waƙa

Salo Asirin Waƙa
 

BABI NA HUƊU

Nau’o’in Salo

Mun riga mun lura da cewa salo a filin waƙa wani irin kandamin fage ne. Kandami ne saboda kusan a ce kowane furuci a cikin waƙa yana cikin nau’i na salo. Haka kuma kandami ne saboda koyaushe mawaƙi yake ƙirƙirar waƙa mai yiwuwa ne ya zo da wani irin salo wanda a da ba a taɓa lura da shi ba. Wato ke nan a duk lokacin da aka zo yin nazarin waƙa dole ne idanunmu su zamo a buɗe, saboda watakila mu ci karo da wani salo da ba mu san da shi ba.

A kan haka ne ake jan hankalin mai karatu da cewa kada ya ɗauka cewa wannan littafi ya ƙunshi dukan nau’o’in salo. Abin da ya yi ƙoƙarin yi kurum shi ne yin bayani kan sanannun nau’o’in salo da kuma wasu da ba a ambata sosai da sosai ba.

 

Salon Siffantawa Da Nau’o’insa

Za a fara da salon siffantawa saboda dalili biyu. Da farko, shi dai wannan salo yana da nau’o’i da dama kuma masu fice a kai a kai cikin waƙoƙin Hausa. Dalili na biyu shi ne ganin cewa babu zuƙu idan aka ce mawaƙi bai yi sai da salon siffantawa[20]. Wato a ce mawaƙi ya kauce wa wannan salo wajen tsara waƙarsa, to idan ba a ce bai yiwuwa ba, to kuwa tilas a ce an tauye mawaƙin ne aka yi. Dubi abin da Bahaushe ke nufi da ‘baza’ a cikin kalaminsa, ‘Da bazaar wane yake rawa’, to kamar haka ne salon siffantawa yake ga mawaƙa. Shi ne bazarsu. Duk wata burgewa, duk wata iyawa ta isar da saƙo a cikin waƙa, duk wata fasaha a cikin waƙa, ta fi kammala idan salon siffantawa ya taka rawa sosai a cikin waƙa. Yi ƙoƙarin ka hana mawaƙi amfani da salon siffantawa, take ne za ka gane shi yana kikkimsa waƙa, ko aƙalla waƙarsa ta yi kusa da zama lami, marar armashi. To yanzu shin mene ne ake nufi da salon siffantawa a cikin waƙa. Ana iya a bayyana shi kamar haka:

Salon siffantawa faffaɗan salo ne da ya tara surori ko sifofi da mawaƙi yake bayyana abu, salo ne da ke kawo hoton abu yadda mawaƙi ke bukatar mai karatu ko sauraren waƙarsa ya kalle shi da idon zuciyarsa ko tunaninsa, salon siffantawa hoto ne da kalmomi suka kawo da cikin ma’anoninsu.

 

Shi wannan salo yana da nau’o’i da dama waɗanda muhimmai daga cikinsu su ne kinaya da kamance da jinsarwa da zayyana da alamtarwa.

a) Kinaya

Kiran abu, musamman mutum da sunan da ba shi ne nasa da aka san shi da shi ba, domin wannan suna ya bayar da ma’anarsa da kuma tunanin da ma’anar za ta kawo zuwa ga wanda aka kira da wannan suna, wannan shi ake kira salon kinaya. Salo ne wanda ake yin amfani da kalma ko kalmomi domin tunanin da suke sa mutum ya yi game da ma’anoninsu ya nashe ko ya lulluɓe wani abu ko mutumin da aka danganta kalmomin gare shi. Wato sanin da mai saurare ko karatun waƙa yake da danagane da sifofin abin da kalmar da aka yi kinaya da ita zai wulla zuwa ga wanda aka yi wa kinayar. Wannan kuwa shi zai sa mai karatu ko jin waƙa ya fahimci siffar da mawaƙi yake son a san ko a kalli wanda ya yi wa kinayar.

Idan ka kira abokinka, Yunus da sunan zaki amma sai wani ya ce ai abokin nan naka damisa ne, to kowanenku ya yi amfani da salon kinaya, amma fa kowamenku da tasa ma’ana ta daban. Kai dai kana son a kalli Yunus a matsayin mazakkari, namiji, wanda bai da tsoro kuma a ko’ina ya shiga shi ne babba wanda ake jin tsoro. Wannan shi ne abin da kalmar zaki kan kawo ga tunanin mai sauraren ka kuma da wannan tunani ne zai kalli Yunus. Shi kuwa wancan da ya ce abokinka damisa ne, yana son a kalli Yunus da tunanin cewa Yunus mutum ne wanda ba a taɓa sabo da shi, kome kuwa sanin da kuka yi wa juna, ba zai taɓa amincewa da kai ba kuma ba za ku taɓa zama aminan juna ba, duk kuwa yadda ka so ko ka yi ƙoƙarin wanzar da hakan. Da waɗannan ire-iren tunani ne Hausawa ke kallon zaki da damisa da su, kuma da su ne mawaƙa kan gina salon kinaya cikin waƙoƙinsu.

Wannan misali ya nuna mana cewa ashe kullum ne akan samu salon kinaya cikin hulɗar da muke yi da juna. Saboda zama jikin da wannan salo ya yi gare mu shi ya sa har ba mu saurin lura da shi. To amma shi mawaƙi ya kwana da sanin muhimmancin wannan salo wajen ayyana yadda abu yake ba tare da kawo wata rashin fahimta ba. Saboda haka ne yakan yi matuƙar amfani da shi. Ba za mu fasa sake kawo misalin nan ba na cikin waƙar Haliru Wurno inda yake cewa:

Ga ruwa gulbi ban zuwa tabki

Ga akwatina ban biɗar danki

Ga masallaci ban biɗar gumki

Ba ni cin gwaza ga su alkaki

Tela riga tun bara nib bar ta

 (Alƙali Haliru Wurno: Safiya Da Gaskiya Taka Aiki)

 

Waƙar da wannan misali ya fito daga gare ta waƙa ce ta yabon Sarkin Musulmi Abubakar Na III. Saboda haka a wannan baiti muna iya lura da cewa mutane biyu ne Haliru ya yi wa kinaya. Mutum na farko shi ne gwarzonsa, wato Sarkin Musulmi. Mutum na biyu kuwa ‘ya’yan sarauta ne masu haƙƙin su nemi sarautar Sarkin Musulmi idan ta faɗi, ko kuma wasu sarakuna waɗanda Haliru bai faɗa mana sunayensu ba. Duk waɗannan kan shiga cikin mutum na biyu da mawaƙin ya yi wa kinaya. To, idan aka yi la’akari da wannan bayani sai mu ga muna iya fitar da kinayar da ke wajen Sarkin Musulmi da kuma wadda ke wajen waɗannan mutane, wato jinin sarautar ko wasu sarakuna. Bari mu yi hakan dalla-dalla:

 

 ‘Ya’yan sarauta masu jiran

 Sarkin Musulmi Sarautar Sarkin Musulmi

Gulbi

Tabki

Akwati

Danki

Masallaci

Gumki

Alkaki

Gwaza

 

A yayin da Haliru ya yabi Sarkin Musulmi ta amfani da salon kinaya sai kuma ya yi wa abokan hamayyar Sarkin Musulmi zambo ta amfani da salon. Sarkin Musulmi shi ke ƙwad da kowa ya zo wurinsa ba tare da wata alama ta raguwa ba. Kowa ya je wurinsa zai ƙoshi, zai samu wadata. Saboda haka Sarkin Musulmi gulbi ne. Haka kuma Sarkin mai tabbatar da mutunci da irlin duk wanda ya je wurinsa ne, tsaron mutunci da rayuwa da irli shi wannan sarki ya shahara da yi. Saboda haka akwati ne. Sarkin Musulmi shi ne sarkin da kan aza Musulmi bisa ga hanyar tsira, shi ke tattalin addinin Musulunci. Ba ya ma’amala da ɓata. Duk wanda ya zo wurinsa zai samu shiriya ta Musulunci. Saboda haka masallaci ne. A wurin Sarkin Musulmi ne daɗi da daula da ni’ima suka tare. Duk mai bukatar waɗannan to ya je wurinsa. Saboda haka Sarkin Musulmi alkaki ne.

Wannan shi ne abin da salon kinaya ya kawo mana a cikin tunaninmu game da Sarkin Musulmi Abubakar Na III cikin wannan baiti na waƙar Haliru Wurno.

Su kuwa manema sarautar Sarkin Musulmi, wato abokan hamayyar Abubakar Na III, ko kuma wasu sarakuna, ba su da halin ƙwarai, ba su taimakon talakawa, talaka bai samun ƙoshi daga gare su. Saboda haka su tabki ne. danki ne su. Don haka ba su tsaron mutanci ko irli balle rayuwar talaka. Azzalumai ba a su samun shiriya ta addini daga waɗannan mutane. Kowa ya bi su ya ɓace bai samun tsira. Saboda haka su gumaka ne. duk wanda ya je wurin waɗannan mutane to lalle kuwa zai shiga cikin ɓata da wahalar banza. Rayuwarsa ba za ta yi kyau ba. Saboda haka waɗannan abokan hamayyar Sarkin Musulmi gwaza ne su masu sa maƙaƙi ga wuya.

A waƙar Infiraji I, Alhaji (Dokta) Aliyu Namangi ya yi amfani da salon kinaya kamar haka:

In kira shi kira garibai

Ya fitillar haska duffai

Sabulun wankan zunubbai

Ya tafarkin iske rabbai

Ya jirgin fid da bai a ɗamba

 (Alhaji (Dokta) Aliyu Namangi: Infiraji I)

 

A wannan babi Alhaji Aliyu ya yi wa Annabi Muhammadu (S.A.W) kinaya da sunaye har guda huɗu. Annabi Muhammadu (S.A.W) fitila ne. wato haske ne mai haskakawa. Haka kuma sabulu ne wanda ke wanke ƙazanta, wato zunubi. Aliyu Namangi ya kira Annabi Muhammadu (S.A.W) da sunan tafarki. Wato hanya mai kai zuwa ga manufa kuma abin bukata. Haka kuma ya kira Annabi Muhammadu (S.A.W) jirgi mai yin fiton bayi daga cikin ɓata zuwa rahamar Allah Ubangiji.

Ya kamata mu lura a nan cewa a yayin da Namangi ya yi amfani da salon kinaya domin ya siffanta Annabi Muhammadu (S.A.W) sai ya yi amfani da salon alamtarwa ga abubuwan da aikin wanda aka yi wa kinaya zai hau a kansu. Muna magana a kan duffai da rabbai da ɗamba waɗanda ke a maƙwafin jahilci/kafirci da Aljanna da kuma ɓata.

Alhaji Aƙilu Aliyu shi ma mai amfani da salon kinaya ne cikin waƙoƙinsa. A waƙar da ya kira Amsa Ga ‘Wasiƙa Ta Sha’irci” yana cewa:

Cikin zancen ga ba gilli

A warware buɗe ba ƙulli

Kadan mun sami ma hali

Mu je mu ziyarci falali

Na ilmi ba na nauyi ba

Fasaha Hausa ba shakki

Tana gode wa jan zaki

Fa Alƙalinmu mai aiki

Zumunci mai yawan ɗinki

A kullum bai taƙaita ba.

 

A ya Allahu Fattahu

Ka taimaki namu miftahu

Fasihi Shehu mallahu

Manomin hairu fallahu

Kadan na kira shi ban yar ba

 (Alhaji Aƙilu Aliyu: Amsa Ga ‘Wasiƙa Ta Sha’irci)

 

Aƙilu Aliyu ya kira gwarzonsa, wato Alƙali Shehu Alƙanci da sunan falalin ilmi domin ya nuna cewa Alƙali shehu mutum ne mai ɗimbin ilmi, ilmin da ke da tarin yawa wanda da abin a auna shi ne da za a tarar da ya yi nauyin falalin dutsi!! Haka kuma ya siffanta gwarzonsa da jan zaki domin ya bayyana zamansa mai ƙwazo kuma sadauki a wajen aiki. Har ila yau Shehu miftahu ne, wato mabuɗi ne na ire-iren su Aƙilu Aliyu, wato mawaƙa. Hasili kai gwarzon Aƙilu Aliyu shi ne ‘sarkin jirgi’ na tekun fasha’. Don haka ne Aƙilu ya kira shi mallahu. Ba nan Aƙilu ya tsaya ba. Ya sake darajanta gwarzon nasa da kinayar manomin hairu. Wato yadda sarkin noma kan noma nasa hatsi haka Shehu Alkanci yake noman alheri. Mawaƙin ya ƙara da jadadda wannan magana ta amfani da kalmar Larabci, wato fallahu wadda ita ma cikin salon na kinaya aka zo da ita. Ma’anarta dai ita ce manomi. Manufar mawaƙin a wannan ɗango na huɗu ita ce cewa a koyaushe Shehu Alkanci tattalin aikata alheri ne aikinsa. Aikata alheri shi ne nomansa.

Shi kuwa Malam Muhammad Wada Hamza a ƙoƙarinsa na ya wasa kansa a matsayin zakara, sannan kuma ya muzanta abokin hamayyarsa, ga abin da yake cewa:

Ni nake naman jimina

Shi kitsen kolo ko yake

 

Mujiya ce shi a dawa

Ni ko alhudahuda nake

 

Kin ga ragon Makka nake

Bodarin daji ko yake.

 

Ni turaren jubda nake

Shi ko jaɓa kar ki sake

 (M.W. Hamza: Son Maso Wani Cuta Ne)

 

A yayin da Wada Hamza ya yi amfani da salon kinaya ya siffanta kansa da naman jimina da alhudahuda da ragon Makka da turaren jibda, sai ya kushe abokin hamayyarsa ta kiransa kitsen kolo da mujiya da bodarin daji da kuma jaɓa.

A ɓangaren waƙoƙin baka ma akan sami wannan salo na kinaya. Hasali ma ganin yadda yake taka rawa a cikin waɗannan waƙoƙi sai mutum ya fara tunanin ko watakila waƙoƙin baka suna da ƙaƙƙarfan tasiri ta fuskar salo kan rubutattun waƙoƙI, musamman salon siffantawa kuma reshen kinaya. To amma da mawaƙin baka da marubucin waƙa duk ‘yan Adamu ne. Amfani da wannan salo, wato salon kinaya, ɗabi’a ce ta ɗan Adam cikin maganarsa ta yau da kullum.

A waƙar Inuwa ɗan Maɗacci, Alhaji Muhammadu Gambu ya yi amfani da salon kinaya sosai. A wannan misali da ke tafe ya ,kira tauraronsa baƙin gora da kuma katakoron kusu. Wato Inuwa ɗan Maɗacci goran tsafi ne da ba a iya fasawa. Baƙin goran kuwa duk yadda ka yi da shi ba zai fashe ba, kuma ƙwamaƙwamansa (aljannu da sihirra) yawa ne da su. Wato saboda tsananin tsafata goran da aka yi babu abin da ke iya taho-mu-gama da shi. To wajen Gambu tauraronsa Inuwa shi ne wannan baƙin gora domin babu yadda maza sa su iya yi da shi. Duk abin da aka sani game da baƙin goran tsafi Inuwa ɗan Maɗacci yana da shi.

Gambu ya kira Inuwa katakoron kusu domin ya bayyana girman ƙasaitarsa. Wannan kusu (ɓera), saboda ƙasaitarsa har barazana yakan yi wa kyanwa. Idan ɓera ya san kyanwa tana a wuri to kuwa ba zai zo nan ba, kome kuwa matsuwa da yake ciki. Misali, a ce ɓera yana cikn ramensa sai ya leƙo ya hangi kyanwa. To kome yunwar da wannan ɓera ke ji ba zai fito ba muddin dai kyanwar nan tana nan ba ta gurgusa ba. Sai dai ya mutu a cikin ramen.

To amma sai ga shi Gambu ya faɗa mana wani irin ɓera (saboda zamansa katakoro) wanda a maimaikon ya guji kyanwa shi furji ma yake yi mata. Wato zai nuna mata idan ba ta san inda dare ya yi mata ba yanzu yana yi mata ƙurmumus.

A wajen Gambu ba kowa ba ne wannan katakoron ɓeara banda Inuwa ɗan Maɗacci. Wato a taƙaice, shi Inuwa ba ya jin tsoron abin da kowa ya tabbata yana iya kashe shi. A maimakon ma ya guji wannan abu, shi Inuwa hari ne zai kai wa abin. Ga dai abin da Gambu ke cewa:

Sai dan nan niy yi Jeaga

Nan niy yini nan nika kwana Jega

Nis sake yini haz zan wucewa

Sai nit tuna Inuwa ɗan Maɗacci

Wawilan, wawilan baƙin gora

Kaiconna kaina Gambu

Ya katakoron kusu na Gambu

Bawa mai wa mage hurji

 (Alhaji M. Gambu: Inuwa ɗan Maɗacci)

 

Haka kuma a yayin da yake son zuga Tudu Tosho (wanda muke ganin shi ne misalin magen da katakoron kusu kan yi wa furji) Gambu ya yi amfani da wannan salo na kinaya. Ya kira Tudu da sunan tsohon kolo wanda saboda ƙwamaƙwamansa maiki ba zai iya saukowa ya ci idon mosai ba. Domin mai karatu ya fahimci wannan kinaya sosai, maiki a nan yana nufin ɓarayi irin su Inuwa ɗan Maɗacci saboda shi Tudu (Tsoho kolo) ya tara dukiya (idanu) wadda ɓarayi ke kwaɗayin su kai gare ta. Ga abin da Gambu ya ce:

Sai nik koma ga kan Tudu

Nic ce tsohon kolo

Kai kad daɗe Tudu

Mai hana maiki cin idanu

Gabanka gabas swai ya yi yamma

Yara ba su ganin takin ƙahwakka

 (Alhaji M. Gambu: Inuwa ɗan Maɗacci)

 

Shi kuwa Alhaji Kassu Zurmi wanda shi ma ba kanwar lasa ba ne a waƙoƙin ɓarayi, ya yi amfani da salon kinaya sosai a waƙar da ya yi wa Muhammadu ɗan Sale ɗan Sanda. A waɗannan baitocin da za mu gani waɗanda kuma ba su da nisa tsakaninsu a cikin waƙar, Kassu ya yi amfani da salon kinaya aƙalla har sau takwas. In ban da ƙananan ɓarayi da Kassu ya kira rangama duk sauran wuraren da ya yi amfani da wannan salo, to Ɗan Sale ne Kassu ke siffantawa. Ga dai abin da yake cewa:

Ƙaramin ɗan duniya ka tonon rairai

Mamman ya hwaɗa ma ƙoram mata

Sai ƙoƙarin ɓantalat tasoshi

Shegen ɓarayi an nan

Rangama ba ta zanen suna

 

Gamshiƙa na Sani in kai ne

In ji kuwwa ana buzanci

Ih! Karenka

Hai! Namiji

Muhammadu in ji ka ba bugaje haushi

To

Mala’ikab bugaje

Ɗan Sale ciyyon cikin ‘yan banza

…..

 

Tarago mai jan kaya

Jirgin bisa mai yat tcela uway yaya

Kana gaba rigimakka na biya dab baya

Ɗan Sanda


Kai masama kowas sami hwan ɗari ya yi

Makka in yaƙ ƙiya su mai sai ga bara

Akwai mu da rairai masu mai da mutane baya

Dukiyab bahili ta yaɗu

Sai masu ci sun kawo

lanya hwatake na dare

Ɗan Sale tayin kura

Tayin kura kare ba ya son goyo nai

 (Kassu Zurmi: Mamman Ɗan Sale)

 

Za mu taƙaita misalan salon kinaya a nan domin mu dubi waɗansu ɓangarori na babban salo wanda kinaya ya fito daga cikinsa, wato salon siffantawa. Abin da muke son mu jaddada kurum shi ne cewa shi salon kinaya a koyashe yakan wulla sanin da aka yi wa abin da ake yin kinayar da shi zuwa ga wanda aka yi wa kinayar. Wato ke nan wajen fahimtar salon kinaya akwai matakai guda biyu: na farko shi ne tilas mai sauraren waƙa ya fahimci abin da ake kinaya da shi (wanda za mu kira sinadari), sannan tilas ne mai saurare ya ɗauki wannan fahimta da ya yi ta sanadarin ya yaɓa (ko ya liƙa) wa wanda aka yi wa kinayar (wanda shi kuma za mu kira cuɗau). Misali da Kassu ya kira Ɗan Sale da sunan tayin kura, Ɗan Sale ne cuɗau, shi kuma tayin kura shi ne sinadari. Sai mun fahimci cewa tayin kura jariri ne wanda ko kusa kare ba zai so ya goya shi ba domin ya san a kwana a tashi tayin ne zai halaka shi. Dole kare ya ji tsoron tayin kura domin kuwa tayin kura kura ne shi ma. Da kare da kura kuwa ba a shan inuwa guda balle har kare ya goya tayinta.

To wannan fahimta ta tayin kura dangane da kare ita ce za mu yaɓa ga Ɗan Sale. Wannan shi zai sa mu kalli Ɗan Sale a matsayin wanda ake tsoro duk kuwa da shike ba wani girma ko ƙarfi ne da shi ba.

 

b) Kamance

Salon kamance ɓangare ne na babban salon siffantawa. Salo ne wanda ke bayyana sifar wani abu ta fuskar kwatanta shi da wani abu daban tare da amfani da kalmomin da za mu ba suna mizani. Da za mu kwatanta wannan salo da salon kinaya sai mu ce a yayin da salon kamance zai siffanta mutum da cewa ya yi kama da wani abu amma ba shi ne abin ba, shi salon kinaya zai siffanta mutum da cewa ai shi ne abin kacokan!! Wato salon kinaya shi ya fi yin azarɓaɓi.

Salon kamance kamar wada aka ambata yakan yi amfani da kalmomin da aka kira mizani. Kalmomin kuwa sun kasu gida uku akwai na daidaito, akwai na fifiko sannan akwai na kasawa[21]. Kalmomin mizani su ke yi mana jagora wajen gane salon kamance a cikin waƙa. saboda haka bari mu kawo misalai na kowane rukunin mizani.

1. Mizanin daidaito: akwai ‘kamar’ da ‘wa’, da ‘i’ da ‘ƙoƙa’ da ‘ya’ da ‘ce, kake’ da kuma ‘daidai da’

2. Mizanin fifiko: ‘Wuce’ da ‘zarce’ da ‘fi’ da ‘take’ da ‘gota’ da ‘furce’ da ‘tsere’ da kuma ‘ɗara’.

3. Mizanin kasawa: ‘kasa’ da ‘gaza’ da ‘wane’ da kuma kalmomi masu soke samuwa kamar ‘bai ….ba’. Akwai kuma kalmomi masu tambayar nuna kushewa kamar ‘ina ya yi…?’ da ‘ina zai kai….?’.

 

i- Kamancen Daidaito

Yanzu sai mu duba yadda salon yakan fito a cikin waƙoƙi. Kamancen daidaito yakan kwantanata abin da ko wanda waƙa ke magana a kai da wani abu daban. Manufa ita ce salon ya kawo ma hoton abu ko halinsa ko sifarsa ko dai wani abu da ya shafe shi, ta hanyar kawo ma wani abu a gabanka wanda ka riga ka sani. To idan ya kawo ma wannan abu a gabanka sai ya ce, to yadda ka san wannan abin haka abin da wannan waƙa ke bayani a kai yake. Wato dai a taƙaice salon kamancen daidaito yakan siffanta ma maƙasudin abin da waƙa ke magana a kai da wani abu daban da ya ɗauka ka riga ka sani, sai ya ce to wannan abin da ka sani da wanda waƙa ke magana a kai duk ɗaya suke ta wannan fuska. Dubi wannan misali:

Ɗaura niyya ka zano Shagari

Jeka garkah Habibu Shagari

Ka ga mota kama da taurari

An jera su ca kakai fari

Don ko ɗai saboda saidawa

 

Dut ranad da nig ga nau ƙwabri

Sun yi ƙwarin shiga cikin wari

Sulu za ni yi kamar tsari

Cilas in sayo ta Shagari

Don ko ɗai saboda morewa

(Alhaji Sambo Wali Giɗaɗawa: Kamfanin Habibu Shagari)

 

A ɗango na uku, baiti na farko, Sambo Wali ya kamanta motocin kamfanin Habibu Shagari da taurari. Wannan kamance yana da aƙalla ma’anoni biyu. Ko dai Sambo yana nuni da cewa motocin kyawon gani gare su kamar taurari a sararin samaniya, ko kuma motocin yawa ne da su kamar taurari. Kowace ma’ana mutum ya ɗauka za ta dace. Sai dai saboda gudun mu zalunci mawaƙin da cewa ya yi maimai marar amfani a ɗango da ke bi ma wannan zai fi dacewa idan aka ɗauki ma’ana ta farko. Wato motocin kyawo ne da su kamar taurari.

A ɗango na huɗu na baitin, Sambo Wali ya kamanta yadda aka jera waɗannan motoci na kamfanin Habibu Shagari. Ga su nan sun jera kamar yadda za ka ga ɗangon fara ya yo cirri. Ma’ana ita ce za ka ga waɗannan motoci an jera su sun yi dafifi har ba za ka iya ƙididdige yawansu ba, tamkar da yadda ba za ka iya ƙididdige yawan farar da ke cikin ɗangon fara ba.

Yadda Sambo Wali zai yi hanzari ya isa kamfanin Habibu Shagari idan ya samu kuɗin da zai sayi mota domin ya shiga cikin tsara, wannan hanzari shi ne mawaƙin ya kamanta da yadda dabbar nan ta cikin ruwa, wato tsari (ko guza) kan yi zallo a cikin ruwa. Wannan shi ne kamancen da ɗango na uku a baiti na biyu ya zo da shi. Sambo zai yi sulu ne ra ruga a guje babu tsaitsayawa, ba zai garge a ko’ina ba sai a kamfanin Habibu Shagari.

Lura da cewa kalmomin da ke a tsakanin abubuwa da aka kamanta su ne kalmomin mizani. Su ke nuna cewa wannan kamance na daidaito ne. Wato abubuwan da aka kamanta kakkakkat suke.

A waƙar “Akwai” (Waƙar Birnin Kano) wadda Yahaya Gusau ya yi kuma Alƙali Bello Giɗaɗawa ya yi wa tamisi, akwai wannan salo na kamancen daidaito kamar haka:

Akwai mai sitati ya sa tozali

Ya zamna ga titi kamar shantali

Akan mai kake taƙamah har da gwali

Fa in ka yi yabƙinka don asili

 Akwai fin ƙabilarka birnin Kano

 

Akwai tsegumi ga yawan za’ida

Akwai kwarmato sai ka ce dai cida

Da zunɗe da baki awa ɗan kada

Munufunci ƙeta da yin hasada

Ku san ba dawa’insu birnin Kano

(Yahaya Gusau/ A.B. Giɗaɗawa: Akwai)

 

Baiti na farko ɗango na biyu mawaƙin yana magana a kan Bakanon da ya fito fes da shi, har ma da shafa kwalli, ya zo ya zauna a gefen hanya. Wannan zama na Bakanon shi ne mawaƙin ya kamanta da zaman buta. Butar da ke ajiye ai za a gane ta ne tsaye ƙiƙam, ba motsi ko ƙanƙani. To haka ne za ka hango Bakano ɗan gaye, ya zauna tsaf ba wani motsi, kamar ba mai rai ba (watakila yana gudun ya motsa karin gugar tufafinsa ya ɓaci). Kamancen daidaiton na zaman ɗan gaye da zaman shantali ne.

Haka kuma mawaƙi ya kamanta kwarmato da kanawa suke da da kwarmaton cida. Wato yadda ka san hadari yana yin cida to, haka ne kwarmatonsu yake. Kwarmatonsu ruɗe kunnuwa ne da shi kamar cida!

A ɗango na uku na wannan baiti kuwa mawaƙi ya kamanta zunɗe da waɗannan mutanen sukan yi da bakinsu da yadda bakin kada yake. Wato idan suna zunɗen wani za su riƙa turo leɓɓansu da tsawo a waje har bakunansu su yi tsawo kamar tsawon bakin kada!!

Shi kuwa Alhaji Ibrahim Narambaɗa kamanta waƙoƙinsa ya yi da waƙoƙin mashahurin mawaƙin nan na waƙoƙin madahu, wato Alfazazi mai Ishiriniya. Muna iya cewa Narambaɗa yana ganin da shi da Alfazazi kakkakkat suke, in dai a fagen tsara waƙa ne. Abin da dai yake a bayyane cikin wannan kamance shi ne cewa yadda Allah ya hore wa Alfazazi fasahar tsara waƙoƙin madahu haka shi ma Narambaɗa Allah ya hore masa tsara nasa irin waƙoƙin. Ga dai abin da mawaƙin ke cewa:

Ni kau kun gane ni na gyare turuna

Sai zuba waƙa nikai kama da ta Alfazazi

(Alhaji Ibrahim Narambaɗa: Gwarzon Shamaki)

 

Idan kuma aka leƙa a waƙoƙin ‘yan mata sai mu tarar da a nan ma akan samu salon kamancen daidaito. A waƙar “Cikinku Wa Ad Da Suna Sambo” akwai wannan salo kamar haka:

Cikinku cikinku wa ad da suna Sambo

Wani ɗan fari sirdaɗe

Hanci kamar allura

Baki kamar Bature ya ci ƙwallo

(Cikinku Wa Ad Da Suna Sambo)

 

Shi kuwa Haruna Uji ya kamanta idanun Jumai a cikin waɗannan ɗangogi na baitin waƙarsa mai suna “Waƙar Jumai”:

Idan ka gano Aljuma

Amma samalo take Jumai

Dubi idanun Aljuma

Kamar madara nonon shanu

(Alhaji Haruna Uji: Jumai)

 

A waƙar “Daina Yin Yanga, Mamman Garba Maraɗi yana cewa:

Ga ki ɗiya ta ƙwarai kamar gazal

In tai magana kamar firal

Ɗiya da ido kamar kaɗa

Kai yin dibi kamar kural

Ɗiya ta ƙwarai kamar lundu

Tabshin leɓo kamar kusal

Tabshin hannu kamar kafsul

Ɗiya da wuya ɗiya fele.

(Mamman Garba Maraɗi: Daina Yin Yanga)

 

A waɗannan ɗangogi Mamman Garba Maraɗi yana siffanta masoyinyarsa ta amfani da salon kamancen daidaito inda yake kamanta ta, ko wasu sasan jikinta, ko abubuwan da sassan kan yi da wasu abubuwa da aka riga aka sani. Da yake dukkan waɗannan ɗangogi in bancin ɗango na ƙarshe, ɗauke suke da wannan salo, zai fi dacewa in aka bayyana kamancen daki-daki kamar haka:

Ɗango na I: Mawaƙi ya kamanta masoyiyarsa da barewa. Wato ke nan kyawonta kamar kyan barewa.

Ɗango na 2: Inda idan masoyiysar mawaƙin ta buɗe bakinta ta yi magana mutum zai gane ta kamar fulawa, wato fure. Yadda furen fulawa ke da ban shawa idan ya buɗe to haka bakin wannan masoyiya yake.

Ɗango na 3: Idanunta fari ne da su kamar kaɗa, wato auduga. Har yanzu dai zancen kyawo mawaƙin yake yi.

Ɗango na 4: Waɗannan idanu kamar lantarki suke a wajen dubawa.

Ɗango na 5: Ita dai wannan masoyiya daidai take da mace ba’indiya a wajen kyawo.

Ɗango na 6: Shi kuwa tabshin leɓon masoyiyarsa daidai yake da tabshin kujera kushin.

Ɗango na 7: Sannan kuma tabsin hannunta kamar tabshin roba yake

Waɗannan su ne ɗangogi masu kamancen daidaito a yayin da ɗangon ƙarshe ya bayyana wuyan masoyiyarsa da cewa sumul-sumul (fele) yake.

 

ii- Kamancen Fifiko

Kamar yadda sunansa yake nuni kamance fifiko yakan ɗauki abubuwa biyu, da wanda yake ƙoƙarin ya siffanta da kuma wanda da shi ne yake ƙoƙarin ya siffanta na farkon, sai ya ce wannan na farkon ɗin ya fi wannan da ya kawo wa wanda ka riga ka sani. Wato dai ya ce gwarzonsa ya fi wancan da aka sani. Aikinsa guda ne da kamancen daidaito in ban da cewa shi ya ɗara na daidaiton tun da cewa yake nasa ya fi a yayin da shi kuwa na daidaito cewa yake gwarzona daida yake da wancan da ka sani.

A waƙarsa ta ‘Yar Gagara” wadda kuma yakan kira “Kwamacala” Alhaji Aƙilu Aliyu ya yi amfani da wannan salo inda yake cewa:

Ta fi kare a ƙazamin wargi

Ta fi kado lahani gangama

(Alhaji Aƙilu Aliyu: “Yar Gagara”)

 

Wato a wajen ƙazamin wargi (wasa), karuwa ta fi kare. Haka kuma ta zarce kada a wajen cutar da mutum.

A kuma waƙarsa ta yabon ilmi mai suna “Kadaura Babbar Inuwa” , Aƙilu Aliyu ya yi amfani da wannan salo domin ya bayyana darajar ilmi kamar haka:

Ilmi ga mai shi ya fi babban rumbu

Domin hatsin rumbu yana ƙarewa

(Alhaji Aƙilu Aliyu: Kadaura Babbar Inuwa)

 

Shi kuwa Alhaji Garba Gwandu a cikin salon tambaya ya yi amfani da salon kamancen fifiko domin ya siffanta ilmi:

Ilmi rabo na wanda babu awa shi

Shim mif fi kowane arziki ce min shi.

Don ba ka yin barci a sace ma shi

Kuma fada ba ka zuwa a ƙwace ma shi

 Na hori ‘ya’yana su je makaranta

(Alhaji Garba Gwandu: Bulaliya)

 

Lura da cewa kalmar mizanin wannan salo, ‘fi’, ta zo ne ba a tsakanin ‘ilmi’ da ‘kowane arziki’ ba. Kalmar ta zo ne kamin abubuwan biyu. Saboda haka ba tilas ne kalmomin mizani su zo a tsakakin abubuwan da salon kamance ke kwatantawa ba.

Alƙali Haliru Wurno shi kuwa ba ma a yanzu ne kwatancin yake ba, a’a mai ci gaba ne domin a cikin aiki mai zuwa ya sanya salon kamancen fifiko. Haliru yana ƙoƙarin ya bayyana yadda daɗin abincin da masoyiyarsa ta dafa ko ta taɓa yake. Yana son ya ce abincin da duk Mairi ta dafa ko kuma ta taɓa to zai fi kowane irin abinci da ka sani daɗi, ko da kuwa abin nan da ta taɓa ya fi duk abin da ka sani rashin daɗi ga baki. Ga dai Haliru:

Hasali wajjen abinci

Ko fatakko bale maɗwacci

Tat taɓa in dai da ɗwaci

Ko shi zam yami da barci

 Zai wuce daɗin gumina

 

Ko hura in ta yi damu

Kyanta ya tcere na kamu

Ta wuce kabrin kununmu

Ɗai da luddai ya ishe mu

 Ni da ‘yan yaran gidana.

(A.A. H. Wurno: Soyayya Ruwan Zuma)

 

A baiti na farko yana siffanta yadda daɗin abubuwan da idan masoyiyarsa Mairi ta dafa zai kasance. Haliru ya ce waɗannan abubuwa za su fi gumi (shinkafa) daɗi. Abubuwan kuwa su ne fatakko da maɗacci waɗanda sun fi kowane irin tsiro rashin daɗi ga baki saboda ɗacinsu, sannan kuma da kowane irin abu mai tsami kamar lemon tsami ko tsamiya, da kuma duk wani abu mai barci kamar goro ko bagaruwa. To duk waɗannan abubuwa ne Haliru ya ce idan Mairi ta taɓe su za su fi shinkafa daɗi!!

A baiti na biyu kuwa cewa ya yi duk furar da Mairi ta dama za ta fi kamu kyawon kallo. Haka kuma furar za ta fi kunu kauri!!

Idan aka waiwaiyi waƙoƙin baka sai mu ga su ma mawaƙan baka sukan yi amfani da wannan salo. Salihu Jankiɗi ya yi haka a cikin waƙar da ya yi wa Sardaunan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Bello inda yake cewa:

Karambanin akuya ya ƙare

Tun ran da tai karo da kura

Farin wata ya fi lantarki

Ko can dauri ba iri ɗai ba

(Salihu Jankiɗi: Sardaunan Sakkwato Ya Fashe Haushinai)

 

A wata waƙa wadda har ila yau ya yi wa Sardauna, Salihu Jankiɗi ya ce:

Ga gaskiya ku bar bin gaibi

In ga farin wata mai haske

Kun san ya fi na tamararuwa

(Salihu Jankiɗi: Allah Taimaki Mai Gaskiya)

 

Shi kuwa a cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Gobir Na Isa Amadu Bawa I, Ibrahim Narambaɗa ya yi amfani da salon kamar haka:

Baƙam magana ba ɓaci ta ba

Amma ta ɗara ɓaci zafi

(Ibrahim Narambaɗa: Gogarman Tudu)

 

Kalmar ‘ɗara’ ita ce mizanin da ke bayyana cewa baƙar magana ta fi zagi (ɓaci) za fi.

Alhaji Musa Ɗanƙwairo shi ma ya yi amfani da wannan salo. Misali a waƙarsa da ya yi wa Sardaunan Sakkwato yana cewa:

Yardakka ita aka nema

Na Bello ka fi zuma zaƙi ba wai ba

(Musa Ɗanƙwairo: Mai Dubun Nasara)

 

 

iii- Kamancen Kasawa

Wannan shi ne kashi na uku na salon kamance. Da wannan salo ne mawaƙi kan kwatanta abubuwa biyu ya ce ɗaya bai kai ga ɗaya ba. Wato shi salon kamancen kasawa kamar na fifiko ne aka yi cikin wata ƙira. Maimakon a ce wannan ya fi wancan sai aka ce wannan bai kai wancan ba, ko kuma wancan bai kai wannan ba.

A cikin waƙar ‘ ‘Yar Gagara’, Alhaji Aƙilu Aliyu ya yi amfani da salon kamancen kasawa har sau biyu a wurare daban daban. Ga yadda ya ce:

Shewar karuwa tare da muna

Gara maja-ciki in yai sara

 

Gara akwara akwai ta da birki

Cutar karuwa ba ta makanga

(Alhaji Aƙilu Aliyu: ‘Yar Gagara)

 

A baiti na farko Alhaji Aƙilu yana nufin cewa saran da maciji zai yi wa mutum bai kai cutar fiton da karuwa ta yi cikin murna ba. Wato dai cutar da farin cikin karuwa ke haifarwa ta fi cutar saran maciji. A baiti na biyu kuwa mawaƙin ya kamanta cutar karuwa da ta keke wadda ta tsufa. A ganin mawaƙin cutar wannan keke mai dama ce tun da tana da birki, mutum yana iya ya tsai da ita. Amma ita ko cutar karuwa ba ta da makama. Mutum bai iya tsayar da ita idan ta dunfaro shi.

Alƙali Haliru Wurno ya yi amfani da wannan salo na kasawa cikin wasu baitocin Soyayya Ruwan Zuma inda yake cewa:

Niy yi A’i da ‘Yar Fulani

Na yi amre da tsakani

Na yi hausawa Fulani

Gobirawa har na Kwanni

 Na yi sunka shigo gidana

 

Nit tuno Mairi ganin su

Kyansu ko halin zamansu

Ba su kai Mairi halinsu

Ko turare na jikinsu

 Sunka sa in za mu kwana

 

Na fi son warin jikinta

Binta-Sudan bai kamatta

Na fi son warin hamutta

Nata ban son ɗan- liwanta

 Dud da mai askar ga jina

(A.A.H Wurno: Soyayya Ruwan Zuma)

 

A baiti na biyu Haliru yana nufin cewa kyawo da hali na matan da ya aura ba su kai kyawo da halin Mairi ba. A baiti na uku kuwa, wanda maganarsa ta faro tun daga na biyu, cewa yake turaren da matan kan shafa ga jikinsu kamar wanda ake kira Binta-Sudan bai yi ƙamshin Mairi ba. Kai wannan turare da ma sauran turraruka ba su kai ƙamshin warin (don Haliru ba ya jin warin) hamuttan Mairi a wurin Haliru ba!!

Kusan gaba ɗayan waƙar da ya kira ‘Waƙar Habbi’, a cikin salon kamancen kasawa Alƙali Haliru ya tsara ta. Ga kaɗan daga cikin baitocin wannan waƙa:

Hasken haƙoran Habbi wa zinariya

Hannunta ko da lu’u-lu’u bai kai ba

 

Mata na Hausa bale Bugaje dut su zo

In ta fito kyawonsu dut ba su kai ba

 

Ita af fara ko Asbinawa sun saki

In sun ga Habbi suna faɗin ba mu kai ba

 

Kwayar ido da baƙinsu ba ya misaltuwa

To bale ƙwai duba shi don bai kai bai

 

Yankin idanun Habbi in dai ka gani

Tsayuwar wata farkonsa dub bai kai ba

 

Hancinta wane Larabawa ‘yan Masar

Ko da na Jodan na ba su yi ba su kai ba

 

Tabshin jiki tabshin hali kyawon wuya

Kyawon ɗuwawu mace duk ba ta kai ba.

(Alƙali Haliru Wurno: Waƙar Habbi)

 

Lura da cewa a baiti na farko kalmar mizani a ɗango na ɗaya, wato ‘wa’, ba kalmar mizanin salon daidaito ce ba. Saboda haka ba gajeruwa ba ce, doguwa ce a wajen furtawa. Shi kuwa yankin jumla mai korewa, wato bai.. ba, wanda ake samu a kai a kai cikin baitocin shi ne mizanin kamancen kasawa a wannan misali.

 

Ibrahim Narambaɗa, a fagen waƙoƙin baka, shi ma yakan yi amfani da wannan salo. A waƙarsa da aka kawo misali da wasu baitocinta a kamancen fifiko, ya yi amfani da kamancen kasawa kamar haka:

Ka san jama’ag ga da an nan

Ƙauye da birni ba su da jigo sai kai

Maɗi bai kai ga zuma ba

Kowal lasa shi ka hwaɗi

Kwandon wake bai kai ga damen gero ba

Ai ɗan akuya ko ya yi ƙahori

Ya san bai yi kamar rago ba

Ɗan sarki komi yaƙ ƙasura

Kak ka raba shi da bawan sarki

(Ibrahim Narambaɗa: Gogarman Tudu)

 

A gaba kaɗan da wannan misali, Narambaɗa ya sake amfani da wannan salo domin ya koɗa kansa da kansa. Mene ne ya ce? Ga shi:

Ai ba a gama ni da yaro

Na san yaro bai yi muƙamina ba

Kak ku gama ni da yaro

Na san yaro bai yi zalaƙata ba

Kak ku gama ni da yaro

Na san yaro bai yi fusahata ba

Kak ku gama ni da yaro

Ƙaryab banza yaro bai kai inda Narambaɗa

Mai tabarukun sarki

(Ibrahim Narambaɗa: Gogarman Tudu)

 

c) Jinsarwa/Jinsintarwa

Yadda amfani da salon kinaya ya zamo jiki gare mu cikin maganar da muke yi yau da kullum haka ne salon jinsarwa yake.

A. Kai yau ɗaliban nan sun taɓa Malam

In ka ji yadda yake cida za ka zaci rufin kwanon nan zai cire.

 

B. Ai daɗa shi ke nan. Ya tsima. Yau Naira sai ta sha kashi

 

C. Haƙiƙa ya gogu a fagen siyasa.

 

D. Duniya ta ɗauke shi.

 

E. Duniya ta yadda shi.

 

A kowane ɗaya daga cikin misalan nan biyar an ɗauko halayya ko darajar wani abu ne aka liƙa wa wanda ake magana a kansa. A misali na A. ai halayyar hadari ce aka ɗora wa mutum, wato Malam. A misali na B. cewa aka yi mutum ya yi halin sassaƙen iccen magani. Wato ya tsima. Haka nan kuma a misali na C. an ce mutum ne ya gogu, kamar dai tufafi ne aka aza wa dutsin guga. Sannan a misali na D da na E aka ɗora wa duniya ikon ɗauka da ajewa, tamkar dai tana da hannuwa kamar mutum.

Amfani da harshe kamar yadda aka gani cikin waɗannan misalai, shi ne ake kira salon jinsarwa a fagen nazarin waƙa. Salon jinsarwa yana nufin ɗaukar wata halayya ko daraja ko aiki na wani jinsi, (mutum ko dabba ko wani abu) a ɗora a kan wani jinsi na daban akasin mai su da aka sani da su, a ce ko a nuna shi ne ya yi su ko ya bayyana su haliyyoyin ko darojojin ko ayyukan. A taƙaice, a ɗora wa wani jinsi halayya ko daraja ko aikin wani jinsi daban da ba shi ba. Saboda haka shi wannan salo ya kasu gida huɗu: mutuntarwa da dabbantarwa da abuntarwa da kuma abuntarwar abuntarwa ko kurwantarwa kamar yadda a nan za a kira na huɗu ɗin[22].

i- Mutuntarwa

Jinsarwa da ake ɗora wa abin da ba mutum ba wata halayya ko darajar mutum, shi ne ake kira salon mutuntarwa.

A ƙoƙarinsa na ya kafa hujjar cewa waƙar da ya yi wa ubangidansa Sarkin Kudu ta yi daɗi kuma kowa yana jin daɗinta, sai Alhaji Sa’idu Faru ya ruwaito mana abin da ya ji suuda (tsuntsu da Hausawa kan ce ya cika surutu) yana faɗi game da waƙar. Sa’idu Faru ya ci karo da suda ne a yayin da shi Sa’idu ya bi sawun ubangindasa da ya sami labarin ya yi tafiya zuwa aikin hajji. Ga dai abin da ya ce:

Sai nis saki hanya niy gabas

Dahir

Can na taɓa yat tafiya kaɗan

Sai ni’ ishe suda na kiyo

Sosai

Yana ta waƙas Sarkin Kudu

Haka nan fa

Rainai ya daɗe Sarkin Kudu

Amin

Alisabbinane ɗan Amadu

Amin amin

Allah shi ƙara mai nasara

Amin

Nic ce suda waƙa akai

Yac ce lalle waƙa nikai

Waƙam Muhamman Sarkin Kudu

Waƙan nan da Ɗan Umma yai mashi

Haka nan fa

Bancin ruwan tsuntsaye nike

Inda kaman milki na nikai

Da nai mai wasiƙa yai man kiɗi

Faru ba

(Alhaji Sa’idu Faru: Gardaye Zo Ka Yi Man Iso)

 

Duk wuraren da aka yi rubutun gicciyen maganar da suda ya yi ce. A nan za a lura da cewa ko bayan darajar yin magana da aka ba tsuntsu (wato suda) wadda halayya ce da mutum kurum aka sani da ita, sai kuma aka ƙara ba shi tsuntsun wata maɗaukakiyar daraja, wato baiwar rera waƙa. Wannan abu da Sa’idu Faru ya yi wa tsuntsu ya haifar da sauyawar tunani da fahimtarmu game da yanayin tsarin rayuwar halittu gaba ɗaya. Sauraren wannan baiti a cikin salon mutuntarwa yakan sa mu yi wa tsuntsuye kallon su ma suna cikin al’ummar mutane. Suna ji kamar mu, suna magana kamar mu kuma suna da baiwar rarrabewa tsakanin abu mai kyau da mummuna. Kamar dai yadda wannan tsuntsu, suda, ya gane cewa waƙar da Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Kudu tana da daɗI, haka kuma ya iya yin begen ko da Sa’idu Faru zai sami damar yi masa waƙa irinta. Da ba don wannan salon mutuntarwa ba da watakila ba za mu yi wa tsuntsaye irin wannan ɗauka ta zama mutane ba.

Shi ma Alhaji Kassu Zurmi ya yi amfani da wannan salo a cikin waƙar da ya yi wa Shayi Ɗan Gidan Labbo. A wannan waƙa Kassu ya sa tantabari yin guɗa, sannan kuma ya ce tantabarin kan yi wƙa da mabanci. Haka nan kuma Kassu ya sa kurciya yin waƙa da kuma ruɗin ɗan Adam. Ga dai abin da Kassu ya ce:

Tantabara goma

Amma yanzu ba su sun ƙare

Yanzu kau saura nai guda baƙi namiji

Ko shi kau don yana yi mai waƙa

Inda sahiya taw waye ya ɗora mabanci

 

Sai in Sha-yaya yaɗ ɗago ɗaki

‘Yan Mazan tantabari ga na yi mai guɗa

Shina ƙudunguru Shayi Ɗan Gidan Labbo

Ƙudunguru Shayi Ɗan Gidan Labbo

Ƙudunguru Shayi Ɗan Gidan Labbo

Ƙunduguru Shayi Ɗan Gidan Labbo

Ashe ko tsuntsayen daji na da azanci

Can yana sarawa tac ce bari dai mu yi mai magana

Kahin dai ya gane dutcin can

Na gane shi na tashi

Shina sarawa tana yi mai launi

Shina sarinai tana yi mai launi

Ko gwallo

Ko gwallo

Ko gwallo

In ji kurciyar gamji

Iro tun da dai kak kore ta

Ba ka ko gwallo

(Alhaji Kassu Zurmi: Shayi Ɗan Gidan Labbo)

 

A ɓangaren rubutattun waƙoƙi ma akan sami irin wannan salo. Idan mai karatu bai manta da cin karo da irin wannan salo a waƙar Haliru wadda ya kira Gudale. Bari a sake kawo wasu baitoci daga wannan waƙa waɗanda suka shafi dila, sarkin dibara.

Na yi gabas wajjen yanyawa

Kila dibaratai ta ishe ni

 

Na ishe limami yanyawa

Ga ni mu’allimu zo ka daɗe ni

 

Na ga ashe shi ma tai zahi

Sa’alabu ya ce tashi ka bar ni

 

Na yi zugun ya ce kai tashi

Ba ka ganin inwa ta bar ni

 

Na yi zufa rana ga zafi

Matata ita ma ta bar ni

 

Na ce Mallam ka san Allah

Yac ce min ai shi yay yo ni

 

Na ce dubi hadisin tanyo

Ba ka yi min girman addini

 

Na ga kamar maganar ta kammai

Sa’alabu ya ce kai ka fi ni

 

Na ga kana iya kanka da kawo

Kwanana huɗu ban da sukuni

 

Na yi biɗar ƙanen matata

‘Ya’yana huɗu dut sun bar ni

(Alƙali Haliru Wurno: Gudale).

 

ii- Dabbantarwa

Mawaƙi kan ɗauki hali ko yanayi ko daraja ko ɗabi’a ko aikin da dabba ce aka sani da shi sai ya ɗora wannan abu a kan mutum. Wannan shi ne manazarta ke kira dabbantarwa. Salon yakan ba mawaƙi damar fitowa da kyawawa ko munanan halaye ko sifofin wanda yake magana a kansa. Wannan fahimtarwa da mawaƙi ke ƙoƙarin ya cusa wa mai saurare takan dogara ne a kan yadda ake duban wannan hali ko sifa ta dabbar a cikin al’umma harshen da aka yi waƙar. misali idan aka ce ga Gazzali can yana gumza, mun san cewa ba za a yi kallon sa da kamanun kura ba sai dai da na zaki. Ita kura ƙugi take yi. Ta wannan fuska ce za a iya fahimtar waɗannan baitoci da mawaƙi yake dabbantar da kansa.

Kin bugan sarƙa a wuya

Ko da yaushe bin ki nake

 

Na riga na miƙa wuya

Rayuwata son ki take

 

In na yo carar zakara

Kyarkyarata gun ki take

(M.W. Hamza: Son Maso Wani Cuta Ne).

 

A baiti na farko mawaƙin ya ce masoyiyarsa ta garƙama masa sarƙa a wuya. Wato ta buga masa sarƙa ta kuma sa kwaɗo ta kulle tamkar dai shi kare ne. kare ne akan sa wa sarƙa a wuya, a kuma ja shi ya bi mai shi a duk inda ya sa ƙafa. Masoyiysar wannan mawaƙi ta saka masa sarƙar soyayya ta kuma ja shi. Shi kuwa bai da ta yi illa biyar ta a duk inda ta sa ƙafarta. Ta yi masa bi-ni-zoizoi[23] ke nan in ji Hausawa!

Haka kuma a baiti na uku mawaƙin ya ɗora wa kansa ɗabi’u biyu na zakaran kaza. Ɗabi’a ta farko ita ce, yin cara, wato ƙiƙiriƙi. Ita kuwa wannan cara da mawaƙin ke yi ba ta faɗar lokaci ba ce. Ta idan zakara ya ga matarsa ce, wato kaza. A nan ke nan mawaƙin yana nufin idan ya yi kirari. Ɗabi’a ta biyu wadda ya yafa wa kansa ita ce kyarkyara. Wato irin rawan nan da kuma tuƙuburin da zakara kan yi a gaban matarsa domin ya nuna mata cewa babu wanda ya kai shi a kome, saboda haka shi ya dace da soyayyarta. Haka mawaƙin yake son masoyiysarsa ta fahimce shi.

Abin lura a nan shi ne mawaƙin ya yi amfani da salon dabbantarwa a cikin baitoci biyu rak domin ya faɗi magana mai nauyi a cikin raha da kuma yi da gaske.

Ibrahim Narambaɗa ya yi amfani da salon dabbantarwa yana mai shawartar Magajin Shinkafi Ibrahim da ya riƙa ba mutane tsoro yana tsawata musu domin kar su fanɗare. Ga abin da Narambaɗa ke cewa:

Riƙa da gaskiya Ibrahim

Mai taimakon ka Allah na nan

Zanka wa maza gurnani

(Narambaɗa: Mai Gida Shinkafi)

 

Damisa ce take da ɗabi’ar yin gurnani kuma takan yi shi ne domin ta tsoratar. Idan ta yi wannan sauti to kuwa ba da daɗewa ba za ta kai hari matsawar wanda take yi wa shi ya ƙi sanin inda dare ya yi masa. To wannan ɗabi’a ce Narambaɗa ya siffanta Magajin Shinkafi da ita. Wato, mai yin gurnani ne. Jan ido da tsawatarwa su ne Narambaɗa ke nufi da gurnanin.

 

iii- Abuntarwa

Kassu Zurmi ya ba mu kyakkyawan misali na salon abuntarwa wanda ke nufin liƙa wa mutum hali ko ɗabi’a ko daraja ko kuma saka mutum cikin yanayi na wani abu wanda ba dabba ba (misali dutse ko ruwa ko mota). A cikin waƙar da ya yi wa Isa Ɗanbuzu, Kassu Zurmi ya yi amfani da salon abuntarwa da kuma na kinaya a cikin magana guda tal. Ga abin da ya ce:

Na zo cikin Gusau

Ban ganai yana yawo ba

Nit tambayi mai ɗakinai Hajiya

Shin dogo na gare mu ko an sa mashi sanke

Shina garemu ko an sa mashi sanke

Komib bunzuma bunzun.

(Kassu Zurmi: Isa Ɗanbuzu)

 

A nan Kassu ya siffanta maigidansa da mota. Wato shi mota ne da akan sa wa sanke domin a hana ta motsawa. Ɗabi’ar mota da Kassu ya liƙa wa Isa Ɗanbuzu ta ma zarce ta sa sanke idan aka yi la’akari da cewa wannan waƙar ɓarayi ce. Mota jidar kaya take yi, yawo takan yi zuwa wurare daban-daban, kuma muddin ba sanke aka sa mata ba ba za ta fasa waɗannan ɗabi’u ba. To haka shi ma ɓarawo jidar kaya yake yi a wurare daban-daban. A kullum bisa ga zuwa wurare daban-daban yake. Ba ya fasa yin haka muddin ba tsare shi aka yi a kurkuku ba, wato aka sa masa sanke kamar mota. A nan ne kuma za a fahimci cewa kalmar sanke a cikin salon kinaya ne Kassu ya kawo ta domin ta ba da ma’anar kurkuku.

Haka kuma ana iya fahimtar amfani da wannan salo da Kassu ya sake yi a cikin waƙar Shayi Ɗan Gidan Labbo lokacin da yake bayyana yadda ‘yan mata suka tarbi Shayi a ƙauyen ‘Yar Magarya. Kassu ya ce lokacin da ‘yan mata suka ga Shayi sai suka yi wasoson sa. A maganar yau da kullum ba a wasoson mutum. Gyaɗa ko kuɗi ko makamancinsu ake wasoso. Kai ko da kalmar ‘ribibi’ ce Kassu ya yi amfani da ita za ta haifar da wannan salo na abuntarwa. Watakila kalmar gardama ce ba za ta yi ba. Ga dai abin da Kassu ya ce:

‘Yam mata sun ganai cikin gebe

Anka ɗora wasoso

Ni wan’in Shayi ni ka jisshe shi

A’a kina ƙarya na riga ki zaɓo shi

Kama a buga

Ga a nan cikin gebe

Nic ce musu ka ku buga

Ya ishe ku jiɗawwa

(Kassu Zurmi: Shayi Ɗangidan Labbo)

Ko a farkon wannan waƙa sai da Kassu ya ari bakin Labbo ya saƙa salon abuntarwa, ya siffanta Shayi da tufa wanda ke da ɗabi’ar koɗewa:

Labbo yac ce ƙaton gidan na banza ne

Komi yab biɗa na mata ne

Dum mata sun bi Iro sun koɗe

(Kassu Zurmi: Shayi Ɗangidan Labbo)

 

Abin da dai wannan magana ke nufi shi ne mata sun wahalar da Shayi sosai har ya zamo bai iya neman na kansa, duk biɗar da ya yi ta ƙare ga mata har ya kasance ƙarfinsa ya ƙare, bai iya taɓuka kome.

A waƙar da ya kira, “Waƙa Yin Tarbiyya”, Haliru Wurno ya zargi shugabannin Nijeriya da zamowa ummal haba’isin rashin ɗa’a da tarbiya a cikin matasa saboda dalilai da dama. Waɗannan shugabbanni kuwa sun haɗa da sarakuna da malamai waɗnda a ganin Haliru Wurno,

Sun ɓata samari sun ture

Ga rashin kumya sun hinjire

Mugun ra’ayi sun kangare

In ka ƙyale sun dasƙare

 Wuta dam murhu taka danniya

Ƙin bin doka bisa ƙa’ida

Manya nan sun bar fa’ida

Sun san haka sunka yi amida

Ga mugun kai ga hasada

Su ne manya ga mu’anida

Su ƙire ƙarya su yi za’ida

In ka yi musu su yi ma cida

Daga Sakkwato har bisa Zariya.

(Alƙali Haliru Wurno: Waƙar Yin Tarbiya)

 

A baiti na farko, ɗango na huɗu, Haliru ya ambaci ‘dasƙarewar’ samari. Ruwa ne ko man shanu da na kaɗe su ne a saninnu ke dasƙarewa, ruwa su zamo ƙanƙara. Ɗora wa ‘yan Adam wannan ɗabi’a ta ruwa (wato yin amfani da salon abuntarwa) ta ba mu damar mu kalli ‘yan Adam ɗin (a nan samari ke nan) da kasancewa mutane marasa jin maganar magabata, mutane waɗanda ba abin da al’umma za ta yi musu domin gyara halinsu. Halinsu ya ‘dasƙare, ba a iya sarrafa shi tamkar dai yadda ba a iya sarrafa ƙanƙara.

Su kuma shugabannin da Haliru ya ambata a baiti na uku ɗango na huɗu, su ne masu yi wa mutum ‘cida’ kamar hadari a duk lokacin da ya ƙalubalanci wata ƙarya da suka fesa. Cewar da Haliru ya yi shugabanni za su yi ma cida, amfani ne ya yi da salon abuntarwa domin ya bayyana irin kwakwazo da tsoratarwa da firgitarwa da shugabannin kan yi wa duk wani wanda ya ƙalubalanci zalunci da suke tafkawa ƙiriƙiri a cikin ƙasa.

A wata waƙa, har ila yau ta wannan mawaƙi akwai wuraren da ya yi amfani da wannan salo na abuntarwa. Dubi yadda yake bayyana halin wata matarsa wadda ta ‘gasa’ shi ainun:

Rabi Tannas ta daina ban shawa

Ga ƙafafunta kama da laulawa

Ta yi ɗwaci wane fatakkowa

Niy yi zafi nik kama yanyawa

 Munka zamna tay yo muguntatta

(Alƙali Haliru Wurno: Waƙar Mairi ‘Yar Marsa)

 

iv- Abuntarwar Abuntarwa/Kurwantarwa

 

Abuntarwar abuntarwa yana daga cikin salon jinsintarwa da Ɗangambo ya ambata cikin littafinsa, Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (2007: 45-47), wanda kuma marubucin wannan littafi, Salo Asirin Waƙa, yake son ya kira, kurwantarwa.

Ɗangambo ya bayyana shi da cewa, ‘a ɗauki wani abu marar rai a kwatanta shi da wani abun daban marar rai’. Misalin da akan samu cikin maganar yau da kullum shi ne, ‘Gari ya yi zafi yau’. Sanin kowa ne cewa gari ba mutum ba ne, ba kuma dabba ba. Abu dai ne marar rai. Haka kuma an sani cewa wuta ce take da zafi. Wuta kuwa ba mutum ko dabba ce ba. Marar rai ce. Saboda haka a wannan jumla, ‘Gari ya yi zafi yau’, marar rai (gari) aka sa wa halayya ta wani abu marar rai (wuta), kamar yadda Ɗangambo ya ce. Ga wasu misalai daga cikin waƙa:

1. Yau duniya ta barkace

 Shin yanzu kam mi za a ce

 (Alƙali Bello Giɗaɗawa: Ce-Ce-Ku-Ce)

A wannan baiti duniya ce aka ce ta barkace, tamkar yadda wani tarkacen kaya ke barkacewa.

 17.Niyya a kyauta kar a sa mata maguɗi

 Kyauta ta aikin zai tafo ya yi ƙyalƙyali

 (Alƙali Bello Giɗaɗawa: Ilmi)

 

A wannan baiti kuwa aiki ne aka ce yana yin ƙyalƙyali , tamkar yadda sabon ƙyalle ko kwalli suke yi.

Daga cikin waƙoƙin baka kuwa, Narambaɗa ya ce:

Kullum ji nikai azanci na hudo min

In wani ya hi ni martaba ni kau na hi wani

Ai kyawon mafarauci ya ɗau kare ya kiyayo yah hi

(Ibrahim Narambaɗa:Gwarzon Shamaki Na Malam Toron Giwa)

A nan azanci ne yake hudo wa Narambaɗa kamar yadda kibiya ke huda jikin ɗan Adam. Azanci ba abu ba ne mai rai. Haka kuma abin da ke huda jikin ɗan Adam, (kamar kibiya ko mashi) shi ma bai da rai. Wato Narambaɗa ya kurwantar da azanci da ɗayan wannan ke nan.

d) Zayyana

A babi na biyu mun bayyana yadda mawaƙi kan suranta wani yanayi har ya kasance mai saurare ko karanta waƙarsa ya riƙa ganin wannan yanayi a cikin ransa ta amfani da idon zuciyarsa. Misali da aka kawo a wancan babin shi ne na wasu baitoci da waƙar Haliru Wurno mai suna Yabon Bello Yahya Sakatare ta ƙunsa kuma a ƙarƙashin kan maganar ‘Isar da saƙo’ aka kawo misalin. To wannan nau’i na salon siffantawa shi ake nufi da salon zayyana.

Salon zayyana yana nufin amfani da kalmoni a cikin waƙa waɗanda tattare da sauran maganar da suka fito cikinta za su ƙirƙiro siffar abu ko yanayi a cikin zuciyar mai karatu ko sauraren waƙar. Yadda mai yin zane-zane ke dubin abin da ke gabansa, ya yi amfani da alƙalamin zane ya zana surar abin nan da ke a gabansa, haka ne mawaƙi ke dubin abu ko yanayi da idon zuciyarsa, ya kuma yi amfani da basirarsa da kalmomin harshen da ya mallaka (waɗanda su ne alƙalaminsa da taddawarsa) ya zana (wato ya zayyana) abin nan ko yanayin nan da ke gaban idon zuciyarsa. A taƙaice salon zayyana salo ne da mawaƙi ke amfani da kalmomi domin ya ƙirƙiro hoton abin da ke a zuciyarsa ta yadda mai karatu ko sauraren waƙar zai ga hoton da idon zuciyarsa. Mawaƙi ta ɓangaren salon zayyana, mai ɗaukar hoto ne ko mai zane.

Zai kasance maiman idan aka ce a kawo misalan wannan salo a nan kamar wada aka yi wa waɗanda suka gabace shi. Zai wadatar idan aka ambaci kaɗan daga cikin waƙoƙin da ake iya samun salon ba tare da wata wahala ba. Daga cikin waɗannan waƙoƙi kuwa akwai Waƙar Fanda ( ko waƙar Danja) ta shi Haliru Wurno da waƙar Tsarabar Madina ta Alhaji (Dokta) Aliyu Namangi. Daga kuma waƙoƙin baka akwai waƙar Inuwa Ɗan Maɗacci ta Alhaji Muhammadu Gambu musamman a wurin da mawaƙin ke bayyana yadda ya riƙa biyar Tudu Tsoho a cikin kasuwar ƙauyen Romo. Waƙoƙin Gambu tarshe suke da irin wannan salo: waƙarsa ta ‘Masu Sata da Biro’, a bayanin da ya yi na karonsa da mai duba aikin gine-gine na gwamnati; waƙar ‘Jibrin Mugun Tsoho’ wadda ta zayyana mana ja-in-jan da ya gudana tsakanin wani daga cikin yaran Jibrin da wata mata mai juna biyu da ya kai wata tara a yayin da shi da Gambu suka shiga cikin gidan da matar take domin su yi sata. Waɗannan waƙoƙi duk sun tara salon zayyana.

Shi ma Alhaji Kassu Zurmi ba a baya yake ba wajen amfani da salon zayyana. Waƙarsa, ‘Garugaru’ ta ƙunshi salon tun daga inda Kassu ke bayani kan kama gunzu har zuwa lokacin da aka ce Garugaru ya tsaya a raba gunzu yadda kowa zai samu har da Kassu wanda a farko aka ce ba za a bashi ko tsunke ba, waƙa ce mai salon zayyana A waƙar Shayi Ɗangidan Labbo, Kassu ya yi amfani da salon tare da na hira a inda iyayen ‘yan mata suka gana da shi Kassu game da gogansa, wato Shayi, idan wai Shayi ya dace da ya auri ɗaya daga cikin ‘yan matan da suka warware baikon da aka yi musu domin ganin Shayi da suka. Haka kuma akwai wani amfani da salon zayyana da Kassu ya yi mai ƙayatarwa a cikin waƙarsa, ‘ ‘Yan Jabanda’. Kusan ana iya cewa wannan waƙa gaba ɗayanta cikin salon zayyna take. Kassu ya sarƙa wannan salo da na hira.

Abin lura game da salon zayyana shi ne ba kasafai ne yake bayyana a cikin waƙa ba tare da waɗansu salailai ba. Daga cikin waɗannan kuwa akwai salon hira da na kinaya da kuma amfani da kalmomi masu kaifin ma’ana da na bi-ma’ana.

 

e) Alamtarwa

Idan mawaƙi ya ɗauki wani sashe na abu ya gabatar da sashin a matsayin dukkan abin (misali Rawani a matsayin sarauta), ko kuma mawaƙi ya kira wani abu da wani suna wanda a cikin harshen da aka yi waƙa, suna ne karɓaɓɓe da ke tsayawa a makwafin wancan abu (misali kalmar gobe da ke nufin lahira), ko ma mawaƙi ya ba wani abu wani suna a cikin waƙarsa bayan sunan da kowa ya san abin da shi (misali a cikin waƙar maza ta ‘yan tauri ko ta ɓarayi, mawaƙi ya kira tauraronsa da sunan ‘goga’). Idan mawaƙi ya yi wannan azanci a cikin waƙarsa sai mu ce ya yi amfani da salon alamtarwa ko alamci. Dubi abin da Alhaji Musa Ɗanƙwairo ke cewa a wata waƙarsa:

Kai ku ji yaro ya yi ɓanɓarma

Sai anka gwada mai an fi ƙarfinsa

Babu kakinai babu bel

Kuma babu hullatai babu takalma

Kuma babu hullatai babu takalma

Duk salare nashi ya ƙare

Bai da fansho kuma ba giratute

Arne koma cikin dutsi

Kai arne

Koma cikin dutsi

 (A.M. Ɗanƙwairo: Waƙar Sarkin Muri Umaru Abba)

 

Ba kowane kaki ba ne, ba kuma kowane bel ba ne Ɗanƙwairo ke nufi. Haka kuma ba kowace hula ba ce kuma ba kowaɗanne irin takalma ba ne Ɗanƙwairo ke nufi a cikin wannan waƙa. Kayan soja ne Ɗanƙwairo ya kawo kuma a matsayin aikin soja suke a cikin waƙar. A taƙaice Ɗanƙwairo yana nufin wannan yaro soja ne wanda aka kora daga aikin soja saboda cika bakinsa. Saboda haka da kaki da bel da hula da taklama dukkansu alamtarwa ne na aikin soja.

Shi kuwa Kassu Zurmi la’akari ya yi da cewa shi ne ya ƙirƙiro sunayen da ya yi amfani da su a wajen saka salon alamtarwa cikin waƙarsa saboda haka ya zama wajibi gare shi ya faɗa mana abubuwan da ƙirƙiren ke nufi:

Tun daw wagga lamba ta gabas

Ɗunke hag ga lambay yamma

Yaro in ka ga rijiya ga baya

‘Yan Jabanda nay yasa ta

Ko shan doguwa da takobi

Ko tsayin wata

Kun san tsayin wata

Saran goshi irin na gunda

‘Yan Jabanda ɗai ka hakan ga

 

Shan doguwa da takobi saran ƙwanda

Hannu ya birkece ba aiki

Su ba Allah ba suna musakan kansu

 

Rijiya bisa baya wanga saran allo

 (Alhaji Kassu Zurmi: Waƙar ‘Yan Jabanda)

 

Wannan waƙa dai ‘yan tauri aka yi wa ita kuma ‘yan taurin garin Jabanda. Kassu Zurmi ya alamtar da raunukan da ‘yan tauri kan yi wa junansu ta hanyar ba kowane tabon rauni suna. Idan aka sari mutun ga allon bayansa raunin zai warke ya bar rame a baya. Wannan rame shi ne Kassu ya kira rijiya a cikin harshe waƙoƙin ‘yan tauri. Haka kuma tabon da mutum ya samu bayan saran da aka yi masa a goshinsa shi ne mawaƙin ya kira tsayin wata. Akwai kuma wani sara da ‘yan tauri kan yi wa junansu ga damtse daidai tarin tsokar da ake kira ƙwanda. Idan aka yi wa mutum rauni a wurin, to hannunsa zai juye ya kuma zamo marar amfani. To wannan sara na takobi da ‘yan tauri kan yi shi ne Kassu ya alamtar da shan doguwa.

A mashahuriyar waƙar nan mai suna, Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya, akwai wannan kyakkyawan alamci:

Mu dai ilmi muka tambaya

Ko a London ko a Arebiya

 (Sa’adu Zungur: Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya)

 

Ilmin boko wanda Turawan mulkin mallaka suka kawo a ƙasar Hausa shi ne kalmar birnin London ta tsaya a Matsayinsa, a yayin da kalmar ƙasar Makka, wato Arebiya, ta tsaya a matsayin ilmin Addinin Musulunci wanda Hausawa suka sani.

Shi ma Alƙali Bello Giɗaɗawa ya yi amfani da salon alamtarwa a yayin da yake nasiha ga ‘yan uwansa game da abinci da abinsha. Ga baitocin da suka ƙunshi salon:

Ya ɗan uwa na yi horo ka ji ni

Ka bar shan abin da ka sa ma jununi

 

Luddai da ɗan cokali sun ishe ka

Batun kurɓe-kurɓe ya janye gare ka.

 (Alƙali Bello Giɗaɗawa: Bargon Hikima)

 

A bayyane take cewa fura ce ‘luddai’ ya tsaya a madadinta, a yayin da ‘cokali’ ya tsaya a maimakon abincin Hausawa, misali dangin shinkafa da aka dafa irin su sakko da surundu. ‘Kurɓe-kurɓe’ kuwa alamci ne na abubuwan da ke sa maye, wato giya.

A ƙarshe bari mu kawo wani misali mai shigen irin na Kassu Zurmi. A wannan misali mawaƙi bai fassara kalmar da ya yi salon alamtarwa da ita ba. Mene ne mai karatu zai ce mawaƙin ya alamtar?:

Wansu mata sun san ni na san su

Su su Hassi ba wansu tamkassu

Ta yi kwarce in so ta na ƙi su

Tun da na bar Daje wadda taf fi su

Ko hali ballanta ƙohoninta.

 (A.A. H. Wurno: Waƙar Mairi ‘Yar Marsa)

 

Salon laƙabi

Wannan salo ne mai kama da na kinaya amma fa shi bai cikin nau’o’in salon siffantawa. Da shi ne mawaƙi kan ja ma’anar kalmar da yake amfani da ita tamkar mai jan alewa a cikin waƙarsa. Wato dai salon laƙabi shi ne amfani da wata kalma ko ƙumshiyar tunani a cikin waƙa wadda ko bayan ma’anarta da aka sani, tana tattare da wata ma’ana daban da wadda ke a zahiri cikin waƙar. Sannan kuma da ma’anar zahiri ce wadda kalmomin laƙabi suka ayyana a cikin waƙar ne mai karatu zai hango ɓoyayyar ma’anar.

Salon laƙabi, a mafi yawan lokuta, yakan ɗauki baitoci da yawa ko ma waƙa sukutun. Misalin da za a iya bayarwa a nan shi ne waƙar Alƙali Bello Giɗaɗawa wadda ya kira, ‘Tsuntsuwa Ma Ta Biɗi Shawara Balle Mutum’[24]. A cikin wannan waƙa za a lura da cewa mawaƙin ya ba ‘yar tsuntsuwa muƙamin talakka a cikin ƙasa, shi kuwa kunkuru aka ba shi muƙamin ‘yan ciko, masu sayen hatsi su kimshe sai talakkawa sun matsu. Saboda wannan salo da aka yi amfani da shi a cikin waƙar sai wata ma’ana ta waƙar ta tusgo. Ma’anar kuwa ita ce, ‘zaluncin ‘yan kasuwa da son kansu shi ke haifar da wahala ga talakawa wadda kuma ba ta da magani idan ba hukuma ta tsayu ga aikin ba, wato ta hukumtar da ‘yan kasuwa sannan ta wadatar da talakawa da abinci ta hanyar da talaka zai iya saye ba tare da matsuwa ko tsada ba’. Ta haka ne sai wannan salo ya mayar da waƙar cikin zubin da za a iya kira zubin yanka – suka mai gauni. A taƙaice, mawaƙin yana cewa magana guda ta gaskiya ita ce hukuma ba ta yin aikinta a halin da mawaƙin ya rubuta waƙar. Ga waƙar:

 

1Yar tsuntsuwa bisa bisshiya ga misali

 Ta tsai da ni ta ce tana da su'ali

 

2Na ce maraba da ke daɗa mi kinka ce

 Don na ga kin gigita kin yi nukuli

 

3Ta ce akwai ajabi ga wannan zamani

 Ga kunkuru har ya zamo dillali

 

4Ya kwashe tsaba ya saye ya kandame

 To kai ina tsuntsu ka samun wali

 

5Shi ba shi kyauta ba shi yin sadaka da su

 Sai dai ya sa tsadad da tac cika tswali

 

6Daɗa shawarakka nike biɗa yaya nikai

 Don bai nufin alher nufi nai mali

 

7Farko hukuma za ki je ki faɗa musu

 Ki faɗi ki ce ƙunƙun ga ya yi gululi

 

8Ita ko hukuma za ta sa a yi bincike

 Kuma za ta kam mai don shi ba ta dalili

 

9In ba dalili sai ta birkice ja'iri

 Ta bugai ga ƙwarya nan da nan shi yi waili

 

10Sannan ta buɗe rumbunan tsaba duka

 Tsuntsu ya san tsaba bi gairi jidali

11Na gode wannan shawara ita za ni bi

 Mai bin nasiha ba shi samun zilli

 

12Don an yi horo ɗan’adam shi yi shawara

 Komi na alheri shina ciki zat tuli

 

13Ga tsuntuwa har ta biɗo a yi shawara

 Balle mutun mai hankali mai hali

 

14Na yo salati da sallama na sallama

 Bisa wanda duk yaf fi mu na yi tawassuli

 

15Tammat bihamdillahi waƙar shawara

 Mai yin ta kwanya tai ka ƙara tala’uli

(Alƙali Bello Giɗaɗawa: Tsuntsuwa Ma Ta Biɗi Shawara Balle Mutum)

 Gamin Bauta

Gamin bauta salo ne wanda manazarta suka bayyana da cewa gwama kalmomi ne a jere, domin su haifar da wata ma’ana ta daban saboda an yi musu haɗin da ba kasafai akan yi shi a maganar yau da kullum ba[25] Ga alamu Ɗangambo ya kira wannan salo haka ne saboda ɗabi’ar nan ta Hausawa ta sanya takalma ta yadda kowace ƙafa take saye da wani nau’i na takalme dabam. Hausawa kan yi haka ne a dalilin rashin hali, ba wai don suna so ko sha’awar yin haka ba.

A cikin waƙar ‘Yin Tarbiyya’ akwai kyakkyawan misali inda mawaƙi ke cewa:

Su ko mallamai dukiya

Suka so sai girman duniya

Duka mai wa’azin ga da kaj jiya

Aika mai can wazobiya

 Bai koma yi ma sharholiya

 

Mi ag gyara mai tambaya

Sai an sawo rigar ƙaya

Ko shaiɗani in ya ƙiya

Ladabi a yi mai bulaliya

 Shi yi jarun sai ya sha wuya.

 (Alƙali Haliru Wurno: Waƙar Yin Tarbiyya)

 

 A sanin Bahaushe rigar saƙi ko yadi akan sa ba rigar ƙaya ba. A nan saboda Haliru ya yi gamin bauta tsakanin riga da kuma ƙaya, sai ya haifar mana da ma’anar mulki mai gauni wanda ba sani ba sabo a cikinsa kowa ya yi za a yi masa, mulki wanda kuma babu sakewa a cikinsa.

Shi kuwa Sa’idu Faru cewa ya yi:

Bajini ɗan gagara amalin sarakuna

Toron giwa ɗan Abdu ƙanen Ali ɗan Iya

 (Sa’idu Faru: Alhaji Macciɗo Jikan Mamman)

 

Amalin raƙuma aka fi ji ba na sarakuna ba. Amfani da salon gamin bauta da mawaƙin ya yi tsakanin amali da sarakuna ya haifar mana da ma’anar cewa Sarkin Kudu Alhaji Macciɗo ɗa ne ga sarkin sarakuna wanda kuma ya kai ƙololuwa ga zama sarki, ba wata sarauta wadda ta rage masa ya samu, ko wata sarauta wadda ta fi tasa. Wato Macciɗo ɗa ne ga Sarkin Musulmi, a ƙasar Hausa kuwa ba sarautar da ta kai, bale ta fi sarautar Sarkin Musulmi.

 

g) Kambamawa

Idan mawaƙi ya yi zuƙu cikin magana, wato ya ƙara mata gishiri, a taƙaice ya bayyana abu fiye da yadda yake a haƙiƙani, za a ce wannan mawaƙi ya yi amfani da salon kambamawa. Dubi abin da Muhammadu Rabi’u Saulawa ya ce game da masoyiyarsa:

Wannan mata mai kyan sifa

Kin mamaye matan duniya

 (M.R. Saulawa: Gurin Zuciya)[26].

 

Anya kuwa mawaƙin ya ga dukkan matan da ke duniya? Idan ma bai gane su ba, anya kuwa ya karanta ko ya ga hotunan duk matan duniya? Gaskiyar magana ita ce ai salon kambamawa ne mawaƙin ya yi amfani da shi domin ya bayyana yadda tsananin kyawon masoyiyarsa ya kai matuƙa.

Shi kuwa Sa’idu Faru cewa ya yi ba mutane ba har shuke-shuke da dabbobi ƙaunar mai gidansa suke yi:

Babban daji kake ɗan Abu

Ko icce ko namun dawa

Ko manya ko ‘yan ƙanƙane

Da mutum da dabba da itatuwa

Kowa ƙamnan Mamman shikai

Mamman jikan Attahiru

Baba na Sidi Mamman gwarzon Cika

 (Sa’idu Faru: Gardaye Zo Ka Yi Man Iso)

 

A cikin wannan baiti salon kambamawa ya haifar da ma’anar da ke nuna yadda farin jinin Muhammadu Macciɗo Sarkin Kudu yake. Farin jininsa ya kai intaha, ɗan Adam ma bai iya bayyana shi.[27]

 

Amfani da Karin Magana

A babi na ɗaya an ambaci cewa mawaƙi yana daga cikin masu ƙirƙiro karin magana. Yana daga cikin masu ƙirƙiro da adana wasu al’adun al’umma ke nan. A nan ba sai an tsawaita bayani kan misalai ba. Mai karatu yana iya waiwayen babi na ɗaya don ganin misalan da aka bayar a ƙarƙashin sakin layi na ‘Mawaƙi Maƙerin Maganganun Hikima Ne’. A nan za a mai da hankali kan dalilan da kan sa mawaƙi amfani da karin magana.

Mawaƙi kan kawo karin magana cikin waƙarsa saboda wasu dalilai da suka haɗa da:

a) yin ishara

b) ƙarin bayani

c) nuna ƙwarewa ga harshen Hausa

d) adana karin magana

da sauransu.

a) Don Yin ishara

Ishara tana nufin nuni zuwa ga wani abu, la’alla abin da ake gani ne kurum ko ake iya kuma taɓawa, ko nuni ga wata magana ko zuwa ga gaskiya. Misali:

Babba laifinsa son zuciya yay yi in

 Ya ƙi bin sidƙu yaransa ram mai sukai

 (Alh. (Dr.) Umaru Nasarawa:Yadda Ya Kamata Najeriya…)

 

A nan mawaƙi ya yi amfani da karin magana domin ya nuna wa mutane cewa idan fa suna son ‘ya’yansu su zamo masu yin ɗa’a da biyayya zuwa gare su, to fa wajibi ne su iyayen su kasance masu kyautatawa da nuna halin tausayawa da gaskiya ga ‘ya’yan ne. Ainihin karin maganan da mawaƙin ya yi amfani da shi shi ne, ‘laifin babba rowa, laifin yaro kuwa ƙiuya’. A gaba kaɗan mawaƙin ya ƙara yin wannan nuni da cewa:

An ga daɗi a bar kore ‘yan yara

 Ga wurin wuya ko a ce ba su hili akai

 (Alh. (Dr.) Umaru Nasarawa:Yadda Ya Kamata Najeriya…)

 

A nan ma nuni ne ya yi ta amfani da karin magana da ya yi daidai da, ‘‘Ba a gane manya sai ci ya samu’’ , ko kuma, ‘’Wayon a ci an kori kare gindin ɗinya’’.

A waƙoƙin baka ma akwai amfani da karin magana don a yi nuni zuwa ga haƙiƙanin gaskiya. Dubi wannan misali:

Shiri gama aiki na Dodo

 (Ibrahim Narambaɗa: Gogarman Tudu jikan Sanda)

 

Abin da wannan karin magana ke yin nuni da shi shi ne, samun sauƙin aiki har a kammala shi daidai, ko kuma samun cim ma guri ba da wahala ba, duk sun dogara ne kan shirin da mutum ya yi tun gabanin fara aikin ko neman cim ma gurin. A waƙar da wannan karin magana ya fito, Narambaɗa yana nuni ne da nasarar da gwarzonsa, wato sarkin da ya yi wa waƙar, ya samu ta zama sarki da kuma ci gaban da ya samu wajen gina ƙasarsa har ya tsere wa ‘ya’yan sarauta da ma sauran sarakuna, duka sun samo tushe ne daga irin shirin da sarkin ya yi tun farko. Duk tanadin da ya wajaba ga ɗan sarki ya yi domin ya gadi sarautar gidansu, to wannan sarki ya yi tun yana ɗan sarkin. Haka kuma duk tanadin da ya kamata sarki ya yi domin ya samu nasarar gina ƙasarsa, ya kuma tsere wa sauran sarakuna, to wannan sarki ya yi tanadin.

Mai sauraren wannan waƙa na iya faɗaɗa wannan nuni da Narambaɗa ya yi da cewa, har ma a addinance wannan nuni haka yake, da duniya da lahira duk sai an yi shiri ake samun ɗayansu.

Dubi kuma yadda Kassu Zurmi ya yi nuni zuwa ga yadda yake son ya bayyana Nomau a sauran ɗiyan waƙarsa, ‘Nomau na Magarya’:

Nomau tushen hwaɗa karem masu gari

Torankawan tciya uban Mairogo

Ko hwatara tai yawa takan zam iko

Nomau ko ba ka jin batun masu gari

 

Na Magaji ƙanƙari ba ka jiƙa

Gauɗe ba ka matanki

Baba kaɗe ba ka baka

Nomau tushen hwaɗa karen masu gari

 (Abubakar Kassu Zurmi: Nomau na Magarya)

 

A waɗannan ɗiyan waƙa, waɗanda ke cike da salon kinaya, Kassu Zurmi ya kawo karin maganganu uku a ɗa na biyu da aka rubuta cikin gicciyen rubutu, ɗango/sheɗara/ƙwar na 1 da na 2 da na 3. Waɗannan karin maganganu suna nuni ne ga yadda Kassu ya bayyana Nomau a sauran ɗiyan da waƙar ta ƙunsa. Wato riƙaƙƙen ɗan tauri wanda saboda tsananin talaucin da tauri ya sa wa Nomau, babu wani arziki da ke samuwa ko zaunawa a gare shi tamkar yadda ƙanƙarin tama ba ya jiƙa ko da an saka shi cikin gulbi ko ma teku. Haka kuma Nomau ba a iya yin wani abin amfani ko rufin asiri da shi domin ko an so a yi wani abin amfani da shi ba za a ci nasara ba. Wato Nomau kamar iccen nan ne wanda ba a iya amfani da ɓawansa domin a ɗaure wani abin amfani da shi. Yadda ɓawan nan bai ɗaure ciyawa ko tarin zangarniyar gero saboda da ko an yi ƙoƙarin a ɓaro shi daga iccensa sai ya tsinke tun ba a kai ko ina ba. Ba a yin amfani da Nomau domin a cim ma wani abin amfani da shi a rayuwa, tamkar dai yadda ba za a iya lanƙwasa reshen iccen kaɗe ba don a yi bakar da za a iya harbin wata dabba wurin farauta ba.

b) Don Ƙarin Bayani

Karin magana kan fito cikin waƙa domin yin ƙarin bayani ga babbar manufar baiti ko baitocin da ya fito. Fitowar kan zo kamin ko bayan ko kuma cikin baitin ko baitocin. Dubi yadda Sa’adu Zungur ya yi amfani da karin magana domin ya yi ƙarin bayani kan saƙon da yake son ya isar:

Sai mu je gun Mallam Yahaya

 Can a birnin Gwandu mu kewaye

 

Shaihu Abdullahi haƙiƙatan

 Ya bar mana gadon gaskiya

 

Ilmi hikima addini duka

 Da dabarar sarrafa duniya

 

Aka lalata aka wargaza

 Ga shi yau sai anai mana dariya

 

Babu tsuntsu ba tarko duka

 Walla mun yi hasarar duniya

 (Sa’adu Zungur: Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya)

 

Ta amfani da karin magana mai cewa, ‘babu tsuntsu ba tarko’, Zungur ya ƙara yin bayani kan cewar da ya yi, /Aka lalata aka wargaza/, da kuma can a baya inda ya ambaci abubuwan da Arewa ta yi gado na ilmi, da hikima, da addini, da dabarun sarrafa zaman duniya, duk daga Mallam Abdullahi Fodiyo da ma sauran magabata. Waɗancan abubuwa da /aka lalalata aka wargaza/, haƙiƙa su ne guzurin gina ƙasa da kuma rayuwar lahira, su ne tsuntsu kuma su ne tarko!

Salihu Jankiɗi shi ma yakan yi amfani da karin magana don yin ƙarin bayani ga abin da yake faɗi. Dubi wannan misali:

Manyan daji giwa an nan

Ruwa ba su yami don banza

Wada Mu’azu yai daga ka riƙa

Halin Shehu shi yay yi Bubakar

 (Salihu Jankiɗi: /Bajinin Gidan Bello Bubakar/Ka Buwai Maza Sai Mazan Jiya)

 

‘Ruwa ba su yami banza’, karin magana ne da ke ƙarin bayani ga cewar da Jankiɗi ya yi cewa Sarkin Musulmi Abubakar III manyan duniya ne kamar giwa saboda ya yi gadon halin Shehu Usmanu Mujaddadi. Yadda ruwa ba su yin tsami sai an surka wani abu mai tsami cikinsu, haka shi ma Abubakar da bai yi gadon Shehu Usmanu ba, da kuwa ba zai ɗaukaka cikin sarakuna ba.

c) Don Nuna Ƙwarewa Ga Harshen Hausa

Karin magana yana cikin Hausa mai zurfi. Fahimtar sa sai wanda ya ƙware sosai da sosai ga harshen Hausa da sanin al’adun Hausawa. Mutum ya nare ga magana da harshen ba dalili ba ne na ya fahimci abin da karin magana ke nufi. Wannan kuwa haka shike a kowane harshe. Saboda haka amfani da karin magana cikin waƙa alama ce ta ƙwarewa ga harshen Hausa da sanin al’adun Hausawa.

Mawaƙa kan yi amfani da karin magana saboda dalilan da aka ambata. Haka kuma sukan yi hakan saboda nuna ƙwarewa ga harshen Hausa. Kyakkyawan misali ita ce waƙar “Ko Ba Ka Raƙumi Ka San Cau” wadda Alƙali Haliru Wurno ya rubuta. Sunan waƙar ma cikin karin magana yake. Haliru ya rubuta cewa nasiha ce ya yi ga ‘ɗiyana’, wato ɗalibansa, sannan kuma shugaban makarantar da yake karantarwa cikinta ya umurce shi da ya yi musu nasihar. Gaba ɗayan wannan waƙa cikin karin magana take. Bayan ya yi basmala da salati da furucin gundarin jigo a baiti na 1-9, sai ya ce:

10. Kunun dare bai rashin gashi

Da ƙwari masu faɗowa

 

11. Abokina matso ka jiya

Garan bari tambayar kowa

 

12. Kashi da yawa ina magana

Hadisi na na watsowa

15. Karin magana shina da yawa

 Halan ba ka san da nunawa

 

16. Tsaya ka yi tuntuni ka faɗi

 Ka bar zankam ga amsawa

 

17. Ka lura da masu kushen ka

 Da mai zumɗe da ƙyabtawa

 

 

18. Ka ce maƙiyi masoyi na

 Ka yarda da tashi shiryawa

 

19. Ya shirya fura ya sa nono

 Guba ciki ba ka ganewa

 

20. Kare ka faɗa gidan da yake

 Ganin baƙo da hafsawa

 

Mutum da jin waɗannan baitoci zai fahimta cewa wannan mawaƙi yana ƙoƙari ne ya bayyana irin naƙaltar da ya yi wa karin maganar Hausa. Wannan waƙa ɗauke take da karin magana cikin kusan kowane baiti, kuma baiti ɗari da ashirin da takwas (128) ne tsawonta.

d) Don Adana Karin Magana

Bayanin da aka yi kafin wannan kaso na (d) zai wadatar a gane cewa waƙa dai rumbun adana karin magana ne. Saboda wannan manufa ce a wani lokaci mawaƙa kan yi amfani da salon karin magana cikin waƙoƙinsu.

 

Gangara

A kan samu baiti a cikin waƙa wadda kan ƙunshi wani ɗango wanda zaren maganarsa bai cika ba sai a wani ɗango mai bin sa. To irin wannan saƙa ita ce ake kira salon ganagara a nazarin waƙa. Ibrahim Narambaɗa ya yi amfani da wannan salo kamar haka:

Ai sai da so aka kyauta

In babu so ba a yin komi

Dokin nan da kab ba ni kyauta jiya

Ko da uban mutum as sarki irinani yakan hausai

 (Ibrahim Naramdaɗa: Sarkin Gorbi Na Isa)

 

A wanann misali ɗango na uku bai cika ba ta fuskar ma’ana sai da ya haɗa da ɗango na huɗu.

A ɓangaren rubutattun waƙoƙi ma akan sami salon gangara kamar yadda kowane baiti daga waɗannan baitoci yake ɗauke da shi salon:

Abin nema a garemu ziyaran

Wannan ɗa mai daɗin suna.

…..

Da Alfazazi da mai Tahmisi

Sun yi ma Imru’u ko-ta-kwana

 (Alhaji (Dokta) Aliyu Narambaɗa: Tsarabar Madina)

Kowane ɗangon fari na kowane baiti daga waɗannan baitoci ya dogara ne a kan ɗango mai bi masa ta fuskar ma’ana. Wato ɗangon fari ya gangara zuwa na biyunsa.

 

Saɓi-Zarce

Salon saɓi-zarce salon gangara ne babba. Salo ne wanda akan ɗauki magana (ko ma a ce wanda kan saɓa/rataya magana) daga wani baiti zuwa mai bi masa. Idan mawaƙi ya fara magana a cikin baiti na uku amma bai kammala ta ba sai a baiti na huɗu ko ma na abiyar, za mu ce mawaƙin ya yi amfani da salon saɓi-zarce.

Idan za a fahimci abin da Sa’idu Muhammadu Gusau ya kira ɗa[28] na waƙa a matsayin baitinta to kuwa a wannan misali akwai salon saɓi-zarce wanda ke da wuyar tantancewa a waƙoƙin baka:

Kuftada da ka sai ma Kuma

Ƙwairo yana roƙon ka sai mai

Ni gaskiya nika hecewa

Don ba ni yin bauta ga banza

Sa’ad da duk kaƙ ƙulla waƙa

Ƙari nikai in ɗora amshi

Ina bugun toho da hauni

 

Tilas kakai domin watarana son kakai

Don a yi ma gudummuwa daɗi gare ta

Ko ni in taimakonai

Baba ƙyale mu da shi

In ya yi ma baƙar magana

Ina nuhin in ɗauke hwansa

 (Abdu Kurma: Waƙar Sarkin Ƙaya Abubakar)[29]

 

A waƙar da Salihu ya yi wa Sarkin Musulmi Abubakar III ana iya kallon waɗannan baitoci biyu na tafe a matsayin waɗanda suka ƙunshi salon saɓi-zarce duk kuwa da cewa ana iya ɗaukar kowanensu matsayin mai cin gashin kansa:

Waƙa dambe da mai ƙarhi tara

Kai na Allah kai na Ma’aiki

Ga jihadi ga alheri

Ga hanƙuri ga ƙarhin arziki

 

Ga muhibba inda Abubakar

Rabbu Allah yai ma ɗaukaka

Gabas da yamma kudu da arewa

Yau darajja kowa Sakkwato

Kway yi gigi yas saki hanya

Babu girmanai nan duniya

Lahira kuma ta kubce masa

Danganen addini ɗan Hasan

 

Mai biɗar shi ga Manzon Allah

Bai sakin hanyar ga ta bi shikai.

 (Salihu Jankiɗi: Shugaban Ɗakin Duniya)

 

A wannan misali za a fahimci cewa maganar da Jankiɗi ya fara a ɗangon ƙarshe na baitin farko ba ta cika ba sai aƙalla ƙarshen ɗangon farko na baitin da ke biye. Wato a kalmar “arewa”.

Idan aka koma ta fuskar rubutattun waƙoƙi gano salon saɓi-zarce ba zai yi wahala ba. Dubi wannan misali.

Fa tushen tarbiyya ne don ka lura

Kula da siffag ga biyu shi a lalura

 

Ka zan yin gaskiya jiddun aboki

Ka bar ƙarya da ke maishe ka doki

 (A.B. Giaɗaɗawa: Magana Cike Ke Sa Gunguni)

 

Duk da maganar da ke ƙunshe cikin baiti na ɗaya jumla ce cikakkaya mai nufin ma’anar da ke cewa: kula da sifofi biyu lalura ne domin yin haka tushen tarbiyya. Cikakkiyar ma’ana da fahimta ba su ayyana sai mutum ya haɗa wannan baiti da wanda ke bi masa. Idan mutum ya yi haka ne zai fahimci cewa mawaƙin yana nufin,

Yin gaskiya jiddun da kuma barin ƙarya su ne sifofi biyu waɗanda kula da su lalura ne domin su ne tushen tarbiya.

 

Saboda haka ashe ke nan Alƙali Bello Giɗaɗawa ya yi amfani da salon saɓi-zarce. Saɓi-zarce kuwa ya fi ƙarfi ta fuskar ma’ana ne ba ta ƙirar jumla ba.

Shi kuwa Alhaji Aƙilu Aliyu ga yadda ya kawo salon:

Faufau ba ka ga ba ka ji mai yare ba

Ya nuna ƙi ga kininsa sai mu Hausa

 

In har akwai biyu masu jin Turanci

Kuma ga na uku cikarsa duk ‘yan Hausa

 

In kai na ukkun ba ka jin Turanci

Biyu ɗin na tare da kai sukan ƙiye Hausa.

 (Alhaji Aƙilu Aliyu: Hausa Mai Ban Haushi)

 

Baiti na biyu da na uku su ne ke ɗauke da salon saɓi-zarce. Maganar da Aƙilu Aliyu ya ɗauko farko a baiti na biyu ba ta kammala ba sai a ƙarshen baiti na uku.

A waƙar da wannan mawaƙi ya yi wa birnin Legas ya yi amfani da wannan salo a tsakanin baiti na 33 da na 34 kamar haka:

Kuma duk faɗin Nijeriyya

In ban da cikin garin Legas

 

Ba za ka ga yaro Dogo ba

Sai dai ka zo garin Legas

 (A.A. Aliyu: Ƙasaitaccen Gari Legas)

 

Salon saɓi-zarcen da ke cikin waɗannan baitoci, ya shafi fuskar ƙira da ma’anar jumla ne domin idan aka ɗauki baitin farko shi kaɗai ba za a ji ya kammala jumla ba, ba kuma za a samu cikakkiyar ma’ana ba face an haɗa wannan baiti da aƙalla ɗangon farko na baitin da ke bi masa.

A ƙarshe ga wani misali makamancin na waƙar Legas:

Rashin ilmi ka sa ka musu

Ka zo ka jiya ka bar cewa

 

Batun ga da niy yi shirme na

A zargan ba ni fasawa.

 (Alƙali Haliru Wurno: Ko Ba Ka Raƙumi Ka San Cau)

 

Lalurar Waƙa

Salon da ake kira lalurar waƙa salo ne da ya karɓi sunansa domin dole ce ta haifar da shi, kuma kalmar lalura, wadda asalinta ta Larabci ce, ma’anarta ke nan wato “dole” ko “tilas”. Hausawa kan ce “Dole ba ta rasa ɗakin kwana”. A addinance ma haka lamarin yake.

Abin da wannan salo ke nufi shi ne karya wata ƙa’ida ta harshe ko waƙa. Kasancewar ɗangogin waƙa daban da maganar yau da kullum muhimmiyar sifa ce ta waƙa ba lalurarta ba. Wato dai idan za a yi wa waƙa da mawaƙa adalci kamata ya yi a fassara salon lalurar waƙa da cewa salo ne wanda ke kawo kalma ko magana wadda ta so ta bijere wa waƙa amma sai waƙar ta gyara mata zama har ta karɓu ga harshe a wannan muhalli nata kurum.

Fitattun dalilai biyu ne ke haifar da salon lalurar waƙa, kari da ƙafiya. ‘Saƙo A Hannun MuminI’ kyakkyawan misali ne na salon lalurar waƙa wanda bukatar dawwamar da karin waƙa ke haifarwa. Dubi yadda mawaƙin ya riƙa rarraba kalmomin ɗaiɗaya zuwa bibbiyu cike da fasaha ta yadda kai mai karatu ko saurare za ka ɗauka cewa ko a maganar yau da kullum kalmomin za su zo:

Natsuwa ta faskara nan garan

Bege shina zautar da ni

 

Sai hankalina ya tuman

Ya a kan rashin tafiya da ni

 

Don ni Aƙilu akwai-ya-ba

Bu na zam a wannan zamani

 

Ya Rabbana dawo da su

Kuma lafiya su tarar da ni

 

Amina amin Rabbu a

Min don huwancewar Gwani.

 

Begenku ya zautar da ni

Tafiyarku ta shagalar da ni

 

Ku yi gaisuwa ga Rasulu ka

Kan Alhassan ku isar wa ni.

 (Alhaji Aƙilu Aliyu: Saƙo A Hannun Mumini).

 

Kalmomin da salon lalurar waƙa ya rarraba a cikin waɗannan baitocin su ne /tamanya/ da /akwai-ya-babu/ da /amin/ da kuma /kakan/.

Shi kuwa Alhaji (Dokta) Muhammadu Shata Katsina[30] kalmomin ne ya ƙaƙƙara wa tsawo a cikin waƙarsa ta yabon Ummaru Gwandu. Dubi koken da Shata ya yi wa tauraronsa a cikin dirobobi, Ummaru Gwandu:

 

Ya tafi Nijer

Sanda barandami

Da ya tafi Nijer

Ya tai da Jamma

Ya bar ni birni

Ni da Ka-kanawa

Ummaru ɗan Duna na Gwandu

 

Da ka tafi Nijer

Ummaru Gwandu

Sanda ka komo

Ka ɗauke Jamma

Gun wa ka bar ni

Ummaru-ru Gwandu.

 (Alhaji Shata: Ummaru Na Gwandu)

 

A baiti na farko Alhaji Shata ya ƙara wa kalmar Kanawa tsawo da ‘ka’ zuwa Ka-Kanawa ta hanyar maimaita gaɓar farko.

A baiti na gaba kuwa sai mawaƙin ya ƙara wa kalmar Ummaru tsawo zuwa /Ummaru-ru/ ta hanyar maimaita gaɓar ƙarshe.

To duk waɗannan ƙare-ƙare da Alhaji Shata ya yi misali ne na salon lalurar waƙa, kuma bukatar daidaita karin waƙa ta haifar da salon. Shi kansa salon lalurar waƙa wanda Shata ya kawo a baiti na farko, wato maimaita gaɓar farko ta Kanawa salo ne wanda watakila ba azarɓaɓi ba ne idan aka ce wannan mawaƙi shi ne ya fara yin sa a cikin waƙoƙin Hausa, aƙalla na baka.

Haka kuma Alhaji Shata ya yi amfani da wannan salo ta hanyar maimaita kalma idan ta kasance mai gaɓa guda ce. Misali

An ƙaraurawa

Jirgi zai tashi

Mai shiga

Kai sauri ka hwaɗa

Mai sauka

Kai sauri ka sauka

Jirgi ba ya jiran u-uban wani

 

Ummaru ɗan Duna na Gwandu

Don haka Ummaru

Bai dakata ma-ma kowa

 (Alhaji Shata: Ummaru Na Gwandu).

 

Kalmar da masu nahawu za su kira karan-ɗori wato ‘ma’, ita ce Shata ya ƙara wa tsawo a baiti na ƙarshe, sai ta zamo ma-ma. Wani misali shi ne inda Shata ya ce:

Kura mabi dare

Ummurun gidan Ɗan Duna

 

Amale mai kwarjini

Da-da kaya

 (Alhaji Shata: Ummaru Na Gwandu)

 

Neman ƙafiya shi ne abu na biyu mai iya haifar da amfani da salon lalurar waƙa. Idan haka ta kasance, mawaƙi kan iya ƙara wa kalma tsawo ko ya gutsure ta. Haka kuma yana iya ƙara wata kalma ko ya shafe wata, duk a fafutukarsa ta nemar waƙarsa ƙafiya. Har ila yau mawaƙi kan iya karya ƙa’idar nahawu.

A waƙarsa ta yabon Annabi Muhammadu (S.A.W) Alƙali Alhaji Shehu Alkanci ya nemo ƙafiyarsa ta amfani da salon lalurar waƙa na ƙari da shafewa a cikin wannan baiti.

Annabi dum yabonai kamas sabo na ba shi shuɗewa

Tun farko yabo nai akai haƙ ƙarshe ba a ƙarewa

Komi anka ce mai haƙiƙan na ba za a sokewa*

Girmanai hawa ɗai shikai kullum ba za shi duƙawa*

 Don Allahu yad ɗaukaka shi ga talikai ga danginai

 (A.A.S. Alkanci: Yabon Annabi Muhammadu, S.A.W)

 

 A ɗango na uku mawaƙin ya ƙara wa kalmar ‘soke’ tsawo zuwa sokewa, sannan kuma ya shafe ba wadda ta kamata ta zo a ƙarshe. A ɗango na huɗu ma haka ya yi. Wato ya ƙara wa kalmar ‘duƙa’ tsawo zuwa ‘duƙawa’ sannan kuma ya shafe ba. Ya kuwa yi haka ne domin ya samo ƙafiyar ‘wa’ wadda ita ce amsa-amon ciki na wannan baiti.

Shi kuwa Alƙali Bello Giɗaɗawa a waƙar da ya yi ta tunawa da ziyar Sarauniyar Ingila a Nijeriya a shekara ta 1950 Ga abin da yace:

Na yo ta don in bayyana mata godiya

Domin ziyara wadda tai Najeriya.

 

Ta bar gida ran Jumu’a haka nij jiya

Ishirin sa’annan ga bakwai na Janairiya

 

Ta tashi Jos an ce Makurɗi fa tab biya.

Kuma ta wuce ta je jiha Magabasciya

 (Alƙali Bello Giɗaɗawa: Yabon Sarauniya)

 

Watan Janairu shi ne aka ƙara wa sunansa tsawo zuwa Janairiya a baiti na biyu, a yayin da Gabas ta ƙaru da tsawo da ta sami ‘ma’ da ‘ciya’ a baiti na ƙarshe. Mawaƙin ya yi haka ne domin ya tabbatar da amsa-amo ciki na /ya/.

Dangane da cewar da aka yi akwai karya ƙa’idar nahawu wajen amfani da lalurar waƙa, baitocin waƙar Haliru Wurno kyawawan misalai ne:

 

Sayen girma da zalunci da ƙeta

Da babakere hanyar ƙetare ta

 

Da rana uba uwa da sarakunka

Kamar bayinka na ji abin gudu ta

 

Ana yawo da kai sake babu hulla

Ana wani tsalle wai na gudun ƙazanta

 

 

Bale mata idan sun shace gashi.

Ji ɗankwalin ga hannu ake riƙe ta

 (Alƙali Haliru Wurn: Muhimmancin Al’adunmu Da Haɗarin Rungumar Na Ƙasashen Waje)

 

A ƙarshen baiti na biyu Haliru ya yi amfani da /ta/ a maimaikon kalmar lamiri ta ‘na’. Haka ma a ƙarshen baiti na huɗu ya yi amfani da kalmar lamirin /ta/ a maimaikon kalmar lamiri ta ‘na’. Haliru ya yi haka ne domin ya daidaita amsa-amon ciki na waƙarsa, wato /ta/.

Dibilwa

Amfani da kalma ɗaya mai iya ɗaukar fiye da ma’ana ɗaya a wurin da ta fito a cikin waƙa, ko kuma amfani da kalma ɗaya fiye da sau ɗaya amma kusa da juna (ɗangogi biyu ko kuma cikin baiti guda) amma tare da saɓawar ma’ana shi ne ake nufi da salon dibilwa a fagen nazarin waƙa. A taƙaice ɓad-da-bami ne. Wato idan mai karatu ko sauraren waƙa bai natsu sosai ba take ne zai kasa fahimtar abin da mawaƙi ke cewa. Haka kuma salon dibilwa yakan nuna tsananin gwanintar mawaƙi da kuma yadda Allah ya sallaɓe wa mawaƙi harshe.

A misalin da aka kawo daga waƙar Shata mai suna Ummaru na Gwandu akwai dibilwa a wanann baiti:

Da ka tafi Nijer

Ummaru Gwandu

Sanda ka komo

Ka ɗauke Jamma

Gun wa ka bar ni

Ummmaru-ru Gwandu

 (Alhaji Shata: Ummaru Na Gwandu)

 

Tilas ce ta sa aka rubuta kalmar sanda matsayin kalma guda domin rubutu ne muke yi ba magana ba. Amma yadda ta zo daga mawaƙin (wato Shata), daga bakinsa ne ta zo ba daga alƙalaminsa ba. Idan kuwa haka abin yake, to kuwa ana iya rubuta ‘Sanda’, kuma ana iya a rubuta ‘san da’, a matsayin abin da mawaƙin ya ce cikin waƙarsa. Babu abin da zai barkace waƙar a dalilin wannan bambancin fahimta. Hasali ƙaruwa ce hikimar waƙar za ta yi.

Idan ka ɗauka cewa ‘Sanda’ ne Shata ke nufi to waƙarsa a kan hanya take domin kuwa laƙabin mai suna Umar a ƙasar Hausa shi ne ‘Sanda’. Furucin da za a yi wa wannan laƙabi, ɗaya ne da wanda za a yi a yayin da za a furta, ‘san da’, wato kalmomin da ke nufin ‘lokacin da’, ko ‘sa’ilin da’, ko kuma ‘yayin da’. To idan ka ɗauka cewa abin da Shata ya faɗa shi ne, /san da/, har wa yau dai waƙarsa a kan hanya take domin ma’ana tana nan. Wato sai ma’anar abin da Shata ya ceta kasance kamar haka:

Lokacin da ka tafi Nijer, Umar ka kuma dawo ka ɗauke Jamma, shin a wurin wa ka bar ni?

 

A cikin waƙarsa, ‘Aikin Hajji Ya Wuce Wasa, Alhaji Aƙilu Aliyu ya faɗa mana cewa Alhasan na Mazugal ne ya biya masa kujerar zuwa hajji. A wajen nuna godiyarsa ga wannan bawan Allah, Aƙilu Aliyu ya yabe shi yana mai cewa:

Alhaji Hasan hasan ɗin ne

Halinsa ƙwarai na kirki ne

Mai miƙa wuya ga Allah ne

Mai imani cikin rai ne

Ba za shi biyunta Allah ba

 (A.A. Aliyu: Aikin Hajji Ya Wuce Wasa)

 

A wannan baiti Aƙilu Aliyu ya yi amfani da salon dibilwa da kalmar Hasan. Wato kalmar ‘Hasan’ ta farko sunan wanda ya biya masa kujera ne, a yayin da ‘hasan’ ta biyu take nufin mai kyawon hali ko na kirki a cikin harshen Larabci. Saboda haka ko kusa ba wai maimaita kalmar Hasan ne mawaƙin ya yi ba balle mu ce wai ya yi amfani da salon lalurar waƙa a inda bai dace ba.

Ga kuma wani misali makamancin na Aƙilu Aliyu:

Na yo lisafi ƙaimun adadinta ke nan,

Alhaji ƙa’imun na ga begen Annabi ga

 (A.A. H. Wurno: Jirgi)

 

A wannan baiti da ya fito daga waƙar yabon Annabi (S.A.W) mai suna Jirgi, Haliru Wurno ya yi amfani da salon dibilwa da kawo kalmar ‘ƙa’imun’. A ɗango na farko abin da ake kira ramzi (wato kawo lissafi musamman na tarihi, amma a nan na yawan baitoci ne). Shi ne Haliru ya kawo idan aka tayar da ramzi sai mu sami 141 wanda shi ne adadin baitocin wannan waƙa mai suna jirgi.

A ɗango na biyu kuwa kalmar ‘ƙaimun’ a ma’anarta cikin harshen Larabci Haliru ya kawo ta. Wato mawaƙin yana nufin cewa ‘shi tsayayye’ ne ga yabon wannan Annabi.

Baitin Mu’azu Haɗeja wanda waƙar ‘Halayen Mutane’ ta ƙunsa tauraro ne a fagen amfani da salon dibilwa:

Kai ka isa da isarka kai ne mai isa

Ka isad da masu isa, isa in sun isa

 (Mu’azu Haɗeja: Halayen Mutane)

 

“Allah mai yi da ikonsa, kuma mai cikakken iko ne. Shi ne mai kai waɗanda za su kai ga muƙamin da kowa ke buri amma idan waɗannan sun cancanta”. Wannan shi ne abin da kalmar isa ke nufi a cikin wannan baiti. Babu almubazzaranci da kalmomi ko da sau ɗaya a cikin baitin.

Shi kuwa Kassu Zurmi ya so ya ɓatar da iyayen ‘yan matan da suka zaɓi Shayi domin su aure shi. Kassu dai yana son iyayen ‘yan matan nan su fassara kalmar /ɗa/ ta ma’anar da ke nufin cewa Shayi mutumin kirki ne, alhali shi a wajensa (Kassu) yana nufin Shayi mutum ne wanda iyayensu suka haifa, illa iyaka. To amma ina! Ai iyayen ‘yan matan nan sun fi Kassu naƙaltar harshen Hausa. Sai suka nuna masa cewa suna sane da salon dibilawa da ya yi amfani da shi. Ga dai baitocin waƙar:

Amma fa ku ba shi in kuna ba shi

Na Abu shaye dai ɗa ne.

 

Sunka ce ba haka munka so ba ɗan yaro

Ai mun san ɗa ne tun da anka haihe shi

Ba mu labari in akwai gidan kirki

 (Kassu Zurmi: Shayi Ɗan Gidan Labbo)

 

Ala tilas Kassu ya yi watsi da salon dibilwa bayan wannan jawabi da tsoffi suka yi wadda ta nuna masa cewa sun gane ɓulonsa.

 

Hira

Idan baitocin waƙa suka ƙunshi muryar mai magana fiye da ɗaya, wato, mawaƙi ya ƙaddarta da shi da wani ne ke magana, ko kuwa wasu masu magana biyu ko fiye ne ke wa juna magana, to a fagen nazarin waƙa sai a ce mawaƙi ya yi amfani da salon hira a cikin waƙarsa. Mai karatu ko sauraren waƙa zai ji muryoyi na masu magana a cikin waƙar.

Salon hira yakan taimaka wa mawaƙi a ƙoƙarinsa na isar da saƙonsa ta hanyar sa mai saurare ko karatu ya zamo ya ƙara kusantar mawaƙin. Wato sai mai saurare ya ji daga bakin waɗannan mutane ne mawaƙin ke magana, ba wai daga bakinsa shi mawaƙin ba.

Alhaji Kassu Zurmi yana daga cikin mawaƙa masu amfani da wannan salo sosai. A waƙarsa ta Shayi Ɗan Gidan Labbo ya yi amfani da salon a wurare da dama. Watakila mafi burgewa a waɗannan wurare shi ne inda salon ya haɗa da shi kansa mawaƙin da kuma iyayen ‘yan mata. To amma ko wurin da salon ya ƙunshi Shayi da budurwar da ta zaɓe shi, ba a baya yake ba a wajen burgewa:

Can ana rawa tac ce yaka Ɗan gidan Labbo

Yat taho yana takawa gu ‘yan rawa

Tak kau da kanta yarinyas Shayi

Taƙ ƙi dubo shi

Hay yac ce ke ki yi min magana

Ke kira ni ke habre

Yi min magana kada rawa ta bashe ni

Yi min magana wagga ke ji an sake

Kada hwa ki sa yarin ‘yan rawa ya kamo ni

 

Sai tac ce kai na ƙi yi ma magana

Ashe da ɗaiɗaiɗai dauri za ka kwasam mu

Gida ba ku da ko ƙwara

 

Yac ce mata ke wac ce

Wane ke wac ce

Mun ji ko ‘yan kajimmu ba ka maishe su

Wai kai sai taƙamaw wutaɓ ɓota

Shayi ‘yan mazan ‘yan ya rabbi

Way yi mai tashi.

 (Kassu Zurmi: Shayi Ɗan Gidan Labbo)

 

Nasarar da Kassu ya samu saboda amfani da salon hira a waɗannan baitoci ita ce, da bambancin haliyyar da Shayi yake ciki da wadda ‘yarinyar take ciki. Shi dai Shayi ana iya fahimtar cewa da farko dai cikin murna ya karɓi gayyartar da ‘yarinyarsa ta yi masa na ya shigo filin rawa. To amma nan da nan sai aka gane shi ya shiga cikin damuwa. Wannan damuwa ta same shi ne saboda yarinyar ta ƙi ta yi masa magana, haka kuwa abin da zai sa yarin ‘yan rawa ya kama Shayi. Idan haka ta auku kuwa ya yi kumya. Wannan ita ce haliyyar da salon hira ya cusa ga Shayi.

Ita kuwa ‘yarinyar Shayi za a ga tana cikin haliyyar fushi. Ta cika da fushi, fashewa kurum ke da saura. A ƙarshe dai ta fashe ɗin domin mun ji irin kalaman da ta yi wa Shayi na tozartawa. Wannan fashewa da fushi ta ƙara fitowa fili idan aka yi la’akari da cewa bayan da ta yi maganar farko, wato wadda ta ƙare da, /Gida ba ku da ko ƙwara/, shi kuma Shayi ya tambaye ta da /ke wac ce/, sai Kassu (mawaƙi) ya koma gefe guda ya bar mu da su muna jin maganarsu kai tsaye. Wato Kassu bai ce “sai tac ce” ba kamar yadda ya yi a can baya. Rashin yin wannan furuci na mawaƙin ya daɗa nuna mana irin ciccikar da yarinyar Shayi ta yi da shi.

Shi kuma Usman Sa’ad Zuru ya yi amfani da salon hira domin ya faɗakar da mutanen Nejiriya ta Arewa dangane da siyasar da ake batun yi, wato siyasar Jumhiriya ta biyu wadda aka yi tsakanin 1978 zuwa 1983. Salon ya ƙunshi mawaƙin shi kansa da kuma wani tsohon ɗan siyasa daga kudancin Nijeriya. Ta amfani da wannan salo Usman Sa’ad ya sami nasarar faɗakar da mutanensa dangane da yaudarar da yake hangen ake da niyyar yi musu:

Na ishe su a bakin rafi

Sun yi gungu yara da tsoffi

Har da goga sarkin laifi

Jagoran ‘ya’yan wofi

Na faɗa mashi ‘yar maganata

 

Tsofa daɗa an lalace

Ka dawo nan kay yi kwance

Maganar sata ka mance

Ya ce, ai na iya ƙwace

Sata kuma ba ni barin ta

 

Shawara aka yi a wurin ga

Zan biɗo auren wata mata

 

Nac ce mashi ni maganata

Nika son fa ka ban amsarta

In ka auro wannan mata

Yaya maganar jama’arta

 Mu ne tsakiyar jami’arta

Yac ce zai gyara Arewa

Kayansu fa zai ƙwacewa.

A wurin da ba su ruɓewa

Babu mai gane ajiyata

 

Kuma in rufe hanyassu

In tankwafe duk manyansu

Makarantu in rushes u

Janaral fosofis mu hana su

Jami’a in sa a rufe ta

Nan mun matsu ba mu sakewa

Kuma ba filin ƙarawa

Wasu zam maishe su Arewa

Ta fi nan fili mai yalwa

Don zuwa gaba mu gade ta

Na ce mashi na ji nufinka

Ba ka son wasu sai danginka

Matan nan ba ta fa son ka

Tsohon jaki ita kanka

Ka yi nisa da wannan mata

 (Usman Sa’ad Zuru: Gangar Mafarauta)

 

Labari

Sau da yawa akan sami salon labari ya zo tare da salon hira a lokaci guda cikin waƙa. Abin da ake nufi da salon labari shi ne, mawaƙi ya kawo baitoci waɗanda ke bayyana abin da ya gudana tsakanin mutane biyu ko fiye. Da salon labari da na hira duk sukan yi ƙoƙarin shigar da mai saurare ko karatu cikin lamarin da mawaƙi yake ciki

Lokacin da Haliru Wurno ya so ya bayyana yadda aka yi ya rubuta waƙar da ke a gaban mai karatu sai ya yi amfani da salon labari. Yin haka kuwa ya fito mana da muhimmancin da Haliru ya ba rubuta irin wannan waƙa. Ga baitocin da suka ƙunshi salon:

Waƙar da niy yi yabon mutane na tuna

Na wa aminnai ‘yan uwa na yo kina

Wasu ko ga fili nif faɗi nib bayyana

Na ɗaura waƙoƙi ubana yah hana

Ta yabon mutane na bari sai taka.

 

Ya ce da ni waƙar fululu da kas sani

Zunubi akan yi ga yin ta Alhaji yo tuni

Koma yabon Manzo madihun nis sani

Domin madihu siwahu ya’abusu ka sani

Bil aƙli ya ɗana ina horon ka

 

Ya ce tsare halshen ka kar fa ya ja maka

Ka san akwai haɗari ina sheda maka

To ɗauki Alburda Siyar a faɗa maka

Ya ce ina Ishiriniyar da na sai maka

Ko Daliya ga madihu nih hore ka

 

Na ce ma tsoho na jiya ban tasuwa

Na yo Alamtara na gama ta da Ƙulhuwa

Begen Muhammadu Sidi shi nika tarsuwa

Kullum akwai guri cikina mai yawa

In tsara waƙa wadda zan yi yabonka

 (A.A. H. Wurno: Ƙorama).

 

Da yawa cikin waƙoƙin Kassu Zurmi (na ‘yan tauri da na ɓarayi) ya saƙa su ne cikin salon labari kamar kuma yadda mafi yawan waƙoƙin Muhammadu Gambu suka ginu ta amfani da salon. To amma fa wannan bai nufin cewa irin waɗannan waƙoƙin baka kurum ne suka ƙunshi wannan salo. Dubi misalin waƙar Sa’idu Faru wadda ya yi wa Sarkin Kudu (daga bisani ya zama Sarkin Musulmi na 19), wato, ‘Gardaye Zo Ka Yi Min Iso’. A cikin wannan waƙa Sa’idu Faru ya yi amfani da salon labari domin ya tabbatar mana da darajar ubangidansa da kuma daɗin da waƙar da ya yi masa take da. A nan ana nufin inda Sa’idu Faru ya ci karo da suda yana kiyo yana kuma rera waƙar da Sa’idu ya yi tare da begen wai Sa’idu ya yi masa irin wannan waƙa.

Salon Tsattsafi[31]

Tsattsafi salo ne da ke nufin kawo wata ƙumshiyar tunani ko cusa wata haliyya a wurare daban daban cikin waƙa ko kuma amfani da wani salo a kai a kai (wato, a yayyafa ko a barbaɗa) cikin waƙa, ko kuma a mafi yawan waƙoƙin marubuci idan gaba ɗayansu ne ake nazari. Tsattsafi a waƙa haka yake kamar ƙyallin taurari cikin sararin samaniya, ko ɗiyan rana (ƙawalwalniya) cikin yashi, ko kuma ƙyallin kwalli wanda ya barbaɗe kan daɓe. Haka nan kuma ya kyautu a lura da cewa salon tsattsafi yakan ƙunshi wasu salailai. Wato ko bayan zamansa salo mai cin gashin kansa, yana iya ya ginu da wasu salailai na daban kamar salon zayyana da na tambaya da na amfani da kalmomi masu kaifin ma’ana da kalmomin fannu da waninsu.

Ta la’akari da wannan ma’ana za a fahimci cewa salon tsattsafi yana da rassa da dama waɗanda suka haɗa da tsattsafin haliyya da na harshe da na al’adu da sauransu. Su ma waɗannan rassa suna iya kasancewa da nasu rassa daban. Wato ke nan idan aka ɗauki waɗannan rassa guda uku da aka ambata ana iya a yi musu taswira kamar haka:

Salon Tsattsafi

Salon Tsattsafi

a) Tsattsafin Haliyya

Yanayin da zuciya take ciki ko kamar yadda Hausawa kan ce, labarin zuciya, shi ne ake kira haliyya. Haliyyoyin zuciya kuwa suna da yawa. Akwai fara’a ko raha, akwai ɓacin rai da fushi da baƙin ciki da murna da nadama/da-na-sani da bege da ƙauna da ƙiyayya da dai sauransu.Saboda haka idan aka ce salon tsattsafin haliyya ana nufin an barbaɗa ɗaya ko fi na waɗannan haliyyoyi cikin waƙa. Wato ke nan ga misali ana iya a sami salon tsattsafin raha ko na fushi ko na bege.

Fahimtar cewa akwai salon tsattsafin haliyya ya dogara ne a mafi yawan lokaci kan alaƙar zuciya da kalmomin waƙa. Zuciyar mawaƙi ko ta manazarci ita ce za ta ji ko ta ɗanɗani ko ta ga ko ta jinjini kalma ko kalmomi masu haliyya cikinsu. A wani lokacin kuma mawaƙi kan yi amfani da wasu salailai domin ya cusa haliyyar cikin waƙoƙinsa. Misali, yana iya amfani da kalmomi masu kaifin ma’ana domin yin haka, kamar inda Sambo Waliyyi Giɗaɗawa ya yi amfani da kalmomin, ‘injoyin’ da ‘yo ni kaina’ domin ya cusa haliyyar nishaɗi da raha a inda yake gargaɗi ga ‘yan matan zamani da ke jinkirta yin aure da hujjar cewa wai suna son su shaƙata ne tukuna:

Ilminki babu amre sharri na

Sheɗan ka ɗunguza ki cikin ɓanna

Ki yo ta ba ki dubin aibi na

Kullun faɗin kikai injoyin na

 

 

Sai radda kig ga ke rasa mai son ki

Duw wanda kin nuhwa bai dubin ki

Mai son ki dauri ya bar shawak ki

Sannan ki sa kiran yo ni kaina

(Sambo Waliyyi Giɗaɗawa: Waƙar To Da Ke Nike)[32]

 

Tsattsafin raha

Wannan ɗaya ne daga rassan tsattsafin haliyya. Akan sami waƙa mai ɗauke da raha a kai-a kai cikin baitocinta. Raha tana nufin abin da ke sa nishaɗi ko ban-dariya (dariya ko murmushi). Sambo Waliyyi Giɗaɗawa da Alƙali Haliru Wurno mawaƙa ne da ke sanya tsattsafin raha a kai a kai cikin waƙoƙinsu. Misali, a waƙarsa mai suna, ‘Gaskiya Mugunyar Magana’, Sambo ya fara da basmala sannan ya faɗi cewa manufarsa ita ce ya ‘kwatsi’, ya yi gargaɗi ga jama’a don su daina aikata munanan ayyuka domin suna cuta wa ƙasa. Har zuwa baiti na shidda maganganunsa duk masu nauyi ne. Amma a baiti na bakwai sai ya jefo raha dangane da alƙalai da ke karɓar rashawa, inda ya bayyana sunan zamani da aka ba rashawa:

 

7.Wani suna garai yanzu hanci anka ce mai

Taɓa hancinka an san nufi don mi a kai mai

Naira za a ba shi kowa ya san nufinai

Ya rufe gaskiya da ƙarfi ya san ta daidai

 Duk wani mumini ba shi yin aiki hakan ga

(Sambo Waliyyi Giɗaɗawa: Waƙar Gaskiya Mugunyar Magana )[33]

 

A ɗango na ɗaya zuwa na uku ne raha ta shigo. Mutum zai fahimci haka ta yin la’akari da wani sunan rashawa, wato ‘hanci’, inda Sambo ya nuna cewa amfani da wannan kalmar a madadin rashawa wani abu ne sabo a harshen Hausa. Haka kuma Sambo ya yi bayanin yadda ake aiwatar da tambayar rashawa da bayar da ita. Ya ce hancinka kurum za ka taɓa sai alƙali ya fahimce cewa za ka ba shi rashawa. Shi ma alƙali haka ne zai yi don wanda ake tuhuma ya fahimce shi. Duk wani da ke a wurin, ko da kuwa mai leƙen asiri ne ko kuwa mai ƙara ne, ba zai gane cewa an yi wa alƙalin alkawarin za a ba shi rashawa ba. Saboda haka ba za a kama shi da mirɗe gaskiya don an yi masa alkawarin rashawa ba.

A baiti na tara da na goma ya sake kawo wannan raha amma dangane da masu aikin kwastan yana mai cewa:

 

9. Kwastam na ganai can cikin daji tsugunne

Wani ko ya shige cikin ofis ya yi zaune

Amma can gida ana yo mishi gine-gine

Na rasa inda yab biɗo kuɗɗin zane-zane

 Ko zinariya yake tonowa ƙasag ga

 

10. Binciki kanka ka ji kwastam ka haɗa da lura

Komi mun sani ka bar wani tad da ƙura

Rimbiɗi sa ka rabki taiki ka kula da gora

In har kab buge ta na san kai anka ƙwara

 Kai ka shiga cikin baƙin takalihu cikin ƙasag ga

 (Sambo Waliyyi Giɗaɗawa: Waƙar Gaskiya Mugunyar Magana )[34]

 

A waɗannan baitoci Sambo Waliyyi ya yi amfani da salailan zayyana da tambaya tare da gwalewa domin ya cusa raha cikin maganarsa. Wannan kuwa duk ci gaba ne na gina salon tsattsafin raha cikin waƙarsa.

Watakila lalurar waƙa ta sa Sambo ya ci gaba da gina salon tsattsafin raha a baiti na 34 da na 35 domin ya sa masu saurare har ma sarakunan da baitocin suka shafa su yi dariya. Ya kawo wannan salo domin gudun fushin sarakuna, kamar dai yadda Mamman Shata ya yi amfani da shi a waƙar da ya yi wa Sarkin Zazzau Shehu Idris[35]. Ga baitocin:

34Ga wata gaskiya da taz zo da ɗiminta sosai

Wada niɓ ɓangaro ta yau kowa ba ni tausai

Jifa ce ta far ma kan kowa ad da tsotsai

In bi a kan sarakuna in lema ta sosai

Don kuwa na ga su ka bukin gadon ƙasag ga

 

35Ka aje gemu an yi ma dagaci mai takarda

Ko kuwa emiya cikakke Cif had da sanda

Kuma kun sa ido tsakaninmu da ‘yan ta’adda

Sai ku shige kuna ta shan farfesu da ganda

Ai gadonku kare dukkan jama’aƙ ƙasag ga

 (Sambo Waliyyi Giɗaɗawa: Gaskiya Mugunyar Magana )[36]

 

Sambo ko kansa bai bari ba domin kuwa a ƙarshen waƙarsa shammatar kansa ya yi don ya kamala amfani da salon tsattsafin raha:

44. Tammat na cika Waliyyi bai bar kira ba

 Allah agazan ni tun ban bar duniya ba

 In bar bin mayaudara tun ba mu kai daras ba

 Na san nawa aibu in ku ba ku sani ba

Ɓannata guda tana shafe rabin garin ga

 

45. Masu irin halin ga nau su nika yo ma kaito

 Ga su cikin ƙasa dawaman bisa ci-da-ceto

 Bisa ga wuyan mayaudara nan muka namu ƙoto

 Don yawo garan kamar wani ɗan rahoto

 Yawace-yawacen ga nau sun yi yawa ƙasag ga

(Sambo Waliyyi Giɗaɗawa: Waƙar Gaskiya Mugunyar Magana )[37]

 

 

Alƙali Haliru Wurno gwani ne na amfani da salon tsattsafin raha cikin waƙoƙinsa. Maƙalar da ta gabata, Yahya (2004) ta isa misali ga tabbatar da wannan magana. Duk da haka dubi yadda ya yi suka mai gauni a kansa da kuma duk wani mai aiki irin wanda shi ma ya taɓa yi, wato alƙalanci irin wanda Turawan mulkin mallaka suka kawo a ƙasar Hausa. Ya kuwa yi hakan ne tattare da ci gaba da salon tsattsafin raha da ke cikin waƙar:

 

124.Ina hujjarka Alƙali Halir nau

Wane nassi gareka na tabka ɓanna

 

125.Ƙisasi ba ka yi uznun bi uznin

Yadan bi yadin ka ce min ja’izun na

 

Ina nassi da yac ce ma halan na

Faɗa mini gaskiya in shedi kaina

 

Da ɗarɗurinka ga ka da saulajani

Da zunnarinka zainul kafirina

 

Bale ƙiyyaru mai shafa ta hoda

Da barniɗa ji fullar kafirina

 

129.A sa gashi kamar namijin agwagwa

Ana bahasi da halshen zalimina

 (Alƙali Haliru Wurno: Sabilul HaƙƙI, Bi Ƙaulis Sidƙi …)

 

A nan Haliru yana zayyana yadda joji-joji da majestarori (alƙalan Turawa) suke fita zuwa kotu. Suturar da sukan sa tana sa musu wasu kamannu da ba a gani da ƙima a ƙasar (Musulmi) Hausa, domin ta kafirai ce, Musulunci kuwa ya hana mabiyansa yin kama da kafirai. To amma Haliru ya yi wannan zayyana ne ta hanyar da za ta sa mai karatu ko saurare ya yi dariya, wato ya cusa tsattsafin raha a baitocinsa. Shi kansa mawaƙin ya san da cewa ya cusa wannan salon tsattsafi domin a baiti na 137 ya ce babu zarafin yin dariya a wurinsa:

 

137.Ina nika dariya na cuci kaina

Sanin haka na ji tsoro kaico kaina

(Alƙali Haliru Wurno: Sabilul HaƙƙI, Bi Ƙaulis Sidƙi …)

 

 

Tsattsafin fushi

 

Shi ma wannan reshe ne daga rassan tsattsafin haliyya. Akan sami waƙoƙi waɗanda kan ƙunshi tsattsafin fushi duk kuwa da cewa ba cikin haliyyar fushi aka tsara su ba. Abin nufi shi ne sau da yawa mawaƙi kan rubuta waƙarsa domin faɗakarwa ko nasiha. Saboda haka zai yi amfani da harshe mai taushi, da salailai masu jan hankalin mai saurare ko karatu domin neman yardarsa. To a irin wannan yanayi watakila mawaƙi ya haɗa har da tsattsafin raha. A lokaci guda kuma saboda wasu dalilai sai ka sami mawaƙi ya shigo da haliyyar fushi. Nan take sai ya tsattsafa fushi cikin baiti ko baitoci na gaba.

Irin haka ne Malam Sa’adu Zungur ya yi a ƙarshen waƙarsa, Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya wadda a cikinta ne ya faɗakar da sarakunan Arewa ya kuma yi musu nasiha, duk a kan makomar siyasa a Nijeriya. Ga faɗakarwar da nasiha tattare da fushinsa:

 

138.Tutocin Shaihu Mujaddadi

Daɗa ba su zama Jumhuriya

 

In sha Allahu mu tsarkake

Bisa fatan za mu bi gaskiya

 

Domin fa Arewa da hargitsi

Da yawan ɓarna ba kariya

 

Matuƙar Arewa da karuwai

Wallah za mu yi kunyar duniya

 

 

142.Matuƙar ‘yan iska na gari

Ɗan daudu da shi da magajiya

149.Matuƙar da musakai barkatai

Da makaho ko da makauniya

 

Ba mahallai nasu a Hausa duk

Ba mai tanyonsu da dukiya

 

Birni ƙauye da garuruwa

Duk suna yawo a Nijeriya

 

152.Kai Bahaushe ba shi da zuciya

Za ya sha kunya nan duniya

 

153.A Arewa zumunta ta mutu

Sai nashaɗi sai sharholiya

 

154.Sai alfahari da yawan ƙwafa

Girman kai sai ƙwambon tsiya

(Malam Sa’adu Zungur: Arewa Jumhuriya ko Mulukiya)

 

Baitoci uku na ƙarshe haƙiƙa suna cike da fushin Sa’adu Zungur. Kalmomi da kalamai masu nuni ga wannan fushi sun haɗa da /Kai/ da /za ya sha kunya/ da /zumunta ta mutu/ da /sai sharholiya/ da /Girman kai/ da kuma /ƙwambon tsiya/. Hasali, tun daga baitoci masu kalmar /matuƙar/, mutum zai fara jin ɓurɓushin fushi.

Mu’azu Haɗeja, a waƙarsa mai kama da ta Sa’adu Zungur, shi ma fushinsa a kan Baushe yake kuma bisa ga dalili irin wanda Sa’adu ya bayar. Dubi amfanin da ya yi da tsattsafin fushi a waƙar:

61.A yanzu ga jahilci

Ƙasarmu har yai kauci

Dole mu je mu yi naci

Domin mu samo ‘yanci

Ko ma kwance karkiya

 

62.Bahaushe mai ban haushi

Da ba ruwansa da kishi

Na-Tanko mai kan bashi

Shi dai a sam mai dashi

Ba ya son ɗawainiya

70.Mazambata, mahilata,

Mayawata, mayunwata,

Makarkata, maɓarnata,

Matabbata cikin ɓata

Don sun kauce gaskiya

 (Mu’azu Haɗeja: Tutocin Shehu da Waninsu)

 

A fusace ne Mu’azu ya yi wa Bahaushe kirari (kirarin da a zahiri zagi ne) a baiti na sittin da biyu. Tun ma a ɗangon farko na wannan baiti mawaƙin ya bayyana fushinsa kan halin Bahaushe. Ya yi haka ne da amfani da kalmar ‘haushi’. Haushi kuwa shi ke haifuwar fushi (a Sakkwatance, hushi!).

A baiti na saba’in sai Mu’azu ya cika tsattsafin fushi inda ya ya yi amfani da baitin sukutum yana la’antar wannan al’umma tasa ta ƙasar Hausa. Haƙiƙa a wannan baiti Mu’azu yana cike da fushi kuma kalmomin baitin suna ƙara tabbatar da haka saboda kusan dukansu kalmomi ne na raujin fushin zuciya. Furucin /ta/ shi ne mai yin wannan furji.

A waƙar da ya kira “Jihadin Neman Sawaba”, Sa’adu Zungur ya yi tsattsafin fushi sosai dangane da yadda talakkawan Arewa ke shan uƙuba a hannun Turawan mulkin mallaka da sarakuna da kuma ‘yan siyasar jam’iyyar N.P.C.. Bayan da ya zayyana irin ribiɗin harajin da sarakuna ke yi wa talaka da bakin Turawa da ‘yan siyasa, sai Sa’adu ya kasa ɓoye fushinsa dangane da wannan ƙawancen zalunci, ya ce:

26. Sun maida talakka kamar dabba

Dokin sukuwarsu na masu gari

 

27. Komai na Arewa da bambanci

Da na al’ummomi sun fi ɗari

 

28 Daularsu dabam cinikinsu dabam

Ilminsu dabam don ba nazari

 

29 Daularsu kamar rigarsu take

Ga yawa ba amfani nagari

 

30 Cinikinsu kamar wandonsu yake

Bujensu da ba shi da alkadari

 

31 Ilminsu kamar rawaninsu yake

Ɗaure-ɗauren banza ba nazari

(Sa’adu Zungur: Jihadin Neman Sawaba).[38]

 

Kalmomi musamman, /don ba nazari/ da /ba amfani nagari/ da /da ba shi da alkadari/ da kuma gaba ɗayan ɗangon ƙarshe na baiti na 31, /ɗaure-ɗauren banza da ba nazari/, duk suna ɗauke da karsashin fushi wanda takaici ya bungulo tun daga zuciyar Sa’adu Zungur har zuwa ga bakinsa/alƙalaminsa.

Sa’adu ya sake yin wannan furjin fushi a baiti na 111 zuwa na 119 kuma da gauni tattare da bijirewa kamar haka:

111. Domin fitina da wulaƙanci

Da yawan ɗauri na kisan garari

 

112. Mu ba za mu toge ba bare mu bari

Za mu daddage sai mun ci gari

 

113. Ba farau ne ba a ɗaure mutum

A duhun zaluncin masu gari

 

114. An ci tarar wasu kuɗi da yawa

Bisa cin rashawa ta kisan garari

 

115. In don ɗauri an ɗauri wasu

Bisa zamba da zaluncin masu gari

 

116. Hakimai alƙalai har dagatai

Sun sha ɗauri na kisan garari

 

117. A cikin daular birnin Bauci

An ɗaure mutane sun fi ɗari

 

118. Waɗannan duk da ka ɗaure su

‘Yan NEPU ne ko masu gari

 

119. Gaskiya dai mu kam za mu faɗa

Ko ana ɗauri har kan zakari

 (Sa’adu Zungur: Jihadin Neman Sawaba).

 

Kalmomin da suka fi gaunin fushi a waɗannan baitoci sun haɗa da /domin fitina da wulaƙanci/ da /kisan garari/ da /mu ba za mu/ da /ba farau ne ba/ da /in don/ da tambayar da ya yi a ɗango na biyu na baiti na 118, da kuma gaba ɗayan baiti na 119.

b) Tsattsafin Harshe

A tsattsafin harshe mawaƙi yana amfani da wani harshe ne daban da kuma harshen Hausa wanda da shi ne yake tsara waƙarsa. Tsattsafin harshe shi ne manazarta waƙoƙi suka fi kira da sunan ‘aron harshe’. Mawaƙi zai yi waƙarsa cikin harshen Hausa, to amma saboda wata manufa sai ya yi amfani da kalmomi ko jumloli daga wani harshe daban. Zai kawo kalma ɗaya ko fiye, ko ya tsara wani ɗango ko ɗangogi, ko wani baiti ko wasu baitoci, duk ba tare da ya sa mai saurare ko karatun waƙarsa cikin duhu ba. A mafi yawan lokuta kalmomi ko ɗangogin da suka biyo bayan baƙon harshen, ko ma kafinsa, sukan fassara shi. To amma fa a lura da cewa wannan ba yana nufin cewa ba za a sami waƙoƙin da yin tsattsafi da wani harshe kan ɓata su ko sanya ma’anarsu ta shiga duhu ba.

Ana iya cewa a cikin waƙoƙin Wazirin Gwandu Alhaji Umaru Nasarawa akan sami tsattsafin harshe. Harsunan da suka yi tsattsafi cikin waƙoƙinsa su ne na Larabci da na

Fulatanci da na Ingilishi. Abin nufi a nan shi ne waƙoƙin Wazirin Gwandu suna da tsattsafin harsunan nan guda uku da aka ambata. Dubi wannan misali:

 18. Yarinya saboda dai duniya na ruɗinki

Mini shi kis sawo ki sa shi kina tallak kanki

Ke ko bayyano idon jama’a na dubinki

Ko dai ke kiɗe ginin hurumin addininki

Ke dai son zama tsirara, ba yayi na ba

20.Amma shi a bar batun azumi ba su hwara ba

Yi ab ba su yi hwa wai ba don ba su isa na ba

Ba su da hanƙurin a buɗa giya ba su kurɓa ba

Ba a yi mai tayi ga shan whisky bai amsa ba

Masu halin ga ko musulmi na ban gane ba

 26.Namiji da mace na rawa haɗe shin ko culture na

Tambayi Baba Soja mai culture ko minana

Mu kam dai ga namu addini shi halɗi na

Halɗi ko ga namu addini ya zam ɓanna

 Kuma Baba Soja ya yi kurum bai tanka ba

 (Alh. (Dr.) Umaru Nasarawa: Gargaɗi Ga Matasa)

A wannan misali Waziri ya yi tsattsafi da harshen Ingilishi ne. Ba abu ba ne mai wuya a gane cewa ya yi amfani da wannan salo domin ya nusar da hankalin mai saurare zuwa ga yanayin rayuwar da matasa suke ciki ta ɗauke-ɗauken ɗabi’u da al’adun da ba nasu ba. A kan haka ne ya kawo kalmomin da matasa suke amfani da su kamar ‘mini’ wanda shi ne fatari amma na Turawa ba na Hausawa ba, sannan kuma ya kawo kalmar ‘culture’ domin yin tuni ga babban maƙasudin ƙungiyar da hukuma ta tanada domin gyaran al’adunmu.

A waƙar Yabon Sarkin Gwandu Yahaya ta biyu, Waziri ya kawo salon tsattsafin harshe amma da harshen Fulatanci:

37. Zamanin Yahaya Uban Amo

 Min joɗike walla der jamo

 Jomi en kanko mellimo

 Gam jikku mo Allah hokkimo[39]

 Daɗin rai duk na duniya ya komo

 (Alhaji (Dr) Umaru Nasarawa::Yabon Sarkin Gwandu Yahaya, waƙa ta 2)

Kamar yadda za a lura, Waziri ya yi amfani da salon tsattsafin harshe a tsakanin ɗangon farko da na ƙarshe. Haka kuma salon ya nuna kamar Waziri yana son ya nuna gwanintarsa ta iya tsara waƙa da kuma nuna ƙwarewarsa a harshen Fulatanci. Wannan a bayyane ne idan aka yi la’akari da cewa sai mutum ya ƙware ga harshe yake iya tsara waƙa cikin harshen. Tattare da wannan hasashe ana iya ɗaukar cewa Waziri yana son ya tabbatar wa mai gardama cewa shi fa da gaske yake yi lokacin da a wata waƙarsa ya ce:

4. Ku jiya za ni fassara,

Waƙa ba ta gagara,

Wada duk munka tanƙwara,

In mun miƙa sheɗara ba ta karewa.[40]

 (Alhaji (Dr) Umaru Nasarawa: Yabon Sardauna Ahmadu Bello)

A cikin waƙar yabon Sarkin Gwandu Yahaya wadda aka ambata ɗazu ma yana cewa:

53.Na saba miƙa sheɗara,

 Ta tsaya cif babu tanƙwara,

 Ai waƙa ba ta gagara,

 In dai na tashi fassara,

 Wada duk nika so ina faɗi rarara.

 (Alh. (Dr.) Umaru Nasarawa: Yabon Sarkin Gwandu Yahaya, waƙa ta 2)

Bari mu rufe kawo misalai dangane da tabbatar da hasashenmu da wasu misalai uku domin mai nazari ya gane cewa shi ma wannan iƙirari na gwaninta ga waƙa da Waziri ya yi ai wani salon tsattsafi ne na waƙoƙinsa. Ga abin da yake cewa:

1.Bismilla babu fariya

Zan fara abin da ni iya

Hanya ta wadda ba ƙaya

Don waƙa wagga nahiya

Goga nike wanda ba shi tsoron kaya

(Alhaji (Dr) Umaru Nasarawa: Yabon Sarkin Gwandu Yahaya, waƙa ta 2)

Ga na biyu:

43.Waƙa daɗa mun yi tammat gare ta

Waƙag ga way yo ta yaw wallafe ta,

Waƙa ƙasar Gwandu kun san gwaninta

Wahhabu yo min ijaba gare ta

Kai mai yawan jinƙayi anka sanka

 (Alhaji (Dr) Umaru Nasarawa: Waƙar Addu’a)

 

Ga na uku:

Waƙa hanya ta da nis sani kwata-kwata

Inda duz za ta ƙule in sake in bi wata

Kuma in za ta kwana in miƙe ta ta farta

In shiga gulbin waƙa in yi iyo, in yi nuta

 Gwanin iyo nike ko na noce ba ni shan ruwa

 (Alhaji (Dr) Umaru Nasarawa)[41]

 

Idan manazarci yana da ra’ayin cewa mawaƙi ba ya da dole to a wani ɓangaren salon tsattsafi akwai togiya. Togiyar ita ce inda mawaƙi yake son ya koyar da wani harshe daban da harshen da yake tsara waƙarsa. Wato ga misali, idan mawaƙi yana son ya koyar da harshen Larabci cikin waƙarsa da yake tsarawa cikin harshen Hausa, to a nan kam tilas ne ya yi amfani da salon tsattsafi. Ai ko ba kome da harshe biyu ne zai tsara ta.

Alƙali Haliru Wurno ya yi amfani da salon tsattsafi har aƙalla iri biyu a waƙarsa ta koya wa ɗalibansa harshen Larabci. Da farko dai akwai tsattsafin harshe, sannan akwai tsattsafin raha domin shi ne fitaccen salon waƙoƙinsa. Dubi wannan misali:

1. Ja’a abun ce ya zaka baba

Jaddun kaka ne na zumunci

 

 

2. Ummu uwa uhtun ƙanwa ta

Zauju mijin mata ta mutunci

 

3. Zaujatu mata ce ta mijinta

Ce waladun yaro ni nic ce

 

4. Kalbu kare dikun zakara na

Mussa hirru ka ba ta abinci

15. Assanduƙu akwati na icce

Kama himaru da za ka fatauci

 

16. Hausa ka ce jaki to hau shi

In kas sabka ka ba shi abinci

 

17. Ɗauki haƙibatu jikkar fata

Dubi jarabu akwai banbanci

 

18. Shi burgame na fa jarabu

Don zuba naman mai wanzanci

21. Albaƙara sunan ‘yan nagge

Taisu yana da halin iskanci

 

22. Ko jamalun geloba na Adar

Naƙatu matatai ta halacci

26. Ga na’aja matar rago ta

Matar kabshu tana da zumunci

 

27. Ɗan akuya taisun mun yo shi

Don jaraba bai ƙyale budurci

 

28. Baɗɗatu ce kuti dud da agwagwa

Duk wada kac ce ba shi da gacci

43. Jemage huffashu ƙazami

Inda shike kashi shika kwanci

 

43. Ce wazagun tsakaka subanun

Mesa ce mai zaɓɓace hanci

 

44. Aƙarabu bindinai nika tsoro

Wagga kunama mai ƙanƙanci

 

45. Nahalatu ka ji zuma mai zaƙi

Zubabu ƙuje na masu ƙazamci

(Alƙali Haliru Wurno: Waƙar Koyon Larabci)[42]

 

Duk kalmomi masu gicciyen rubutu na harshen Larabci ne. Haliru ya yi amfani da salon tsattsafi don ya koya ma ɗalibansa harshen. Tattare da wannan salon tsattsafin harshe, Haliru kuma ya cusa salon tsattsafin raha domin waƙarsa ta dace da tunani da haliyyar yara. Kalmomi kamar / ni nic ce/, da / ka ba ta abinci/ da / Don zuba naman mai wanzanci/ da /Taisu yana da halin iskanci/ da /Don jaraba bai ƙyale budurci/ da /…ƙazami > Inda shike kashi shika kwanci/ da /Mesa ce mai zaɓɓace hanci/ da kuma /… bindinai nika tsoro/. Tambaya a nan ita ce, ta yaya Haliru zai iya koyar da waɗannan kalmomi ba tare da salon tsattsafin harshe ba? To amma wannan salo bai wadatar da Haliru ba domin ya san koyon harshe yana da wuya. Saboda haka sai ya ƙara da salon tsattsafin raha. Manya ma, ba yara kaɗai ba, za su ji daɗin haka.

 

c) Tsattsafin Al’adu

 

Mai nazari zai iya ya yi mamakin kawo wannan kashi na salon tsattsafi ganin cewa ai waƙa gaba ɗayanta tana magana ne a kan al’adun Bahaushe. Mamakinsa a kan hanya yake. To amma akan sami wani ɓangare ko wasu ɓangarori waɗanda duk da yake Hausawa kan rubuta waƙoƙi a kansu, suna da keɓantaccen yanayin da suke ɗauka. Misali waƙoƙin wa’azi da na madahu da dai kusan dukan waƙoƙin da suka shafi addinin Musulunci. Waɗannan waƙoƙi suna da irin nasu harshe da akan yi amfani da shi domin tsara su. A taƙaice suna da kalmomin fannu waɗanda da ka ji su za ka gane cewa ga irin waƙar da ake yi. Misali a waƙar madahu idan ka ji an ce ‘ya fi kowa’ ko ‘yana da mu’ujiza’ ko ‘ina horon ka ɗanuwa ka tsare yabon sa’, kai ka san waƙar madahu ce ake yi. To amma idan ka ji an ce, ‘ ‘yan akayau’ ko ‘naɗe hannu’ ko ‘dambe’ ko ‘zaune a zaure’ ko ‘sorona’ ko ’filin gona’ ko ‘ta Ilori na sa riga mai aiki’ da dai makamantansu, kalmomi ne waɗanda sai ka ji abokan gaminsu sannan za ka fahimci cewa waƙar madahu ce ake yi.

Idan aka sami irin wannan barbaɗin kalmomi masu ayyana wasu al’adu na ƙasar Hausa cikin waƙoƙin madahu, a nan ne za a iya cewa an sami salon tsattsafin al’adu cikin waƙar. Dubi wannan misali daga waƙar Alhaji Aliyu Namangi, waƙar da aka kawo misalan kalmomi daga cikinta:

 

10. Ba ni da guru ba ni da laya

Sunan Annabi ne shingena

 

11. Ba ni da ƙarfi ba ni da ƙarfe

 In koma Makka ne fatana

 

25. Da Alfazazi da mai tahmisi

Sun yi ma Imru’u ko-ta-kwana

 

26. Su kai ma Imru’u shi da Zuhairu

A kan waƙansu na daɗin kwana

 

27 Ni ma ga wasu nan na samo

Zan taka masu ‘yar akayauna

 

 28.Masu yabon sa su ce ɗan gata

Don su na fara naɗe hannuna

 

29. Batun da Kirista ke ma Isa

Na ji ƙaninsa ga ‘yan dambena

 

30. Suna nema su ɗafa ma Muhammad

Shi fa ya sa ni shirin dambena

 

31. Su ban hujja in babu su tuba

Izan ko sun ƙi su sha kurhuna

 

84. Aka kwaɓe halcena da yabonka

Har ya zame mani filin gona

 

85. Tun tuni sunayenka Muhammad

Sun shuka mata baitotina

 

86. Gonar ta yi gamo da yabanya

Kowa na sha’awar nomana

(Alhaji (Dr) Aliyu Namangi: Tsarabar Madina)

 

Al’adun Hausawa biyu zuwa uku ne Aliyu Namangi ya yi salon tsattsafin al’adu da su a waɗannan baitoci. Akwai al’adar dambe wadda kalmomin ‘guru’ da ‘laya’ da ‘dambe’ da ‘kurhu’ ke ayyanawa. Akwai al’adar da ta danganci noma wadda Namangi ya ayyana da kalmomin, ‘filin gona’ da ‘yabanya’ da ma ‘noma’ ɗin shi kansa. Tattare da al’adar dambe akwai tattakin da ‘yan dambe kan yi saye da akayau gewayen ƙwauri da ijiyar ƙafa. Saboda haka a waɗannan baitoci akwai tsattsafin al’adar rawar Hausawa a filin da suke dambe. A taƙaice Aliyu Namangi ya yi amfani da salon tsattsafin al’adun Hausawa cikin waƙarsa ta madahu mai suna ‘Tsarabar Madina’. Hasili ma, sunan waƙar yana tattare da ɓurɓushin tsattsafin al’adu. Al’adar Hausawa ce a riƙo wa ‘yanuwa da abokan zama da na arziki da ke zaune a gida, wani abu daga gari ko ƙasar da ɗanuwan ya ziyarta. Wannan al’adar riƙo tsaraba akan bayar da ita har ma ga wanda bai ba matafiyin guzuri ba.

Shillo

Abin da ake nufi da salon shillo shi ne jerangiyar da mawaƙi kan yi ta musamman a farkon waƙArsa wadda a dubin farko mai karatu ko saurare zai ɗauka abin da mawaƙi ke faɗa bai da wata nasaba da (babban) jigon waƙar, to amma a haƙiƙani akwai wannan dangantaka.

Wata waƙa mai suna Gudale ta ƙunshi baiti 100 kuma ‘yar ƙwar biyu ce. To a cikin baitocin nan ɗari, baitoci 6 na farko Basmala suka ƙunsa. Daga baiti na 7 har zuwa na 53 za a ga mawaƙin tare da dabbobi iri-iri suna hira. Hirar kuwa ba ta wuce neman taimakon da mawaƙin ke yi ba. Kowace dabba ya je wurinta sai ta kore shi ko kuma ta nemi ta cutar da shi.

Abin da zai zo ma mai karatu ko saurare a rai shi ne watakila mawaƙin yana ƙoƙarin ya bayyana halayen waɗannan dabbobi ne. To amma sai a baiti na 54 ne za a fahimci cewa wannan waƙa an yi ta ne domin a yabi mutum guda. Dabbobin da mawaƙin ya je gare su da fari duk laƙabi ne na jinsunan mutane. Halayen dabbobin halayen waɗannan mutane ne, kuma halayen da sam-sam ba za ka same su ba ga mutumin da dominsa ne aka rubuta waƙar. Wannan shi ne muhimmancin baiti na 7 zuwa na 53. Wato a taƙaice baitocin da ke magana a kan dabbobi suna nuni ne da cewa mawaƙin bai da wani mutum a duniyar nan wanda ke iya taimakon sa, sai fa wanda ya ambata da sunan Gudale. Ya san mutanen kuma dukansu ba su kai ga wannan mutum ba. Wanann mutum shi ne Gudakle wadda ta kiraye shi domin ta shayar da shi.

Saboda haka daga baiti na 7 zuwa na 53 salon shillo ne mawaƙin ya yi amfani da shi domin ya fito da matsayin Ibrahim Giɗaɗo, wato Gudale. Haka kuma a bayyane take cewa yabon Gudale ya fara ne tun daga baiti na 7, ba daga na 54 ba.

Bin Sawu

Bin sawu yana nufin a samu mawaƙi ya rubuta waƙa wadda ta ɗauko jigo ko jigogi, da kari da jimloli, har ma da salo, irin na wata waƙa ɗaya (ko fiye) ta wani mawaƙi daban, har wannan waƙa ta daga baya ta kasance kamar dai waccan ce ta farko, to amma fa akwai bambanci duk da waɗannan kamannu. Waƙar Haliru mai suna “Tura Ta Kai Bango” misali ne na bin sawu. Waƙar ta bi sawun shahararriyar waƙar nan ta Wazirin Gwandu Alhaji Umaru Nasarawa, mai suna ‘Zaɓaɓɓiya’. Dubi wannan misali:

 Zaɓaɓɓiya

 (Alhaji Umaru Nasarawa)

 Tura Ta Kai Bango

(Alƙali Alhaji Haliru Wurno)

1. Na kirayi mai iya jinƙai na

 Wanda shi ka ɗaukaka sunana

 Nan da nan shi kammala girmana

 Tun da na kirai ban donewa

 

7.Ko da ban yi ƙwazon komi ba

 Ya Azimu kai ɗai nika duba

 Tun da ko daɗai ban san wani ba

 Ban da kai Guda Mai gyarawa

 

 

9. Can wurin da kac ce ‘Fad’u ni

 Astajib lakum’ ba nisyani

 ‘Ba-ni-ba-ni’ bai sa ma ramni

 Naka arziki bai ƙarewa

 

 

 

12.Dauri anka kasan nid daure

 Anka koma kasan nij jimre

 Yanzu hanƙurina ya ƙare

 Ƙadiran nufan ni da ramawa

 

 

18.Ga garinmu ban kwana daji

 Ga Ka ban biɗar wani budeji

 Tun da na sani Kai am Munji

 Malja’inka nan nika dagewa

 

 

50.Wanda yay yi waƙa sunanai

 ‘U’ da ‘Ma’ da ‘Ru’ ga mazamninai

 Sai ka zo ka ‘Bi Ke’ birninai

 Nasarawa can kaka komawa

1. Na kirayi Allah Ƙahharu

 Wanda ad da baiwa Jabbaru

 Shi ka yafane mini Sattaru

 Ga ni na yi laifi Gaffaru

 Nai kure ina son yafewa

 

18. Ko da ban yi aikin daidai ba

 Jalla ban fa mance laifi ba

 Ban ga wanda za ni ya cetan ba

 Ban da Kai Ilahi don Ɗaiba

 Ba ni nau muƙamin takawa

 

23. Rabbu tun da ka ce ‘Fad’u ni’

 ‘Astajibu’ Allah kama ni

 Na ɗime jikina yai ramni

 Ba ni kai ka bai in ka ba ni

 Ba ni duk wadat da ka ɗorewa

 

14 Rabbu dut abina ya ƙare

Dauri anka yo mini na jimre

Yanzu hankalina ya tsere

Ga shi hanƙurina ya ƙare

 An buge ni ban iya ramawa

 

11 Na ɗimauta har na kwan daji

Na yi kwance ba inwar gamji

Ni kaɗai ga rana sai tuji

Wanda bai kiyo ga hakin samji

 Ya Ƙawiyyu na so komawa

 

49 Mai biɗat sanin ma’ajin waƙa

‘Ha’u’ ‘Dadu’ ‘Ra’ shi yas sarƙa

Wurno ag garinsu gida haƙƙa

Fassararsa Alhaji Ishraƙa

 Ko da yaushe bai rasa shiryawa

 

Salon Mawaƙi

Akwai salon da za a kira salon mawaƙi a nazarin waƙa. Wannan shi ne salon da aka fi samu cikin waƙoƙin mawaƙin da ake nazari akai. Takan kasance a waƙoƙin mawaƙi a samu cewa a kusan kowace waƙa ko ma dukansu akwai ambaton sunansa don a iya tantance wanda ya wallafa su. Misali, Alhaji (Dr.) Umaru Nasarawa Wazirin Gwandu yakan yi haka, ko dai ya ambaci sunansa kai tsaye ko ya taƙaita sunan ko kuma ya ambaci laƙaninsa. Wato, yakan ce Umaru kamar a waƙarsa mai suna “Godiyar Allah” da “Yabon Annabi Wajibi Ne”, ko kuma ya ambace shi da haruffan karatun allo, kamar na Fulatanci. Misali a waƙarsa mai suna “Godiya Ta Biyu” inda ya ce:

52.Mai tambayam mawaƙi,

Aina gyaran gyal da mimi ra su sanasshe ka.

 

A nan ‘U’ da ‘m’ da ‘r’ ne ya faɗa yadda ake faɗar haruffan na Larabci cikin Fulatanci. Yadda kuwa ake faɗar waɗannan da ajamin Hausa ko bokon Hausa, shi ne kamar yadda ya kawo su cikin waƙarsa,“Yadda Ya Kamata Najeriya Da Mutanenta Su Zamo” inda ya ce:

95.Mai biɗa duk shi san way yi waƙag ga,

Gama U da Ma, Ra da U gane suna kakai

 

96.In kana son ka san har garin namu,

Nassarawa Birnin Kabi in biɗa ta kakai.

 

Wani lokaci Alhaji (Dr.) Umaru yakan ambaci laƙaninsa, kamar ‘Gizama’ a waƙarsa, “Gargaɗi Ga Aboki” ko ‘Gizo’ a waƙarsa “Murnar Bonas” ko waƙar “Tsuntsayen Zamani”.

Saboda haka ana iya cewa salon wannan mawaƙin ko kuma fitaccen salonsa a waƙoƙinsa shi ne ambatar sunansa a waƙar da ya yi.

Shi kuwa Alƙali Alhaji Haliru Wurno ana iya cewa fitaccen salonsa shi ne na ambaton sunansa kamar yadda Alhaji (Dr.) Umaru Nasarawa yake yi, da kuma amfani da salon raha a mafi yawan waƙoƙinsa.

 28. Na yi mata sun fi sittin

Yo ƙida sun kai tamanin

Anguwa na Mairi birnin

Macce yau na bar tunanin

Kowace na kama kaina.

 

29. Kai tuna wasu na gidanka

Rakkiya ta san halinka

Mairi na nan ba ta ƙin ka

Nana ko ita aɗ ɗiyakka

Ga su nan bari ƙin batuna.

 

 30. Alhajin Allah na Tumba

Dauri can yau ta yi arba

'Yan ɗiya sun ɗauki gaba

Rakkiya Mairi ku duba

Nana ta ce mi ruwana.

 

 31. Bai zama dangi ya so su

Ba shi daurewah halinsu

Ga shi sun koma ƙasassu

Ba shi mancewah halinsu

Yanzu ya zan turja'una.

 

32. Na jiya to Nana ke san

Na laɓe ke so ki tas san

So guba na Nana ke san

Ɗemuwa tas sa ni ko can

Ko da niy yi rashin sani na.

 

33. Ke tsaya gwaggonki na yo

Kabo har 'Yas Shada juyo

Nana ko 'Yar Ummu mun yo

Ga ki ke zaka kak ki koyo

Ba ni mummunan ɗumina.

 (Alƙali Alhaji Haliru Wurno:Soyayya Ruwan Zuma)

Bayan salon ambaton suna akan samu salon zubin waƙa. Abin nufi shi ne waƙoƙin mawaƙi su kasance masu ɗangogi iri guda a baituka. Misali, a samu duk ko kusan waƙoƙinsa ‘yan ƙwar bibbiyu ne ko ƙwar uku uku da makamancin haka. Haka kuma akan samu cewa mafi yawan waƙoƙi ko dukansu su kasance da baitoci masu amsa-amo mai ‘yanci. Wannan amsa-amo shi ne wanda ke bambanta a kowane baiti. Misasi, da yawa cikin waƙoƙin Mallam Abubakar Maikaturu Sakkwato ‘yan ƙwar bibbiyu ne kuma baitocinsu masu amsa-amo mai ‘yanci ne da su. Misali, waƙarsa mai suna, “ ‘Yan Jahadi” tana daga cikin waƙoƙinsa ‘yan ƙwar bibbiyu, sannan baitocinta masu amsa-amo mai ‘yanci ne. Dubi wasu baitocinta:

7. Kowane zamani akwai na Allah

 Akwai waɗanda ac cikin jahala

 

8. Dubi hadisin ga na ‘La tazalu

 Jama’ati’ don ka fice dalalu

 

9. Kowani lokaci akwai kuffaru

 Akwai munafukai akwai ashararu

 

10. Tun Makka ko can haka anka yo su

 Kway yi kama da su shina cikinsu

 

11. Ka lura ‘man shabbaha’ ad dalilu

 Ga Bubakar don ka jiya halilu

 (Abubakar Maikaturu: Waƙar ‘Yan Jahadi)

 

Abin da ya kamata mai nazari ya lura shi ne kowane mawaƙi bai rasa salon da ya fi amfani da shi cikin waƙoƙinsa.

Salon Sawun Mawaƙi / Ambaton Sunan Mawaƙi

Salon da mawaƙi ke amfani da shi ya bayyana sunansa cikin waƙarsa shi ne za a iya a kira ‘sawun mawaƙi’[43]. Baitocin da aka kawo dangane da bayani kan ‘salon mawaƙi’ sun wadatar a matsayin misali. A waƙoƙin baka akan samu wuraren da mawaƙi ke faɗin sunansa. Dubi wannan misali:

Ɗanƙwairo yai mafalki

Yana jin ƙara’ injin

Ko mota za a ba ni

Albarkacin Ciroma

Ƙwairo an ba ka mota

An koma an ba ka mota

Sai Alhaji Bukar Mandara

Ya ce ya ba ka mota

A.A. Abubakar Hamza

Ga Naira dubu da yab ban

Mai ban tsoro sadauki

Hasan ɗan Shehu Malam

(Alhaji Musa Ɗanƙwairo: Hasan ɗan Shehu Malan)

Shi kuwa Alhaji (Dr) Mamman Shata, ga abin da ya ce a wata waƙarsa:

Kai Cika kura cikin dawa taka rurinta

Hasan na Husaini mai tsuntsaye

Shi kuwa Shata cikin gari yaka waƙatai

Hasan na Husaini mai tsuntsaye

Kiɗan na Husaini mai tsuntsaye

Na ƙaga ta

Na shirya ta

Don na Usaini mai tsuntsaye

Kowas sanya kanshi to shi ya ji Shata

(Alhaji (Dr)Mamman Shata: Hasan na Husaini Mai Tsuntsaye)

A lura da cewa akwai banbanci babba tsakanin wannan salo da salon ‘bin sawu’ wanda aka yi bayani kansa.

JELAR KALMOMIN FANNU

AbuntarwaMallakar (kalmomi)

Abuntarwar abuntarwa = kurwantarwa

AlamtarwaMartani

am baya. (ambata a baya)Mizani

AmoMutuntarwa

Ambaton suna/Sawun Mawaƙi

Ba’aNau’’o’in (jumla

Ba-shamakiRauji

Bi-amo Salo

Bi-ma’ana

Bin sawuSarrafa (tunani)

 Sawun mawaƙi

Cuɗau Saɓi-zarce

Dabbantarwa Shillo

DaidaitoSiffantawa

ƊanɗanaSinadari

Dangantakar (tsari) Sosa zuciya

DibilwaTambaya

FifikoTsarin (tunani)

Gamin bautaTubali

Gangara Tsattsafi

Haliyya Yanayi

Hira Yanka (zubin-)

Ishara Zango

Jaddadawa Zaren (tunani)

Jinkirtawa Zayyana

Jinsarwa

Jumla (waƙa)

Kacici-kacici

Kamance (-n)

Kambamawa

Kasawa

Ƙasƙantarwa

Kinaya

Ƙumshiyar tunani

Labari

Lalurar waƙa

Laƙabi

Maimai

Maimaitawa

Post a Comment

0 Comments