Ticker

6/recent/ticker-posts

Jaye Karar Tsana: Uzuri da Tuni Daga Mantuwa Ta Abu-Ubaida Sani



Ta

Abu-Ubaida SANI
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara
Phone No: 08133529736
Email: abuubaidasani5@gmail.com


Ya Allah mahalaccin komai,
Wanda ya ƙaga yawan mancewa.

Ba don zuci akan mance ba,
Da mu yau duka mun zama gawa.

Domin da tuni an ta bala’i,
Kowa na riƙe haushin kowa.

Ƙara salati gun Manzonmu,
Alaye da sahabbai kowa.

Ya Sarkin da ya yi mu mutane,
Masu kure hanyar kaucewa.

Ya Sarki da ya sa mana tuba,
Idan mun yi ta kake yafewa.

Ya Sarki da ka yi mu ajuzai,
Tsakanin juna muke saɓawa.

Ya Sarkin da ya yo mana hanya,
Domin mu bi ta ga sasantawa.

Ya Sarki da ya sa mana rauni,
Rayin juna muke ɓatawa.

Ya Sarki da ya ba mu dabaru,
Na rarrashi da fararrantawa.

Ya Sarkin da ya sa dokoki-
Da in an bi su ake dacewa.

Ya Sarkin da ya sa mana doka,
Amma ga shi muna karyawa.

Ya Sarki da ya tanada tuba,
Saɓonninmu yana yafewa.

Ya Sarkin da ya ba mu farillai,
Sai ko mutane muke tsallakewa.

Ya Sarkin da ya yo hanyoyi,
Idan mun tuba yake ƙyalewa.

Ya Sarkin da ya turo manzo,
Wanda gare mu yake tausayawa.

Ya Sarkin da ya nuffi da manzo,
Don a gare mu ya yo roƙawa.

Ya Sarkin da ya amsa kiransa,
Ba a kife mu har ran tsaiwa.

Ya Sarkin da ya ce mu yi roƙo,
In mun roƙa yake amsawa.

Ya Sarkin da shi ya hane mu,
Gun wani nasa mu yo roƙawa.

Ya Rabbani, na goggode,
Baiwarka gare ni ba yadawa.

Farko dai baiwar Musulunci,
Babu kwabo nai yo fansowa.

Kana baiwar nan ta mutunci,
Sai da nufinsa ake dacewa.

Ya Sarkin da yake sa natsuwa,
Ga zucin wanda ya yo dogewa-

Kan bautarsa da bin dokoki,
Ga duk alfasha yai kaucewa.
Ya Sarkin da yake kuma yarda,
Ga bayinsa da suke dogewa-

Kan hanyar daidai da ɗabi’u,
Da halayen da suke nunawa.

Ya Sarkin da idan ya yarda,
Da ɗan Adam ya yo dacewa.

Domin shi ne zai saka yarda,
Nasa ga zuci na kowa da kowa.

Ya Sarkin da yake bayarwa,
Babu waninsa da za ya hanawa.

Manzo ya ce ko an taru,
Duk al’umma kowa da kowa-

Don a rage ka da ƙwayar zarra,
To ko sam-sam ba a iyawa.

Hakka idan kowa ya taru,
Mutum har aljan dukkan kowa-

Don a daɗe ka da ƙwayar zarra,
To lallai ba a ko iyawa.

Sai dai in Allah ne yas so,
Shi ɗai ke mulkin badawa.

Idan dai kenan har mun yarda,
Mun yi imani ba mu raba-

Cewa Allah shi ɗai ke yi,
Waninsa da ɗai ba ya ko iyawa.

To ko ba za mu wurin boka ba,
Shirka ba ma ko farawa.

Ya Sarkin da ya sa littafi,
Kan kowa tun kan haihowa.

Ya Sarki mai Lauhil Mahfuz,
Wanda cikinsa ake adanawa-

Dukkan samu koko rashinmu,
An zana ba ya gogewa.

Ya Sarki mai son Musulunci,
Cika-cikansa ya yo tsarawa.

Ɗaya a cikinsu ko imani ne,
Da ƙaddara in tai aukowa.

Ko dai mai kyau ko mummuna,
Kadda su sa mana kafircewa.

Idan dai duk mun yarda da wannan,
To ko mu lura mu zam ganewa.

Cikinmu a bar samun mai zamba,
Ko cin hanci karɓar rashawa.

Koko sumogal ko wani wayo,
Don fa kuɗi ya yiwo tarawa.

Mai imani dole ya gane,
Wayo bai sa ai sauyawa.

Wayon bai ƙarar mu da komai,
Wai don dukiya mui tarawa.

Ba ya ko ɗauke mana nauyi,
Sai ma gare mu ya zan ƙarawa.

Idan mun yarda da ikon Allah,
Neman tuwonmu muna gyarawa.

Mu nemi halal ziryan mu yi hamdan,
Kadan mun samu mun tarawa.

Idan ma babu mu dai ce hamdan,
Allah shi ne zai kawowa.

Idan muka doge kan wayonmu,
Ko da mali muna tarawa.

To mu tuna da hadisin manzo,
Sam Allah bai ko amsawa-

Ko da bawa ya yi du’a’i,
Idan dai haram yake taunawa.

Koko haram ya saka a jinkinsa,
Ko a haram yake kwantawa.

Ya Sarki da yai yi kashedi,
Kan bayin da ake cutarwa.

Mun ji batu bakin manzonsa,
Ya ce: “Allah na amsawa-

Du’a’in wanda ya sha zalunci,
Da ya yi Ilahu yake amsawa.”

In har dai mun yarda da ƙaulin,
Sata dole mu yo dainawa.
Dole mu daina rashin adalci,
Dole muna tausan talakawa.

Dole mu lura da haƙƙin marayu,
Amanar tasu mu yo kamawa.

Dole mu daina ko tauye mudu,
Duk fannin ciniki kasuwa.

Dole uba ya kula ‘ya’yansa,
Ga su tarbiya ya yi bayarwa.

Dole mu’allim yab bi a sannu,
Ɗalibbansa ya rinƙa kulawa.

Kun ji mu lura mu bar zalunci,
Mu tsoraci Allah kan ran tsaiwa.

To ma in har mun tuna zance,
Ilahu da kansa yai furtawa.

Je ka ka duba cikin Kur’ani,
Alƙawari ne yai zanawa:
“Duk makashin wani mai imani,
Dole Jahannama zai ƙarewa.”
Idan mun yarda da Alƙur’ani,
Sannan wataran mu muke gawa.
Idan mun yarda da wannan aya,
To da dole mu yo sauyawa.
Domin dole mu bar yin sata,
Ba mu zama ‘yan kwakkwantarwa.
Dole mu daina fashi da makami,
Yara dole mu bar sacewa.
Dole mu daina batun kidnapping,
Idan mun yarda muna shuɗewa.
Yanzu bara in ba da misali,
Mu sa natsuwa domin ganewa.
Misali ne kan tsoron Allah,
Ya wuce baki kawai furtawa,
Dole ya zan na nan daga zuci,
Har ayyukanka suna nunawa.

Yanzu a ce an sa doka ne,
Kada mashin kowa ya hawowa.

An ba sojoji ko umarni,
Da an hau to su yiwo kamawa.

A nan to dole ɗayantar uku ne,
Ga su ko a jere ina ƙirgawa.

Ko dai ka ji tsoron wannan doka,
Hawan mashin ka yiwo dainawa.

Ko ka ji ba ka tsoron doka,
Ka hau kayinta ka yo takawa.

Koko ka zamto kana wasi-wasi,
Nan sa’arka ka yo jarabawa.

To in har mun yarda da Allah,
Mun ko aminta yana kamawa.

In mun yarda da akwai mutuwa,
Sannan raɗaɗinta akwai wahalarwa.

In mun yarda da kwanan kabari,
Mai ƙunci ko gwanin tsukewa.

In mun san da duhu na cikinsa,
Mai ban tsoro mai rikitarwa.
In mun yarda cikinsa macizai –
Har da kuna sukan tasowa.

In mun yarda yakan yo matsa,
Har awazu sai sun saɓawa.

In mun yarda yana da kaɗaici,
Kowa shi ɗai zai kwantawa.

In mun yarda da ba a motsi,
Ba a tashi ko juyawa.
In mun yarda da ba shi da iska,
Ba dama a yi numfasawa.
In mun yarda ƙaho za a busa,
Dukkaninmu mu yo tasowa.

In mun yarda da za a yi tsayuwa,
Har kowa sai ya ƙosawa.
In mun yarda da za a yi rana,
Daidai kai za tai saukowa.
In mun yarda da littattafanmu,
Da za mu karɓa ranar tsaiwa.
In mun yarda da za mu yi ƙunci,
Idan da hagu mu kai amsawa.

In mun yarda da za ai hisabi,
Nan tambaya za mui amsawa.

In mun yarda da za a bi kadun,
Dukkan wanda mu kai cutarwa.
In mun yarda a can da siraɗi,
Sannan ta kansa ake takawa.
In mun yarda mutanen kirki,
Tamkar haske suke gilmawa.
In mun yarda mutanen banza,
In sun hau shi suna faɗawa.
In mun yarda akwai ɗaiɗaiku,
Sai sun jikkata za su wucewa.
In mun yarda wuta na dakon,
Duk wani wanda ya yo kaucewa.
In mun yarda cikinta azaba,
Har ya zarci gaban furtawa.

In mun yarda da din-din-din ne,
Bayan an mutu ba dawowa.
To me ne zai sa mu ji daɗi?
Har da bushasha ko holewa?
To me ne zai sa girman kai?
Mu fa mutane ne duka kowa.

To me ne zai sa mu yi ƙyashi?
Allah dai shi ke bayarwa

To me ne zai sa mu yi rowa?
Ilahu da ya so zai ƙwacewa.
To me ne zai sa mu yi ƙarya?
Bayan Allah ya yi hanawa?
To me ne zai sa mu yi zamba?
Tun da ko Allah na kamawa?
Kai jama’a ku taho mu yi tuba,
Kar mutuwarmu ta yo iskowa.

Tun da ko kullum mu kan hau titi,
Cikin motar da ake tuƙawa.
Gefen hanya mukan ko yi kallo,
Haɗarin da ake yi har da macewa.
To ai ko mu rayayyu ne,
Wa ya sani ko mui gwabzawa!
Wa ya sani ko in ajalinmu,
Muna mota ta yiwo ƙwacewa!
Mu doki wata da rashin son ranmu,
Take ranmu a yo zarewa!
Wa ya sani? Sai ikon Allah,
Ko gobara za tai tasowa!
Ga ƙofar ɗaki ko ta kulle,
Cikin ƙunci mu zamo ƙonewa!
Wa ya sani ko tsallake hanya,
Nan ajalin zai yo riskewa.
Garam! mai mota ya kaɗemu,
Take wuyanmu ya zam karyewa!
Ya Allah ka tsare mu da wannan,
Da dukka Musulmi mai ganewa.
Mun dai san mutuwarmu farilla,
Amma hanyar tai saɓawa.
Wani a sauƙaƙe za ta kasance.
Wani ko a wahalce yake sheƙawa.
Ya ke sister dubi batuna,
Sassauto mu yi daidaitawa.
Kwanan baya na faye tsauri,
Zuci ta ja ni na yo lulawa.

Har da su zagi nai ta sakawa,
Yanzu bayanin zan sauyawa.
Na yi shirin in sabon zance,
Zuci da baki na yo gyarawa.
Gare ni kira an kai da ɗiyani,
An ce ai na yo kwafsawa.
An ba ni bayani na kuwa gamsu,
Na ga kurena nai gyarawa.
An ce tsaurin ya wuce ƙima,
Na kuwa lura nai ganewa.
An ce zancen har da su zagi,
Lallai baki yai suɓucewa.
An ce waƙar can ta tsana ce,
Na ga hakan ne nai amsawa.
To ku biyo ni mu koma daidai,
Ni har ku mu yi daidaitawa.
Na ga kuna son dai ku yi tsaf-tsaf,
‘Yammatan da suke tasawa.
Na ga kukan zo babu hijabi,
Don ga samari kui burgewa.
Shin me zai sa ku bi sheɗan,
Wanda gare ku yake turawa?
Shi fa miji ikon Allah ne,
In kin bi shi yana zaɓowa.

Har dar in kin kama mutunci,
To na ƙwarai zai yo turowa.
Sai ki ga sheɗan na tsoron ki,
Hakka matasa ‘yan holewa.
Amma in kin zub da mutunci,
Kowane gaye zai yi matsowa.

Shi ma ya san ba shi da hali,
Don aurensa a yo ɗaurawa.
Sai ki ga ya zam tamkar bawa,
Nan a gare ki yana bautawa.
Sai ki zata ai son gaske ne,
Har zuciyarki ya zam kamewa.

Sai daga ƙarshe ya zam ya bar ki,
Da na sani ba ta maidowa.
Za ki ga sheɗan na ruɗar ki,
Shigar banza ita ce wayewa.
Za ki ga ai hulɗa da mazaje,
A yanzu salo ne mai ɓullewa.
To saurara dai ki ji sister,
A gare ki ina son in faɗakarwa.
Duk fa mazajen nan da kike bi,
Babu na kirki ki yi dubawa.
A nan zan miki satar amsa,
Gane samari tantancewa.
Idan an zo wurinki da fari,
Ki ce masa gidanku ya yo aikawa
Idan gaye ne nan zai tsere,
Ba kya sake ga ya zagowa.
Domin duk wani ɗa mai kirki,
Gidanku a fari zai aikawa.

Duk wani mai son ki na haƙiƙa,
Ba ya bari ki shigar watsewa.
Zai riƙa son ki tsare kayinki,
Don aurenki yake son yowa.
Ba yadda za ai ya yaba ki,
In fa tsiraici ki kai fiddawa.
In kika yo hoto a sitatus,
Babu hijabi yai dubawa-
Sai ko ya ce: “nice!” to walla-
Ba ya son ki, ko farawa.

Sai dai a ce yana sha’awarki,
Alfasha ce yake tsarawa.
Idan dai mai so ne a gare ki,
Da kin ɗora ya yo dubawa-
Zai tuna ai wasu za su gane ki,
Zai ko ji kishi na tasowa.
Bayan wannan dai ki ji sister,Sirrinmu a yau naka tottonawa.
In dai har gaye ya taɓe ki,
Ko hannunki ya yo kamawa.
To ba so sai dai sha’awarki,
Wani shiri ne yake ƙullawa.
Ko kuma sai in shi ya kasance,
Marar bin Allah mai saɓawa.
Mai miki so na a zo a yi aure,
Ko kallonsa yana gyarawa.
Bai miki kallo mai cutarwa,
Balle taɓin ki, ko farawa.
Da kin ga mutum na kar miki kuɗɗi,
Ba ƙima to ki yi ganewa.
Ba shi nufin aure a gare ki,
Shirinsa daban ne ki yi dubawa.
Shi masoyi mai niyyar aure,
Zai nunin hanyar ɓullewa.
Zai nuna miki a nan duniya,
Tattali ne hanyar dacewa.
Duk mai sa ki a mota tinted,
Ga AC ya yiwo kullewa-
Bi shi a sannu yana da muradi,
Mijin ƙwarai ba ya farawa.
Shi na ƙwarai kan je shi gidanku,
Shi hirar shari’a aka yowa.
Ki tuna Musulunci ba soyayya,
Da babu dalilin ai farawa.
Ki tuna jin daɗin zance ma,
Musulunci sosai ya yi hanawa.
Ki tuna in kin nuna tsiraici,
Mutuncinki kike zubdawa.
Duk namiji mai sauraron ki,
Nufinsa bushasha rinƙa kulawa.
Shi na ƙwarai me zai yi da ke ne?
Burinsa Musulma mai kamewa.
Ko shi gaye in kin duba,
Burinsa ya auro mai kyan nitsuwa.
Bayan duk kun ɓarnata loto,
Sai ya guje ki bai juyowa.
Ga shi sannan kina son aure,
Don makaranta kin yi gamawa.
Dukka samari na tsoron ki,
Gwanjo ce ki zanka tunawa.
Tun da a baya kina soyayya,
Kuncen nan wa zai ɗaurawa?

Sai ki ga aure ya zama aiki,
Sai da dabaru ai ta haɗawa.
Amma can ita wadda ta kame,
Tun ma kafin tay yi gamawa-
Za ki ga kowa na ƙaunarta,
Har sai ta yo tantancewa.
Nan Allah zai ba ta na kirki,
Auren nan ka ga ya ɗorewa.
Ke ko a sannan har kin tsofe,
Shekarunki suna turawa.
Kin je fati kin je casu,
Duk an san da kina zagawa.
Duk yanzun wanda ya gane ki,
Rayuwarki ta baya za ya tunawa.

Ya sister kin yarda da Allah,
Kan shi ɗai ne ke bayarwa?

Shin ko kin yarda haƙiƙa,
Jin daɗi shi ke samarwa?
Shin ko kin kuwa yarda,
Zama na ƙwarai shi ne ɓullewa-
Domin ba kya auren kirki,
Sai na ƙwarai kin yo zamtowa?
In haka ne to sai fa ki gyara,
Riƙe Allah ɗai Sarkin kowa.
Ki sha kuruminki ki yi ta du’a’i,
Miji na ƙwarai ko ki yo dacewa.
Mai ƙaunar ki kina ƙaunar sa,
Har ‘ya’yanku su yo tasowa.
Wanda ke ba girma ga iyaye,
Wanɗanda gare ki su kai haihowa.
Wanda ko ya fita ba kya zargin,
Ko wata can ne zai riskewa.

Wanda ku girma ku tsofe tare,
Har mutuwarku ba ku rabewa.
Har ku haɗe a gidan aljanna,
To nan aƙ ƙarshen dacewa.
Kai kuma gaye sake tunani,
Alƙawari ne bar mantawa.
Duk wata yarinya da ka ɓata,
Dole gare ta a yo ramawa.
Ko a ɗiyarka koko a ƙanuwa,
Gwara ka tuba ka zan gyarawa.
Ba wai alfasha ce ɗai ba,
Ko da yaudara ce kai ƙullawa.
Za ko a yaudari taka haƙiƙa,
Sannan ne za kai ganewa.
Iyaye ku ma dai ga naku,
Ya zama dole ku rinƙa kulawa.
Tarbiya dai tun daga farko,
Ciyar su halal da ka yo samowa.
Ban da sakalci, nuna kulawa,
Musulunci yadda ya yo nunawa.
Idan ko ɗiya ta je makaranta,
Ba ta abinci kuɗin ɓaddawa.
Ka ba ta da dama masu isarta,
In ka ƙi ita kan nemowa.
Idan ta nuna tana son aure,
To ɗaura mata babu tsayawa.
Idan ka ƙi ita za ta yi auren,
Babu sadaki ba shaidawa.
Ko a gida tambai ta buƙatu-
Nata ka bi su, ka ba ta kulawa.
Idan kuwa ka ƙi, buƙatun nata,
Can a waje za ai ta biyawa.
Ke mama ki rinƙa fa lura,
‘Yar ki mutum ce tamkar kowa.
Ba mota ba da za a yi tsada,
Sai an gamsu ake saidawa.
Ba ko gida ba da za ai ciniki,
Idan ga riba ai sallamawa.
Hakan ga kina janyo haɗari ne,
Ku da ita za kui faɗawa.
Ke ko hukuma sake tunani,
Nauyin kanki ki zam sauƙewa.
Sai kin yo bitar dokoki,
Dokar kana a tilastawa.
Bara in matsa ga sahun malammai-
Na addini masu faɗakarwa.
Sai ku zage ƙaimi da hazaƙa,
Har ga du’a’i kui dogewa.
Ku ce Allah shiryar da ɗiyanmu,
Albarka mu yiwo samowa.
Malammai can fannin boko,
Musamman jami’a nai leƙawa.
Na rantse ku ji tsoron Allah!
Ranar mutuwa ranar tsaiwa.
Kuna ɗaɗɗauke da ƙarfin iko,
Kukan sa koko ku yi hanawa.
Sa ikonka ka kawo gyara,
Lada ne za kai samowa.
Hana ɗiyar da ta fidda tsiraici,
Shiga laccar da kake koyarwa.
Ka sam loton da kake jan zance,
Kay yi nasiha cike da ƙwarewa.
Ka bi su salonka cike da dabaru,
Yadda batun za sui kamawa.
To zan dawo nan a gare ku,
Da dai ku naka yi dattawa.
Na san dattawanmu na dauri,
Su ke sa a riƙa gyarawa.
Me kuke yi yau komai ya ɓaci,
Tarbiya ta yi lalacewa?
Ya Allah sa mu taru mu gane,
Kowanenmu ya yo gyarawa.
Idan wani ya yi kure a cikinmu,
Saura gare shi su zanka tunawa.
Mu haɗu guri ɗaya ga yaƙar sheɗan,
Wanda gabanmu yake shinkewa.
Wanda yake gaba da ganin mu,
A kan hanyar da take ɓullewa.
Allah sa mu gidan aljanna,
Dukka kurenmu ka yo yafewa.
Abu-Ubada maƙagin waƙar,
Ɗan Sani nake mai dubawa.
Ɗari biyu ne baitocin waƙar,
Arba’in da shida sannan ɗorawa.
Nai godiya gun Allahu,
Na yi addu’ar samun dacewa.
Na yi salati gun Mahamudu.
Da shi Allah sa mu yiwo ganawa.

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.