Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mutumin Da Ya Ce Shi Bai Yarda Da Hadisan Annabi (SAW) Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum Malam mene ne matsayin mutumin da ya ce shi bai yarda da hadisan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba? Kuma ya ce bai yarda dukkan litattafan Musulunci ba??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Karyata Hadisan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) baki ɗaya ko kuma musun litattafan da aka amince da su, ana daukarsa a matsayin abin da yake fitar da mutum daga addinin Musulunci, saboda yana nuna ya musanta wani babban sashi na wahayi da umarnin Allah.

Malaman Musulunci suna cewa irin wannan mutumin yana zuwa karkashin hukuncin murtadi (wato wanda ya bar Musulunci), kuma ana bukatar a nuna masa gaskiya tare da gabatar masa da hujjoji ta hannun kwararrun malamai don su cire masa shakku ko jahilci.

Akwai masu cewa Alkur'ani kaɗai suke yarda da shi (wato ƘALA-ƘATO) amma suka musanta Hadisi gaba ɗaya. Malaman sun ɗauki musanta Hadisi ingantacce a matsayin babban bidi'a kuma karkacewa mai tsanani, ballantana kuma haɗa da cewa bai yarda da dukkan litattafan Musulunci ba. domin hakan yana nufin ya karkata zuwa ga kafirci ko ridda.

Irin wannan mummunar aƙeedah ce ta 'yan ƘALA-ƘATO da kuma 'yan SHI'A. Duk mai yinta ba za'a kirashi musulmi ba.

Dukkanin maluman musulunci sunyi ittifaƙin cewa wajibi ne muyi imani kuma mubi dukkan abinda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya zo mana dashi. Domin Allah yana cewa:

 ؕ وَمَاۤ اٰتٰٮكُمُ الرَّسُوۡلُ فَخُذُوْهُ وَ مَا َنَهٰٮكُمۡ عَنۡهُ فَانْتَهُوۡا ۚ

kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne. (Surah: Al-Hashr, Ayat: 7).

Duk mai irin wannan akidar kafiri ne domin kuwa ALLAH yana cewa:

فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُوۡنَ حَتّٰى يُحَكِّمُوۡكَ فِيۡمَا شَجَرَ بَيۡنَهُمۡ ثُمَّ لَا يَجِدُوۡا فِىۡۤ اَنۡفُسِهِمۡ حَرَجًا مِّمَّا قَضَيۡتَ وَيُسَلِّمُوۡا تَسۡلِيۡمًا‏ 

Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'annan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama maka cikakkiyar sallamãwa. (Surah: An-Nisaa, Ayat: 65).

Bai halatta ayi koyi da irin waɗannan mutane ba. Kuma ya kamata hukuma ta ɗauki mataki akansu. Domin kuwa Sayyiduna Umar (ra) ya kashe wani mutum ya yinda yaki yarda da hukuncin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

  ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments