Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Da Ke Kin Saduwa Da Mijinta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum malam. Tambayata ita ce: mutum ne ya nemi saduwa da matarsa ta sunnah sai taki Amincewa har ta kai ya nemeta ta karfi, bayan an gama ya ce da ita har zuwa lokacin da zai tashi daga bacci kar ta sake ya ganta da kaya a jikinta, Cikin ikon Allah bacci ya kwasheshi bai tashi ba sai da safe. Yayin da ya tashi kuma ya ganta sanye da kaya ajikinta. Da ya tambaya ta ko me ya sa ya gan ta sanye da kaya sai ta ce wai sallah ta yi. Amma fa ba ta tashe shi ba ko da ta tashin don yin sallar. Dan Allah malam meye hukuncin wannan? na gode dan Allah ataimaka a amsa min tambayata malam.

HUKUNCIN MATAR DA KE ƘIN SADUWA DA MIJINTA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullah.

Allah ya wajabta wa mace wasu hakkoki game da mijinta. Ta fuskar yi masa ladabi da biyayya da kyautatawa cikin duk abin da ba saɓon Allah ba ne.

 Daga cikin kuma hakkokin da ma'aurata ke da shi a kan junansu akwai hakkin biya wa junansu bukatarsu ta jinsi da jinsi. Wato bukatar sha'awa wacce Allah ya sanya atsakanin juna. Domin shi dama aure ana yinsa ne domin samar da zuriyya tsarkaka ta hanyar biyan wannan bukatar da kuma tsare juna daga ketare iyaka da ayyukan Ɓarna.

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Idan mutum ya kira matarsa zuwa shimfidarsa sai taƙi zuwa, kuma ya kwana cikin fushi da ita, to Mala'iku ma suna tsine mata har zuwa wayewar gari".

To amma idan tana da larura kamar rashin lafiya mai tsanani ko zazzabi ko ciwon ciki, ko wata larurar ya kamata shi mijin nata ya yi mata uzuri zuwa lokacin da za ta warke. Hakanan idan yarin ya ce karama wacce ba ta saba ba, ya kamata mijinta yabi a hankali da lallami da kyautatawa har ya samu biyan bukatarsa ba ta hanyar kokuwa ko fin karfi ba.

Irin wannan yakan janyo Ƙaruwar kiyayyar juna da hayaniya da rashin fahimtar juna. Wasu lokutan ma za ka iya jin rauni ko kaji mata rauni, harma a kan iya rasa rai ta wannan hanyar.

Don haka ina baka shawarar ka bita a hankali banda kokuwa. Kuma umurnin da ka ba ta wai ta zauna tsirara kada ta sanya sutura, ba ta yi laifi ba cikin saɓa maka. Tunda lokacin sallah ya yi, kuma umurnin Allah yana gaba da naka.

Atakaice dai Malam ka ji tsoron Allah ka gyara alakarka da matarka. Itama tana da hakkin kyautatawa akanka kamar yadda kaima kake da shi akanta. Ka dena daukarta kamar baiwarka, ka dauketa amatsayin abokiyar rayuwarka, wacce kuke zaman ibadah tare. Kada ka zama tamkar wani soja a gidanka. Murmushi, Kyautatawa, wasa da juna, da tattaunawa da juna duk hanyoyin daidaitawa ne ako yaushe.

Muyi koyi da Shugaban halitta (SAW) irin yadda ya zauna da nasa iyalan, In shaAllahu zamu rabauta.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments