Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Hada Sahu Daya Tsakanin Maza Da Mata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum barka da yamma. Malam miye hukunci haɗa sahu ɗaya mata da maza ko kuma asa mata tsakiya na gode 🙏

HUKUNCIN HAƊA SAHU ƊAYA TSAKANIN MAZA DA MATA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.

Idan tambayar ita ce a cikin sallar jam'i, shin mata za su iya tsayawa sahu ɗaya da maza, ko kuma mata su kasance a baya/tsakiya?

A tsarin Sunnah, maza su kasance a sahun gaba, mata kuma a bayan maza. Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce

«خَيْرُ صُفُوفِ الرِّجَالِ أَوَّلُهَا، وَخَيْرُ صُفُوفِ النِّسَاءِ آخِرُهَا»

Daga Abi Hurairata R.A Ya ce: Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Mafi alkhairi sahun maza shi ne sahun farko, kuma mafi sharrin sahun maza, shi ne sahun karshe kuma mafi alkhairin sahun mata na karshe, mafi shirrin sahun mata na farko) (رواه مسلم).

Saboda haka, idan maza da mata suna sallar jam'i tare, ba a haɗa mace da namiji a sahu ɗaya ba, sai dai mata su kasance a bayan maza.

Idan kuma mata kaɗai ne suke sallah, za su iyayin sahu ɗaya; idan akwai mata da yawa, su cike sahu daga dama zuwa hagu, ba sai an bar mace ɗaya ita kaɗai a tsakiya ba.

Mace za ta tsaya bayan namiji idan ya limance ta. Haka nan idan za ta yi sallah da maza za ta tsaya a bayan sahu ne. Idan mata za su yi sallar jam’i, to a sunnah limamiyarsu za ta tsaya a tsakiyarsu ne, ba za ta shiga gabansu ba. Idan mata za su yi sallar jam’i tare da maza, to a sunnah za su yi baya da maza, su yi sahu irin na maza.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments