Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Jam’iyyar PDP a Bakin Marubuta Waka (Kundin Digiri Na Biyu)

TARIHIN JAM’IYYAR PDP A BAKIN MARUBUTA WAƘA

Na

Jibril Yusuf

Tsakure

Taken wannan bincike shi ne: “Tarihin Jam’iyyar PDP a Bakin Marubuta Waƙa”. Manufar wannan binciken shi ne ƙoƙarin fito da tarihin jam’iyyar PDP a cikin rubutattun waƙoƙin Siyasa, domin buɗe wani sabon fagen nazarin tarihi daga cikin waƙoƙi, ba rubutattu kaɗai ba har ma da na baka. Tun da farko an shimfiɗa tabarmar aikin ne ta hanyar kawo ma’anar siyasa da mafarinta, sannan aka kawo bayanai kan siyasar zamani har zuwa kan samuwar waƙoƙin siyasar zamani. Binciken ya kankama ne daga farkon babi na uku zuwa ƙarshen babi na huɗu, inda aka kawo bayanai kan abin da ya shafi tarihin jam’iyyar PDP tun daga tunanin kafa ta, sannan aka ci gaba da jan zaren tarihin har zuwa faɗuwarta a matakin ƙasa. Dukkan wata gaɓa ta tarihin da aka kawo an kafa hujja da baitocin waƙoƙin siyasa waɗanda suka goya wa binciken baya don tabbatar da irin abubuwan da suka faru da jam’iyyar a tsawon shekarun da ta shafe tana mulki. Daga ƙarshe, binciken ya gano cewa rubutattun waƙoƙin siyasa cike suke da tarihi musamman na abubuwan da suka faru a fagen siyasa.

Abstract

The title of this research work is; “The History of Peoples’ Democratic Party (PDP) from poets’ perspective”. The aim of this research work is to analyze the history of PDP as a political party from the realm of Hausa poetry. This will set a pace in the field of literary history, especially on trying to fish out the history of political parties in the poetry work.  Initially, the research brings about the meaning and origin of politics as well as the issues concerning modern politics and contemporary political verse. The main part of the research started in chapter 3 and concludes in chapter 4, in which anything that is related to PDP has been stated right from its inception in 1998 to 2015, when the party was defeated in election at national level.  The research tries to bring evidences from stanzas of political verses at any juncture, to prove that all the happenings related to PDP has been preserved in the political verse. The research is concluded in chapter 5 where the research found out that there is history in the Hausa verse, especially in the political verse.

Post a Comment

0 Comments