Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Cin Bashin Banki Domin Yin Kasuwanci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam, mene ne hukuncin mutum ya ciwo ko ya sa a ciwo masa bashin banki domin ya yi business?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

A farkon mun amsa irin wannan tambayar, mun ambaci cewa:

Haramcin bayarwa ko karɓar bashi-da-ruwa (interest) abu ne sananne a wurin dukkan masu addini ma, ba wai addinin musulunci ba. Dalilin haramcin a musulunci yana nan a cikin Ayoyi da Hadisai Sahihai da suka zo a kan haka. Sannan kuma ga maganganun manyan malamai masana a kan batun, tun daga zamanin Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum) har zuwa yau.

Don haka musulmi ba zai nemi bashi daga irin waɗannan bankuna masu ta’ammali da riba (interest) ba, sai in ya zama masa tilas, kuma ya shiga takura sosai. Musamman kuma idan har ya zama rashin karɓar zai janyo wani abu daga cikin haƙƙoƙinsa ɗan ƙasa ko na sauran musulmi zai salwanta, ko ya bai wa arna da fasiƙai iko da dama har su cigaba da danne musulmi.

Amma a lokacin da ake da bankunan da ba su yin ta’ammali da riba, to ya wajaba musulmi ya yi ƙoƙarin mayar da harkokinsa a can. Sai dai ko in an gano cewa su ma ɗin ba da gaske suke yi ba, ungulu ne da kan zabo suke yi ko yaudara ce kawai suke yi domin neman yawan masu ajiya. Allaah ya kiyaye.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments