Header Ads Widget

Request to place your ads here.

Kanu

6/random/ticker-posts

Hoton Waibuwar Hausawa A Cikin Waƙoƙin Mamman Shata


Yakubu Aliyu GOBIR

Abu-Ubaida SANI

Tsakure:

Masana da manazarta sun tafi kan cewa, daga cikin adabin al’umma (na baka ko rubutacce), mutum na iya fahimtar salon rayuwar al’ummar na gaba ɗaya. Wannan ya haɗa da tunaninsu da imaninsu da fahimtarsu da al’adunsu da tsarin zamantakewa da sauransu. Mawaƙa na taka muhimmiyar rawa wurin fito da tunanin al’umma. A bisa wannan zaren tunani ne wannan takardar ta ginu, inda take ƙoƙarin hango waibuwar Hausawa daga bakin Mamman Shata. Shata yakan danganta mutum da
aljani ko kuma ya ba shi wata siffa ko ɗabi’a ta aljani domin nuna shahara da buwayar mutumin. Haka ma yakan danganta magani da aljani a wasu daga cikin waƙoƙinsa. Wannan takarda ta bibiyi irin waɗannan waƙoƙi da suka haɗa da ‘Malam Babba na Ƙofar Gabas,’ da ‘Hassan Sarkin Dogarai,’ da ‘Mamman Sakkwato Kyaftin,’ da kuma ‘Waƙar Sarkin Bori Sule.’ Daga ƙarshe takardar ta fahimci cewa, Bahaushe ya yarda da wanzuwar aljani har ma ya ɗauke shi a matsayin halitta mai matuƙar hatsabibanci. A taƙaice, Bahaushe ya tafi kan cewa, ƙololuwar buwaya kan samu ga ɗan’adam yayin da ya yi cuɗanya da aljani.

Muhimman Kalmomi: Hausaswa, Waibuwa, Aljani, Mamman Shata

Also read...

Post a Comment

0 Comments