https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 Daga


 


Aliyu Muhammadu Bunza


Department of Languages and Cultures


Faculty of Humanities and Education


Federal University Gusau


 


 


Takadar da aka gabatar a Faculty of Arts and Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo University Sokoto, Second National Conference: Theme: History, People, Religion and Culture of Kebbi (Kabi) Kingdom since 1515, 10th-12th July, 2017


 

Gabatarwa


Farfajiyar k’asar Hausa tana da nagartattun dauloli bakwai da suka mamaye duniyar adabin Bahaushe: Kano, Katsina, Gobir, Zazzau, Zamfara da Kabi[1]. A Kano, Bagauda ya kere kowa. A Katsina kamar ba kowa sai Katsi. A Gobir, Jangwarzo ya hana a ji wani gwarzo. A Zazzau, Amina ta yi wa rawuna da wanduna fintinkau. A Zamfara, ‘Yargoje ta ciri tuta. A Kabi, Kanta ne kan kowa. Muradin wannan takarda kallon Daular Kabi a dunk’ule, tare da baje hajar nazari a kan ikon Sarkin Kabi Muhammadu Sama cikin taskar bakandamiyar mawak’in masarautarsa Buda ‘Dantanoma mai take: “Gagara K’arya Sadauki; Sama Gwarzon Alk’ali”. Alk’iblar nazarina ba ta rena da kallon zubi da tsari, salo da sarrafa harshe da fyace diddigin jigo/jigogin wak’ar ba. Na bar su ga k’wararrun masana adabi su yi nasu buki a kan wak’ar. A nawa tunani, zan yi amfani da ma’auni al’ada na biyar k’ididdiga da fashin bak’in kuramen d’iyan wak’ar da ke da d’aukar hanakli da shiga zukatan wad’anda aka wa wak’ar, da abokan gwagwarmayar su. Wanda duk ya saurari fasahar Buda cikin bakandamiyarsa ya san wak’ar yak’i ce, wak’ar tarihi ce, wak’ar tankiya ce, wak’ar tawaye ce, kuma wak’ar gwagwarmaya ce, kar ta san kar, aljani ya taki wuta.[2]  Wad’annan su ne gurabun da ake son a harara a cikin wak’ar.

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Wane ne Buda ‘Dantanoma?


A iya sanina, Sa’idu Muhammadu Gusau ya sha cewa wani abu a kan ‘Dantanoma a rubuce.[3]  K’ari bisa ga binciken Sa’idu shi ne, Buda ‘Dantanoma mutumin k’asar Yabo ne. An ce, shi ne babban makad’in sarkin Yabo Shehu. Tun fil azal makad’in tankiya ne. Idan ya ‘baro kid’insa na tankiya ya yi jaye-jaye, ya yi wa Sarkinsa Shehu laifi aka koro shi, sai ya ruga Argungu ya ‘boye wajen maigidansa Muhammadu Sarkin Muza Bawaya. Da dubu ta cika, ya dinga yi wa Sarkin Kabi Sule habaici a wak’a aka tare shi aka kar’be turayensa aka rataye su gidan Sarki[4].  Bayan rasuwar Sarkin Kabi Sule, maigidansa Muhammadu Sama’ilan Nabame ya hau, ya dawo Kabi ya kama halinai.

Asalin sunan Buda Muhammadu, sunan “Buda” suna ne na yanayi na wanda aka haifa ana matsanancin hazo. A k’asar Hausa, sunan “Muhammadu” ba ya ambatuwa k’arara gaya domin kamar sunan uban kowa ne. Ana yi wa Buda lak’abi da “‘Dantanoma” ya yi rinjaye. Yana da ‘yan kar’bi a wak’arsa, an ce, kotso yake kid’a. Yana da ‘ya’ya biyu sanannu, d’aya mace mai suna “Abingani” da namiji “Muhammadu”. Abingani a Argungu ta rasu, Muhammadu kuwa ya fara ‘yan wak’e-wak’en gado, ya bari, ya shiga duniya babu d’uriyarsa. Akwai sa’bani da yawa a kan barin wak’ar Buda da rasuwarsa[5].

 

Salsalar Sarkin Kabi Muhammadun Sama (1920-1934)


Bayan Sarkin Kabi Kanta babu sarkin da ya yi amo a daular Kabi da zukatan Kabawa kamar Sarki Sama. Sarkin Kabi Sama’ila jikan Sarkin Kabi Sama’ila Karari ne kuma d’an tsatso ga Sarkin Kabi Yakubu Nabame. Shi ya gaji Sarkin Kabi Muhammadu Toga. Yakubu Nabame yana kan karagar mulki daula ta rushe ‘ya’yan sarauta suka warwatse don kare mutuncin gidajensu ga hannun mak’iya. Wasu suka yi Mungadi, wasu suka doshi Kamba, wasu suka yi Argungu, wasu suka yi Arewa (cikin Arawa da Zabarmawa da Buzaye)[6]. Yakubu Nabame kakan Sarki Sama ya nufi Arewa wajen mahaifiyarsa Ba’ara. Da ya dawo Kabi da iyali ya dawo, ita ta haifa masa Sarkin Kabi Muhammadu Ba’are. Ya auri Bafulatana a Gwandu ta haifa masa Sarkin Kabi Sama (Mayak’i).

Bayan da Nabame ya dawo gudun hijira daular Fulani ta kafu aka kama shi aka tura Sakkwato. A Sakkwato aka saka shi cikin mayak’a, ya yi fice sosai[7]. A Sakkwato ya haifi Sarkin Kabi Sama. An ce, d’ai rana aka zana musu suna shi da Sarkin Musulmi Audu ‘Danyen Kasko[8]. Nabame a cikin gumuzun jihadi shi ya kashe wa Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo d’a. Gorin da Sarkin Gobir Bawa ya yi masa ya sa, ya yi murabus daga sojojin Fulani ya nemi ya dawo gida, Sarkin Musulmi na wancan zamani ya aminta. Aka yi masa rakiya har Gande ya k’araso Gudale ya sauka. Daga nan, ya shigo Argungu ya fitar da su k’angin Fulani ya k’wato k’asarsu ta gado duka ya kafa sabuwar duniyar Kabawa[9]. Bayan ya rasu, Yusuf Mainasara ya gaje shi. Bayan mutuwar Yusuf, Sarki Muhammadu Ba’are (d’an Ba’arar da Nabame ya auro k’asar Arewa) k’asar mahaifiyarsa ya yi mulki. Daga gare shi sai Sarkin Kabi Abdullahi Toga wanda ya sa aka tsagaita wuta na yak’e-yak’e da Fulani[10]. Toga na gurgusawa Sarkin Kabi Sama ya hau karaga, ya tsinke/farke layar tsagaita wuta da Fulani ya ci garuruwan Fulani (99) da yak’i.

Bayan rasuwar Sarkin Kabi Sama (1883-1915) k’anensa Sulaiman ya gaje shi 1915-20. Bayan rasuwar Sulaiman, Muhammadu Sama d’an Sarkin Kabi Sama ya dawo 1920-1934. Bayan wucewarsa d’ansa Muhammadu Sani (jikan Sarki Sama) ya hau 1934-1942. Daga rik’on Muhammadu Sani sai Sama’ila Mudi daga Kamba (fararen Lekawa) ya hau 1942-53. Daga nan, sai Muhammadu Shehe 1953-59 (kuma k’anen Sama). Daga nan, sai Muhammadu Mera 1959-1996 (Tankad’a Hau’bin Sama). Daga gare shi sai Sama’ila Muhammadu Mera (1996-yau) (Taka Kusheyin Sama) ya hau. A bisa diddigin tarihi Sarki Sama Mayak’i har yanzu bai kau ba yak’e-yak’e kawai suka kau.

Na yarda da fad’ar Aliyu ‘Dandawo:

Gindi  :       Shugaban tahiya Sarkin Kabi mai Sudani

:       Ila marin rugga d’an Yakubu sa gurfani

Jagora:       Ko yanzu mai rabo ya samu ya gak’e kowa an nan

Yara   :       Mahassada su kau an bar su suna shawagi

 

Hoton Daular Kabi:


K’asaitacciyar daula ce a k’asar Hausa wadda Sarki Muhammadu Kanta ya kafa shekaru (502) da suka gabata. Farfajiyar daular ta kai har cikin Nguru ta daular Borno. Mayak’anta sun dardaza fad’in ta har cikin k’asar Oyo. Silalen ikonta ya kai har cikin k’asashen Benin da Niger da Burkina Fasso ta yanzu. Sarki Kanta na daga cikin dakarun yak’i na Sarki Muhammadu Askiyya. Da k’arfi ya kawo tsoro ya d’ebe, ya ‘balle ya kafa tasa daula ta daban mai suna Kabi[11]. Daula ce da aka kafa tsakanin yak’i, cikin yak’i, da rigingimun hare-hare da d’aukar fansa. Addinin Musulunci ya yi shekaru aru-aru a cikinta. Asalin sarautar Kabi takenta Amirul Muminiina, (Sarkin Musulmi)[12]. ‘Daya daga cikin manyan k’abilunta Kyangawa, Sarkinsu Kyanga Manu ya yi aikin Hajji a k’arni na (17k’n)[13]. Daula ce da ta tattara Hausawa da Arawa da Zabarmawa da Nufawa da Dakarkari da Fulani da Azbinawa da Larabawa da Wangarawa da Shangawa da dai sauran k’ananan k’abilu. A tarihance, daga Sarki Muhammadu Kanta zuwa Sarkin Kabi Sama’ila Muhammadu Mera (1996-yau) an yi sarakuna (33). Cibiyar daular ta taso daga Surame zuwa Birnin Kabi lokacin rik’on Sarkin Kabi Tomo, Sarki na (13). Ta sake dagargajewa Argungu lokacin Sarkin Kabi Yakubu Nabame Sarki na (22). Daular ta shigo mulkin Turawa lokacin  Sama (1883-1915) Sarki na (26). Gwagwarmayar Kabawa da Fulani ya sa daular durk’usawa lokacin Sarki Sama’ila Karari Sarki na (21) Sarkin Kabi Yakubu Nabame Sarki na (22) ya dawo mata da ruhinta[14]. Wannan gwagwarmayar ita ta haifar da darusan adabi da dama tsakanin Kabawa da Fulani wanda wannan wak’ar da za mu yi nazari ta yi wa kakka’ban gara[15].

Dabarun Bincike:


Tunanina na nazarin wak’ar makad’a Buda ‘Dantanoma bai ba ni mamaki ba sai da na shiga aikin gadan-gadan. Na farko dai, Buda ba shi a raye. Na biyu, babu yaronsa ko yaransa na wak’a a raye. Na uku, Sarkin da ake yi wa wak’ar shi ma ba shi a raye. Abin ban haushi, babu wurin da za a samu wak’ar rerawar Buda da muryarsa. Don haka, dole matakin bincike na farko shi ne, neman d’iyan wak’ar ga wad’anda suka ji ta suka kama wani abu a ciki. Jerin kayayyakin rubuce-rubucenmu na bincike da kundaye babu wurin da za a tsinci wak’ar bale bayananta. Dole na shiga masarautar Kabi da Gobir domin samun wasu d’iyan wak’ok’in daga bakunan manya. Haka kuma, na dawo masarautun Sakkwato da Gwandu da Kano da Katsina domin samun wasu d’iyan wak’ar da ba a rasa ba. Na bi sawun tattaunawa da gidajen wasu fitattun mawak’an masarautun Kabi da Gobir da Yawuri da Sakkwato domin samun d’an abin da ba a rasa ba. Bayan tattaro wak’ar, na sake tsara ta, da bitar ta, na kwatanta ta da ainihin tarihin da take son tabbatarwa. Wannan ta sa dole a tuntu’bi fitattun ayyukan da aka yi a kan daular Kabi domin kwakkwahe zaren tunanin Buda ‘Dantanoma[16]. Shiga d’akunan karatu da gidajen adana tarihi musamman na daular Kabi da Sakkwato ya agaza ainun. An tattauna muhimman mutane a fadar Kabi da Sakkwato da ke da alhakin sanin wani abu a kan daulolin da shi kansa ‘Dantanoma da wak’ok’insa. Na yi amfani da d’iyan wak’ar da na samo babbarkatai domin daidaita tunanin wak’ar a tsarin salon wak’ar baka.

 

 

Bakandamiyar Buda:


A tarihi, Kabawa ba su da wata wak’a a masarautarsu da ta cancanci sunan bakandamiya in ba wannan ba. Fitattun jaruman mawak’an masarautar Kabi irin su Ata da Kaaree (makad’in jama’a) da Aliyu ‘Dandawo (makad’in Mamman Shehe) da Gero Zarto da ‘Dan Kawu da Jatau (makad’in S. Shiko) da Ata (makad’an Nabame) ba su yi wa masarautar Kabi wak’ar d’ebe takaici irin wak’ar da Buda ‘Dantanoma ya yi ba. Gindin wak’ar shi ne:

: Gagara k’arya sadauki

: Sama gwarzon alk’ali.

 

Asalin wak’ar ita ce, bakandamiyar da yake yi wa Sarki Sama[17]. Babban abin da ya sa ta yi fice sosai shi ne, a taron dabar da aka yi a Kano zamanin Sarkin Kano Shehu na tarbon d’an sarauniyar Ingila Prince Edward 1925. A taron, Sarkin Kabi Sama ya fita da doki (500) mayak’a yan baka (500) masu harugga (500) dakaru (1500) ke nan. A gaskiya, Sarki Sama fitan yak’i ya yi, don haka duk wani basarake da ya halarci taron tsawonsa bai kai na Sarkin Kabi Sama ba. Sarki Sama bai sauka cikin garin Kano ba, ya nemi a ba shi babban fage da zai sauka da dakarunsa. Sarkin Kano Shehu ya ba shi farfajiya babba a wajen birnin Kano aka sauke kayan yak’i. Wurin ya zama wata babbar matattara, a zo a ga Sarki, a ji Sarki, a ga dakarun Sarki. Bayan k’are taro, wurin ya zama babbar unguwa mai suna “Fage”[18]. Bakandamiyar ta kakkamo duk abubuwan da suka faru, tun fitan Sarki Sama daga Argungu har ya je Kano ya dawo, da abubuwan da suka faru a taron daba. Bakandamiya wak’a ce, ba dole duk abin da ta kamo iya tsawonsa da fad’insa ke nan ba, wani a k’ara masa tsawo, wani a rage masa fad’i, wani a bar shi yadda yake. Duk da haka, bakandamiyar ‘Dantanoma daular Kabi ta kasa a faifai ga mai tababa ko musun d’aukakarta da k’asaitarta a duniyar zamaninta.

 

Zaren Tunanin Bakandamiyar Buda:


Ga d’an abin da na kalato na wak’ar bayan na yi tankad’e-da-rairaya sosai na riwayoyi daban-daban da na samo. A d’an ma’aunina ana iya regon kayan cikin wak’ar Buda kamar haka:

 

K’asar Kabi da Abokanta


A cikin amon turun Buda k’asar Kabi ba ta da abokiyar da ta kai Gobir. Da Kabi da Gobir ba su tak’ama da komai face yak’i na kare martabar gida da darajarar kakanni[19]. Bugu da k’ari, da Kabi da Gobir su ne alak’ak’ai ga Fulani da mulkinsu tun gabanin jihadin k’arni na (19k’n) da lokacin jihadin, da kuma bayan jihadin. Da yak’e-yak’en addini, da na fad’ad’a k’asa, da na mulkin mallaka suka lafa, aka share jini abin ya koma wasa. Buda ya ta’bo wannan silalin tarihi a turunsa da ke cewa:

Jagora: Kanta da Bawa nis sani

: Jangwarzo ba mu san Hillani ba

: Gagara k’arya sadauki

: Sama gwarzon Alk’ali

 

 

 

Wane ne Sarki Sama a Tafashen ‘Dantanoma?


Sarkin Kabi Muhammadu d’an Sama’ila wanda aka fi sani da Muhammadun Sama ko “Sama” kawai a tafashen Buda, ba kanwar lasa ga abokan adawa ba ne. Tsananin yak’in Sama ya sa ake yi masa lak’abi da “Mayak’i" Buda ya ta’bo gwarzantaka da muhibba da buwayarsa kamar haka:

Jagora: Sama na Audu mai hawan ban kashi

: Mai tamburran fama

Gindi: Gagara k’arya sadauki

: Sama gwarzon Alk’ali

Jagora: Sama d’an Nabame da dambun Masu[20]

: Ba cin yaro na ba.

 

A ganin Buda, babu wani Sarki a farfajiyar Sudaniyya in ba Sama ba, domin jarunta ce sarauta, Sama ko a ko’ina ya kai. Dubi yadda Buda ke cici’ba shi da fad’ar:

Jagora: Sarkin sarakuna shiryayye

: Ba kowa nan sai kai

Gindi: Gagara k’arya sadauki

: Sama gwarzon Alk’ali

Jagora: Ka ji Sarki ka zo ka iske Sarki

: Ba Sarkin k’age ba.

 

Bayan Buda ya kore duk wani sarki in ba Sama ba, ya kuma jaddada fad’ar duk wani sarki a sudaniyya in ba Sama ba ne Sarkin k’age ne. Sarkin k’age shi ne Sarkin da ke kar’bar umurnin wani Sarki domin haka ‘Dantanoma ya tabbatar da cewa:

Jagora: ‘Dan nana Hausa ba a mai da awa shi,

: Dac can kuma ba a yo ba[21].

Gindi: Gagara k’arya sadauki

: Sama gwarzon Alk’ali.

Jagora: Mamman mai komi mai kowa

: Kuma kai aw wan kowa

: Ba matsuwa na Bubakar

: Sa tuba ba sake fad’in na yi.

 

Wad’annan d’iyan wak’ok’i duk suna hararar sarakunan daular Sakkwato ne da ke hannun Fulani. Don haka “kowa” ga Fulani take komawa. Haka kuma “Sarkin Sarakuna” ya had’a da Fulani. Tirk’ashi ji wannan:

Jagora: Mamman mai wada yas so

: Sarkin d’ibah haushi[22].

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Matsayin Sarautar Kabi:


A al’adance, sarauta ba ta amo ta yi tasiri sai ta yi gwagwarmaya da abokan hamayya ta fatattake su, a kama na kamawa, a kashe na kashewa, mai rabon ganin bad’i ya tsere ko ya yi hijira. Daular Kabi tana tink’aho da nagartattun kakanni da ba su mik’a wuya ga kowa ba kamar ragon suna. Don haka, Buda ke kiran mai Kabi Sama da cewa:

 

Jagora: Sama maganin k’iyayya rabuwa

: Kore k’aton banza

Gindi: Gagara k’arya sadauki

: Sama gwarzon Alk’ali

Jagora: Sama kore tsagera ba ni gidanai

: In sa turayena.

 

‘Dantanoma na tabbatar da cewa, masarautar Kabi ba ta da sauran mak’iya domin ta k’ore Fulani. An raba su da k’asar Kabi, kare jini biri jini, don haka yake son a kore sarakunansu a kar’be gidajensu a matsayin ganima, makad’an fadar Sama su samu wurin rataye turayen fama. Buda ya sake nuna irin matsayin sarautar Kabi da ta ci Fulani da kar’be musu tamburan kakaninsu.

Jagora: Ga wani ya ga tamburan kakanai,

: Ba za a kid’a mai ba.

Gindi: Gagara k’arya sadauki

: Sama gwarzon Alk’ali

 

Dukkanin makad’an masarautar Kabi sun tafi a kan cewa Sarautar Kabi ita ce shakundum. Da yawa sukan ambaci sarakunansu da: Shugaban dama da hauni, ko babban bajini, ko shugaban tahiya, ko sarkin sarakuna, ko mai dama da hauni ga su nan dai.

Kushe Sarkunan Fulani:


Babban dalilin da ya sa Buda ‘Dantanoma da wak’arsa suka yi fice shi ne zambo da habaicin da yake yi wa sarakunan Fulani. Da Buda ya fara da babbar sarautar daula ya fara da ita wato sarautar Gwandu yana cewa:

Jagora: Sarkin Gwandu ya nashe mu da yula

: Hat taf hwad’a gulbi

 

Raddin da Buda ya bayar kan nashinsu da yula da aka yi shi ne:

 

Jagora: Sarkin Gwandu d’an gajere

: Daidai kwa’bin laka.

 

Bayan an ta’bo Sarkin Gwandu, sai aka bi k’ananan sarakunansa, d’aya bayan d’aya, ana muzantawa. Ga d’an abin da aka ruwaito daga ‘Dantanoma:

 

 

Jega  :

: Sarkin Jega yau tsawo yai kauri

: Daidai kamun kura.

 

‘Dakingari  :

: Sarkin ‘Dakingari dogo rusheshe

:  Daidai takin dambe.

 

Tambuwal  :

: Sarkin Tambuwal Ba’uden banza

: Sheshenai na jimen

: Runji shi ka wa yanka[23].

Alero :

: Alero nig ga guntun Sarki

: Daidai kwa’bin laka.

 

Ambursa:

: Ni na zo Ambursa na ga Sarki

: Da bak’i k’ok’e d’an mai shuni

: Sarki da k’uraje ga jikinai

: K’ok’e d’an mai k’warya.

 

Wajen K’asar Hausa:


Hatta da sarakunan da ke huld’ar arziki da k’asar Gwandu ‘Dantanoma bai sa musu ido ba. Da ya je Doso Zarmakwai ya ji an ce, yana zagin Sarkin Gwandu sai ya ji tsoronsa, ya ba shi doki kyauta toshiyar baka, kar a tallata halayensa ga abin da ‘Dantanoma ya ce:

Jagora: Doso nig ga wawan Sarki

: Shi had doki yab bai.

 

Yawurawa ba su ce masa uffan ba, amma saboda dangantakarsu kyawawa da Gwandu da kuma daular Sakkwato ‘Dantanoma ke cewa:

Jagora: ‘Dansanholama na bakin kogi

: Ba mu san tushenai ba.

Gumuzun Sarkin Kabi da Sauran Sarakuna a Kano (1925):


Dabar da aka shirya Kano 1925 k’asaitacciya ce. Kowane Sarki k’wazo yake son ya yi, a ga ya cira tsara, a hawan dabarsa. A fagen dabar, babu Sarkin da ‘Dantonoma ya ragawa, sai in bai gan shi ba. Ga yadda ‘Dantanoma ya fasa bak’i.

 

Had’uwar Sarkin Musulmi Tambari da Sakrin Gwandu Shehu da Sarkin Kabi Sama a Bungud’u kan Hanya zuwa Kano


 

An ce, Sarkin Musulmi Tambari ya fara riskar Sarkin Kabi Sama a Bungud’u. Ya zo ya tarar da su, karo na farko da suka fara gaisawa ta girma da arziki. Sarki Tambari ya ce wa Sarkin Kabi Sama: “Mai Kabawa muna lahiya”, Sarkin Kabi ya amsa da cewa: “Mai Hillani lahiya lau”[24]. Yana cikin motarsa, Sama na kan dokinsa. Nan ‘Dantanoma ya ce:

Jagora: Ga wani ya shigo barayar kusa[25]

: Yac ce mota yah hau

: Ga wani ya shigo cikin kwandonai

: Yac ce mota yah hau

: Motar k’warai tana ga Nasara

: Katako na Hausa.

Bayan da Sarkin Musulmi Tambari ya fito mota aka gaisa, ya shiga mota aka ruhe gam! ‘Dantanoma ya ce:

: Mu sarkinmu bai shiga zunguru[26]

: Don ba balli na ba

: Ko dai an tai Kano da sauri

: Jayen munta an kai.

 

Jim kad’an ga Sarkin Gwandu cikin mota “A kori kura” da shi da Sarkin Kabin Jega Modi suna gaba, sauran k’ananan sarakuna na bayan bodi zaune. Suka gaisa da Sarkin Kabi, sai kallo ya koma ga wad’anda ke cikin mota, ana ta kururuwa da mamakin yadda mota d’aya ta d’auko manyan mutane haka. ‘Dantanoma ya hau bakinsa:

Jagora: Na hore ka kak ka sai katako

: Saye d’an Azbin Sarki!

: Doki shi ka tak’ama a yi kallo,

: Ba katakon wofi ba,

: (K’yale iskan banza)

: Motak’ k’warai tana ga Nasara

: Katako na Gwandu.

 

Ganawar Sarkin Zazzau da Kano da Sarki Sama:


An ce, sun zauna wuri d’aya suna tattaunawa a dandalin taro. Sarkin Kano ya sha alkyabba da nad’i da sandar sarauta da kayan alfarma. Sarkin Zazzau ya shawo babbar riga mai aiki d’aba-d’aba a fuskanta mai d’aukar hankali. Sarkin Kabi Muhammadun Sama ga al’adansa, koyaushe fararen kaya yaka yi ba su da aiki gaba da baya, tun fil azal malami ne. Da ‘Dantanoma ya ga kallo ya koma sama shaho ya d’auki rak’umi, domin aiki Sarkin Zazzau na riga ya burge ‘yan kallo sai ya ce:

Jagora: K’awa da ulu sai ‘yan mata[27]

: Sai dottijon banza,

: Kai Sarkin Kano taho ka ga Sarki

: Ba d’ai ga wad’annan ba.

 

 

 

Shirin Hawan Sarkin Kabi Sama da K’warjininsa:


A ganin ‘Dantanoma wajen hawa wani Sarki ke tsere wani Sarki. Sarauta iko ce, iko ko da k’arfi ake yin sa da gwarzantaka. Tun a cikin gida Fulani suka fara firgita. ‘Dantanoma ya ce:

Jagora: Sarkin Isa ya ga damman masu

: Bai san yak’i na ba.

 

Da aka biyo ta Sakkwato suka firgice sosai domin ganin irin shirin da Sarkin Kabi ya fito da shi. ‘Dantanoma ya ce:

Jagora: Hawan da yay yi Sakkwato

: Sada zumunta na

: Bai so su ji tsoro ba

 

Da aka shiga birin Kano cewa aka yi:

 

Jagora: An ce ba a wa Kano takakka

: Mamman ya tattake ta

:An ce ba a zo a Kano takakka

: Amma Mamman ya yi

: An ce ba a wa Kano takakka

: Sama ya tattake ta

: Don mun zo Kano da dambun masu

: Ba mu samo gaba ba[28].

 

K’arfin Sojan Daular Kabi:


Idan aka ce wak’a bakandamiya ce, babu abin da ba a iya samu a ciki. Ga al’adar wak’a, bakandamiya ba a k’are ta domin duk wani muhimmin abu da mawak’i ke son ya adana, a ciki yake kai shi. A cikin k’ok’arin fayyace Dabar Kano, ‘Dantanoma ya baje kolin irin k’arfin dakarun daular Kabi da ya gagari Fulani, kar ta san kar! Dantanoma na cewa:

Jagora: Taron Kano da an ka yi

: Sama shi Allah Yas so

: Shi Sarkin Kano da yas san daidai

: Tarbon bahago yay yi

: Ko sarkin Kano da yas san daidai

: Tarben manya yay yi

: Sarkin Kano da shi da garinai

: Rannan daji yak kwan

: Malaman gari ka cewa Sarki

: Taso ka shige birni.

 

Iya irin makaman zamaninsu Daular Kabi ta tanada wa dakarunta, don haka ba ta kwana da fargaban  kowace daula ba, a k’ark’ashin kowane suna aka kafa ta. ‘Dantanoma ya fi kowa sanin haka, don haka yake ce wa Sarkin Kabi Muhammadun Sama:

 

Jagora:        Gyara takubba na Yari tallabi masu

:        Shiga birni ba kowa.

 

Cikin d’awainiyar tafiya zuwa Kano Buda na cewa:

 

Jagora:       Bahago ya zo Gusau da rarar k’arfi[29]

:        Ba a sake haye mai ba

:        Nan yai karo da Sarkin K’aura

:        Yaw watce mutanenai.

Ga alama, irin wannan arangamar ya sa Sarkin Bunza ya ji tsoron kai wa Gwandu gudunmuwa a yi karo da Sarkin Kabi. Buda cewa yake yi:

 

Jagora:       Bunza nag ga karnan Sarki [30]

:        ‘Dan Gurumad’an Bunza

:        Da yaj ji za a gamamma

:        Rancen ciwo yay yi.

A tsarin k’arfin sojan Sarkin Kabi akwai dawaki da rak’umma da dakaru ‘yan k’asa. Da za a je Kano taro Buda yi lisafo su kamar haka:

 

Jagora:       Doki ya yi fiffike ya yi bak’i

:        Ba mu gane iyaka ba.

:        Dan nan baya rak’umi ya fi dubu

:        Tsinin mashi zalla

:        Can gaba ko uban dawa da d’iyanai

:        Tsinin kibiya zalla

:        Ga sulke da bindiga ga masu

:        Ga tamburran fama.

 

Taron Dabar Kano:


A hanyar zuwa Kano Sarkin Kabi sama ya bi hanyar Shuni ya sauka Dange wajen Sarkin Bauran Dange Hassan ‘Dan’mu’azu (1931-38). Ya kwana Sanyinna da Shagari da Kam’bama da Tsamiya da Tureta da Murai da Bungud’u da Kwatarkwashi da Gusau. Ya bi ta Tsahe da ‘Yankuzo, darzaje daki-daki[31]. Sarkin Kabi gamgami ya yi sosai zuwa taron domin Buda ya ce:

Jagora:       Daga Ilo hak Karekare

:        Duka sun zo jid’ag gwannan farko.

Makad’a Buda ya ba Sarkin Kabi hak’uri cewa ba kiran Fulani ne ba, taron gwannati ne.

 

Jagora:       In ba don yana kiran taro ba

:        Sama ba mu zuwa Hausa

:        Bahago kak ka ji komai

:        Ba nasu kira na ba

:        Mamman kak ka ji komai

:        Ba su ka kiran nan ba.

 

Duk da haka, ‘Dantanoma ya ce, su suka ci k’wallo a taron domin a tasa fad’i cewa ya yi.

 

Jagora:       In a je gida a ce wa Tsahara

:        Mu namu nuhi ya kai

:        Don kai gwanna yam mik’a ma hannu

:        Sannan yab ba kowa.

 

A zaton ‘Dantanoma, in an zo dabar Kano, Sarkin Nupe Kabi zai mara wa ba Sakkwato ba, domin daular Kabi ta kai har k’asar Yarbawa kuma Nufawa sun more wa tsaron daular Kabi[32]. Da ‘Dantanoma bai ga sarkin Nupe bayansa ba, ya ce:

 

Jagora:       Ga wani ya zo Kano

:        Kamar bai zo ba

:        Inda d’an mai koko.

 

Ana wata ga wata:


Baya an kammala dabar Kano, aka fahimci akwai buk’atar a samu had’in kan sarakuna gaba d’aya, a share jini a koma wasa. Daga can aka shirya yadda za a yi sulhu tsakanin daular Kabi da Sakkwato kowa ya fahinci juna[33]. Wurin da Gizo ke sak’a shi ne: wace k’asa za a yi zaman sulhu? Wa zai kira wa, a yi sulhu? Wa zai jagoranci taro? A wata riwaya an ce, da aka dawo daga Kano a kan hanyar zuwa gida a mararrabar Kanoma aka ce Sarkin Kabi ya biyo Sarkin Musulmi Tambari a bi hanya d’aya. An ce, nan ‘Dantanoma ya hana ya ce:

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Jagora:       In an je gida a ce wa Tsahara

:        Tabkin da tas sani bana ya koma laka

:        In an je gida a ce ma Tsahara

:        Kabi ta koma rugga

:        In an je gida a ce wa tsahara

:        Gaba ta koma baya

:        Don sarkinmu bai biyan wani Sarki

:        In ba Allah na ba.

 

Da jin haka, sai Sama ya d’an jinkirta aka sake shawara. Da ‘Dantanoma ya ga ‘yan shawara na son su ci nasara, a bi hanya d’aya da Sarkin Musulmi, a fara shiga k’asarsa (wato Hausa) yana gaba Sarkin Kabi na baya. Kai! Wane mutum in ji mutuwa, ya dafi tafashen fama ya hau bakinsa da cewa:

 

Jagora:       Haba Sama in biya ka kai

:        Ka zo ka bi Turai in san manya kab bi

:        Kanta da Bawa nis sani

:        Jangwarzo ban san Hillani ba.

 

Da furta wannan d’an wak’a, miki ya koma sabo, aka tashi baran-baran, kar ta san kar, kowa ya kama hanyarsa.

 

 

Tsarin Hawan Daba:


An tsara hawan dabar bisa tsari irin na hukuma ba na gargajiya ba. A tsarin, Turawa ne na farko, don haka dai ana nan zaman bayinsu biye da su ake a koyaushe. Wannan abin ban haushi ne ga wanda ya fahinci wulak’anci irin na mulkin mallaka. Wajen da aka ta’bo ‘Dantanoma sai aka ce, bayan Turawa sai wak’ilan gwannati bayansu. Sarakuna su biyo baya a bisa tsarin darajar da gwannati ta yi. A tsarin Sarkin Kabi shi ne Sarki na goma sh uku (13). ‘Dantanoma bai yarda ba, sai ya tsare ido a fagen, ana fara kiran Turawa ya dafi turunsa ya kira Sarkin Kabi Sama da cewa: (Sama/Haba!)

 

Jagora:       Zaburo biyo Turawa

:        In san manyan Kab bi

 

Jagora:       Maza furce gabansu

:        Bi ma Bature in san manya kab bi.

 

Wayyoyoyo! ‘Dantanoma ya yi makad’i: Sama ko ya yi Sarki ko’ina aka Sarki. Haba! in kai ne yaya zaka yi?

 

Barazanar Daular Kabi ga Daular Fulani (Hausa)


A lisafin Kabawa, duk wata k’asa da ba ta Fulani ba, kuma Fulani suka k’waci mulkinta sunanta “Hausa”. A tarihin artabun Kabawa da Fulani, Kabawa suna ik’irarin su suka ci nasara. Dalilan Kabawa kuwa shi ne, Sama ya ci garuruwan Fulani (99). Kabi ta ci Ambursa, ta kuwa ragargaza Fulani a yak’in Alwasa. Ba za a musanta cewa, Fulani sun ta’ba cin galaba a kan Kabawa ba musamman idan aka nazarci karon battan Sarki Muhammadun Sama da Sanyinnawa k’ark’ashin jagorancin Mijin Jewo[34]. A koyaushe, idan ana bukin shekara-shekara na salla da kamun kifi da shan kubewa da gad’a da annashawa taken Kabawa shi ne:

 

Jagora:       Kabi ta ci Hausa

:        Da mi tac ci Hausa?

:        Da k’arfi da yaji

 

Wannan barazanar har gobe ba ta guje ga bakunan Kabawa ba, wai ko ana taya fansa. Tsananin tsoron da ake yi wa Sama ya sa ‘Dantanoma cewa:

 

Jagora:       Wani ya fad’i ya kare ga tsaratai

:        Bai san rame na ba.

:        Wani Sarki shina bid’an barwanai

:        Bai san jama’atai ba

:        Da dai a yamutsa na

:        Da wasu sun yi baran k’osai.

Matsayin Wak’ar Buda ‘Dantanoma a K’sar Hausa:


A wajen Buda da Kabawa babu wata wak’a da ta fi wak’ar Buda tasiri. Wak’ar Buda bakandamiya ce, komai ake son adanawa a ciki ake kai ta. A d’an nawa bincike, tsofafi da Sarakunan Kabi na da wannan wak’a tarshe take bakunansu kamar Fatiha a bakin liman. A gaskiya, talakawa na d’an jin tsoro rera ta saboda cin zarafin Sarakuna da ke ciki. Mawak’an Gobir da Kabi, bayan mutuwar ‘Dantanona suka dinga rera ta da muryoyi daban-daban da ‘yan k’are-k’are da rage-rage. Wak’ar ‘Dantanona wata taskar tarihi ce da ba a yi kamarta ba a gabaninta, a bayanta ba a samu ba. Don haka, za mu iya cewa; wak’ar Gagara k’arya ta Buda:

 1. A wajen Kabawa furen kallo ce domin kakaninsu ake zugugutawa da cicci’bawa a kan abokan adawa.

 2. A ‘bangaren daular Sakkwato wani k’alubale ne ga Sarakunanta da jama’arta a kan dad’ad’d’iyar adawa.

 3. Wak’ar wata taskar tarihi ce, duk da sanin cewa, ba a rasa hazon soyayya da k’iyayya a ciki, wanda zai kawo cikas ga hak’ik’anin tarihi.

 4. Wak’ar wata allura ce da a koyaushe za a ji da sauran rina a kaba. Tattare da sanin cewa, rinar ta tafi abinta, amma wak’ar Buda ta yi wa kabar da rinar ta yi wa gije kadada don tuna baya.

 5. A hangen Buda, abin da ke tsakanin Kabi da Sakkwato ba addini ba ne, siyasar mulki ce, don haka bai ta’ba kawo zancen addini ciki ba, wannan wani haske ne na fuska biyu da wasu Hausawan k’asar Hausa ke kallon jihadin k’arni na (19k’n)[35].


Sakamakon Bincike:


Yadda jihadin k’arni na 19k’n ya yayatu a k’asar Hausa; haka wak’ar Buda ta yayatu a k’asar Hausa. Da su Kabawa da Fulani duk suna rera ta a matsayin tuna baya da raha. Mafi yawan daulolin duniya da k’asaitattun Sarakuna da masu mulki sukan yi amfani da hazik’an adibbai/mawak’an lokacinsu domin kare kansu da sarautunsu. Da ba don wak’ar Buda ba, da tuni an manta da irin artabun da Kabawa suka yi da Sakkwato. Daga cikin  abin da na hango akwai:

 1. Da d’an gari akan ci gari. Asalin Buda d’an Yabo ne k’ark’ashin rik’on Sakkwato don haka Kabawa ke amfani da shi a matsayin d’an lek’en asirinsu.

 2. Bakandamiyar Buda tattare da farin jinin da ta yi a halin yanzu, babu ita a rubuce, babu ita a kowace irin taskar taskace adabi[36].

 3. Dalili da wannan sai a ga kowa abin da ya ga dama yake fad’i a kan sarkin da yake so ko baya so sai ya ce: inji Buda[37].

 4. Babu Bakaben asali da ke tir da wak’ar Buda, haka kuma babu Bafulatanin k’warai da zai yi madalla da ita.

 5. ‘Da ba don Buda ba, da dabar da aka yi wa Prince Edward, a shekara (1925) ba ta samu shiga adabin Hausa ba.

 6. Da Kabi da Gobir yak’i da Fulani ya had’a su zumunta, kowanensu abokin adawa ne da daular Sakkwato. Haka kuma, daulolin biyu da yak’i suke bugun gaba, makad’in yak’i ya fi kar’buwa gare su da samun yardarsu, don haka Buda ya samu kar’buwa kabi da Gobir.


Nasarar da wannan bincike ya yi ita ce k’wak’walo ‘batattun d’iyan wak’ar Buda daga bakunan da suka san shi, suka ji shi, ko suka kwaikwaye shi. Samar da d’an wani abu a rubuce nata cigaba ne tare da fashin bak’in kuramen wasu d’iyan nata.

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Nad’ewa:


Raya daula da d’aukakar martabarta yana a hannun masarautanta. Sarki shi kad’ai ba ya mamaye daula/k’asa sai da cikakken goyon bayan mutanenta. Daular Kabi ta samu wadatattun Sarakuna ‘yan kishin k’asa da amintattun talakawa ‘yan ga-ni-kashe-ni. Cikin wannan d’awainiyar aka ci karo da fasihin mawak’in tankiya da ba a yi kamarsa ba a k’asar Hausa. Makad’a Buda Allah Ya had’a jininsa da daular Kabi, babu yadda Sarakunan Yabo ba su yi ba, su tsayar da shi k’asarsu ya k’i. Kabawan ma da suka yi masa d’awainiyar nuna isa don ya tabbata k’asarsu ya gaya musu cewa, k’auna ce yake da ita gare su ba don abinsu ba, kamar yadda yake cewa:

 

Jagora:       Algargi ba ta wa mai turu

:        Da ya koma Yabo[38].

 

Hak’ik’a, gawurraccen makad’i shi ne rayuwar kowace daula da adana martabartar ta. Ba don Buda ba, da sunan Kabi bai mamaye k’asar Hausa ba. Ba don Narambad’a ba, wa ya san Isa da Sarkinta. In ba turun Dan’anace ba, sunan Shago ba zai wuce Mafara ba. Ba don Gambo ba Muhammadu Inuwa Danmad’acci ko Jega ba a ji d’uriyarsa ba. Lallai makad’a Aliyu ‘Dandawo ya tabbatar da k’unshiyar bakandamiyar ‘Dantanoma a fad’arsa.

 

Jagora:       In hadari ya taso

:        Cikin iyawar Allah

:        Giragizai su ka zuwa

:        Su taushe kaihin rana

:        Mutane waw waye duhu

:        Nabame yaw waye duhu

:        Yay yi ma azna fitila

:        Yag gak’e Torankawa

:        Gudunmuwa kaz zaka ka ya ishe shi ya sha kaihi

:        Mutun guda ya hi gaban mutum dubu

:        Magabata abin da sun ka hwad’i

:        Ai mai da hwad’i ‘banna na.

Gindi:         Shugaban tahiya Sarkin Kabi mai Sudani

:        Ila harin rugga d’an Yak’uba sa gurfani.

 

 

Manazarta


 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

[1] .            An yi ayyuka masu ma’ana a kan wad’annan dauloli. Fitattu daga cikinsu akwai: Dokaji, Kano ta

Dabo ci Gari da Smith, Government in Kano, da Usman, Transformation of Katsina, da Augi

“Gobir. Factor, “da Smith Government in Zazzau, da Nadama, “Zamfara in the 19th Century”,

1968.

[2] .            Gaba d’aya wakar a kan Fulani ta k’are da masu goyon bayan mulkinsu. Wak’ar yak’i ce mai

tabbatar da rinjayen Kabawa ga Fulani a fagen daga. Wak’ar tarihi ce, domin ta yi waiwaye

ainun a kan tarihin yak’e-yak’en Kabawa. Wak’ar ta tankiya ce, babban burinta ta hasa wuta a zukatan Kabawa su tsaya matsayinsu komi taka zama ta zama. Wak’a ce mai jaddada tawayen daular Kabi a kan daular Sakkwato da suke ganin daular Fulani ce kawai. Don haka, wak’ar gwagwarmaya ce tsakanin k’abilu biyu Kabawa da Fulani.

[3] .            Ya ambace shi cikin littafinsa S.M Gusau, Makad’a da Mawak’an Hausa, 1996, Kaduna; FISBAS

[4] .            Riwaya biyu ke ga wannan tarihi. Wasu kuwa ce wa suka yi, lokacin da ya rera wani d’an wak’a:

Jagora   : Lamso nis sani da Tsahara

: Ban san kingin nan ba

Lamso da Tsahara su ne matan da ke yi masa kyauta. Da sauran matan kishi ya kama su aka ce musu “kingi” suka ce, a kawo turayen a rataye ya daina wak’a. Ya mayar da raddi da cewa:

Jagora    : Turu aka amsa a rataye

: Bakin Buda yana garai.

[5] .            Wasu mutane musamman Gobirawa suna cewa, Sarkin Musulmi Tambari ya sa aka yanka shi.

A nawa bincike a Argungu da Bunza da Dukishi da Geza da Zariya. Bayan mutuwar Sarki Sama

Buda ya yi hijira da yaransa zuwa yamma. Na sami wasu tsofafi a garin Dukushi da suka tabbata cewa, sun gamu da Buda da yaransa wani k’auye mai suna Balu ta k’asar Kabi a kan hanyarsa ta Kamba. Ana zaton can cikin k’asar Kamba ko jamhuriyyar Nijar ya rasu. Wasu kuwa cewa suka yi, ya rok’i Allah ya kashe shi gabanin Sama Allah ya kar’bi rok’onsa.

[6] .            Tattaunawa da Sulaiman Nabame, d’an Sarautar Kabi kuma ma’aikaci a gidan Tarihin Kabi. Na

yi hira da shi cikin Gidan Tarihin Kabi kusan awa 2-3, ranar 20/06/2017. Suleiman yana da

digirin Hausa a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto, 2003.

[7] .            Dukkanin Kabawan da na yi hira da su, sun ce an yanke wa Nabame hukuncin kisa, daga baya

aka ce a tura shi fagen yak’i ya mutu can a huta. Da Allah bai yi mutuwarsa ba sai da ya d’auko fansa. Tattaunawarmu da Sambo Wali da Yakubu Bagaye da Suleiman Nabame ta tabbatar da wannan. 26/006/2017.

[8] .            Da Sarkin Kabi Muhammadun Sama (1920-1934) da Sarkin Musulmi Audu ‘Danyen Kasho (

) duk rana d’aya aka haife su.

[9] .            Sarkin Gobir Bawa ya gaya wa Nabame cewa,“Kana nan kana k’ok’arin raya gidan wasu (Fulani)

ga naku gida can ya rushe, k’asar kakaninka ta yamutse babu Sarki, ga su can suna yi wa Fulani bauta”. Daga lokacin jikinsa ya yi la’asar, ya nemi ya dawo gida. Hira da na yi da Alhaji Muhammadu Sambo Wali Sakkwato, da Suleiman Nabame da Yakubu Bagaye (Masani tarihin  Sarautar Kabi) duk sun yi canjaras da wannan kalami, 26/06/2017 da 30/06/2017.

[10] .           Ana yi wa wannan tarihin tsagaita wuta da Fulani da Lafiyan Toga zamanin Sarki  Abdullahi

Toga (1963-1883) an yi Lafiyar Toga (1870-1878) Shekara 10 ana yak’i.

[11] .           An ce, bayan da aka ci nahiyar da yak’i kason da aka bai wa Kanta bai gamshe shi ba, bisa ga

irin famar da ya taka. Don haka ya yi wa Askiyya Muhammadu tawaye ya kafa k’asarsa mai suna Kabi.

[12] .           A k’arni na (16k’n) Sarkin Musulmi na Maroko ya aiko wa Sarkin Kabi da wata wasik’a ta

shawarwari. A wasik’ar an kira shi da suna Amiirul muminiina na Kabi. Wannan ya nuna daular Kabi ta riga ta Sakkwato kar’bar Musulunci da kafa daular Musulunci. In babu k’ira me ya ci gawai?

[13] .           Kyangawa k’ark’ashin daular kabi suke, sun barbazu a Bunza da Kyangalwai da Kamba da Yelu

da Geshoru da Illo da Dukushi da Geza da Argungu da Kangiwa da Yeldu da Sauran manyan garuruwa da k’auyukan Kabi da jamhuriyyar Nijar da Benin.

[14] .           Ya tattara d’iyar sarauta suka tsayu a  babban gungun farfajiyar fadamar Kabi da ake yi wa suna

“Argungu” a yanzu. Wasu na ganin, daga yekuwarsa ta kiran danginsa Kabawa: “Ar! Ku zo nan gungu mu tsaya” ko “Ar! Ku zo mu yi gungu” aka samu suna “Argungu”. Akwai tatsuniyar cewa, wai had’uwar da suka yi wuri d’aya mak’iya suka hange su suka ce: “Ar! Sun yi gungu” wai daga nan aka samu “Argungu”. A nawa hasashe na d’alibin al’ada, ina takin sak’a da su. Kalmar “Ar!” a Hausa kalma ce ta farga ko ku’buta, kuma tana fita a fagen kirari. Gungu kuwa, in da tsibiri in kuwa taruwan jama’a mai jiran dako ko firgittu ko mad’auka fansa. Don haka, in dai ya kasance: “Arnan Gungu” wad’anda suka kafirce wa masu son su mallake su. Ko “Ar! Ga gungu” wato ga wurin da suke can; ko kuma ya kasance na “tsakar gungu in idan muka yi la’akari da tarihin cewa, Kabawan da suka zo Argungu sun tarar da garin “Buntsari”. Buntsari kuwa daga kifi sai naman ruwa ke yin sa a tsakiyar gurbi. Wato garin “Gungu” ne.

[15] .           Yak’e-yak’en kabi da Sakkwato ya haifar da karuruwan magana da tatsuniyoyi da tarihi da

tarihihi da wasan barkwanci da tashe da wak’e-wak’en yara maza da mata da wak’ok’in baka na manya kamar: Iyakar Kabi Sawwa; wurin da duk ka sha furar shinkafa nan ne Kabi gare ka;  ja ya fad’i ya d’auke; dudduk’e har Kabi; da Kabi har Kabara karan gamba guda ne, ga su nan dai.

 

 

[16] .           Fitattun ayyuka su ne na Bello Alk’ali da P.G Haris daga baya aka samu aikin PhD na Nasiru

Aminu, 2015.

[17] .           Buda ya yi wak’ok’i da yawa amma wannan kawai ce aka sani. Haka kuma, shi kansa Buda da ita

yake tak’ama an ce duk lokacin da ya je wak’a in ba ita ya yi ba, ba ya tsima kowa. Da ya fara ta kyauta sai ya kau da kai.

[18] .           An ce, Sarkin Kabi cewa ya yi a sama masa “Fege” Kanawa ba su san “Fage” ba sai dai jeji/daji

ko karkara. Fage a Kabawa ana nufin babban wuri irin na noma shinkafa ko dandalin wasan dambe ko kokuwa yalwatacce. Aka fassara wa Sarkin Kano Shehu ya gane ya je wajen gari ya ba shi. Hira da Yakubu Bagaye Argungu 29/06/2017, gidan Sarkin Kabi Sama’ila Muhammadu Mera.

[19] .           Gobirawa da Kabawa abokan juna ne domin sai hali ya yi daidai ake abota, ‘yan kishin

k’asashensu ne da ba su yarda da gurgusa in zauna ba, su dai biya ka wuce kamar kowa.

[20] .           Dambun masu ma’ana biyu ke gare shi: masun yak’i a tarshe wani bisa wani tarshe ka ce damin

gero ko dawa, ana ce da shi dambun masu”. Akwai kifin da ake ce wa masu/harasu, mai k’aya zargo-zargo in an yi miya ko dambun kifi yaro ba zai iya ci ba gudun ya lak’e masu ga mak’ogoro.

[21] .           “Hausa” yana nufin Sakkwato da Ko’ina take rik’o a daularta. Fadar “Dac can” yana nufin

sauran k’asashe masu ikon kansu irin su Gobir.

[22] .           “Mai wada yas so” wanda babu wani Sarki irinsa da zai tilasta shi ga abin da bai so ba,

Sarakunan k’ark’ashin mulkin Fulani sun rasa wannan. Idan sarkin Kabi ya fad’a babu wani Sarki a daular Kabi da zai fad’i akasinsa.

[23] .           An ce, a taron Sarkin Tambuwal babu sarkin da ya fi shi ‘yan busar sheshe k’wararru. Asalin

sheshe kuwa Fulani Udawa masu kiyon tumaki zalla sun fi shahara da shi. Sheshen nan da ya burge ‘yan daba Buda ke son kushewa.

[24] .           Tattaunawa da Alhaji Muhammadu Sambo Wali Sakkwato ta wayar hannu, a lambarsa

07034224741 ranar 26/6/2017 a ranar ina Gidan tarihin Kabi da ke garin Argungu.

[25] .           Motar k’arama ce mai zurhi ciki, da k’ozo kamar kunkuru, ta yi kusa ga irin sak’ar gidan ‘bera

(kusa). Don haka aka kira ta “barayar kusa wurin hutawar ‘bera cikin raminsa.

[26] .           Zunguru da duma ake yin sa, da shi mata ke sa lalle (k’unshi). Yana da d’an tsawo kamar shantu

ciki ake tura hannu a sa lalle. Hannu na ciki kamar kifi a cikin gora. Balli wani bak’in kifi ne mai rigima da karmanci irin na tafiyar karuwa. Kabawa na yi masa kirari da: Balli kamar kifi”.

[27] .           Ulu abin k’awa ne ga mata a saka a wuya da kwankwaso a yi masu adandani launi daban-daban

da fari da ja da bak’i da algashi da shud’i ga su nan dai. Dattijon banza shi ne Dandaudu ko cali na wasanni. Calin ‘yan dambe na sa ulu a kwankwaso ya yi rabaja. Ke nan da mata sai dottijon biri ke sa ulu.

[28] .           Kalmar “gaba” tsohuwar kalma ce, ma’anarta “yak’i”. Asalinta rashin jituwa da juna da

hamayya da sa-in-sa da jayyaya da fad’i-in-fad’i.

[29] .           “Rarar k’arhi” wato k’arhin da ya yi gumuzu da garuruwan k’asar Hausa da Zamfara da ‘Burmawa

bai k’are ba. A wata fassara tana d’aukar bai gaji ba

[30] .           “Karma” Kamar namiji mai kamar ‘yan mata da kasala irin ta ‘yan daudu.

[31] .          :Ranat Attanin na Yakubu yah hau

:Daga Sanyinna yak kwan

:Shagari ya’ aje yak kwana

:Ga Hausa tana kallo

:Tsamiya can uban Jibo yak kwana

:Ga Hausa tana kallo

:Ya kwan Tureta gagara k’arya

:’Burmawa na kallo

:Murai can uban Jibo yak kwana

:Zamfara dut na kallo

:Bungud’u can gadan-gadan yak kwana

:Zamfara duk na kallo

:Ga bak’on mutan K’watarkwashi

:Sarki in don Allah ya so.

:Bahago ya zo Gusau da rarar k’arhi

:Ba a koma haye mai ba.

:Nan yag game da Sarkin K’aura

:Yaw watce mutanenai

:Ni na so shi kwana Tcahe da yaz zo

:Sai yar ra’bawatai

[32] .           Lokacin ana Surame tare da Nufawa ake. An ce, sun ta’ba laifi har aka sa su yi ya’bin katangar

birnin Surame da man kad’e. Dalili da haka, an share k’arnuka da yawa kowace shekara idan zafin rana ya tsananta sai kufan ganuwar Surame ta nashe da mask’i. Bugu da k’ari, Nufawa abokan wasan Katsinawa ne, Kanta kuwa mahaifiyarsa Bakatsina ce. Bai kamata Nupe ta mara wa wata daula baya ba in ba Kabi ba.

[33] .           An ce, k’ok’arin wannan sulhi shi ya haddasa aka k’irk’iro bukin kamun kifi a Argungu. A dubi

Birnin Tudu, “Bukin kamun Kifi a k’asar Argungu”, 1984, kundin BA.

[34] .           An yi artabu da Sarki Sama a wajen garin Sanyinna bayan ya dawo da kai Hari wajajen garin

Dono. A filin Fuloti na da, nan aka yi, gumuzun d’ebe takaici, kowanensu ya bar accakwama. An ce, shi ne yak’i na k’arshe da Sarki Sama ya yi a rayuwarsa.

[35] .           Idan aka dubi yadda tsarin sarautun daular ya koma bayan jihadi, babu shakka k’abilanci da

tu’assubanci da ‘bangaranci da zalunci ya yi katutu. Hak’ik’a, a kan haka ne Kabawa da Gobirawa suka ja daga cewa, kowa ya kare gidansu ganin abin ya koma yak’i ba jihadi ba.

[36] .           Farfesa ‘Dalhatu ya yi hira da Bango a Gobir da wani mai Molo a Argungu da suka rera wak’ar

Buda sosai. Na amfana da ita duk da yake ban san shekarar da aka yi hirar ba. Ina godiya ga farfesa Magaji Tsoho Yakawada da ya nemo wak’ar a Jami’ar ABU ya ba ni faifai na saurara.

[37] .          Na fahimci duk garin da na je, in na tambaye su abin da Buda ya ce a kan Sarkinsu, in mai muni

ne ba sa fad’a, sai su juya wak’ar. Don haka, wak’ar na buk’atar bincike na musamman a bi rariya-rariya a k’asar Hausa a tattaro d’iyanta a tace su. Misali wasu na cewa ya ce:

Jagora    : Sarkin Tambuwal Ba’uden Banza

: Runji shi ka wa yanke.

Hak’ik’anin gaskiya a d’an bincikena ba haka abin yake ba cewa ya yi:

Jagora    : Sarkin Tambuwal Ba’uden Banza

: Sashenai na jimai

: Sarkin Tambuwal Ba’uden Banza

:Tsoron Mamman yaj ji

[38] .           Da Buda ‘Dantanoma ya je Argungu Muhammadu Sama ya sa aka ba shi Saulo (500) na gero,

Cukurfa (500) na shinkafa aka ba shi sarkawan da za su kai mai kifin miya da rundawan da zai kai masa mama. Ya ce, duk wad’annan ya baro su Yabo don haka shi jaruntaka da gwarzantaka ya biyo, soyayyarsa da Kabawa a zuci take.

 Daga


Haruna Umar Bungud’u


K’ibd’au:harunaumarbungudu@gmail.com


Lambar waya: 08065429369Da


Haruna Umar Maikwari


K’ibd’au: maikwariharuna@gmail.com


Lambar waya: 07031280554


Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya, Gusau. Jihar Zamfara.


Paper Presented To The Department Of Nigerian Languages, Bayaro University Kano, At The 1st International Conferance on Hausa Studies In The 21st Century, On Monday 10th – Thursday 13th November, 2014.
Tsakure.


        Wannan Muk’alar za ta yi tsokaci ne dangane da wasu al’adun aure wad’anda aka gudanar a garin Bungud’u masu nason maguzanci ko tsafi, wannan al’ada ita ce ake kira “Albiris”. Takardar za ta kalli dalilan da suka sa Hausawan wannan yankin gudanar da ita tare da muhimmancinta. Haka kuma takardar za ta binciko yadda ake gudanar da wannan al’adar mai kama da tsafi har da masu yin ta da kuma dokokinta.

GABATARWA


Garin Bungud’u wani gari ne da ke cikin yankin Zamfara wanda yake kimanin kilomita goma sha shida daga babban birnin jihar Zamfara wato Gusau. Kasancewar jama’ar wannan gari Hausawa ne mafi yawansu sai kuma Fulani. Jama’ar garin sun had’a da Katsinawa da Gobirawa wad’anda akasarinsu Hausawan ne ko kuma Fulani. K’asar Bungud’u ta yi iyaka da k’asar Maru da Maradun ta gefen Yamma, ta yi iyaka da Gusau ta Gabas. Sannan ta yi iyaka da k’asar Anka da ‘Dansadau a ‘bangaren Kudu, a sashin Arewa kuwa ta yi iyaka ne da k’asar K’auran Namoda.

K’asar Bungud’u k’asa ce mai fad’in da albarkar noma, kuma akwai gulbin Sakkwato wanda ya ratsa gefen garin, ya fito daga Gusau zuwa nan Bungud’u ya zarce Maru har dai zuwa Sakkwato. (Gusau, Babu shekarar bugawa).

1.1 Ma’anar Al’ada


        Wani masanin cewa ya yi “Al’ada ita ce tarsashin rayuwar mutum tun daga haihuwarsa har zuwa balagarsa da girmansa da mutuwarsa (Ibrahim, Y. Y. 1977).

Al’ada sababbiyar hanyar rayuwa ce wadda akasari jama’a na cikin al’umma suka amince da ita. (Gusau, S.M. 1986).

Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar d’an Adam tun daga haihuwa har zuwa kabarinsa (Bunza, 2006).

Babu tabbacin cewa al’ummar garin asalinsu maguzawa ne amma dai wasu al’adun irin wad’annan da suke gudanar ne ke sa a rik’a ganin wani d’an nason hakan a cikinsu, wato dai abubuwa irnsu albiris kan nuna cewa kamar wata bauta ce mutanen ke yi wa rana. Domin hak’ar wannan binciken ta cim ma ruwa zai fi kyau mu dubi yadda masana suka bayyana ma’anar tsafi don yin k’ok’arin fayyace dangantakar su da albiris kamar haka:

Tsafi na nufin bin wasu hanyoyi na gargajiya musamman yi wa iskoki hidima, da yanka, da bauta, domin biyan wata buk’ata, ko samun wani amfani, ko tunkud’e wata cuta. Bunza (2006).

2.0 Al’adar Albiris


Albiris wata al’ada ce da ake gudanarwa a garin Bungud’u a lokacin da ake bukin auren budurwa. A ranar wankan amaryar ne k’awayen amarya tare da amaryar ke zuwa a tsakiyar gulbin Bungud’un a turbud’e tuwo a yi ta dukan wurin da kara ko tsumomi sannan a je dutsin Babakiyawa a shiga wani kogonsa a fito ta hanyar bin wasu k’a’idoji.

2.1 Yadda Ake Gudanar Da Albiris


          A lokacin auren budurwa bayan an d’aura auren a ranar wankan amarya ne amarya da k’awayenta kan shirya don zuwa wurin albiris. Daga cikin shirye-shiryen sukan tanadi tuwon dawa malmala uku, daga cikinsu za su d’auki d’aya sai su hau kan turmi su d’aga ta sama su fara wasu maganganu kamar haka:

Ranata ranata,

Iyeriye, iyeriye,

Sa uwaye kuka,

Sa kakanni kuka.

Daga nan sai su sako wannan malmalar k’asa a kan faifai, daga nan sai a tattara ta a kwashe a nufi gulbi ana yin wak’ok’in gad’a iri daban-daban har sai sun kai tsakiyar gulbin sai su tona wani d’an rami su jefa tuwon tare da gashin jikinsu na mara da na hammata da kuma na kai, sai su turbud’e su. Da sun gama turbud’ewar sai su fara dukan wajen da sanduna ko karan da suka tanado, sukan d’auki lokaci kamar minti goma ko k’asa da haka suna dukan wurin, daga nan sai su ruga aguje don babu mai son a bar ta a baya.

Da barin wannan wurin sai su nufi falalen dutsin gulbin mai suna Babakiyawa, wannan dutsen yana da wani kogo mai fita daga k’asa zuwa sama, wannan kogon ne kowa zai shiga amma da d’ai-d’ai da d’ai-d’ai, ana yi ana ‘bollowa ta sama har sau bakwai. Daga nan sai a nufi gida ana cigaba da wak’ok’in gad’ar kamar dai yadda aka zo da farko.

Idan an koma gida to albiris ya k’are sai a cigaba da wankan amarya kamar yadda al’adar garin ta tanada. Ana tu’be amaryar ne sai alwanka ta je ta yi mata tsarki (kama mata ruwa) sai a dawo da ita a d’ora ta kan turmin nan da aka hau a lokacin da za a je albiris, k’awayenta da sauran danginta har da wasu ‘yan kallo na wurin sai a saka mata wasu manya-manyan goro farare guda biyu a cikin bakinta (gefen dama da na hagu).

Alwanka wata tsohuwa ce k’ak’k’arfa wadda ke yi wa amaryar wanka idan za a kai ta gidan angonta, akan samu wata tsohuwar ta taimaka mata da zuba ruwa ita kuma tana cud’awa, amaryar tana kuka su kuma k’awayen sai wak’ok’in gad’a suke yi kamar haka:

Jagora:         Daga bana ba ke raya ba,

‘Yan amshi: Daga bana ba ke raya ba,

Jagora:        Ke raya ga bangon d’akinki,

‘Yan amshi: Ke raya ga bangon d’akinki,

Jagora:        Ba ta koma hira ga darni,

‘Yan amshi: Ba ta koma hira ga darni,

Jagora:        Ba ta koma wane sakanni,

‘Yan amshi: Ba ta koma wane sakanni.

Haka kuma akwai wata wak’ar da suke cewa:

Jagora:         Gangara gangara ga mu gangara mu je aljanna,

‘Yan amshi: Gangara gangara ga mu gangara mu je aljanna,

Jagora:         Allah Sarki,

‘Yan amshi: Iye,

Jagora:         In ya ga dama ya maida tsohuwa yarinya,

‘Yan amshi: Gangara gangaraga mu gangara mu je aljanna,

Ko kuma su rera wannan wak’ar da suke cewa:

Jagora:         ‘Yar tsohuwa mai d’an k’ok’o,

‘Yan amshi: ‘Yar tsohuwa mai d’an k’ok’o,

Jagora:         Allak kashe ki watan gobe,

‘Yan amshi: Allak kashe ki watan gobe,

Jagora:         Allak kashe ki mu sha gumba,

‘Yan amshi: Allak kashe ki mu sha gumba,

Suna dai rera wak’ok’i daban-daban har a k’are wankan amaryar. Da zarar abokan sun ga an gama wankan sai su fara ce mata:

Ke ar lik’e, ke ar lik’e.

K’e ar lik’e, ke ara lik’e.

Ita kuma sai ta kame turmin ayi ‘bam’bara ta k’i saki sai an sha wuya sosai a cire ta a d’auke ta a kai ta cikin d’aki inda iyayenta mata kad’ai ne tare da wasu tsofaffi mata ke shiga a cigaba da ba ta nono har lokacin da za a d’auke ta zuwa gidan mijinta. Ban nono shi ne wasu shawarwari da za a rik’a ba amarya na zaman gidan miji kamar na cewa duk abinda mijinta ya ce ta yi ta yi ba tare da gardama ba, da cewa ta yi biyayya ga mijin da sauran mutanen gidan da kuma bin umurnin iyayen mijinta da barin ragwanci da yin k’ok’arin biyan buk’atun mijinta da sauran shawarwari makamantan wad’annan.

 

2.2 Muhimmancin Albiris


Albiris yana da muhimmanci k’warai ga jama’ar yankin, amma babban muhimmancinsa shi ne korar miyagun aljanu wad’anda za su iya kawo matsala ga wannan auren. Ana ganin cewa duk auren da aka yi albiris wajen yinsa za a samu zaman lafiya, babu wani abun da zai kawo matsalar zaman saboda an magance shed’anun aljanun. Idan bak’ak’en aljanu suka so mace sukan hana ta d’aukar ciki ko mijinta na haihuwa. A wani lokaci su saka mata zubar jini koyaushe, dole a gaji da ita a sake ta, ko su dinga zubar mata da ciki bayan ta d’auka. (Bunza, 2006).

        Wani muhimmancin albiris shi ne tsarkake ma’auratan, jama’ar suna ganin cewa duk lokacin da aka yi albiris to an tsarkake amaryar daga wasu laifuffuka da ta yi na baya, daga nan sai ta kiyaye wasu laifuffukan a gaba.

Albiris yana rage samuwar kwantai daga cikin k’awayen amaryar domin a cewarsu bayan an turbud’e tuwon a tsakiyar gulbi aka gama dukan wurin, kowace daga cikinsu zata ruga a guje babu wadda zata yi kwantai sai wadda bata ruga ba har aka bar ta a baya, amma duk wadda ta tsere zata yi saurin samun miji.

Yin albiris na kawo sassaucin fad’a a tsakanin mata da miji a lokacin da aka kai amaryar gidan mijinta, saboda wasu k’a’idoji ne ake shimfid’awa don miji ya yi hak’uri da matar kuma ita matar ta yi biyayya ga mijin, idan haka ta samu babu wani fad’a da kan taso sai wanda shed’anun aljanu suke haifarwa, shi ma manya kan shawo kansa.

2.3 Su wa ke Yin Albirs


        Masu yin albiris su ne amarya tare da k’awayenta da sauran ‘yan kallo kuma su duka ne sharud’d’an albiris kan fad’awa. Ba a son wani namiji ya shiga cikin masu yin albiris domin wad’ansu abubuwan da ake yi a lokacin sirri ne mata kawai suke jin su ba tare da maza ba. Ko ma ‘yan matan sai wad’anda suka isa aure ne ke zuwa.

 

2.4 Dokokin Albiris


Albiris yana da dokoki da farko dai ba a yin albiris sai ga sha’anin aure, kuma auren budurwa kawai ba da sauran mata ba, wato ba a yin sa a auren bazawara da na tsofaffi da sauransu.

Sai da yamman ranar wankan amarya ne ake yin albiris ba a yinsa da safe ko da rana ko da a ranar wankan ne.

Ba a tsayawa wani abu da zarar an dawo daga albiris sai wankan amarya kawai.

Bayan an gama dukan wurin da aka turbud’e tuwon albiris dole ne kowace budurwar ta ruga aguje don duk wadda bata ruga ba za ta yi kwantai.

Doka ne a wajen albiris cewa duk wanda ya shiga cikin kogon dutsen nan kar ya yi tusa don in ya yi tusa kogon zai had’e da shi ya matse shi kuma ba zai bud’e ba sai an samo kwandon k’eya (kwarkwata) an zuba a cikinsa.

    2.5 Matsayin Albiris


              A halin yanzu an daina yin wannan al’adar ta albiris. Ana ganin cewa an sami kimanin shekara talatin da daina yin wannan al’adar, amma dai an gudanar da ita tun lokacin da garin ya kafu har wannan lokacin da aka fara daina ta. Ana ganin babban dalilin da ya sa aka daina wannan al’adar shi ne shigowar k’ungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a Wa’ik’amatus Sunnah (IZALA) ne a garin a sakamakon wa’azantarwar da suka rik’a yi wa jama’a da su bar ire-iren wad’annan abubuwan da ba su da tushe bare makama.

KAMMALAWA


Saboda la’akari da k’aramcin lokaci da kuma la’akari da muhimmancin abubuwan da wannan takardar take k’unshe da kuma la’akarin da kasancewar mahalartan wannan taron mafi yawansu Hausawa ne sun san abin nufi, halin da ake ciki an daina gudanar da wannan al’adar a garin an dube su ne a matsayin tunatarwa ga manya-manyan mutane na cikin wannan taron kar zancen ya zama na kunne ya girmi kaka kawai. Sannan wannan takardar ta zama matsayin d’and’ano jiran rabo ga matasanmu da fatar mu k’ara had’uwa wani lokaci idan abokin gabarmu lokaci zai d’aga mana k’afa mu shek’e ayarmu a kan lamarin aure a al’adar Hausawa.

     Manazarta 


 

https://www.amsoshi.com/contact-us/