Amsoshi

Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan Ph. D


Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe


Jami’ar Jihar Kaduna.


e-mail: ibrasskg@gmail.com


Tel: 0803 6153 050


 
1.0       GABATARWA


 

Rayuwar Maguzawa da tsafi kamar dangantakar tsoka da jini ce. Wannan ne ma ya sa ake ganin sunan da ake kiran su ya bambanta da na sauran ’yan’uwansu Musulmi wad’anda suka k’aurace wa wannan rayuwa ta tsafi. Kasancewar tsafin da suke aiwatarwa yana da alak’a da rayuwarsu gaba-d’aya, Maguzawa sun yi tanadin tsafe-tsafe iri-iri wad’anda ke yi musu jagoranci a hanyar neman abinci da magani da sana’o’i da wasanni da tsaro da dai duk wani abu da ya shafi rayuwa ta yau da kullum.

 

Mak’asudin wannan nazari, shi ne k’ok’arin gano irin tanadin da Maguzawa suka yi wa tsafi a wasu daga cikin matakan rayuwarsu na aure da haihuwa. An yi tunanin ke’be nazarin ga aure da haihuwa saboda a tabbatar da dugadugan nazarin wurin duban irin yadda tsafi yake da tasiri a lamurran da suka shafi murna da jin dad’i a rayuwar tasu. A tak’aice, nazarin zai yi k’ok’arin tabbatar da hasashen da ke nuna cewa tsafi wani ginshik’i ne da ke d’auke da rayuwar Maguzawa. Wato bai ke’banta ga bauta kawai ba.

 

2.0       TSAFI


Manazarta yanayin tunani da imanin Hausawa sun karkasa addinin gargajiya na Bahaushe zuwa gida uku (Ibrahim 1982, Bunza 1990 da 1995). Wad’annan kuwa, su ne Bori da Camfi da kuma Tsafi. Daga cikin wad’annan rassan, kusan a ce tsafi ya fi sauran jagorancin rayuwar Bamaguje. A ra’ayin Bunza (2006:35), tsafi na nufin bin wasu hanyoyi na gargajiya musamman yi wa iskoki hidima, da yanka, da bauta domin biyan wata bukata ko samun wani amfani ko tunkud’e wata cuta.

 

Nau’o’in tsafi ga Maguzawa ba su da iyaka musamman da yake iskokin da suke bauta wa sun bambanta. Kowane rukuni na Maguzawa da irin hanyoyin da suke bi wurin aiwatar da tsafe-tsafensu ta la’akari da abin da suka gada daga iyaye da kakanni ko tasirin wurin zama ko wata fahimta ta musamman.  A wajen bautar tsafe-tsaten Maguzawa ne iskokin da ake bauta wa suke bayar da lak’anin magungunan da za a harhad’a, a sarrafa don a sami biyan bukata. Wannan yakan zama wani abin sirri ga jagoran wannan tsafin ko mutanen gidan da ke aiwatar da tsafin. Ga sauran zuri’ar gida ko mabuk’ata, sai dai kawai a ba su magani a lokacin da buk’ata ta taso.

 


  •      TSAFE-TSAFEN DA SUKA SHAFI AURE
A rayuwa ta yau da kullum, samun ma’anar kalmar aure abu ne mai sauk’i ga duk mai hankali da aka tuntu’ba, ba masana kad’ai ba. Wannan ya kasance haka ne domin mu’amala da ake yi ta abin da kalmar ta k’unsa a kowace rana ko kowane lokaci. Ko da baligi bai sami kaiwa ga yin aure ba, to yana da makusanciyar alak’a da ita ko masu aiwatar da rayuwarta ko ma abin da take d’auke da shi. To amma a nazari irin wannan, akwai bukatar samar da abin da zai iya kar’buwa a ilmance. A tak’aice muna iya cewa, aure  hanya ce ta rayuwar da ake so ta zamo mai d’orewa tsakanin mace da namiji wadda ake ginawa ta hanyar shimfid’ad’d’un k’a’idoji da al’umma ta tanada wad’anda kan haifar da nishad’i tsakanin ma’auratan da taimakon juna da samar wa ’ya’yansu asali da kyakkyawan reno.

 

A al’adar Maguzawa, akwai matakai daban-daban da ake aiwatar da tsafe-tsafen da suka danganci aure tun daga neman aure har zaman auren. Wasu daga cikin su ana aiwatar da su ne saboda biyan bukatar rayuwa ko don a nuna buwaya ko don kariya ko kuma don a tabbatar da abin da al’ada ta tanadar wanda ya shafi kare zuri’a daga gur’bacewa.

 

3.1       Magungunan Tsafe- tsafen Farin Jini da Neman  Aure


Magani muhimmin abu ne a rayuwar d’an Adam. Rayuwa ba ta ta’ba gudana ba tare da magani ba (Abdullahi 2000). Idan ba a nemi magani don warkar da cuta ba, za a nema don kariya, ko cutarwa, ko kuma biyan bukatar rayuwa. Magungunan farin jini na neman aure sun fad’o a k’ark’ashin rukunin magungunan biyan bukatun rayuwa.

 

Hausawa na cewa, “Idan kana da kyau ka k’ara da wanka.” Maguzawa mutan ne da suka ba irin wannan magani na farin jini muhimmanci a rayuwarsu. Ko ba komai, sun yarda da akwai miyagun mutane ko mak’iya da ke sha’awar ganin rayuwar wani ta wulak’anta. Tsoron shiga tarkon irin wad’annan miyagu ko abokan hamayya yakan sa su samar wa ’ya’yansu maza da mata magungunan farin jini dangane da lamarin aure. Haka kuma, abin takaici ne musamman ga budurwa a al’umar Maguzawa ta wuce munzalin aure ba tare da ta samu mai sonta ba.

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/bamaguje-da-dan-akuya-kauna-ko-kiyayya/

Gano ainihin tushen magani ko mahad’in magani na mutane irin Maguzawa abu ne mai wuyar gaske, musamman da yake lamarin ya k’unshi sihiri da tsafe-tsafe iri-iri. Duk da haka an gano cewa, samari suna neman magungunan farin jinin ’yanmata ne daga tsoffi ko kakanninsu. Saurayin Bamaguje ba ya jin kunyar gaya wa kakansa labarin budurwar da yake so da k’alubalen da yake fuskanta na gwagwarmaya da sauran samari wajen nemanta. Maganin da samari suka fi yi na jan hankalin budurwa ko farin jini ya shafi yin hayak’i kafin a fita dandali.[i] Haka kuma wasu na shafa wani magani da aka had’a da mai a ce su yi k’ok’arin ta’ba budurwar da suke so da maganin. Da zarar an yi haka, ta so shi ke nan har abada. A wannan ranar ma tana iya bin shi su kwana tare.[ii] Wasu nau’o’in magungunan kuma garin magani ne za a kad’a cikin ruwa, saurayi ya wanke fuska da ruwan. Idan ya fita dandali shi ’yanmata za su yi ta sha’awa a wannan ranar har sai ya darje ya za’ba.

 

Su kuma ’yanmata sun fi samun irin nasu magungunan farin jini ne daga wurin iyayensu mata ko kakanni mata. A sakamakon ba lamarin muhimmanci da Maguzawa suka yi, tun yarinya tana goye ake sa mata maganin farin jini a cikin abinci ko abin sha, don kawai ta tashi samari suna son ta. Haka kuma idan iyaye mata da kakanni suka ga alamar sa’o’in budurwa suna ta fito da maza ita ba ta kawo kowa ba, to akan tashi tsaye wajen neman magani. Ire-iren wad’annan magungunan sukan shafi tsafe-tsafe ne na gargajiya wanda su ke bayar da sak’esak’i da sayyun da za a yi amfani da su. Maguzawa sukan yi wa budurwa hayak’i in za ta tafi dandali wurin wasa ko in za a halarci hidimar wani buki na k’awaye ko dangi. Idan wad’annan magunguna suka ci, to za a ga samari suna ta karakaina a kanta. Wani lokaci ma har da fad’ace-fad’ace, musamman a lokacin da wani daga cikinsu ya kasa sauran.

 

3.2       Karfa


Karfa a al’adar Maguzawa yana nufin yin magani ta hanyar tsafi don kowane iri don k’untata wa abokin hamayya a wurin neman aure. Samari sukan dad’e suna neman budurwa, sai lokaci d’aya wani ya zo ya kasa su. Idan irin haka ta kasance, ba kowa ke hak’ura ba. Dole akan d’an ratse ta yadda za a ‘bata lamarin. Sakamakon irin wad’annan magunguna sukan bambanta dangane da k’arfin tsafin da aka  yi amfani da shi wurin had’a maganin, ko kuma irin sakamakon da ake bukata. Wasu sai bayan an yi aure mace ta kasa zama gidan miji. Wasu kuma ko auren ba za a yi ba, matsaloli su shigo, a rabu baram-baram. Ga misali, Maguzawan Batsari (ta jihar Katsina) suna da wani nau’i na karfa wanda ake raba saurayi da budurwa in suna son junansu. Daga cikin samarinta wani yakan kasa yin hak’urin kasa shi da aka yi. Irin wannan karfa garin magani ne mabukaci zai tauna da jar kanwa, sai an zo dandali ya fesa wannan yawun maganin ga wanda ya kasa shi. Wannan saurayin da budurwar ke so (wanda aka fesa wa maganin) ba shi ba ita har abada. Ya rink’a ganin wulak’anci ke nan daga gare ta, da rashin k’auna har sai ya gaji ya nemi wata. Haka kuma idan budurwar ta yi wa wani wulak’anci saboda son wani saurayi na daban da take yi, to wannan saurayin da ta  yi wa wulak’anci yana iya fesa mata wannan magani, in ya kasa hak’uri. Ita da auren saurayi har abada. Sai dai ta sami wani tsoho ta aura don gudun kada ta mutu ba ta yi aure ba. Wato ba a sake samun wani saurayi da zai so ta, sai kuwa in an sami  lak’anin karya maganin.

 

Su kuma Maguzawan K’wank’i (a k’asar Bakori ta jihar Katsina)sai bayan an fara bukin aure suke fara yin nasu karfan. Duk da yake abu ne mai wuya su ambaci sirrin maganin nasu, an gano cewa bak’ar kaza mai rai ake d’aurewa cikin bak’in k’yalle a yi tsafin da ita a kai kan suri (gidan gara ko ji’ba) a ajiye. Ana kai amarya gidan miji, ta bar wannan gidan ke nan har abada, an bar ango da takaici. Idan shi ma namiji ne, ko tsafin gidansu ya fi na abokan hamayyar to ana k’ok’ari a karya maganin ko ma ya k’i ci.  Gudun cin karo da irin wad’annan mishkiloli shi kan sa Maguzawan Kainafara (da ke zaune a Birci ta k’asar Kurfi a jihar Katsina) suke yin nasu dabarun in za a kai amarya, kamar yadda za a gani nan gaba.

 

3.3       Tsafe-tsafen da Suka Danganci  Bukin Aure


Baya ga tsafe-tsafen da Maguzawa ke aiwatarwa don samar da soyayya ko kare ta, ko lalata ta a lokutan da ake aiwatar da ainihin bukin aure, akan sami wasu Maguzawan da suke gudanar da tsafe-tsafe don neman amincewar abin da ake bauta wa ko don tabbatar da d’iyaucin mace, ko magance matsalar wabi ko don a zaunar da amarya a cikin d’aki, da karya duk wasu tsafe-tsafe da abokan gaba suka yi.

 

A al’adar Maguzawan Kainafara, a  safiyar ranar  da za  a d’aura  aure,  za a kai bak’in d’an akuyar  da  iyayen  ango suka kawo cikin dutsen  ‘Dantalle a  garin  Birci inda a nan  ne tsafin nasu yake. Sarkin  noma (shugaban tsafin) zai yanka wa iskokin Kainafara wannan d’an akuyar  kafin a ci gaba da sauran al’adun d’aurin auren. Haka  ma  lokacin da aka zo da amarya k’ofar d’akinta aka sauko da ita daga kan god’iya, jama’a za su yi dafifi a k’ofar d’akin. Za a sami wani namiji a ba shi bak’ar kaza da jan zakaran ya rik’e a hannu. Zai kama hannun amarya su shiga d’akin tare. Sai su fito, su k’ara shiga, su fito. Sai sun yi haka har sau hud’u. Sai ya kewaya mata wad’annan kajin a kai. Idan ya k’are sai ya saki kajin. Daga nan sai ta shiga d’akin, sannan sauran jama’a su shiga d’akin. Wad’annan  Maguzawan sun yi imani da cewa, duk amaryar  da  aka yi wa haka, to ita da ango mutu ka raba.

 

Su kuma Maguzawan Kaibaki da ke k’asar Fago ta jihar Katsina, idan an k’are wankan amarya, za a fito a d’unguma tare da dangin ango zuwa wajen garin inda tsafin garin yake. Idan an isa za a yanka d’an akuya a babbaka shi a daddatsa. Wanda ke jagorancin wannan tsafin zai fara ci. Sai a ba sauran jama’a su ci. Daga can za a ji k’arar iskar wu-wu-wu-wu…. Da zarar an ji haka za a fara tafiya ana wak’a zuwa gida. A kan hanyar dawowa in aka zo daidai gidan da wata mace ta yi lalata tana da aure, ta haifi shege ba a sani ba, za a ga  tsafin ya kware mata rufin d’akinta kamar dai yadda guguwa ko iskar damana ke ‘barna, wato tsafin ya tona mata asiri ke nan.

 

Maguzawan Gidan Gwarzo (k’asar Matazu ta Jihar Katsina) daga wurin d’aurin auren dangin ango za su nufi wurin da tsafinsu yake tare da d’an akuya da zakara. Ana isa, babba a cikinsu ko wanda ke jagorancin tsafin zai hau k’ololuwar itacen tsamiya tare da zakara a hannunsa. Daga can saman itacen zai sa bakinsa ya tsinke kan zakaran, ya d’aure k’afafun a jikin wani reshen itacen tsamiyar, zakaran na reto, jinin na d’igowa. Ba zai sauko ba sai jinin ya gama d’iga.

 

Yana saukowa za a kamo d’an akuyar nan a yanka, a babbake shi da wutar da aka hura da kara. A nan ba a yarda a sa itace ba. Karan zai k’one ba tare da naman ya gasu sosai ba. Haka za a rarraba wa jama’a su ci naman. Sai a koma gida ko gidan amarya a ci gaba da shagali. Wannan shi ake kira rawar gunki. Haka kuma idan an zo d’aukar amarya bayan an fito da ita, (an ba da d’auka) za a yanka d’an akuya. Ga mak’unshiya, ga mawanki, sai a kira amaryar ta k’etare jinin sau uku. A na hud’un sai a turo ta. Daga cikin abokan ango wani zai d’auke ta ya d’ora kan god’iya a kama hanya. Naman d’an akuyar kuma za a raba wa dangin uwa da na uba su ci.

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/bamaguje-da-dan-akuya-kauna-ko-kiyayya/

3.4       Kai Bante


Kai bante a al’adar aure yana nufin amarya ta yi aure ba tare da wani namiji ya ta’ba tarawa da ita ba sai wannan mijin da ya fara aurenta. A Maguzance abin farin ciki ne ga ’ya mace da ma iyayenta a ga yarinya ta kai d’iyaucinta. Haka kuma, abin bak’in-ciki ne ga iyaye da dangi da ma ita kanta amarya a wayi gari ranar aurenta a gane cewa, ta ta’ba yin lalata. Wannan yakan rage kimarta da kimar iyayenta a idon jama’a.  Tsoron sakamakon irin wannan ranar kan sa ’ya’ya mata ba su ta’ba yarda su sadu da namiji sai fa bayan an yi aure. Akwai hanyoyi da dama da Maguzawa suke amfani da shi wajen gano d’iyaucin mace a daidai lokacin da ake bukin aurenta kafin a kai d’akin miji.

 

Ga misali, Maguzawan Kaibaki an nuna cewa, kafin a ba da d’aukar amarya akan tafi wurin tsafin garin a yanka d’an akuya a babbake, a ba mutane su ci. A wannan lokacin ne tsafin ke yin wani kuka wu-wu-wu… Wad’annan Maguzawa sun nuna cewa, wannan kuka da tsafin yake yi kamar alama  ce ta nuna ya yarda da wannan aure kuma amaryar ta kai bante, watau ba ta ta’ba yin lalata da namiji ba. Idan har tsafin ya k’i yin kuka to ba ta kai bante ke nan ba. Wannan na iya zama sanadiyyar mutuwarta. Ga amaryar da ta san ta ta’ba sanin d’a namiji, za ta yi k’ok’arin gaya wa iyayenta. Su kuma su yi ta ’yan dabaru a k’i zuwa wurin tsafin. Sai dai kawai a ba da d’aukan amarya. Da zarar an ga haka sai a fara tsegumi, a gane cewa, amaryar ba ta kai bante ba.

 

Su kuma Maguzawan K’wank’i, d’an akuya ake yankawa a daidai k’ofar gidan bayan an k’are wankan amarya an fito da ita. Baya ga wannan jini na d’an akuyar, za  a gitta ta’barya, amaryar ta zo ta k’etare sau uku. Idan har ba ta ta’ba sanin namiji ba, to ba abin da zai same ta. Sai a d’auke ta a d’ora kan doki ana ta murnar ta kai bante. Idan kuwa ta ta’ba sanin namiji, kuma ta k’etare wannan ta’baryar da jinin d’an akuyar, to za ta fad’i a nan. In ma ba ta yi sa’a ba yana iya zama ajalinta. Gudun haka kan sa su ma iyeye su yi ta ’yan dabaru a k’i yin duk wasu al’adu, a fito da amarya ta wata k’ofar a ba da d’auka. Da an ga haka an san abin da ya faru ke nan, sai bukin ya rage armashi.

 

A al’adar Maguzawan Gidan Bakwai (k’asar Faskari), idan za a kai amarya dangin amarya sukan yi sihirce-sihircensu na kiran tsafin da suke bauta wa. Sun nuna cewa, idan dangin amaryar ’yan Magiro ne sukan kira shi ya yi wa amarya rakiya. Za a rik’a jin k’uginsa a lokacin da ake tafiya kai amarya. Idan aka kira shi ya k’i zuwa to, wannan ya nuna amarya ba ta kai d’iyaucinta ba. Wannan shi kowace uwa, da ’ya mace ke gudu a lamarin aure. Wato ya ishe su abin kunya a al’umma. Ya ishi uwa da ’ya abin gori idan ana magana. Da zarar haka ta faru za a ga ba su yawan shiga jama’a ana hira, gudun kada su sami sa’bani da wani ya yi musu gori.

 

A wasu al’ummu na Maguzawa, al’adar kai bante ba ta tsaya ga ‘ya mace kawai ba. Wato har da ango akan yi tsafin da ke nuna cewa ya ta’ba saduwa da ‘ya mace kafin aure ko bai ta’ba ba.  Misali a al’adar Maguzawan Gidan Gwarzo, a ranar da aka d’aura aure bayan an dawo gida da dare, idan tsafin Bagiro iyayen angon suke bauta wa, za a ji tsafin yana kuka a bayan gida. Wannan kuka alama ce da ke nuna tsafin ya amince da auren. In kuwa har gari ya waye ba a ji kukan tsafin ba, to angon ya ta’ba yin lalata da mace. Daga nan zumunci ya yanke tsakaninsa da abokansa. Haka kuma ba za a ci gaba da sauran hidimomin auren ba, ya rasa wannan matar ke nan sai dai a ba wani. Don tsananin kasancewar wannan abin kunya,  hakan na iya sa ya bar wannan garin ko k’auyen har abada. Idan kuma mace aka gano ta ta’ba sanin d’a namiji, to sai dai a ba wani tsoho ita ya yi hak’uri amma ba dai ta auri saurayi ba.

 

4.0       AL’ADUN TSAFI A HAIHUWAR MAGUZAWA


Haihuwa dai k’aruwa ce ta hanyar fitowar wani abu mai rai daga jikin wata halitta jinsin mace. Wannan abu yakan ‘boyu a wani wuri na musamman na wani k’ayyadadden lokaci don samun kamanni ko siffa kwatankwacin na zuriyarsu, wanda ke aukuwa a sakamakon saduwa da jinsin namiji na wannan halittar.

 

A fasalin da ya gabata an dubi tasirin da ke ga tsafe-tsafen Maguzawa a sha’anin su na aure. Wannan lamari bai tsaya ga aure kawai ba. Akwai wasu ’yan tanade-tanade da suka yi dangane da haihuwa. Maguzawan da suka yi fice wurin gudanar da irin wad’annan al’adun su ne Maguzawan Kainafara.

 

4.1       ‘Bacewar Jinjiri


Idan mace tana da ciki, aka ga alamar cikin nan ya kusa kai wata tara, za a ja kunnenta da cewa, da zarar ta haihu kada ta kuskura ta gaya wa kowa, in kuwa ta bari mutane suka sani,  za ta mutu. A al’adarsu, mace tana haihuwa ne ita kad’ai a d’aki. Ana cin nasarar haka ne saboda yawan magungunan da ake sha na sauk’in gwiwa. Duk da haka a wasu lokuta akan ci karo da matsalolin da za su sa a nemi taimakon wasu na kusa, ko su ma a asirce. Su ma d’in da zarar an sauka lafiya za su kulle bakinsu. Ana haihuwar, wannan jinjirin zai ‘bace. Ba za a sake ganin shi ba sai bayan makonni biyu cur. Za a wayi gari a gan shi cikin d’akin. A wani ra’ayin kuma, za a dawo da shi ne a daren rana ta sha bakwai da haihuwar. Akan ba mai jegon maganin firgita. In ba haka ba sai ta ta’bu ko ma ta haukace saboda tsoron ‘bacewar jinjirin. Maguzawan sun yarda da cewa, Iskokinsu ne ke d’auke yaron su rik’e a wurinsu don ladabtar da shi na tsawon  wad’annan kwanakin.

 

4.2       Tabbatar da Iyayen Jinjiri


A ranar da jinjirin zai dawo, ranar za a yi suna. A wannan ranar kuma za a yi al’adar tsafin da zai tabbatar da cewa, wannan jinjirin Kainafara ne. Idan ba Kainafara ba ne, wato uwarsa ta tara da wani can daban to ranar zai mutu. Abin da ake yi shi ne, za a sami kundon karan dawa (ga’ban kara) a koma gabas da d’akin da yaron yake ciki. Sai a d’aga jinkar d’akin daga waje da karan nan, a tokare da k’asa ta yadda za a sami k’ofa tsakanin ginin d’akin da jinkar dakin. Sai wani ya shiga cikin d’akin, wani ya tsaya waje daidai inda aka tokare jinkar. Sai na cikin ya d’auki jinjirin ya mik’o wa na waje ta wannan kafar. Bayan ya kar’ba zai mayar da shi ta wannan kafar ga wanda ke cikin d’akin. Za su yi haka har sau hud’u. Idan wannan jinjiri ba nasu ba ne, ko kuma uwar ta bi maza ta sami cikin, wato ba na mijinta ba ne, to da an mik’o jinjirin, karan nan zai goce ko ya karye, jinkar ta fad’o ta danne jinjirin da jikin gini ya mutu. Idan kuwa jinjirin jinin Kainafara ne, to wannan kara ba zai goce ko ya kare ba.

 

4.3       Tsagar Gado


A wata al’adar mai dangantaka da tsafi ga su wad’annan Maguzawa na Kainafara, ba a tsaga su. Idan aka kuskura ana yi wa jinjirin Kainafara tsaga ko da cikin rashin sani ne, to wannan wanzami zai mutu. Haka shi ma jinjirin zai mutu. Idan ma ba a yi sa’a ba, hatta da uwar d’an za ta bar duniya saboda sakacinta na barin a tsaga jinjirin Kainafara. A fahimtarsu, Iskokinsu ba su amince a tsaga musu shi ba.

 

 

5.0       NA’DEWA


A wannan nazarin, an waiwayi wasu abubuwa da suka danganci tsafi a al’umar Maguzawa. Wad’annan tsafe-tsafe sun shafi aure da haihuwa kawai. Tunanin da aka yi a baya, shi ne, ba a sa ran rayuwar Maguzawa kacokan ta karkata ga tsafi har a harkokin da suke da alak’a da jin dad’i ko k’aruwa ko annashuwa kamar na aure da haihuwa. To da yake an kwatanta dangantakar Maguzawa da tsafi da irin alakar da ke tsakanin tsoka da jini, sai ga shi nazarin ya tabbatar da kusan kowane sha’ani na aure da haihuwa tsafin ya kutsa a ciki. Mun ga yadda tsafi ya yi tasiri a harkar aure kamar a wujen gwagwarmayar neman aure da na tabbatar da d’iyaucin amarya da dai makamantan su. Haka ma a sha’anin haihuwa, nazarin ya gano hanyoyin da Maguzawa ke amfani da su wajen tabbatar da halaccin ’ya’yansu da gabatar da jinjiri ga Iskoki ta hanyar tsafi na wasu kwanaki bayan haihuwa. Don haka, ba zai zama wani abin gardama ba idan aka ce tsafi shi ke jagorancin rayuwar Maguzawa.

6.0       MANAZARTA


Abdullahi, I. S.S. (2000) “Magani Da Siddabaru Cikin Rubutattun  K’agaggun Labarun Hausa.” Sakkwato, Kundin digiri na  biyu, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo.

 

Abdullahi, I. S. S. 2008, ”Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan

Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa.” Sakkwato, Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa Culture) Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

 

Abu, M. (1985) “Al’adun Aure da Canje-canjensu a Katsina” Sakkwato. Kundin Digirin farko,  Jami’ar Sakkwato.

 

Adamu,  M. T. (1997) Asalin Hausawa da Harshensu, Kano, ‘Dan Sarkin Kura Publishers.

 

Alhassan, H. da Sauransu (1982), Zaman Hausawa

 

Bunza,  A. M.  (1995) “Magungunan Hausa a Rubuce:  (Nanzari Ayyukan Malaman Tsibbu),” Kano, Kundin digiri na uku,  Jami’ar Bayero.

 

Bunza, A. M. (2006) Gadon Fed’e Al’ada, Lagos  Tiwal Nig. Ltd.

 

Bunza, A.M. (1990), “Hayak’i Fid Da Na Kogo: (Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa)”, Kano, Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayero.

 

Charanchi, R. (1999), Katsina Dakin Kara: Tarihin Katsina Da Garuruwanta, Zariya, Northern Nigerian Publishing Company Limited.

 

Elias, T. O. (1957) “Hausa Marriage” In Nigeria , A Quarterly Magazine  of General  Interest No 53, Marina, Lagos, published by the  Federal Government of Nigeria, Exhibition Centre.

 

Gwarjo, Y. T. da  wasu  (2005)  Aure a Jihar Katsina Hukumar BincikenTarihi Da Kyautata Al’adu ta Jihar Katsina,

 

Ibrahim, M. S. (1982), “Dangantakar Al’adu da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa”, Kano, Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Bayero.

 

Ibrahim, M. S. (1985), Auren Hausawa: Gargajiya Da Musulunci, Zaria Cyclostyled Edition – Hausa Publications Centre.

 

Kado, A. A. (1987), “Kainafara Arnan Birchi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Sakkwato.

 

Safana, Y.B. (2001), “Maguzawan Lezumawa (Babban Kada) Gundumar Safana”, Sakkwato, Kundin Digiri na farko, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.[i] Don k'arin bayani a kan yadda ake sarrafa magani ta hanyar haya}i, dubi kundin Aliyu  Muhammad

Bunza na digiri na biyu  mai  take, “Haya}i Fid Da Na Kogo: (Nazarin  Siddabaru da Sihirin Hausawa)

Jami’ar  Bayero, Kano, 1995, shafi na 144.

 

[ii] A nan kwana tare ba yana nufin ya yi lalata da ita ba. Wannan al’ada da ake kira Tsarance ita ke tabbatar da cewa, budurwa tana son saurayin.