Header Ads Widget

Request to place your ads here.

Kanu

6/random/ticker-posts

Najasa A Mahad’in Maganin Iska

Amsoshi

Yakubu Aliyu Gobir


Department of Nigerian Languages


Usmanu Danfodiyo University, Sokoto


yagobir@yahoo.co.uk


08035605024
Gabatarwa


Nazarin hikimomin al’adun Hausawa da harshensu a kullum k’ara bunk’asa yake yi.  Lamarin iskoki abu ne da ya mamaye al’adun Bahaushe a rayuwarsa. Bahaushe na ganin iskoki wasu halittu ne masu k’ima da daraja ta musamman, da jin cewa suna iya cuta masa a rayuwa. A tunaninsa, cutukan da iskoki ke haddasawa su ne manyan cutuka, domin suna nak’asa rayuwa kuma suna da wuyar magani. Duk da samun wayewar kai da bunk’asar kimiyyar zamani, Bahaushe bai yarda akwai maganin iskoki a asibitocin nasara ba, ya fi son ya tunkari matsalar a Bahaushiyar al’ada. Najasa na d’aya daga cikin hanyoyin al’ada da Bahaushe ke bi wajen warkar da cutar iskoki. Nazarin yadda Bahaushe ke amfani da najasa wajen sarrafa maganin iska shi ne mak’asudin wannan muk’alar.

2.0 Ma’anar Magani


A k’ark’ashin kiwon lafiya, kalmar magani sananniya ce ga kowane Bahaushe. Wasu masana, sun yi hasashen cewa, kalmar ba ta rasa nasaba da kalmar ‘gwaji, wato a gwada abu a ga ko zai yi. Suna ganin kalmar ‘hatsin bara’ ce, wato had’e-had’en kalmomi ne na Hausa suka samar da ita. Kalmomin su ne: “ma” da “yi” da kalmar “gani”.  Idan Bahaushe ya sami wata cuta ko rashin lafiyar da yake son kawar wa, sai ya sami ’yan ganyeyyikinsa da saiwowi ya harhad’a ya ce: “Ma gwada wannan mu gani”, har dai kalmar ta koma: “ma yi wannan mu gani”. Daga baya ta koma, “ma yi ma gani”, har ya zuwa kalmar ta koma: “magani”, ma’ana, bari mu yi ma gani (Bunza:135).

Dangane da k’unshiyar ma’anar kalmar magani, masana da d’aliban nazarin al’adun Hausawa sun sha d’auki-ba-dad’i kan hak’ik’anin gano ma’anarta. Da farko ga yadda K’amusun Hausa na Jami’ar Bayero Kano (2006) ya fassara ta:

 • Abin da ake sha ko shafawa a jiki ko d’urawa a jini ta hanyar yin allura, don neman samun lafiya.

 • Abin da samuwarsa kan kore wani daban, misali, tarko yana maganin ‘beraye.

 • Sammu, wato harhad’a wasu abubuwa da yin surkulle da nufin cutar da wani, musamman abokin gaba.

 • Harhad’awa ko yin wasu abubuwa na musamman don shawo kan wani, ko samun galaba a kan wani abu.


Dangane da hasashen masana kuwa, Ahmad, (1984), yana cewa:

Magani shi ne duk wani abu, da za a yi, ko wata hanya, ko kuma wata dabara da ake yi don gusar da cuta daga jikin mutum d’ungurungum ko kawo kwantar da ita don kawo jin, dad’i ko ga zuciya da sauk’ak’e duk wahala da damuwa da ita cutar kan iya haifarwa.

Musa (1986), yana  cewa:-

Magani wata hanya ce kawai ta neman biyan buk’atar wata matsala da ke damun mutum, ko kuma yana ganin matsalar tana yi masa barazana.

Zulai (1984), cewa ta yi:-

Magani hanya ce ta neman kawar, da cuta kowace iri ko kuma neman kariya daga gare ta ko kuma neman gwanewa ko k’warewa kan wani abu.

Alhassan da wasu (1982), sun ba da tasu ma’anar maganin gargajiya, suna cewa:

Maganin gargajiya shi ne yin amfani da itatuwa ko rubutu ko addu’a ko surkulle don warkar da wata cuta ko neman wani amfani ko gusar da sharri ko haddasa wani abu saboda biyan bukata. [i]

 

Bunza, 1995 ya bayar da ma’anar magani kamar haka:

Magani wata hanya ce ta warkarwa ko kwantar da, ko rage wata cuta ta ciki ko ta waje ko wadda aka samu, daga had’ari; ko kuma neman kariya ga cutar abokan hamayya ko cutar da su, ko neman d’aukaka, da daraja ta hanyar ‘yan siddabaru, da sihiri na ban al’ajabi.

Duk wad’annan masana, kowanensu ya yi k’ok’arin fito da nasa ra’ayi a kan ma’anar magani. Wannan ya nuna cewa, ‘magani’ kalma ce mai iya d’aukar ma’ana mai fad’i, wadda kan sa dole a yi taka-tsantsan wajen bayar da bakandamiyar ma’anarta. Duk da haka, daga abin da aka kalato daga bakin masana ana iya cewa magani wata hanya ce ta kawar da, ko kwantar da, duk wata cuta ta jiki ko ta zuciya, ko neman d’aukaka, ko kariya daga makaru da jifa da sihiri ko siddabaru.

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/kacici-kacici-rumbun-fikira/

3.0 Ma’anar Najasa


Kalmar ‘najasa’ ba Bahaushiya ba ce, aro ta Hausawa suka yi daga Larabci. A luggar Larabci najasa na nufin………Ma’anarta a Larabci ta yi canjaras da ta Hausa, saboda dukkaninsu a muhalli  iri d’aya ne suke amfani da ita. Duk da haka, a K’amusun Hausa, an ba ta ma’anar:

K’azanta mai tauri-tauri ko ruwa-ruwa ga wari wadda mutum kan fitar ta duburarsa.

Har  ila yau, K’amusun ya kuma kawo kalmomin najasa na Hausa kamar haka: ‘kashi’ da ‘ratsi’ da ‘ba-haya’ da ‘tutu’ da ‘taroso’ da ‘gayad’i’ da ‘artai’.

Idan aka nazarci wannan ma’anar najasa da K’amusun Hausa ya bayar, za a fahimci cewa, abubuwan da Bahaushe ke kira najasa sun wuce abin da ke fita ta dubura kawai. A fahintata, duk abin da ya fito ta dubura da ta al’aura da duk wani ru’ba’b’ben abinci mai wari ko abin sha, ko jini ko mushe ko wani sashe na jikin mushe, da duk wani nau’in k’azanta, ko k’asar wurin najasa, ana kiransu najasa.  Kalmar ‘k’azanta’ tana da kusancin ma’ana da ‘najasa’, amma najasa ta fi samun kar’buwa ga masana addini, musamman a zaure ko soro wajen karatun furu’a. Saboda haka, tasirin addini da zamani sun taimaka k’warai wajen d’aure wa kalmar najasa gindi da samun kar’buwa, saboda ma’anarta ta fi fad’i kuma ta fi sakayawa.

 

 

4.0 Mazaunin Iska:


Wuraren najasa na d’aya daga cikin manyan mazaunan iskoki. Wad’annan  wuraren su ne  kamar haka:

 1. Bola ko juji: Bola shi ne wurin zuba shara da tarkacen k’azanta, kamar sauran abinci da k’assan da aka gurgure aka yar a bola. Idan kuma rame ne aka hak’a don zuba shara ya zama birbizo. Iskoki suna zama irin wannan wurin ko ramen, saboda suna cin sauran abincin da bani Adam suka ci da k’asusuwan da suka tsotse suka zubar a bola.

 2. Wuraren bahaya: A nan ana nufin wurare na musamman da aka killace ko filin wajen gari wanda ba a killace ba, don kewayawa a biya bukata, kamar masai ko shadda ko bayan gida. Iskoki musamman nau’in bak’ak’e ko kafirai, masu tsananin cutarwa, suna sha’awar zama wuraren bahaya, saboda shak’ar warin wannan k’azantar ko najasar. • Mayanka ko mahauta: Mayanka ita ce wurin da ake yanka dabbobi kamar shanu da awaki da tumaki da sauransu. Irin wannan wuri ba a raba shi da iskoki saboda akwai manyan nau’o’in abincinsu iri biyu a wurin, wato jini da k’ashi. 1. Wuraren wanke-wanke: A nan ana nufin wuraren da ake wanke kwanonin abinci ana samun ’yan gutsattsarin abinci da k’ananan k’assa da sauransu, ruwan wanke-wanken suna taruwa su zama kwata ko kwatami. Iskoki suna sha’awar zama wurin don k’azantar da ke wurin da kuma tunanin samun na-baka.

 2. Majema: Shi ne wurin da ake jeme fata ana fitar da gashin jikinta. Kamar yadda muka sani wuri ne mai mugun wari. Shi ya sa Bahaushe ke ce wa a karin maganarsa: ……………………………. Iska kan zauna irin wannan wuri saboda wannan dagwalon wurin mai wari da ke wurin.


Daga cikin aljannu wad’anda suka fi zama  wauraren  k’azanta su ne, kafiran  aljannu, kamar  yadda  Wahid Baliy  ya ce, ya tambayi  wani  aljani  Musulmi, ko yana  zama a  makewayi?  Sai  aljanin  ya ce,  “a'a”, sai  ya ce  masa, amma an ruwaito cewa,  kuna  zama  a  wuraren  najasa: sai  ya ce,  “I,  amma  wannan  ya  ke’banta  ga  kafiran  aljannu,  domin  su  sun  fi  son   wuraren  k’azanta.”[ii]

 

5.0 Mahad’i Da Najasa :


A fagen ilimin magungunan gargajiya, sinadari ko mahad’i na nufin harhad’a itace da wasu albarkatun k’asa ko sama, ko had’a wani ganye da wani ko wata saiwa da wata ko gamingambizar tsirrai da itace da k’waro da wasu abubuwa, don yin magani (Bunza 2004). Saboda haka, mahad’an magungunan Iskoki na nufin tarsashin abubuwan da za a tanadar, na daga itace da tsirrai da makamantansu, da lokacin da za a nemo su, da had’a su, da yanayin had’a su. Bahaushe yana mahad’i da najasa a wajen magungunan  da zai warkar da cutar iskoki ko wad’anda zai nemi taimakonsu don su cutar ko don biyan wata bukata, saboda a kimiyyarsa, ya fahimci suna da sha’awar lazimtar wuraren najasa. Bisa ga haka, akan samu najasa a mahad’in  dukkanin rukunnan magunguna, amma an fi samunta a rukunnan magungunan warkarwa ko na cutarwa, kamar haka:

 

5.1 Magungunan Warkarwa:


Magungunan warkarwa su ne wad’anda ake amfani das u don warkar da cutar iska ga jiki ko zuciya. Misali:

 • Cutar ta’bin hankali, ana had’a sassak’en itacen jirga da d’od’d’oya da kashin tunku da tsabre, a dake su a turara wa mai cutar, zai warke da yardar Allah.

 • Idan farfad’iya ce, ana yin turare ta hanyar had’a: kashin tunku, da kashin bak’in jaki, da kan tsabre, da bunsurun fadama, da bunsurun doguwa, da hankufa, da kimbar maharba, da kwalfar jigo, da kitsen bak’in sa, da kitsen bak’ar akuya. Za a dake su wuri d’aya ana yin turare da garin, kullum, safe da yamma, zai warke da yardar Allah.[iii]

 • Akan yi mahad’i da fitsarin rak’umi a shak’a wa mai cutar iska ko k’asar wurin kwanciyarsa, don magance cutar iska.

 • Akan turara kashin kaji ga mai cutar farfad’iya don ta sake shi nan take.

 • Akan yi turare da k’ashi don kama gawurtaccen macijin da ake jin iska ne ko iska ya shige shi.

 • Akan yi turare da matattar ja’ba don k’one iskan da ya k’i fita ga jikin d’an Adam.[iv]


5.2 Magungunan Cutarwa:


Magungunan cutarwa su ne (Bunza 1995) ya kira su magungunan sharri. Mafi yawan magungunan cutarwa sai an had’a da iskoki, wato a neman taimakonsu ta amfani ko mahad’in najasa don cutar da rayuwar wani mutum. Ga abin da (Bunza, 1995) ke cewa:

Mafi yawan magungunan da za a had’a da najasa miyagun magunguna ne na sharri. Abubuwan da aka fi yin mahad’ar magani da su na najasa, sun had’a da maniyi, da jini mai feshi, da maziyyi, ko wadiyyi, da fitsari, da kashi, da mushe, da dai sauransu.

Haka kuma, falsafar Bahaushe ta yin mahad’i da najasa ga neman taimakon aljani ko iska ita ce don ya yi wa iska abin da yake so, shi kuma ya biya masa bukatarsa ta cutar da wani. Misali:

 • Ana mahad’i da wani kifi mai suna gawo da wutsiyar kurege don kashe zakarin namiji. Mushen dabba ko sassanta duk najasa ne. Idan aka yi mahad’i da sassan jiki ko makamantansu, a matsayin mahad’in magani, to a fahimtar Bahaushe, an yi tsafi ko sihiri, wato an nemi taimakon iskoki ke nan.


 

 • Ana mahad’i da salintar maciji da kashin ungulu don raba mata da mijinta.

 • Ana mahad’i da matattar kul’ba da yatsun d’an Adam don kuturta wani, da sauransu.

 • Akan yi mahad’i da gashin kan mutum wanda aka aske don a yi masa makaru.

 • Idan malama tsibbu suna son su haukata mutum za su samo icen da tsawa ta fad’a wa, da k’wai wanda ya lalace (ya zama dunge). Za a rubuta sunan wanda ake son a haukata a icen da jikin k’wan, a sanya shi cikin garwashin da babu hayak’i a gare shi, a karanta Fatiha k’afa d’ari uku da tamanin da takwas. Ga hatimin da za had’a da shi. Da an k’are aikin mutumin zai kuwwata, ya dinga cin najasa (Bunza, 1995).

 • Bahaushe na cewa, hannu musamman yatsu dahi gare su saboda amfani da ake da su wajen fitar da najasa ga jiki da yawan saduwarsa da yawun d’an Adam. Bahaushe na ganin idan ana shafar k’urji da hannu zai dad’a rurewa. Duk wata cuta ta jiki idan aka sa hannu tsiraransa za ta d’ara ha’baka. Haka kuma, yana ganin, idan aka doki yaro da hannu, ko aka doki wata dabba da hannu. Idan aka ga alamar suma rayuwa na son ta yi halinta, a umurci wanda ya yi dukan da ya hura hannayensa a tafin hannunsa da yatsu cutar ba za ta halaka abin da aka doka ba (Bunza, 1995).

 • A cikin camfin Bahaushe akwai cewar idan mutum ya shafa kwantsar jaki ko ta doki ga idonsa zai ga aljani amma zai mutu.


Wad’annan su ne kad’an daga cikin misalai na mahad’i da najasa wajen maganin cutar iskoki ko neman taimakonsu ga cutarwa.

Har ila yau, daga cikin abin da ke tabbatar mana cewa akwai alak’a tsakanin najasa da iskoki, shi ne kula da siffa ko yanayin da mahaukaci ko mai ta’bin hankali yake ciki na zama cikin k’azanta da daud’a da wari da ragga/tsumma. Idan yana tsare ko sake duk cikin wannan siffar yake. Hausawa kan ce, ‘abin ba dad’i, wai mahaukaci ya ci kashi.’

https://www.amsoshi.com/2017/11/06/aladar-rokon-ruwa-a-kasar-gobir-daga-riwayar-bakandamiyar-malam-muhammad-umar-kwaren-gamba/

 

6.0   Masu Bayar da Maganin Iska


Masu bayar da magungunan iskoki a al’ummar Hausawa suna da yawa, wasu ma ba a ko san da su ba, sai buk’atar bayar da maganin ta taso, da yake ba su mayar da abin sana’a ba. Sanannu kuma shahararrun masu bayar da magungunan iskoki, kuma wad’anda suka rik’i bayar da maganin a matsayin sana’a, sun had’a da:

 1. Bokaye


Magabata kuma masana al’adun Hausawa sun tattauna a kan boka da yanayinsa[v]. Gabanin bayyanar addinin Musulunci a k’asar Hausa, bokaye su ke cin karensu ba babbaka wajen warkar da cuta ta jiki da ta k’wak’walwa da buk’atocin jama’a. Haka kuma, su ne masu kulawa da huld’a tsakanin mutane da iskoki. Haka kuma, bokaye suna yin amfani da iskoki wajen tsafe-tsafen sharri, kamar halbin kasko ko kurciya ko kashe rayuwa gaba d’aya.

 

 1. ’Yan bori


’Yan bori suna cikin nau’i na bokaye a k’asar Hausa, domin duk wani k’asurgumin boka daga bori ya fara. ’Yan bori su suka fi huld’a da iskoki, musamman miyagu masu haddasa ciwon hauka, da sauran rashin lafiya. Hanyoyin bayar da magungunansu su ne ta fuskar wasan bori, da girka. Ga abin da Shata ke cewa a kan d’an bori cikin wad’ar Sarkin Bori Sule:

                        Jagora           :           :Yau wannan zamani,

:Wannan lokaci,

:Kowa yake zazza’bi,

:Ka ga ana gai da shi,

:Yana amsawa jifa-jifa,

:Ku zo gun mai bori Sule!

:(Yanzu) sai ka ga ya warware,

:Yana yawon duniya.

 

Amshi            :           :Sarkin Bori Sule

           Gindin Wak’a:        :Sarkin Bori Sule

:Na Kande Uban-

:’Yan boru Sule

 

 1. Malaman Tsibbu


Ayyukan Malaman tsibbu sun gabata a cikin littattafan magabata (Grenbergh: 1946, ’Yan d’aki: 1990, Bunza:1995). Malamin tsibbu shi ne kishiyar boka, don shi ya fara dushe hasken boka da d’aukakarsa a cikin al’umma. Malamin tsibbu, yakan yi amfani da iskoki ko rafanai wajen aikata magungunan sharri ko halakar da wani. Shi ya sa ake yi masa kirari da cewa:

Kigo mai Rangwangwan,

Yini karatu, kwana salla.

 

 1. Masu Ruk’iyya


Malamin ruk’iyya wani nau’in malami ne daga cikin malaman Musulunci da ke ba da magungunan cutukan iskoki ta hanyar karanta ayoyin Alk’ur’ani cikin kunnen maras lafiya. A k’asar Hausa, goshin k’arni na ashirin da d’aya ne, aka samu bayyana da shaharar Ruk’iyya, saboda samun wad’anda suka rik’e ta a matsayin sana’a. A halin yanzu, a k’asar Hausa da mak’wabtanta, babu wad’anda kasuwarsu ke ci gadan-gadan, daga cikin masu ba da maganin Iskoki, kamar masu ruk’iyya. Wannan shi ya kawo ha’bakar ruk’iyya, aka samu tasirin zamananci a wajen gudanar da ita. Suna kafa Santoci masu kama da asibitocin zamani a wurare daban-daban cikin garuruwan k’asar Hausa. Wannan nazarin ya gano santoci fiye da 30 a garuruwan Sakkwato da Kabi da Gusau da Katsina da Zariya da Kano da Kaduna, inda marasa lafiyar iskoki ke tururuwa wajen amsar magani da yi musu ruk’iyya. Haka kuma, Santocin sun zama wata hanya ta samar da harkar yi da bunk’asa tattalin arziki, musamman ganin yadda masu Santocin ke ta bud’e rassan Santocin, da kuma yadda suke tafiyar da harkokin rayuwarsu.

 

 

 

 1. Masu Sana’o’in Gargajiya


Bayan shahararrun masu bayar da magungunan iskoki da aka yi bayaninsu, akwai kuma sarakuna ko shugabannin wasu sana’o’i na gargajiya. Sana’o’in gargajiya su ne wad’anda aka gada kaka da kakanni. Bayan gudanar da sana’ar, suna kuma taimakawa da magungunan cutukan da suka shafi sana’ar, da na iskoki. Kamar yadda bayani ya gabata, daga cikin dalilan huld’ar Hausawa da iskoki akwai: don kare martabar gida ko sana’a. A k’ok’arin kare martabar sana’a, da neman kariya daga wani mai k’yashin sana’ar, ko nuna wata waibuwa da gwaninta, sai a nemi abota ko huld’a da iskoki kai tsaye ko ta hanyar bokaye ko shugabannin tsafin gari. Wannan shi ya haifar da, da wuya a samu wata dad’ad’d’iyar sana’ar gargajiyar da masu ita ba su gadi iskokin ko tsafin kare martabar sana’ar ba. Kodayake a halin yanzu, an fara samun jikokin ire-iren wad’annan gidajen, sun fara watsi da ire-iren wad’annan kayan gadon, saboda tasirin Musulunci a rayuwarsu. Daga cikin shugabannin sana’o’in gargajiya masu ba da magungunan cutukan iskoki akwai:

 • Ma’aska/Wanzamai: Su ne wad’anda ke yin aski da kaciya da tsagar gado a fuska ko ta ciwo a jiki. Wanzamai suna da alak’a da iskoki, saboda suna tu’ammali da jini, d’aya daga cikin abincin iskoki. Bayan magungunan da suke bayarwa wad’anda suka danganci cutukan da suka shafi sana’arsu, Wanzamai sukan bayar da maganin cutukan iskoki, kamar matsalolin jinin al’ada ga mata ko karya sihirin d’an baka da sihirin kashe zakarin namiji, da maganin maye, da sauransu.

 • Masunta: Su ne masu sana’ar su (kamun kifi). Kabawa suna kiran su Sarkawa, wato daga sunan wata k’abila da ake kira ‘Soroko’ a k’asar Mali, tsohuwar daular Songhai. Soroko su suka kawo wa Kabawa sana’ar kamun kifi. Masunta Suna da alak’a da iskokin Ruwa, saboda yawan shiga ruwa da suke yi. Bayan magungunan da suke bayarwa na sanyin ruwa da sauransu, suna kuma ba da maganin cutukan iskokin ruwa, kamar su makwakkwafa, wato yawan shan ruwa amma ba su kau da matsalar k’ishirwa ba. Sukan kuma karya duk wani makaru da aka yi aka jefa ruwa, da sauransu. Sukan kuma yi ’yan tsafe-tsafensu da iskoki don nuna gwaninta da waibuwa, kamar siddabarun fito da k’aya a jikin mutum, da dabon kifi a ruwa da kuma sihirin rage zurfin ruwa, ko taka saman ruwan gulbi suna tafiya kamar suna taka k’asa, da kiran dabbar ruwa ta fito ta kwanta a gaban wanda ya kira ta da kamun kifi bisa fak’o da sauransu. Fulani Jogwadawa su suka fi shahara da wannan tsafi.[vi]

 • Mahauta: Su ne ake kira Runji a Sakkwato, wato masu sana’ar yanke dabba da sayar da namanta. Suna da alak’a da iskoki saboda tu’ammali da abincin iskoki, wato jini da k’asusuwan dabbobin da suke yankawa. Sukan siddabaru a wajen wasan hawan k’aho. Haka kuma, mafi yawan ’yan dambe rundawa ne. ’Yan dambe suna cikin rukunin Hausawa da suka yi suna wajen amfani da iskoki wajen tsafe-tsafensu na neman galaba ga abokin wasa.

 • Maharba: Su ne masu sana’ar harbi ko farautar namun daji, wato dabbobin da ke rayuwa a dawa ko daji. Suna mu’amala da iskokin dawa, saboda koyaushe suna cikin daji, dare da rana. Maharba sukan ba da maganin ta’bin iskokin dawa irin su ‘Dan tsatsumbe da ‘Dan dagizge, da iskokin Tsamiya da Kuka da sauransu. Suna kuma ba da maganin ciwon daji da na halbin kasko, da ciwon tsuntsu (k’yan-k’yan), ciwo ne da kan kama yara a ga suna firgita kamar suna jin sanyi. Haka kuma suna tsafe-tsafe wajen kama dabbobin daji, kamar tsafin baduhu da kauda da k’uk’uwa da birkita-kwanci. Dubi arangama tsakanin maharbi Ilaje Mai baka ‘Danmamman da zaki, kamar yadda Mai komon daji ‘Dan Hanne ya kawo a cikin wak’arsa, yana cewa:


Sai Ilaje yac ce a’a,

Zaki yac ce a’a,

Gardama tas sulle,

Cana tsakanin daji,

Ilaje sai yac ce mai,

Arewa k’wallare ya ey,

Tun da Allah Yay yi ni,

Tun ina yaro ban ta’ba harbin,

Naman dawa shi kai labari,

Yau ana wadda akai,

Sai Zaki yac ce mai,

Arewa k’wallare ya ey,

Tun da Allah Yay yi ni nan tsakanin daji,

Ban ta’ba murza naman gida,

Yak kai labari,

Yau ana wadda akai,

 

7.0 Nad’ewa


Tirk’ashi!, ashe ‘sanin asali ya sa kura cin kanjilo’. Hausawa tun suna cikin Maguzanci ba su yi k’asa-a-gwuiwa ba kan sha’anin kiyon lafiyarsu. Babu shakka kimiyyar had’a magungunan Bahaushe ba abin renawa ba ce idan aka kasa ta a faifan nazari, musamman ta k’ok’arin gano alak’ar najasa da iskoki domin yin mahad’i da ita a magance cutukansu ko neman taimakonsu. A wannan mak’alar, akwai hasashen cewa, najasa wata kadarko ce a cikin sinadarai ko mahad’in maganin iska a Bahaushiyar al’ada. Wannan ya tabattar da cewa, akwai cutukan da har yanzu asibitocin zamani ba su samo musu k’wayoyin had’iya ba, sai dai a dawo ga “Masu abu”, wato iskoki. Ashe gaskiyar Bahaushe da ke cewa, ‘karen da ya yi cizo da gashinsa ake magani.’

 

MANAZARTA


Abdullahi, I.S.S. (2000), “Magani da Siddabaru Cikin Rubutattun K’agaggun Labaran Hausa”, Kudin digri na biyu, Jami’ar Usman Danfodiyo, Sakkwato.

Abubakar, S.Y. (1997), "Bori A Zariya," Kundin digiri na biyu (M.A), Sashen Koyar da harsunan Nijiriya, Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya.

Abul-Mundhir, K.I.A. (2005), The Jinn and Human Sickness: Remedies in the Light of the Qur’aan and Sunnah. An English translation of Atturuq hisaan Fi Ilaji Amraad Al-jinn. Darussalam, Jeddah.

Adamu, S.A. (2011) “Gurbin K’wari a Magungunan Gargajiya na Hausawa”. Kundin digiri na biyu (M.A), Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Alhassan, H. da Wasu (1982), Zaman Hausawa. Institute of Education Press, ABU Zaria.

Al-Jauziyah, I. I. (1999) Healing With the Medicine of the Prophet (SAW). Fassarar Turanci daga Jalal Abual Rub. Darussalam, Riyadh, Saudi Arabia.

Bergery, G.P. (1934) A Hausa-English and English-Hausa Vocabulary. Oxford      University Press, London.

Bunza, A.M.(1990), “Hayaki Fid Da Na Kogo”. Kundin digri na biyu (M.A.), Sashen        Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.

Bunza, A.M. (1995), Magungunan Hausa A Rubuce.” Kundin digiri na uku (PhD) Sashen                          Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero,     Kano.

Bunza, A.M. (1999) Radadi Da Zogin Cuta A Ma’aunin Bahaushe.” Muk’alar da taron     K’arawa juna sani, Sashen Koyar da Hasrsunan Nijeriya, Jami’ar Usman          Danfodiyo, Sakkwato.

Bunza, A.M. (2004) “Mahad’in Mugungunan Gargajiya”, Muk’alar da aka gabatar a        Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu’Danfodiyo,       Sakkwato.

Bunza, A.M. (2006) Gadon Fed’e Al’ada . IBRASH LTD. Lagos

C.N.H.N (2006) K’amusun Hausa, Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar       Bayero, Kano.

Gobir, Y.A (2002) “Iskoki a Idon ’Yan bori da Masu Ruk’iyya”. Kundin digiri na biyu     (M.A), Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu   ‘Danfodiyo,   Sakkwato.

Gobir, Y.A (2010) “Huld’ar Soyayya Tsakanin ‘Dan Adam da Iska”. Cikin KONJOLLS: Kontagora Journal of Languages and Literatures. FCT        Kontagora.

Greenberg, J. (1946), The influence of Islam Sudanese Religion. Monographs of the           American Ethnological society, 10, New York Seattle, London.

Gummi, A. M. (1997) Alk’ur’ani Maigirma Da Kuma Tarjamar ma’noninsa Zuwa Ga Harshen Hausa. Ma’akatar Kula da Harkokin Addinin Musulunci, da Wak’afai, da kuma Wa’azi da Shiryarwa, ta K’asar Saudi Arabiya.

Hamza, M.W. (1977), “Magungunan Hausawa”. Kundin digirin         farko, Jami’ar            Bayero, Kano.

Ibrahim, S.M. (1982), “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci   Kan     Hausawa” Kundin Digiri Na Biyu Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,      Jami’ar Bayero, Kano.

Ingawa, Z.S (1984), “Magungunan Hausawa Don Mata”. Kundin digirin      farko, Jami’ar Bayero, Kano.

Isma’ila, H.A. (1981), “Islamic Medicine and Its Influence on Traditional    Hausa Practitioners in Northern Nigeria.Unpublished Ph.D Thesis.Madison    University of Wisconsin.

Jinju, H.M. (1990), Maganin Gargajiya Na Afrika, tare da mai da k’arfi a kan Nazarin Itatuwan Magani Na Hausa. Kamfanin Gaskiya Zariya.

Rodney, M.C. (1970) Sociology of Medicine. McGraw-Hill Book company, New York.

Sa’eed, A.M.A. (2005) The Evil Eye. Minaeret Books International. Lagos, Nigeria.

Tremearne, A. J.  N. (1968) The Ban of Bori Demons and Demon, dancing in West Afirca, London.

Wahid, A.B. (1988), Wik’ãyatul Insãn Minal Jinn Was Shaid’ãn. Darul Bashir Alk’ahira (Misra).

Wall, L. (1988) Hausa Medicine: Illness and Well-Being In a West African Culture. Durhma, NC Duke Univeristy Press.

’Yand’aki, A. I. (1990) “A History of the Izala Movement in Northern Nigeria up to          1989”. M.A. Thesis, Department of History, Usmanu Danfodiyo University,            Sokoto.

Zakariyya, M.N.Z. (1997), Maganin Kowace Irin Cuta. Littafi na d’aya.Kamfanin Alkauthar, Kaduna.

 

[i] Dubi Habib Alhassan da Wasu, Zaman Hausawa (1982). Shafi na 52.

[ii]  Dubi Wahid A. Bali (1988) Wik’ayatul Insana Minal Jinni Was Shaid’an. Darul Bashir Al-K’ahira (Masar), shafi na   13

[iii] Hira da Ada mai Rafani sabon Birni. Ranar 15/9/2000.

[iv] Hira da Mal ‘Danjuma Zuru mai maganin iska, a gidansa da ke Farfaru Sakkwato.

[v] Don k’arin bayani, dubi Tremearne,  (1968)  The Ban of Bori Demons and Demon, dancing in West Afirca, London, da lamba ta 1 a wannan mak’alar.

[vi] Dubi Musa Shehu, “Waibuwar Masunta”. muk’alar da aka gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Post a Comment

0 Comments