Amsoshi

DagaRabiu Aliyu RamboSashen Koyar Da Harsunan Najeriya


Jami’ar Usmanu Danfodiyo; Sakkwato.


Email: rabiualiyurambo@yahoo.com


GSM:08125507991Muk’alar da aka Gabatar a Taron K’ara wa Juna Sani na K’asa da K’asa a  kan  Ta’bar’barewar Al’adun Hausawa a yau, Wadda aka Gabatar a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’ aduwa  da ke Katsina. 25-26 Yuni 2013


 

https://www.amsoshi.com/2017/11/06/noma-igiya-madura-kaya-yi-ba-da-kai-ba-su-watse/

Tsakure


Haihuwa ko samar da ‘ya’ya shi ne babban manufar yin aure ga al’ummar Hausawa, kamar yadda yake a mafi yawan al’ummun duniya. Shi kuwa lamarin haihuwa yana samuwa ne ta hanyar yin aure, kuma ta hanyar haihuwa ne ake samun wanzuwar al’umma tun daga farkon wannan duniyar har zuwa k’arshenta. Mai yiwuwa dangane da hakan ne al’ummar Hausawa ke  fad’i-tashi wajen yin aure domin neman haihuwa. Ba sai an fad’a ba, ana iya ganin irin darajar da Bahaushe ya ba wa lamarin haihuwa idan aka dubi irin damuwar da yake nunawa idan ya yi aure bai sami haihuwa ba. Bisa ga wannan matsayi na haihuwa ne, a wannan mak’ala  za a yi tak’aitaccen bayani a kan nason zamananci a cikin al’adun haihuwar Bahaushe. Za a yi k’ok’arin kawo yadda nason wasu bak’in al’adu ya haifar da ta’bar’barewar wad’annan al’adu na haihuwa. Daga cikin abubuwan da muk’alar  za ta yi nazari a kansu sun had’a da: goyon ciki da kayan k’auri da zanen suna da wankan jego da gara da reno.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

1.0 Gabatarwa


Haihuwa na d’aya daga cikin manya-manyan ginshik’an dalilan yin aure a cikin al’ummar Hausawa. Duk da yake lamarin haihuwa lamari ne da ya bambanta daga wannan al’umma zuwa waccan. Domin wasu al’ummu ba su buk’atar haihuwa kamar yadda wasu suke da. A k’asar Hausa d’a (mace ko namiji) baiwa ce da kowa ke burin ya samu. A al’ada, yaro ko ba kai ka haife shi ba muddin ka girme shi zai yi maka ladabi (C N H N . 1981 :16) Wannan ya nuna ‘ya’ya suna da muhimmanci a cikin al’ummar Hausawa.

A al’adance, a duk lokacin da aka sami  k’aruwa ta haihuwa a k’asar Hausa, ana aiwatar da wasu al’adu wad’anda ke nuna murna ko farin cikin k’aruwar da aka samu. Don haka , wannan mak’ala za ta yi k’ok’arin nazarin wasu daga cikin al’adun da ake aiwatarwa a lokacin gudanar da bikin haihuwa a k’asar Hausa. Daga cikin abubuwan da za a yi nazari sun had’a da al’adar goyon ciki da ta kayan k’auri da ta zanen suna da ta wankan jego da ta kayan gara da ta shayarwa.

Bisa haka ne a wannan mak’alar za a yi k’ok’arin kawo irin yadda zamananci ya yi tasiri a cikin al’adun haihuwar bahaushe a yanzu . Ma’ana,  za a dubi yadda nason bak’in al’adu ya taimaka wajen ta’bar’barewar  al’adun haihuwa na Bahaushe.  A k’arshe mak’alar ta yi k’ok’arin ba da shawarwari  yadda za a tsare a kuma inganta wad’annan al’adu  musammam a cikin al’ummar Hausawa domin muhimmamcinsu.

 

2.0  Ma’anar Haihuwa


Dangane da abin ya shafi ma’anar haihuwa kuwa, a nan ana iya cewa akwai ra’ayoyi daba-daban dangane da ma’anar haihuwa . Domin wasu sun d’auki ma’anar ne ta fuskar samun da wani ya  yi  na wani abu. Misali a ce ‘yawan dariya barkatai na haifar da hauka’ A nan haihuwa na matsayin musabbabi. Amma idan muka ce ‘Aisha ta haifi Musa’ A nan wannan na nuna a sanadiyyar saduwa da Aisha ta yi da mijinta ta d’auki ciki har ta haifi Musa.

Ta  wannan fuska, ana iya cewa haihuwa tana nufin samuwar d’a namiji ko mace da mutane kan yi ta hanyar saduwa tsakanin namiji da mace musammam ta hanyar aure. Ga kad’an daga cikin abin da masana suka tofa dangane da ma’anar haihuwa. Abdullahi  ya rawaito Alhassan da wasu suna cewa ‘-----yayin da miji da mata suka k’aru da samun d’a ko’ya ‘ (Abdullahi  2008:225)

A ma’anar k’amussan Hausa na C N H N an  bayyana ma’anar haihuwa da cewa: ‘samun d’a ko ‘ya bayan mace ta yi ciki wata tara’ (kamussan Hausa C N H N .2006:189) Haka kuma a wani ra’ayin cewa aka yi:

K’aruwa ce ta hanyar fitowar wani abu mai rai daga

                   jikin wata halitta jincin mace wanda ya ‘boyu a wani

                   wuri na musammam na wani k’ayyadadden lokaci

                   don samun kamanni ko siffa kwatankwacin na

                   zuriyarsu,wanda ke aukuwa a sakamakon saduwa

                   da jinsin namiji na wani halittar.

(Abdullahi, 2008:228)

Bisa ga wad’annan ma’anoni, ana iya fahintar haihuwa a wannan muhalli tana nufin irin k’aruwar da matan Bahaushe kan samu na ‘ya’ya musamman bayan sun yi aure. Domin a al’adar Bahaushe ana iya samun k’aruwa ta haihuwa amma maimakon a yi farin ciki sai ya zama na bak’in ciki,wannan kuwa  a fili yake idan aka dubi irin k’yamar da ake nuna wa matar da ta haihu ba tare da miji ba, ma’ana samun d’an da aka Haifa ba tare da aure ba.

 

3.0 Wasu Al’adun Haihuwa a Al’ummar Hausawa


Idan ana maganar  k’asar Hausa, ana nufin wata farfajiya wadda take shimfid’e, tare da gulabe da duwatsu da tsaunuka da suka ratsa ta jefi-jefi. K’asar Hausa tana da manyan birane da k’ananan k’auyuka da suka had’a da Kano da Katsina da Daura da Gobir da Zazzau da Rano da Garun gabas         da Gaya da sauransu.

Ta fuskar harshe kuwa, Yahaya da wasu  (2001:95) sun ce:

                      Harshen Hausa shi ne wanda Hausawa suke amfani da shi,

                     kuma shi ne babban jigo wanda ya had’a dangantaka

                  da kasuwanci tsakanin wad’annan garuruwa, sai kuma

                  harakokin kasuwanci da ciniki da saye da sayarwa  

Don haka, mazauna k’asar Hausa kamar sauran k’abilun duniya, suna da d’abi’unsu da al’adunsu da suka ke’banta da su, wasu daga cikin al’adun suna tattare ne da wasu bukukuwa da suke aiwatarwa a tsakanin su. Wad’annan bukukuwa suna k’ara dank’on zumunci da kawo annashawa a tsakanin su. Kuma wad’annan bukukuwan su ne k’ashin bayan jin dad’in zaman al’ummar Hausawa.  Wad’annan bukukuwa sun had’a da; haihuwa da aure da sallah da kalankuwa da shan kabewa da sauransu.

A  wannan muk’alar za a yi bayani ne a kan wasu al’adu da ake aiwatarwa lokacin bukin haihuwa a cikin al’ummar Hausawa.

3.1 Al’adar Goyon Ciki

A k’asar Hausa, ana da al’adar mayar da yarinya haihuwa a gidansu idan cikin ya kai wata bakwai, kuma galibi wannan na faruwa ne ga mace mai haihuwar fari. Wannan al’ada ana yin ta ne domin mai ciki ta sami kulawa na musammam a gidansu .A wannan lokacin ana kula da lafiyarta, kuma ana sanya mata wasu sharud’a na hani ko horo ga aikata wasu ayyuka ko cin wani abu musammam wad’anda za su taimaka mata sauka lafiya.

Haka za ta ci gaba da zama gidansu har lokacin da nak’uda ta taso mata. Nak’uda ita ce wata alama da mai haihuwa za ta fara ji ko gani kamar ciwon mara da baya da fitar  ruwa fari a gabanta . Lamarin nak’uda wani abu ne mai matuk’ar wahala .Wannan ya sa har wak’a aka yi mata kamar haka:

Wayyo nak’uda ta tashi

Ciwon nak’uda ya tashi

Kuma ciwon nak’uda ya motsa

Yau kam babu zama zaure

Wayyo Inna ki cece ni

Wayyo nak’uda ‘yar ziza

Ciwon nak’uda bori ne

Ko ko nak’uda hauka ce

Amshi ki d’an kur’ba

Ba toka ce ba rubutu ne

Ko Allah nai maki sauk’in ta

(Yahaya  da wasu 2001:99)

Ga al’ada, da zarar mace ta je goyon ciki iyayenta za su rink’a tanadin wasu kayan goyo. Haka kuma shi ma miji zai tanadi nasa kayan ,wani lokaci ana kai mace ne gidansu, wani lokaci kuwa iyayenta ne ke zuwa su d’auke ta. (CNHN. 1981:17)

Kamar yadda aka ambata a baya, idan nak’uda ta fara ana kiran wata tsohuwa a unguwa mai d’aukar bik’i (ungozoma). Ita ungozoma tana da masaniyar dabarun kar’bar haihuwa. Bayan an sauka lafiya ungozoma za ta yanke cibiyar abin da aka haifa, ta wanke jinjiri ta kuma taimaka wurin gyaran d’akin mai haihuwa. Tana kuma taimakawa da wasu ‘yan sak’e-sak’i wadanda za a  ba jariri da uwarsa domin gyaran jiki da kariya ga wasu cututtuka. Kuma za ta ci gaba da yi wa jariri da uwar jaririn hidima har sai bayan uwar ta gama wankan jego.

3.2 Kayan K’auri

A al’ada ana kai kayan k’auri ne bayan an yi kwana hud’u da haihuwa . Kuma mafi yawa ana amfani da k’afafun sa ko kai had’e da kayan yaji kamar citta da kanunfuri da masoro da barkono da kanwa da hatsi da sauransu. A kwana na biyar za a yi rabon k’aurin bayan an cire wa mai jego nata, inda za a ba mak’wabta da sauran dangi da abokan arziki. A lokacin wannan rabon k’aurin,  ana had’awa da kunun kanwa duk a raba wa mak’wabta. Kuma a al’ada, duk namijin da matarsa ta haihu ba a yi bikin shan k’auri ba, to wannan ya yi abin kunya a cikin  al’umma.

3.3 Bikin Suna

Kamar yadda sunan ya nuna , bikin suna wani yanayi ne da ake had’a ’yan uwa da abokan arziki a ci a sha, kuma a yi annashuwa da raha. Ana aiwatar da bikin suna ne idan ranar da aka haifi jaririn ta zagayo; ma’ana bayan mako guda. Ranar suna, rana ce da za a rad’a wa jaririn da aka haifa sunan da za a rik’a kiran sa da shi. Galibi a k’asar Hausa ana sanar da ‘yan ‘uwa da abokan arziki su had’u musammmam da safe lokacin kalaci domin gudanar da wannan al’ada.

A ranar suna, ana yanka rago a raba goro, liman ya yi wa jariri hud’uba galibi bayan kwana bakwai da haihuwa, duk da yake ana iya hud’uba tun ranar da aka haifi jinjiri a rad’a wa yaro suna sai dai ba za a bayyana sunan ba sai ranar suna. Kuma galibi da yake Hausawa mabiya addinin Musulunci ne, don haka, ana za’ben sunan ne daga cikin sunayen addinin Musulunci.

Ranar rad’in suna ,za a taru tsakanin dangin mai

 haihuwa da mijinta .Idan wad’anda duk ake jira ya

                             taho, za a raba goro ga jama’a inda za a fara fitar da

                             na malamai da wanzamai da mata . Daga nan sai

                             liman ya yi wa abin haihuwar addu’a da ita kanta

 mahaifiyar da uban da sauran jama’a baki d’aya

(Yahaya da wasu . 2001:99)

Shi kuwa (Gusau, 2012:42) Yana da ra’ayin cewa:

Zanen suna ko rad’in suna ana gudanar

da shi ga abin da aka haifa, bayan mako

d’aya da haihuwa. Zanen suna ko rad’in

suna ya kasu kashi biyu, akwai zanen

 suna a gargajiyance, akwai kuma zanen

 suna a addinance.

Ta kowace fuska dai za a fahinci bikin zanen suna yana haddasa had’uwar dangin mace da na namiji wuri d’aya domin taya juna murnar samun k’aruwa ta haihuwar da aka samu.

3.4 Wankan Jego

Wankan jego wanka ne da mace mai haihuwa kan yi da tafasassun ruwa har na tsawon a k’alla kwana arba’in bayan ta haihu safe da marece. Daga nan sai ta ci gaba da yi da safe ko da yamma kawai zuwa kwana sittin ko ma fiye. A lokacin wannan wankan, ana yin amfani  ganyen sabara ko na doka ko na geza ko darbejiya ko sanga-sanga. Ana amfani da wad’annan ganyayyaki ne saboda muhimmancinsu wajen samar da waraka daga cututtuka daban-daban. A al’adance mace mai haihuwa tana fara wankan jego ne tun daga ranar da ta haihu. Wannan wankan yana matsayin wata hanya ta jinyar raunin da ta samu lokacin haihuwa. A wannan lokacin ne ake ba jinjiri dauri domin kula da lafiyarsa.

A al’adance idan mai jego ta yi ak’alla kwana arba’in tana yin  wankan, har  d’an k’warya-k’wary an biki ake yi,  inda za a toya waina a ci a yi sadaka. Bayan wannan lakacin ne mace za ta fara kwalliya.

3.5 Kayan Gara

A k’amussan Hausa, an bayyana ma’anar gara da cewa:

Kaya, musamman na abinci da iyayen

 amarya kan kai wa ‘yarsu bayan an

 gama bikin aure ko haihuwa.

(CNHN.2006;157.)

A zahiri ana iya fahintar ana amfani da wannan kalmar ta gara a muhalli biyu ne lokacin bikin aure da haihuwa. Ana kai garar haihuwa a ranar suna , wato kayan toye-toye  wani lokaci har da kud’i . Sannan ana kai gara lokacin da mai haihuwa za ta koma d’akinta bayan ta k’are wankan jego. A nan ana had’a mata kayan abinci irin su shinkafa da dawa da mai da daddawa da gishiri gwargwadon k’arfin iyayenta. Wani lokaci har  makad’i ake kira ya raka su, ana tafe ana wak’e-wak’e kamar sabuwar amarya.

3.6  Renon Abin da aka Haifa

Bayan an rad’a wa jinjiri suna da sauran hidimomin al’ada kamar wankan jego da gara,  al’ada ta gaba mai muhimmanci ita ce renon shi abin  da aka haifa. Reno shi ne ci gaba da kulawa da shi, ta hanyar ba shi dauri da nono sau da yawa wannan yana faruwa har tsawon wata shida . Daga nan ne za a fara ba shi kunun hatsi  yana sha, duk da yake ana yi mashi d’ure ne. A lokacin da jariri ya kai wata takwas zuwa tara ne  za a fara bashi abinci , sannu a hankali har ya fara ci da kansa.

Haka a wannan lokacin ne ake koya wa jinjiri zama daga nan sai rarraife da ta-ta-ta (koyon tashi tsaye) daga nan ya fara koyon tafiya . Abin lura a nan shi ne, kusantar da jinjiri yake yi da uwarsa a lokacin reno. Wannan kuwa yana taimakawa wajen samun shak’uwa da soyayya a tsakanin jinjiri da uwarsa. Duk da yake, a k’asar Hausa akwai al’adar d’an reno, inda uwar jinjiri tare da amincewar mai gidanta za su samo wata ‘yar yarinya domin ta taimaka wa uwar wajen renon jinjiri musamman lokacin da take aiwatar da wasu ayyuka na gida. Bayan reno, abu na gaba ga abin da aka haifa shi ne yaye.  za a cire jinjiri ne daga shan nonon mahaifiyarsa. Galibi ana kai yaron ne wajen kakanninsa zuwa wani lokacin da zai manta da nono. Daga baya sai a dawo da shi wurin iyayensa.

4.0 Nason Bak’in al’adu a Cikin Al’adun haihuwar Hausawa


Tarihi ya nuna  cewa dukkan inda aka sami wata al’umma ta shigar

                   wa wata al’umma, wad’anda yake tilas ne ya zamana al’adunsu

                   sun sha bamban, to za ka taras al’adar al’ummar da ta fi k’arfi ta yi

                   tasiri a kan rarraunar. Im ma ba a mayar da hankali ba sai a

wayi gari a tarar k’ak’k’arfar ta mamaye rarraunar baki d’aya.

(CNHN, 1981:32)     

Kasancewar k’asar Hausa k’asa ce  mai dad’ad’d’en tarihi wadda ta sha fad’i-tashi da sauran al’ummu daban-daban na kusa da na nesa wannan ya taimaka wajen kawo wasu sauye-sauye a cikin al’adun haihuwar Bahaushe.  Kasancewarya kullum duniya a cikin sauyi take, wannan  shi  ya haifar da sauyi a cikin al’adun haihuwar Bahaushe. Don haka, ci gaban zamani (wayewar kai) ya taimaka wajen sauya tunanin Bahaushe shi kansa. Haka lalurar kwaikwayon bak’in al’adu shi ma sun taimaka wajen ta’bar’barewar al’adun haihuwar Bahaushe. Don haka, akwai dalilai da dama da suka taimaka wajen ta’bar’barewar al’adun haihuwa a yau, wanda inda an tsaya  tsayin daka aka rik’i wad’ancan al’adu na gargajiya da sun taimaka  ainun wajen wanzar da rayuwa mai nagarta fiye da yadda ake a yau.

4.1 Ta’bar’barewar Al’adar Goyon Ciki

Kamar yadda bayani ya gabata , goyon ciki shi ne zuwa gida da mai haihuwa kan yi  gidan iyayenta, musammam a lokacin haihuwar fari, yawanci tun cikin na  wata bakwai. Idan aka lura wannan al’adar an kusan mantawa da ita duk kuwa da irin muhimmancinta ga al’ummar Hausawa. A yanzu za a taras zuwa goyon ciki ya yi  k’aranci  sosai a cikin al’ummar Hausawa. Masu ‘bar’bashin wannan al’adar su ne wad’anda ke bari sai matar ta haihu a mai da ita gida tare da jinjirinta. A nan za a ga irin kulawar da za ta samu idan tana gidan iyayenta ba za ta same ta ba a gidan mijinta musamman ga mazauna birane.

A nan, za a fahinci mai haihuwar ta yi hasarar irin shawarwarin da iyayenta kan ba ta na hani ko horo ga aikata wani abu, musammam wanda zai taimaka mata inganta lafiyarta da samun sauk’in haihuwa. Don haka, al’adar komawa gida goyon ciki ta ci baya ainun a cikin al’ummar Hausawa a yau. Hakan na faruwa ne saboda nason bak’in al’adu da nuna wayewar kai na zamani.

Bugu da k’ari, idan aka dubi irin hidimar da ungozoma ke aiwatarwa na kula da jinjiri ta hanyar yi masa wanka safe da maraice na tsawon kwana arba’in da ba shi dauri wanda zai taimaka wa lafiyarsa da kula da lafiyar uwarsa duk wad’annan an yi watsi da su. A yanzu an mai da haihuwa asibiti, su kuwa asibiti babu rowan su da dauri.

4.2 Ta’bar’barewar Al’adar Kayan k’auri

Kayan  k’auri abu ne mai muhummanci ga uwar jinjiri , domin suna taimaka mata wajen kulawa da lafiyarta . A  halin  yanzu wannan al’adar ta yi rauni ainun a cikin al’ummar Hausawa. Zai yiwu saboda matsalar tattalin  arziki  ko kuma wayewa ta zamani, ta yadda a yanzu kowa yana zaune a gidansa ne babu wanda ya damu da wani.

Baya ga k’arin lafiya ga mai haihuwa , rabon k’aurin da akan yi yana k’ara dank’on zumunci a cikin al’ummar Hausawa. Don haka, rashin aiwatar da wannan al’ada ya haifar da wani gi’bi a cikin lamarin zumuncin bahaushe. Haka ma, ana iya cewa a  yanzu  a tsakanin al’umma babu  jinkai da tausayin juna, uwa-uba sai tsabar rowa, domin a yanzu mak’wabci na iya ci ya hana  mak’wabcinsa ba tare da wata damuwa ba.

4.3 Ta’bar’barewar Al’adar Bikin Suna

Kamar yadda bayani ya gabata, Hausawa sun ba bikin suna muhimmanci k’warai da gaske, musammam idan  aka dubi irin kai –komo da gidan uba da na uwar jinjirin kan yi na shirye –shiryen suna. A al’adance za a ga ranar suna rana ce da ake tara dangin uwa da na uba da ‘yan uwa da abokan arziki domin taya d’an uwa murnar samun k’aruwa. Wannan na zaman wata kafa ta k’ara had’a dank’on zumunci a tsakanin al’umma, inda za a had’u da wanda aka dad’e ba a had’u ba . Wata fa’ida ta taron zanen suna ita ce wani bagire ne da ake tattauna wasu matsaloli na al’umma.

Amma a yau, zai yiwu ko dai saboda fahintar addini  ya sauk’ak’a abubuwa. Wannan ya sa al’ummar Hausawa sun yi saku-saku da wannan al’ada.  Ta wata fuskar, ya yiwu matsatsin tattalin arziki da al’umma ke fuskanta ya sa aka  yi saku-saku da wannan  al’ada. Babu shakka, idan aka yi karatun-ta -natsu, za a ga wannan al’ada ta ta’bar’bare.

4.4 Ta’bar’barewar Al’adar Wankan Jego

Hausawa na cewa, ‘Zamani riga ce, tana daidai da wuyan kowa’. Duk da yake a al’adance an sani  wankan jego ko bik’i abu ne mai muhimmanci musamman ga mace mai haihuwa, a yanzu al’ummar Hausawa na son ta yi watsi da shi.  A  zahiri a yanzu ta ci baya ainun. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da wayewar kai ba, musamman ganin yadda wasu matan Hausawa suke cewa wai amfani da ruwan zafi yana dafe masu jiki. Wasu kuwa suna jin tsoron amfani da ruwan zafin ne saboda zafinsu. A yanzu saboda yawaitar haihuwa da ake yi a asibiti ba a cika wankan jego ba. Wannan kuwa yana faruwa ne saboda a yanzu  akwai  k’wayoyin magunguna da allurai da ake yi wa mai haihuwa a asibiti da zarar ta sauka  maimakon wankan jegon. Sai dai abin lura a nan shi ne, duk da wad’annan allurai bai kamata a bar wankan jego ba saboda irin muhimmancinsa a al’ummar Hausawa.

4.5 Ta’bar’barewar Al’adar Kayan Gara

Kayan gara kamar yadda bayani ya gabata, ‘yan kayayyaki ne da ake kawo wa uban jinjiri a lokacin suna ko lokacin da za a dawo da mai haihuwa daga gidansu zuwa d’akinta. Wannan al’ada ana yin ta ne domin a d’an taimaka wa miji da wani abu, ganin  ya yi d’awainiyar biki. Duk da irin wannan manufa ta kayan gara, a yanzu al’adar ta ta’bar’bare sosai a cikin al’ummar Hausawa. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da nason bak’in al’adu ba. Domin a tsarin zamantakewar Bature kowa tashi ta fisshe shi ne, in ba ka yi ba ni wuri. Zamantakewa irin wannan kuwa ba ta buk’atar taimakon juna, sai dai kowa ya yi ta kansa. Zai  yiwu kuma, saboda yanzu akwai matsin tattalin arziki, musamman a Arewacin Najeriya wanda shi ya taimaka wajen raguwar aiwatar da wannan al’ada.

4.6 Ta’bar’barewar Al’adar Reno A Al’ummar Hausawa

A yanzu idan aka lura, za a ga al’adar reno ta ta’bar’bare ainun a cikin al’ummar Hausawa, musamman saboda nason wasu bak’in al’adu a cikinta A  zamanance ana ganin wannan a matsayin ci gaba; Amma a zahiri  ci baya ne . Misali idan aka dubi tsawon lokacin da uwa kan samu tana goye da d’anta ko rungume da shi, Wannan yana k’ara dank’on zumunci da soyayya da jink’ai a tsakanin jinjirin da uwarsa. Haka kuma, nonon da take ba shi yana matsayin kariya ga wasu cututtuka gare shi. Don haka, uwa kan d’auki d’an reno domin ya rink’a taimaka mata da renon.

A yanzu lalurar d’an reno ya kusa zama tarihi, domin yanzu zamani ya zo da cibiyoyin reno na musamman, inda za a kai jinjiri reno, uwar kuwa ta wuce wurin  aikinta. Bugu da k’ari , a yanzu an samar da magunguna wad’anda suke k’umshe da abinci. Wannan kuwa na taimakawa sosai wurin rage shan nonon jinjiri. Wata matsala ta zamani da kawo cikas ga harkar reno ita ce rashin gaskiya a cikin al’umma, inda sau da yawa za a tarar an had’a kai da ‘yar reno an cutar da jinjiri domin wasu buk’atu na duniya.

5.0 Shawarwari


Domin tabbatar da wanzuwar al’adun haihuwar Hausawa da aka d’an yi bayanin su a wannan mak’alar, za a ga ta la’akari da muhimmancinsu a cikin al’ummar Hausawa bai kamata a bari wad’annan al’adu su salwanta ba wai don kawai nason bak’in al’adu da ya shige mu. Domin duk al’ummar da take watsi da  nata al’ada tana kwaikwayon na wasu, to kul-a jima za ta manta da nata. Bisa ga wannan ne ake kira ga al’ummar Hausawa da mu yi rik’o da kyawawan al’adunmu na haihuwa  babu kama hannun yaro.

Ta fuskar amfani da kayan zamani kuwa musamman kayan kallace-kallace, a yanzu sun maye gurbin hirar da ake yi da dangi a lokacin bikin haihuwa. Domin a yanzu sai dai a shiga kallace-kallacen fina-finan zamani. Don haka akwai buk’atar a yi watsi da wannan al’adar ta kallace-kallace a yi amfani da dandalin suna wanda yakan zama  zauren tattauna matsalolin da suka shafi rayuwar al’umma.

Bayan haka, shigowar hukuma cikin lamarin yana iya taimakawa wajen kauce wa ta’bar’barewar al’adun haihuwa a al’ummar Hausawa. Domin wasu al’adun aiwatar da su na buk’atar kud’i. A yanzu saboda matsin tattalin arziki mafi yawan  Hausawa suna fama da wannan matsala ta kud’i. Don haka, hukuma na iya taimaka wa al’umma da bashi ba tare ruwa ba . Hukuma na iya k’irk’iro  wasu dokoki wad’anda za su taimaka wajen wanzar da al’adun haihuwa. Yin haka, zai taimaka wajen maganin ta’bar’barewar wad’annan al’adu.

Bugu da k’ari, wannan mak’alar na ganin ya kamata a sami wasu k’ungiyoyi na maza da mata da za su taimaka wajen wayar ma jama’a da kai dangane da muhimmancin wad’annan al’adu. Al’adun kuwa sun had’a da na goyon ciki, da na bikin suna, da na reno, da sauransu. Kuma su wad’annan k’ungiyoyi su  zama a k’ark’ashin kulawar shugabannin kowace al’umma wad’anda suka san darajar al’adun.

Shawara ta gaba ita ce, matsawar ana son kauce wa ta’bar’barewar wad’annan al’adun haihuwa, to akwai buk’atar a d’an yi ma wasu gyaran fuska ta yadda za su dace da zamani . Misali al’adar yankan rago . Tun da an fahinci ba dole ba ne, to ya kamata jama’a su fahinci rashin rago ba ya hana suna. Domin a yanzu, sau da yawa za a tarar saboda rashin rago an dad’e  ba a yi suna ba. Haka idan aka dubi al’adar shan-k’auri da gara, sun so su d’an yi tsauri musamman ga marasa abin hannun su, domin wani ba ya da k’arfin aiwatar da wannan al’ada. Amma kuma sai al’umma ta zarge shi a kan ya kasa.  Maimakon haka, kamata ya yi a ba mai gida shawara ya rik’a yin hak’uri da duk abin da Allah ya ba shi.

A k’arshe, bisa ga shawarwarin da aka bayar a sama , za a ga  al’adun haihuwa sun taimaka musamman wajen adana da kuma ha’baka zumunci a tsakanin al’ummar Hausawa duk kuwa da irin barazanar da nason bak’in al’adu yake yi a kansu.

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/gudummuwar-sanaoin-zamani-wajen-bunksa-tattalin-arzikin-ksar-hausa/

6.0 Kammalawa


Al’amarin haihuwa, al’amari ne mai matuk’ar muhimmanci a wurin al’ummar Hausawa. Hasali ma, haihuwa ita ce k’ashin bayan yawaitar kowace al’umma a duniya. Shi kuwa lamarin haihuwa yana samuwa ne sanadiyyar yin aure a tsakanin namiji da mace. Buk’atar wannan haihuwa ya sa al’ummar Hausawa ta ba wa aure muhimmanci domin samun haihuwa.

A wannan mak’ala an yi k’ok’arin nazarin wasu al’adu ne da suka ke’banta ga al’adun haihuwa a al’ummar Hausawa. Daga cikin su akwai al’adar goyon ciki da ta nak’uda da ta kayan k’auri da ta bikin suna da ta gara da ta reno da sauransu. A nan mak’alar ta yi k’      ok’arin bayanin yadda suke a da, da kuma yadda suke a yanzu bayan an sami nason bak’in al’adu a cikin su. Haka kuma, bisa ga binciken da aka gudanar an fahinci  a yanzu wad’annan al’adu sun ta’bar’bare a cikin al’ummar Hausawa. Don haka, an kawo shawarwari yadda ake ganin za a iya kare al’adun daga k’ara ta’bar’barewa. Ko shakka babu, wad’annan al’adun haihuwa sun taimaka wa al’ummar Hausawa wajen wanzar da zamantakewa mai nagarta a tsakanin al’ummar Hausawa tare da inganta kiwon lafiya.

 

 

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/gudummuwar-sanaoin-zamani-wajen-bunksa-tattalin-arzikin-ksar-hausa/

Manazarta


Abdullahi  I .S. S. 2008.’ Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye A Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa Na Aure Da Haihuwa Da Mutuwa’. Kundin Digiri na uku, Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato.

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. 1981. Rayuwar Hausawa. Thomas Nelson Publishers. Lagos.

Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya. 2006. K’amusun Hausa

Gusau G. U. 2012. Bukukuwan Hausawa. Ol-faith. Gusau.

Habib Alhassan da wasu. 1988. Zaman Hausawa. Islamic Publication Bureau. Lagos

Madauci, I. 1975. Hausa Customs. Zaria. Northern Nigeria Publishing Company.

Magaji, A 2002. ‘Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye-Yanayensu A K’asar Katsina’ Kundin Digiri na uku, Jami’ar Bayero Kano.

Umar M B. 1980. Al’adun Haihuwa A K’asar Hausa. Hausa Publications Centre, Zaria.

Yahaya I Y da wasu. 2001. Dasussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandare. Littafi na uku. University Press Plc. Ibadan.