Amsoshi

DagaRabiu Aliyu Rambo


Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya


Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto.


Email: Rabiualiyurambo@yahoo.com


GSM:08125507991Mak’alar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani, Sashen koyar da Harsunan


Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,Sakkwato. Ranar 23-5-2013. 

TSAKURE


Aure al’ada ce wadda ta dad’e a duniya baki d’aya. Hasali ma tushen aure ya samo asali ne tun lokacin da Allah (S W A) cikin ikonsa ya halacci mutum na farko a doron k’asa, watau Annabi Adamu (A S). Sannan cikin k’addarawarsa ya halicci Hauwa’u domin ta zama matarsa. A wannan mak’ala za a yi k’ok’arin nazarin kwatance ne na wasu daga cikin al’adun neman auren Hausawa da na Dakarkari. Don haka, mak’alar ta yi tsokaci ne a kan tsarin neman auren Hausawa da na Dakarkari  musamman abin da ya shafi wasu ke’ba’btattun al’adu kamar: soyayya a tsakanin saurayi da budurwa da zance ko tad’i da matsayin d’anrakiya da matsayin iyaye da al’adar na-gani-ina-so da dai sauransu. Da yake muk’alar ta shafi al’adun al’umma biyu ne, don haka, an yi k’ok’arin kawo bambanci da kamancin tsarin yadda ake aiwatar da wad’annan al’adu. A k’arshe mak’alar ta yi k’ok’arin bayanin wasu hikimomi ko falsafar da ke tattare a cikin wannan rumbu na al’adun neman auren Hausawa da na Dakarkari.

 

1.0 GABATARWA


Neman aure  a al’adar  al’umar Hausawa da na Dakarkari abu ne da ke tattare da kai-komo na iyaye da saurayi da budurwa . Wannan kila shi ya sa Hausawa ke masa kirari da cewa: Aure marmari daga nesa, ko Aure wane yaro, ko Ba neman aure ke da wuya ba shiga da fita. Wannan ya nuna muna cewa akwai gwagwarmayar da mai neman aure zai yi ta cin karo da su a lokacin neman aurensa. Don haka, mallakar mace ga al’umar Hausawa da na Dakarkari ba k’aramin aiki ba ne, sai namijin gaske . Duk da yake, kafin zuwan addini, Hausawa na da wasu hanyoyi na mallakar mace kamar : Neman aure da yak’i da samame da hari da cire da tsituwa da bashi da saye da kyauta da kwartanci.

Al’umar Hausawa da na Dakarkari al’uma ce da ke da dad’ad’d’iyar dangantaka da cud’anya a tsakaninsu mai dad’ad’d’en tarihi. Don haka, wannan mak’ala za ta yi k’ok’arin nazarin wasu daga cikin al’adun neman auren Hausawa ne da na Dakarkari . Da yake al’adun aure yawa ne da su, don haka, wannan mak’alar ta tak’aita ne ga irin gwagwarmayar da ake yi a wurin aiwatar da wasu daga cikin al’adun neman auren wad’annan al’umma guda biyu (Hausawa da Dakarkari).

A k’ok’arin nazarin wad’annan al’adu ,wannan mak’alar ta yi nazarin yadda ake aiwatar da kowace al’ada daga al’ummomin Hausawa da na Dakarkari. Bayan wannan, mak’alar za ta yi k’ok’arin kawo irin kamance-kamance da kuma bambance-bambancen da ake samu a lokacin aiwatar da wad’annan al’adu a tsakanin wad’annan k’abilu biyu. Haka kuma , yana daga cikin manufar wannan mak’ala ita ce, zak’ulo wasu hikimomi ko falsafofin da ke tattare da aiwatar da wad’annan al’adu a tsakanin k’abilun Hausawa da na Dakarkari

Daga cikin al’adun neman auren da za a yi nazari a wannan mak’ala sun had’a da: soyayya da zance ko tad’i da matsayin iyaye da isa gida da gaisuwar abokai da al’adar na-gani-ina-so da sauransu.


  1. 0 Ma’anar Aure:
A gaskiya zai yi wuya kai tsaye a ce ga ma’anar aure guda d’aya kar’ba’b’be kuma gamsasshe ga al.uma baki d’aya.Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da ganin cewa kowace al’umma tana da yadda ta d’auki aure ba .Bisa ga wannan ne masana ilimin zamantakewa da d’aliban al’adun al’umma musammam na Hausawa da na Dakarkari suka kawo ra’ayoyinsu dangane da ma’anar aure .Misali Habibu Alhassan da wasu (1980) sun had’a hannu suka bada ma’anar aure kamar haka:

Aure alak’a ce ta halaccin zaman tare

tsak’anin namiji da mace. Ana yin sa ne saboda

abin da aka haifa ya sami asali da mutunci da

kiwon iyaye. Kuma shi ne maganin zina da ‘ya’ya

marasa iyaye.

Wannan ma’anar ta nuna aure zamantakewa ce a tsakanin namiji da mace tare da amincewar juna .Amma ita kuwa Fatihiya Migdad Sa’ad (1998:196) tana da ra’ayin aure a musulunci kamar haka:

Aure shi ne halaccin zaman namiji da mace

tare da cika wasu dokoki , tare da  ba kowa nasa

hakkin zamantakewa a tsakaninsu. Wannan

yarjejeniyar ta zama tare kuma za a yi ta bisa

koyarwar addinin musulunci wanda ake samu

a cikin al’kur’ani da hadisan manzon Allah(SAW)

 

Haka ma M A Rauf (1970:78) ya bayyana cewa; bisa ga shari’ar musulunci aure shi ne :

K’ulla wata yarjejeniya da za ta haifar da

halalcin saduwa da mace dasamun zuri’a.

Kuma wani bangare ne na mu’amula da ibada.

 

Harwayau, wasu masana zamantakewar al’umma (sociologist) sun kalli aure ta wannan fuska. Misali: Burgess da Locke (1953) sun bayyana aure da cewa:

 “  Zamantakewa ce ta amincewar mutum d’aya ko fiye da d’aya ko mace d’aya ko fiye da d’aya mai dangantakar mata da miji”.

Anan muna ganin cewa,  ga tasu fahinta ba dole bane aure ya kasance a tsakanin mace da namiji. Domin ana iya samun inda mace zata auri mace, namiji kuma ya auri namiji domin wasu al’adu ba su hana haka ba . Amma a ra’ayin wani masanin Dr Wester Mark (1984) yana cewa: “Akwai muhimmam abubuwa uku ga kowane aure, sune biyan buk’ata na kwanan aure da dangantaka a tsakanin namiji da mace da kuma domin samun zuri’a (haihuwa)”                              Bisa ga wad’annan ra’ayoyi da ke sama dangane da ma’anar aure  , anan muna iya cewa aure alak’a ce ta zamantakewa tsakanin mace da namiji bisa ga amincewar juna tare da bin wasu k’a’idoji da addini ko al’ada ta aminta da su.

Don haka, aure a al’adar Hausawa da na Dakarkari al’ada ce mai muhimmanci tattare da wasu hikimomi na musamman a cikin al’umma. Daga cikin falsafar yin aure ga al’umar Hausawa da na Dakarkari sun had’a da : Bunk’asar arziki da samun ‘ya’ya(d’iya) da tushen zuri’a da nuna kamala da zumunci da biyan buk’atun aure da sauransu.

3.0 TSARIN NEMAN AUREN HAUSAWA DA NA DAKARKARI


3.1 Soyayya Tsakanin Saurayi Da Budurwa

Soyayya ita ce  k’auna  ta wani mutum ko wani abu daban. A zahiri an fi amfani da wannan  tsakanin namiji da mace musammam saurayi da budurwa. Soyayya  a harkar aure wata aba ce mai nuhimmancin gaske ga auren Hausawa da Dakarkari. Idan babu soyaya da wuya a iya zaman aure , don haka soyayya ita ce k’ashin bayan zaman auren Hausawa da na Dakarkari. Duk da yake ana iya samun zaman aure ba tare wata soyayya ba.

3.1. 1 Tsarin soyayya a al’adar Hausawa:

A al’umar Hausawa, tsarin soyayya ta taka muhimmiyar rawa a tsakanin saurayi da budurwa. Galibi wannan soyayyar ita ke k’ara dank’on zama tare wanda zai haifar da aure. Bincike ya gano cewa, al’umar Hausawa suna da soyayya iri biyu ne zuwa uku .Ga su kamar haka:

  • Soyayyar da ke haddasuwa saboda had’uwar jinni tsakanin saurayi da budurwa. Wannan yana iya shafuwar k’irar jikin saurayi ko budurwa.

  • Soyayya saboda hali, ma’ana d’abi’ar mutum

  • Soyayya saboda hali (arziki) watau ana samun ginuwar soyayyar Bahaushe saboda irin arzikin gidan saurayi ko budurwa.


Duk wad’annan soyayya suna ginuwa ne yayin da saurayi zai rink’a ganin budurwa yana yi mata wata ‘yar k’yauta. Bincike ya gano cewa amfi samun soyayya ta zahiri a tsakanin saurayi da budurwa kafin zuwan addini. Don haka, muna iya cewa soyayya  a wannan zamani ta yi k’aranci, don an maye ta da sha’awa . Za ta yi yu saboda rashin wannan soyayya ake samun yawaitar mutuwar aure a cikin al’umar Hausawa a yau. Domin ita sha’awa gushewa ta ke, amma soyaayya ba ta gushewa. Hasali ma soyayyya ga Bahaushe a wancan lokacin ta dogara ne a kan irin bajinta da kirkin saurayi, domin ba a duban arzikinsa balle a dubi abin da za a samu daga cikin arzikin .

Wani abin kulawa anan shi ne , ga al’adar Bahaushe saurayi ke ganin budurwa ya ce yana so,; duk da yake a al’adance Bahaushe bai yarda saurayi ya rink’a cud’anya da ‘yanmata a tsakaninsu ba .Don haka lamarin soyayya abu ne mai muhimmamci ga zamantakewar neman auren Hausawa.

3.1.2 Tsarin Soyayya a al’adar Dakarkari:

Kamar Hausawa , su ma Dakarkari suna da tsarin soyayya wadda ke wanzuwa a tsakanin saurayi da budurwa musamman a lokacin da samarin Dakarkari ke aiwatar da wata al’ada ta “Golmo” . Duk da yake wani lokaci ana samun auren da iyaye kan tilasta ‘ya’yansu ba tare da soyayya ba, amma galibi Dakarkari suna aurensu ne don soyayya. Duk da yake a yanzu ana samun masu auren sha’awa.

Ga al’adar Dakarkari, budurwa ce ake neman soyayyarta .A k’ok’arin samun soyayyar yarinya saurayi kan shiga aikin “golmo” tun yana da shekaru goma sha biyar (15) zuwa sama. Yin wannan aiki na golmo yana k’ara dank’on soyayyar. Wannan kuma na faruwa saboda irin bajinta da dauriya da hank’urin da saurayi kan nuna wajen ayyukansu na yau da kullum. Haka a soyayyar Dakarkari tana da walwala domin ba su kange cud’anya tsakanin saurayi da budurwa ba.

3.1.3 Bambanci Da Kamancin Tsarin Soyayyar Hausawa Da Na Dakarkari:

Kamar yadda bayani ya gabata a baya , al’umar Hausawa da na Dakarkari duk suna aiwatar da wannan al’ada ta soyayya. Amma ba a rasa wasu ‘yan bambance-bambance ba, haka kuma ta wata fuska sun yi kama da juna.

Da farko dai abin da ya bambanta tsarin soyayyar Dakarkari da Hausawa ita ce walwalar soyayya. Domin a al’adar Hausawa ta hana cud’anya tsakanin saurayi da budurwa, amma su Dakarkari ba su hana wannan ba.

Ta fuskar kamanci kuwa , Dakarkari suna gina soyayyarsu ne ta hanyar golmo inda ake gane bajinta da dauriya da hank’urin saurayi .Ga al’ada duk saurayin  badakkaren da ya kasa yin golmo, to ya yi abin kunya ko zagi a cikin al’umma . Kuma da wuya a samu budurwar da za ta so shi . Wannan kuwa muna iya ganinsa idan muka dubi wasu al’adu na Hausawa kamar d’auko maiki na maguzawan kwatarkwashi. Haka kuma, kamar Hausawa su ma Dakarkari ana samun sha’awa a tsakanin saurayi da budurwa,  amma wannan bai zama hujjar cewa ba su auren soyayya ba .

3.1.4 Falsafa ko Hikimar Da Ke Cikin Al’adar Soyayya

Bisa ga bayanan da aka yi na tsakuren al’adar soyayya, muna iya fahintar cewa, akwai wasu falsafa ko hikima na aiwatar da wannan al’ada ga Hausawa da Dakarkari. Za ta yiyu saboda wannan ne ya sa al’umar ba su cika yin aure ba sai an tabbatar da akwai soyayya a tsakanin saurayi da budurwa .

Da farko dai za mu  ga cewa, tana kawo sanin halin juna . Idan kuwa aka samu matsalar soyayya ,to tun a wannan lokacin ne ake rabuwa . Haka kuma cikin wannan lokacin ne ake samun gyaran halayen juna . Bayan wannan , ta wannan zaman soyayya  ne ake auna irin hank’urin juna da dauriya da sauransu a tsakanin masoya.

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/waibuwar-masunta/
3.2 Zance ko Tad’i

Wannan shi ne zuwa hira da saurayi kan yi a gidan budurwa ko wani muhalli na daban da suke had’uwa a wani lokaci na musamman . Galibi a irin wannan hirar(zance) ana tattauna lamurran yau da kullum ne.

3.2.1 Tsarin Zance A Al’adar Hausawa

Hausawa sun ba wannan al’ada muhimmanci sosai . Don haka, sun tanadi wani tsari na musammam domin aiwatar da ita. Kuma ganin cewa, Hausawa sun fahinci irin hatsarin da ke tattare da wannan al’ada ,sai suka tanadi lokaci da wuri na aiwatar da wannan al’ada. Domin ba su yarda su bar ‘ya’yansu ba tare da sa ido da jagoranci ba. Da farko za mu ga cewa wannan al’adar sai da dare ko yamma  ake yin ta, kuma galibi gidan budurwa ake zancen, inda ake samun gidin bishiya ko zauren gida.

Haka kuma, Bahaushe na da tsarin zuwa da ‘yar rakiya, kuma al’ada ba ta yarda saurayi ya rink’a zuwa zance kullum ba , don haka galibi an fi zuwa zance ranar kasuwar garin . Kuma Hausawa na da al’adar bada kud’in jin-kira . Amma duk da wannan, Bahaushe na da wata al’ada ta tsarance inda saurayi zai rink’a zance da budurwa har ta kai su kwana d’aki d’aya ,amma saboda gaskiya da aminci ba za su san juna ba .

3.2.2 Tsarin C’mene (Zance) A Al’adar Dakarkari

A al’adance Dakarkari ba su hana cud’anya a tsakanin saurayi da budurwa ba ,don haka ba su ke’be wani lokaci ko wuri na musammam da za su had’u ba . Dakarkari a wancan lokacin kafin zuwan addini suna had’uwaa duk lokacin da suka ga dama amma wani abin kunya baya faruwa a tsakaninsu. Saboda irin wannan aminci ne ya sa Dakarkari suna wata al’ada wurin neman aure wadda ake kira “c’mene”(tsarance).A wannan lokacin zancen, saurayi da abokansa suna k’ok’ari ne su k’ara dank’on soyayya a tsakaninsu. Don haka, a al’adar Dakarkari ba su amfani da kud’in kira; duk da yake a yanzu ana samun wannan jefi-jefi.Kuma galibi raha ne da barkwacci ake yi ma juna. Amma duk da rashin k’angin  da ba  a yi wa saurayi ba na ganin budurwarsa duk lokacin da ya ga dama, bai hana sa ido ga iyayensu ba .

3.2.3 Bambanci Da Kamancin Tsarin Zance A Al’adar Hausawa Da Na Dakarkari

Abin da ya bambanta su ta fuskar tsari shi ne, su Dakarkari ba su kange saurayi daga zuwa wurin budurwa ba a kowani lokaci ko wuri na musammam ba. Haka kuma Dakarkari ba su kange cud’anyar saurayi da budurwa ba a kowani lokaci.

Ta fuskar kamanci kuwa, anan za mu ga tsarin zuwan saurayi gidan budurwa da na d’an rakiya da kud’in jin –kira (kindin c’pogo) duk wad’annan ana samunsu a cikin al’adun zance na Hausawa da na Dakarkarkari.

3.2.4 Hikimar Da Ke Cikin Tsarin Zance A Al’adar Hausawa Da Na Dakarkari:

Akwai hikimomi da yawa da ke tattare da wannan al’ada ta zance a tsakanin Hausawa da Dakarkari. Daga cikinsu kuwa sun had’a da; Cusa soyayya a tsakanin saurayi da budurwa,don yana basu damar fahintar juna da tattauna muhimmam zantuka a tsakaninsu .Kuma wannan shi ke nuna ma jama’a ba su da wata muguwar manufa a tsakaninsu . Domin ga al’ada, duk sauaryin da baya iya zance a gidan budurwarsa to yana da wata muguwar manufa, kuma ba auren yake nema ba. Kuma idan budurwa ba ta fita zance wata alama ce ta nuna ba ta son saurayin . Don haka zance wani ma’auni ne na soyayya.  Haka kuma idan muka dubi lokaci da wuri , wannan lokacin iyaye sun dawo gida suna ganin duk wanda zai zo gidansu. Kuma wanan lokacin an ba saurayi da budurwa damar taimaka ma iyayensu wasu ayyukka da rana. Kuma wannan na nuna kunyar surukkai.

Ta fuskar amfani da d’an rakiya kuwa, shi d’ansanda ne mai kawo rahoton duk abin da ya faru tsakanin saurayi da budurwa .Haka kuma yana zama d’an sak’o a lokacin zance, yana kuma kare kad’aitar saurayi da budurwa , domin a wannan lokacin tana d’an yin wasa da shi,don haka za ta fi d’aukan lokaci tana zancen. Bayan wad’annan,d’an rakiya yana taimakawa wajen kai bante.Su kuwa kud’d’in jin- kira (kindin c’pogo) suna k’ara soyayya domin Hausawa na cewa: “Hannun da ke kar’ba ba ya cewa a’a” Kuma k’yautar tana k’ara martaba da daraja a idon budurwa da gidansu.

Bisa ga wannan dan tsokaci, za mu fahinci al’adar zance ta taka muhimmiyar rawa wajen gwagwarmayar neman auren Hausawa da na Dakarkari.

3.3 Matsayin Iyaye Wurin Neman Aure

Bisa ga tsarin neman auren Hausawa,  iyaye suna da muhimmanci. Da yake aure al’ada ce da ake yi domin zaman rayuwa baki d’aya, don haka, al’adar Bahaushe an aza ma iyaye hak’k’in neman ma ‘ya’yansu matar aure. Don haka, iyaye suna bid’an ma ‘ya’yansu aure a gida mai asali domin su suka san tarihin gidajen, kuma suna da masaniyar halin tarbiyar gidan. Anan iyaye suna kulawa da wannan ne domin kaucewa gur’bata zuriyarsu da wani jini mai tarihin wani abin kunya. Misali sata ko wata cuta ta musamman kamar kuturta.

Haka kuma, a lokacin neman auren, iyaye suna duban inda yarinya za ta samu abinci. Domin abin kunya ne ga Bahaushe ya bada aure ga gida wanda ba ya ciyar da matarsa. Za ta yi yu domin tabbatar da wannan ne ake yin al’adun  bikin d’auko Maiki a kwatarkwashi ta yankin Zamfara a matsayin wani ma’auni na nuna jarumtar saurayi.

Iyaye suna bada shawarwari kuma ga su da cika fuska da iya gabatar da Magana.

3.3.1 Fitowa gida (Bid’ar Iyaye) A Neman Auren Hausawa

Iyaye suna fitowa bid’ar aure ne idan sun tabbatar da mutuncin gidan da za su neman auren. Anan idan za su fita sukan ta fi da goro da ‘yan wasu kud’i da za a aza sama. Kuma mafi yawa akan samu dattijai ne ‘yan uwa su kai wad’annan kaya. Duk da yake a yanzu ana samun   masu bada auren ba tare da sanin dangin uwa ba balle na uba. Bisa ga tsari, idan iyaye suka isa gidan yarinya, bayan sun gaisa sai su bayyana abin da ke tafe da su.musamman kuma ana wannan neman ne a wurin iyayen yarinya ko wani danginta na jini kuma namiji. A wannan lokacin sai iyayen yarinya suma su fad’i nasu bayani na amincewarsu ko rashin amincewarsu. Duk da haka, wani lokaci tun yarinya na ciki ko jaririya ake fara neman aurenta ta hanyar ba da zobe da za a sanya mata mai nuna an yi kammenta kenan.

3.3.2 Gaisuwar Abokai

Wannan wani mataki ne daga cikin tsarin neman auren Hausawa. Abokai su ne wad’anda mutum ke zaune da su lafiya suna yawo tare da cin abinci tare da dai sauran mu’amaloli. Ita wannan al’ada ana yin ta ne bayan saurayi da budurwa sun sasanta kansu da niyyar auren juna, kuma iyaye sun isa gida neman auren an kuma amsa saurayin ya ci gaba da neman auren. Anan ne saurayi zai samu abokansa domin su fito gaisuwa.A irin wannan lokacin ne ake tura aboakai gaisuwar sanin dangin yarinyar. A al’adance idan za a tafi wannan gaisuwar, ana zuwa da goro ne da wasu ‘yan kud’i wanda za su rink’a bayarwa. Kuma lokacin wannan gaisuwar, saurayin da ke  neman auren baya magana sai dai abokansa su yi. Wannan al’adar ana yin ta ne domin gabatar da saurayi ga sauran dangi domin su san sa, shi kuma ya san su.

3.3. 3 Tsarin Neman Auren (c’gai) Dakarkari

Lelna (Dakarkari) sun ba aure muhimmanci, don haka sun shimfid’a wani tsari na neman aure tun kafin zuwan addini. Bisa ga al’ada, Dakarkari suna da hanyoyi da dama na neman aure. Daga cikin su kuwa, akwai ta hanyoar iyaye da kuma tsakanin saurayi da budurwa.

Ta hanyar iyaye: Dakarkari sun ba iyaye daraja sosai ta yadda aka bar masu ragamar neman  ma  ‘ya’yansu aure. Domin a al’adance yaro bai da iznin neman ma kansa aure. Tadurga U.,(1997) yana cewa:

Idan aka haifi yarinya a gida,

idan akwai tsohon da ke son neman

wa d’ansa, yana iya shaida wa iyayen

wannan yarinya tun tana jaririya da

cewa ya kama wa d’ansa wannan

yarinya. To wannan ya tabbata domin

ba wanda zai auri wannan yarinya

sai yaron.

Irin wannan neman auren,  ana yin sa ne ta hanyar al’k’awali inda za a kama ma yaro mata ta hanyar kai wani jan zobe. Wannan zoben za a sanya wa yarinya shaidar cewa an yi mata kame.

Amma wasu Dakarkari nasu al’adar ta banbanta. Misali hirar da na yi da Ibrahim Wakaso Galadiman Rambo cewa ya yi:

za a kai masara goyo uku a gidan

yarinyar kame, idan wata shekara ta dawo

a kai biyar. Anan uban yarinya zai

samu kud’i wuri uku, a samu d’an

k’warya a sa a ciki, idan an kai

wannan kayan, to rannan ne aka

tabbatar da kamen auren.

 

Yin wannan shi ya tabbatar da cewa, iyayen suna son had’a jini da juna. Ya k’ara da cewa, bayan an tabbatar da kamen idan yaro ya kai shekara goma sha shida zuwa ashirin ne zai shiga golmo. Daga nan sai a samu kwandon dawa a kai gidan sarukkai.

Ita wannan al’ada ta golmo wata bauta ce da saurayi yake wa surukkansa na tsawon shekara bakwai ko k’asa da haka. A wannan lokacin golmo (nema), saurayi zai rink’a zuwa gonar surukkai tare da takwarorinsa suna noma. Idan rani ya yi, ya yo masu hakin baibayan d’aki. Sai dai a yanzu akwai damar idan saurayi ba zai iya cika shekarun bakwai ba, sai a yanka masa wasu kud’i ya biya a madadin sauran shekarun da ba zai yi golmo ba.

A hirar da na yi da mai unguwar Zuttu (maigari kwai-masa) cewa ya yi:

Iyaye su ne ke bid’an ma yaransu aure,

duk da yake yanzu yara suke neman

ma kansu aure musamman a wurin bukukuwa

ko kasuwanni. Amma mai bid’a ba ya kai

komai sai iyaye sun had’a kansu.

 

Ya k’ara da cewa bayan an samu had’uwar kan iyaye za a kai wasu kaya da ake cema ‘uv-kwanta’  inda ake samun turmin Atamfa da Sabulu da Mai a samu wata tsohuwa da wasu daga cikin dangi a kai gidan yarinya. Daga nan ne saurayi zai shiga golmo bayan ya yi ‘yadato’ na k’are samartakansa.

Amma mafi yawa a yanzu, saurayi ke fara neman wa kansa aure ta hanyar sasantawa tsakaninsa da budurwar. Daga baya a tura iyaye gidan budurwa neman auren.

Bisa ga wannna za mu fahimci Dakarkari suna da tsarin neman aure kusan bai d’aya da na Hausawa musamman idan muka dubi matsayin Iyaye da fitowar Iyaye da gaisuwar abokai da sauransu.

3.3.3 Bambanci da kamancin tsakanin neman auren Hausawa da na Dakarkari.

Al’umar Hausawa da na Dakarkari suna da cikkaken tsari na neman aure. Kuma mafi yawan tsarin ya yi kama da juna illa wasu ‘yan wurare da ba  a rasa ba.

Ta fuskan bambanci, abin da ya shafi gaisuwar abokai; Hausawa suna zuwa da goro da wasu ‘yan kud’i a sama. Amma su Dakarkari ba a zuwa da komai.

Ta fuskar kamanci kuwa, anan za mu ga cewa dukkan k’abilun, iyaye sun taka muhimmiyar rawa wajen neman aure, kana sun amince a nemi yarinya aure tun ana da cikinta, wani lokaci kuwa sai bayan ta yi wayo. Haka kuma, a dukkan k’abilun iyayen namiji ne ke zuwa wurin iyayen yarinya neman aure; kuma a wannan lokacin iyayen na zuwa da wata ‘yar kyauta ga dukkan k’abilun. Bayan wannan kuma, a lokacin neman samari suna yi ma gidajen surukkansu wata ‘yar bauta (golmo ko gayya)  da dai sauransu. Don haka anan za mu ga cewa wad’annan al’adu sun yi kama da juna k’warai da gaske.

3.3.4 Falsafar Da Ke Cikin Tsarin Neman Auren Hausawa Da Na Dakarkari

Bisa ga al’ada, Hausawa da Dakarkari sun ba neman aure muhimmanci sosai. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da irin hikima ko falsafar da ke tattare da wannan tsari na neman auren ba.

Da farko dai za mu ga cewa, falsafan sanya iyaye wurin neman aure shi ne cewa: Su ke da tarihin kowane gida domin sun ga jiya sun ga yau. Da yake Bahaushe ko badakkare baya son had’a jininsa da wani jini wanda ke da tarihin wani abin kunya. Kuma iyaye suna za’ben gida mai tarbiya, domin ga al’ada ba a barin yara kara zube ba tare da jagorancin iyayensu ba. Kuma iyaye suna duban halayen yara domin gane cancantarsu ko rashin cancantarsu. Wata falsafa kuma ita ce, k’ara fahimtar juna da nuna soyayya tun kafin auren. Wannan na haifar da kyautata halayen saurayi da budurwa. Haka kuma gaisuwar abokai na tabbatar da maganar da iyaye suka yi a lokacin da suka fita nema wa d’ansu mata. Wannan gaisuwar tana nuna yaron ya amsa shi ma yana son yarinyar. Kuma a wanan lokacin yana sa iyaye su san surikinsu musamman abin da ya shafi k’irar jikinsa, irin kaifin hankalinsa da dai sauransu.

3.4. 1 Tsarin Na-Gani-Ina-So A Al’adar Hausawa

A  al’dar Hausawa, bayan Magana tsakanin saurayi da budurwa da iyayen yaro da na yarinya ta zauna , watau an amince wa juna. Daga nan ne za a kai kayan Na-gani-ina –so, su wad’annan kayan galibi ana samun wasu dattijai maza ko mata ne su kai wad’annan kayan . za’ben dattijai ba zai rasa nasaba da irin matsayinsu a cikin al’umma ba, domin sun fi sanin irin lafuzzan da za su yi amfani da su. kuma galibi wad’annan kaya ana had’awa da ‘yan wasu kud’i da goro a ciki, sauran kayan sun had’a da tufafin sawa da na kwalliya. Anan yawan kayan ya danganta ne da irin k’arfin arzikin gidan saurayi.

Bayan an kai wad’annan kayan ne za a dawo da bayanin da aka samo daga gidan budurwa dangane da kayan.Wad’ananan kayan za a rink’a yawo da su gida-gida ana nuna ma dangin yarinya , wani lokaci ma, goro da kud’in da aka aza sama ana rabawa sauran dangin shaidar cewa ‘yarsu ta sami masoyi . Duk da yake kafin shigowar addini, Hausawa suna amfani da kayan gona ne da wuri a matsayin kayan na-gani-ina-so.

3.4.2 Tsarin Na-gani-Ina-so A  Al’adar Dakarkari

Dakarkari su ma suna da tsari na musammam dangane da al’adar na-gani-ina-so.  Duk da yake ana samun bambance bambance tsakanin wannan yanki na Dakarkari zuwa wancan.  Bayan saurayi da budurwa da iyayensu sun amince da juna, magana ta zauna.  Daga nan ne za a kai wad’annan  kayan rik’o . Duk da yake wani lokaci iyaye na kai kayan ba tare da sanin saurayi ko budurwa ba. Domin  a  al’adance yara ba su da ikon kansu sai abin da iyaye suka zantar a kansu.

A wani sashe na Dakarkari kuwa, iyaye suna kai kud’i wuri ashirin da jan zobe wanda za a sanya wa yarinya a matsayin shaidar ana kamenta. A wajen Dakarkarin Rambo kuwa, ana fara kai masara goyo uku, idan wata shekara ta zagayo a kai masara goyo biyar. Haka kuma uban yarinya zai samu kud’i wuri uku ya kai, yin wannan shi ke tabbatar da kamen yarinya . Bayan saurayi ya kai shekara ashirin sai ya kai kwandon dawa gidan surukkansa. Haka kuma, zai yi asabari biyu ya kai gidan surukkansa.Amma a yanzu bayan shigowan addini, Dakarkari suna amfani da kudi ne da wasu ‘yan kaya na sawa da na shafe-shafe a matsayin kayan na-gani-ina-so.

3.4.3 Bambanci Da Kamancin Tsarin Na-gani-Ina-so A Al’umar Hausawa Da Na Dakarkari.

Bisa ga al’ada musamman kafin shigowan addini,  bincike ya gano cewa, kusan duk tsarin aiwatar da wannan al’ada ta na-gani-ina-so d’aya ne tsakanin Hausawa da Dakarkari sai dai d’an abin da ba a rasa ba.

Da farko dai za mu ga cewa dukkan Hausawa da Dakarkari suna amfani da kayan gona da zobe kafin zuwan addini, kuma wad’annan kayan gona sun danganta da irin wad’anda ake nomawa a kowani yanki . Kuma dukkan k’abilun suna sanya iyaye dattijai wurin kai kayan na-gani-ina-so. Ta fuskar lokacin kai kayan kuwa, duk tsari d’aya suke bi, domin ba a kai su sai an tabbatar da soyayya a tsakanin iyaye da saurayi da budurwa.

Bayan haka, d’aukan kayan yana nuna an kar’bi manemin, rashin d’auka kuwa yana nuna manemin bai samu kar’buwa ba. Wannan tsarin kuwa duk d’aya ne a tsakanin al’umar Hausawa da Dakarkari.

3.4.4 Falsafar Al’adar Na-gani-ina-so A Al’umar Hausawa Da Dakarkari

Dangane da falsafar da ke tattare a cikin wannan al’ada kuwa , gasu kamar haka:

Da farko dai wannan wata alama ce mai tabbatar wa iyaye da sauran dangi cewa ‘yarsu ko d’ansu ya samu masoyi . Domin wad’annan kayan na-gani-ina-so su ake rabawa sauran dangi su shaida cewa an fito gida neman ‘yarsu.

Wata falsafa ita ce , kar’bar wannan kayan na nuna irin kar’buwar da saurayi ya samu a gidan budurwa. Domin a al’adar Bahaushe, idan aka bada tukuici, to ya samu kar’buwa, idan kuwa aka kar’bi kayan  aka ajiye ba tare da wata Magana ba , wanna yana nuna akwai shakku ga mabid’in. Amma idan aka tsaya binciken kayan, yana nuna dama akwai wani mabid’i. Anan za mu fahinci wad’annan kayan tamkar wani madubi ne da manemi zai kalla ya san matsayinsa.

Kayan ga Hausawa da Dakarkari, suna matsayin nizani na auna arzikin mabid’i. Don haka, kayan suna k’ara ko rage darajjar mabid’i a gidan yarinya ko al’umma baki d’aya. Musammam idan muka dubi yadda ake yawo da kayan ana gwada ma dangi. Kuma wad’annan kayan suna k’ara dank’on soyayya a tsakanin saurayi da budurwa . Yawansu na sa budurwa alfahari , amma idan ba su cika ido ba, za a ji nauyin bayyana su.

A al’adance wasu na ganin ana iya auna arzikin yarinya tun daga irin kayanta na na-gani-ina-so. Domin idan ta samu kaya masu yawa , to wannan wata alama ce mai nuna budurwar tana da k’ashin arziki, idan kuwa kayan ba su cika ido ba , to wannan na nuna ba ta da k’ashin arziki.

https://www.amsoshi.com/2017/06/21/187/

4.0 Kammalawa


Al’adun alumma sun bambanta daga wannan al’umma zuwa waccan. Haka al’adun aure suna da yawa, kuma kowace al’ada akwai yadda kowace al’umma ke aiwatar da ita. A wasu al’adun sukan d’auki tsari d’aya wajen aiwatarwa, wasu kuwa ana samun wasu ‘yan bambance-bambance wajen aiwatar da su a tsakanin wannan al’umma zuwa wata al’umma.

Bisa ga abin da wannan mak’ala ta yi d’an tak’aitaccen bayani a kansu, za mu ga cewa an yi k’ok’arin kawo wasu daga cikin gwagwarmayar da ake yi lokacin neman auren Hausawa da na Dakarkari. Don haka, an za’bi wasu al’adu ne aka yi bayaninsu sama-sama. Daga cikin al’adun da aka duba sun had’a da: Al’adun soyayya a tsakanin saurayi da budurwa da zance ko tad’i da matsayin d’anrakiya da matsayin iyaye da al’adar na-gani-ina-so da sauransu.

Muk’alar ta yi k’ok’arin kawo kamanci da bambance-bambancen da ake samu wurin aiwatar da wad’annan al’adu a tsakanin al’umar Hausawa da na Dakarkari. An yi k’ok’arin kawo wasu hikimomi ko falsafar da ke damfare a cikin wad’annan al’adu a tsakanin wad’annan alummomi.

A k’arshe bisa ga d’an abin da  wannan mak’ala ta yi bayani a kai , za mu fahinci cewa al’umar Hausawa da na Dakarkari suna da tsari kusan iri d’aya da juna musamman abin da ya shafi al’adun neman aure da falsafar da ke cikin aiwatar da wad’annan al’adun a tsakanin al’ummominsu. Ba shakka, wannan nazarin zai k’ara sa fahintar juna wanda zai haifar da zamantakewa mai inganci da nagarta ba tare da kushe wa juna ba a tsakanin wad’annan al’ummomi.

 

MANAZARTA


Aishatu A. 1988. ‘Marriage system in Funtua Town: Problems and their Islamic Solution’ B A Project .Department of Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Al’hassan B etal. 1977. Zaman Hausawa. Zaria. Northern Nigerian Publishing Company.

Augi A R and Lawal S U (eds) 1990. Studies in the History of the People of Zuru Emirate. Enugu: Fourth Dimension.

Bunza A M. 1990. ‘Hayak’i Fidda Na Kogo’. Kundin shaidar neman digiri na biyu. Sashen Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayaro Kano.

Burgess and Locke.1953.The Family .2nd (ed). New York American Book Co.

Dangambo Abdulk’adir, 1984. Rabe-Raben Adabin Hausa Da Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company.

Fatihiya Migdad Sa’ad. 1998. ‘A comparative Study Of Marriage In Two Muslim Communities: Hausa and Swehili’ M A Dissertation, Islamic Studies Department, Usmanu Danfodiyo University,sokoto.

Fortes Meeyer. 1962. Marrieage In Tribal Soceities. London: Cambrige University Press.

Goody J .1971. Class and Marriage In Africa. Eurasia New York American Journal Of Sociology.

Haris P G. 1930. ‘Note on the Dakarkari People 0f sokoto provence’ Nigeria: Journal of the Royal Anthropological Institute, vol 68

Madauci I .1975. Hausa Custom. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

Magaji A. 2002. ‘Wasu Al’adun Hausawa : Yanaye-Yanayensu a k’asar Katsina’ Phd thesis. Bayero university Kano.

Tadurga U A .1997. ‘Tasirin Hausa a kan Tsafe-tsafen Dakarkari a k’asar Zuru. B A Project, Nigerian Langauges Department,  Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Umar M A .1990. Auren Hausawa. Zaria: Institute Of Education. Amadu Bello University, Zaria.

Ra’uf M.A.1977: Islamic View on Women and family. New York, Cambrigde Press.

Rambo R A .2007. ‘Nazari A Kan Wasu Ke’ba’b’bun Al’adun Auren Hausawa Da Na Dakarkari’. M A Dissertation , Department Of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo Univesity, Sokoto.

Wester M .1984. The Future Of Marriage In Western Civilization. Lahore

Hirarraki

Hira da Prof.A M Bunza. A gidansa ranar 23/7/2005

Hira Ibrahim Wakaso, Galadiman Rambo, A gidansa, ranar 16/01/2011

Hira da Maigari kwai-masa, a gidansa ranar 15/3/2013.