Daga


Dano Balarabe Bunza
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
Phone No. 07035141980
E Mail. danobunza@yahoo.com


MaƘalar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa juna sani na Ƙasa da Ƙasa a kan TaƂarƂarewar Al’adun Hausawa A Yau Wanda Hukumar Gidan Tarihi Da Al’adu ta Jihar Katsina ta Shirya Tare da Haďin Guiwar Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua a ranar 25-26 ga watan Yuni 2013 a babban ďakin taro na Jami’ar.Tsakure


“Ka ba manya kashi yara na ganin damarka’. Aure na cikin matakan rayuwar Hausawa guda uku kuma na farko. Wannan maƘalar ta yi tsokaci kan al’adun auren Hausawa na gargajiya da kuma nason da baƘin al’adu suka yi a cikinsu daga neman aure har zuwa kai garar biki. Takardar na ďauke da canje-canjen da suka kutso kai a cikin lamarin auren Hausawa suka yi tasiri ta fuskar taƂarƂarewa. Takardar na tare da rakiyar bayanai da misalai daga wasu makaďan bakan Hausa gwargwadon hali.

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA SHI KE SA FARIN KAI: NASON BAƘIN AL’ADU CIKIN AL’ADUN HAUSAWA TA FUSKAR AURE.

1.0 GABATARWA


Aure na ďaya daga cikin matakan rayuwa guda uku da aka sani da suka haďa da aure da haihuwa da kuma mutuwa da masana suka yi wa bante daidai kwankwasonsa ta fuskar yin bayani mai gamsarwa. Wannan bai tsaya ga al’ummar Hausawa kaďai ba, ya haďa da al’ummomin duniya baki ďaya. Wannan maƘala za ta yi tsokaci a kan nason baƘin al’adu ta fuskar aure a cikin al’adun Hausawa. BaƘin da wannan maƘala za ta yi tsokaci kansu ta fuskar nason al’adunsu na aure a cikin na Hausawa ba su zarce Turawa da Indiyawa da Faransawa, da na cikin gida da suka haďa da Yarbawa da Ibo da sauran irinsu ba. Wannan maƘala za ta kalato baƘin al’adun da suka shigo cikin na Hausawa suka yi kaka-gida a Ƃangaren lamarin aure ta fuskar taƂarƂarewa. Ga abubuwan da zan gabatar kamar haka:

2.0 MA’ANAR AL’ADA


Masana al’ada sun daďa juna sani a fagen ba da ma’anar kalmar al’ada inda wasu ma sun kawo asalin kalmar a taƘaice inda aka ce kalmar al’ada ba Bahaushiyar kalma ba ce. Aro ta aka yi daga Larabci. A Larabci tana nufin wani abin da aka saba yi ko ya saba wakana ko aka riga aka san da shi. A harshen Hausa kuwa kalmomin da suka fi kusa da al’ada su ne, sabo da gado da hali da sada da gargajiya. A Ƃangaren ma’ana kuwa, an ce “Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ďan adam tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa. A ko’ina mutum ya samu kansa duk ďabi’a da ya tashi da ita tun farkon rayuwa ya tarar da wurin da ya rayu ko yake rayuwa, ita ce al’adarsa da za a yi masa hukunci a kai. Babu wata al’umma da za ta rayu a doron Ƙasa face tana da al’adar da take bi, kuma da ita ake iya rarrabe ta da wata da ba ita ba”. Haka kuma al’ada “Wata tsararriyar kimiyyar rayuwa ce da ta shafi rayuwar mutane tun daga haihuwarsu har zuwa kabarinsu”. Falsafar al’ada da kimiyyarta ya Ƙunshi fasahar mutane da aƘidojinsu da taskar ayukkan da suke sarrafa gaƂoƂinsu da abubuwan da suka yi imani da su. Waďannan abubuwa ko dai an gaje su ne, ko ƘirƘiro su aka yi, ko an garwaya su da wasu baƘin al’adu, duk suna cikin hurumin nazarin al’ada.
Akwai Ƙanshin gaskiya a cikin zancen da aka faďa na cewa kalmomin sabo da gado da hali da sada da gargajiya sun fi kusa da ma’anar al’ada domin kowane daga cikinsu akwai abin da Hausawa suka faďa a kansa. Da farko ana cewa sabo turken wawa da kwas saba kai gida sai ya kai. Gado kuma ana yi masa kirari da cewa, ‘gadon gida alali ga raggo’ da ‘gado bai wofinta’. Shi kuma hali ana yi masa kirari da ‘hali zanen dutse’ da ‘halin mutum guzurinsa’. Sada kuma kalma ce da ake amfani da ita a cikin maganganun yau da kullum da kuma waƘa. Misali akwai wurin da ake furta kalmar sada idan ana son a nuna ko da yaushe. Ana ce wa yaro ‘Sada haka kake’. Ma’ana ko da yaushe haka yaron yake. Wannan kalma na da kusancin ma’ana da sabo. Gambo mai waƘar Ƃarayi ya furta kalmar sada a cikin waƘar da ya yi wa Tudu Tsoho inda ya ce:
Gambo:“ In nig ga Tsoho ya kula min,
:Sai in yi wurin ‘yan koli sada,
:Ina cinikin banza da wofi,
: Ko an bar min ban biyanai”.

Kalmar gargajiya kuma na fitowa a bakin makaďan Hausa domin nuni ga abin da aka gada tun kaka da kakanni. ƊanƘwairo da Sarkin Taushin Sarkin Katsina sun yi waƘa kan al’adun gargajiyar Hausawa inda suka kawo kalmar a cikin waƘoƘinsu. Ga abin da ƊanƘwairo ya ce:
ƊanƘwairo:Kar mu sake mu mance,
:Mu bi al’adunmu na gargajiya

Shi kuma SarkinTaushin Katsina ya kawo kalmar gargajiya a cikin waƘarsa kamar haka:

Gindin waƘa: Nufinta ne wasan gargajiya,
:Da za ta sa mu Ƙara fahintar juna.
A wani wuri kuma an ba da ma’anar al’ada da cewa, “Hanyar rayuwar al’umma da jinin haila da wani irin hali daban na mutum da kuma magani ko tsafi”.
A wata mai kama da wannan kuma cewa aka yi “Al’ada ita ce abar da aka saba yi yau da gobe”
Al’ada ita ce, sababbiyar hanyar rayuwa wadda akasarin jama’a na cikin al’umma suka amince da ita.
Al’ada dai ita ce dukkan hanyoyin rayuwa. Al’adar jama’a ta Ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi zaman al’umma. Don haka al’ada ta haďa da addini da ďabi’u da tsarin zaman iyali da tsarin mulki da tsarin ilmi da dai sauransu. Hanyoyin shaƘatawa da nishaďi kamar su raye-raye da waƘe-waƘe da kiďe-kiďe da sassaƘe-sassaƘe ko Ƙere-Ƙere ba su ne kawai al’ada ba.
Haka kuma, akwai wata ma’ana da wani ya ba da inda ya ce “Al’ada ita ce dukkanin cikar jimillar gwaninta ko fasahar waďansu mutane, da kuma abubuwan da suka faru gare su ko abubuwan da suka saba da su, da abubuwan da suka daraja (ba muhimmanci), da irin muradin da suke son su cimma, da kuma matsayin da suka kamala bayan shekarun da suka yi suna ƘoƘarin cimma nasara kan muhallinsu bisa ga matuƘar iyawarsu kuma domin babban amfani da fa’ida gare su.

3.0 MENE NE AURE?


Masana da manazarta sun ba da ma’anar aure gwargwadon fahimta kuma kowane aka ďauki ma’anar da ya bayar za a gamsu da ita. Ga wasu daga cikin ma’anonin aure daga masanan da manazartan kamar haka:
Aure wata hanya ce ta Ƙulla zaman tare tsakanin namiji da mace ba tare da iyakancewa ba, sai in mutuwa ta raba wanda ake tabbatarwa ta amincewar ma’aurata da waliyansu da kafa shaidu.
Aure alaƘa ce ta haliccin zama tare tsakanin namiji da mace. Ana yin sa ne saboda abin da aka haifa ya sami asali da mutunci da kiwon iyaye. Kuma shi ne maganin zina da samar ‘ya’ya marasa iyaye.

4. DALILAN DA SUKA HADDASA NASON BAƘIN AL’ADU CIKIN AL’ADUN HAUSAWA NA AURE


Babu shakka akwai dalilan da suka haddasa nason baƘin al’adu a cikin al’adun Hausawa a Ƃangaren aure. Wani abin kula a nan shi ne, dalilan sun haďa da na ciki dana waje. Na waje su ne da suka fito daga Ƙetare. Na ciki kuwa su ne na gida, wato na tsakanin Hausawa da maƘwabtansu. Ba zan tsaro waďannan dalilan tare da bayanai ba sai dai in kawo su kara zube saboda abubuwa ne da aka sani ba waďanda ke shige wa al’umma duhu ba. Daga cikin dalilan akwai: Shigowar Turawa da mulkin mallaka da auratayya cikin wasu Ƙabilu da cinikayya da canjin lokaci da gwagwarmaya da baƘin da ba Hausawa ba da sauransu.

5.NASON BAƘIN AL’ADU CIKIN AL’ADUN HAUSAWA TA FUSKAR AURE


Hausawa mutane ne da ke da al’adu na gudanar da matakan rayuwarsu guda uku da suka haďa da aure da haihuwa da kuma mutuwa. A lokacin aikata kowane ďaya daga cikin waďannan matakan rayuwa nasu, sai aka ci karo da al’adun maƘwabtansu na nesa da na kusa suka fara naso har suka nashe a cikinsu ta hanyar so da Ƙi. A nan ina nufin sun ďauki wasu da saninsu wasu kuma ba da saninsu ba domin an ce ďabi’a na satar ďabi’a.
Zancen nason baƘin al’adu cikin al’adun Hausawa na aure ba tatsuniya ba ne. Ko wanda ba Bahaushe ba aka tambaya, ko wasu al’adu sun yi naso cikin al’adun Bahaushe na aure? Zai amsa da ‘E’. Hausawa na da al’adun da suke gudanarwa a cikin lamurran aurensu a gargajiyance. Sai dai a kwana a tashi aka sami kutsowar baƘin al’adu har suka yi kaka-gida cikin na Hausawa. Ko da yake an fi samun baƘin al’adu a lokacin shirye-shiryen ďaurin aure da kuma lokacin ďaura shi. Ga bayanin wuraren da takardar ta hango naso a cikinsu da yadda nason ya kasance:

5.1 NASON ZAMANANCI CIKIN AL’ADUN NEMAN AURE


Hausawa na cewa “Zamani riga ne”. Ba shakka zamani ya kawo canje-canje masu yawan gaske a cikin auren Hausawa tun daga neman aure har zuwa ďaurinsa. Dalilin shigowar zamani ya kawo sababbin abubuwa cikin sha’anin auren Hausawa da kuma yin watsi da wasu tsofaffin abubuwan da aka saba da su. Alal misali, a zamanin da iyaye ke nema wa ‘ya’yansu aure ga iyayen yarinyar da suke son ya aura. Ba yara ke zaƂi da kansu ba a da, iyaye ke yi musu zaƂin wadda za su aura domin yaro bai san abin da ya fi cancanta gare shi ba bale ga waninsa. A kan wannan ne Hausawa suka ce “Ta yaro kyau gare ta ba ta da Ƙarko”. Ba a zancen neman aure kaďai ba, akwai nason zamananci a sauran matakan neman aure. Waďannan sun haďa da kayan toshi da kayan zance da dukiyar aure har da sa rana. Zamananci ya yi tasiri sosai domin ana sanya ranar ďaurin aure, sai yaron da ke neman auren ya ce ranar da aka saka domin ďaura aurensa ba ta yi masa ba domin wata ‘yar matsalar da ba ta kai ta kawo ba,ba tare da la’akari da yi wa iyayensa ďa’a ba. Wannan na Ƙara tabbatar da nason zamananci a cikin matakan neman auren Hausawa. Ai shi ya sa Ɗanmaraya Jos ya yi waƘar biyayya ga iyaye tare da barin saƂa musu. Ga abin da ya ce:
“‘Yan yara ku bi ma iyaye,
Ku bi malaman makaranta,
Irin haka Allah ke so”.

Bayan wannan kuma, akwai wata mawaƘiya, Fati Nijar a cikin waƘara mai suna Alan Gidigo da ta Ƙara tabbatar da zancen da ke sama, kan cewa zamani ya yi naso Ƙwarai cikin matakan neman aure na Hausawa. Ta goyi bayan ‘ya’ya mata da su yi tsaye su zaƂi wanda suke so ba wanda aka so musu ba. Ke nan a nan tana horo ne ga ‘ya’ya mata da kada su kuskura a yi musu zaƂen tumun dare. Ga abin da ta ce:
Jagora: Ke yarinya zaƂi dogo
‘Y/Amshi: Ke yarinya zaƂi dogo
Jagora: ZaƂi dogo na Ɗanwuro dokin Iyani
‘Y/Amshi: Ala gidigo”.

Idan aka yi la’akari da abin da Fati Nijar ke kira kansa za a fahimci tana yi ne domin ‘ya’ya mata su yi wa iyaye bore kan cewa zaƂar musu mazan aure da ake yi ya ishe su don haka a bari kowa ta zaƂa wa kanta mijin da take so da aure.

5.2 NASON SUTURA


Wannan ba abu ne da ke Ƃoye ba bale a yi dogon bayani kansa. Idan ba a samun sa gidan kowa da kowa, zan ce mafi yawan gidaje ana samu. Daga cikin suturun, wasu na baƘi ne wasu kuma na gida ne. Akwai nason tufafin Turawa da Larabawa da Indiyawa da Faransawa da sauransu da yawa. Wannan kuma ya faru ne sanadiyar kalle-kallen fina-finan waďannan mutane a cikin talabijin da hotunan kalanda. Ai mafi yawa daga cikin mawaƘan Hausa na fina-finai da ke wannan Ƙasa tufafinsu na mutanen Ƙetare ne musamman mata. Akwai ďinki kala-kala da Hausawa suka ďauka matsayin baƘin al’adu a lokacin bikin aure da suka haďa da fitted da umbrella da pre-fitted da gown da half gown da stella da show me your back da buba da wasila da fitted gown da sauransu. Da jin waďannan sunaye babu kokanto sunaye ne na wasu al’ummu da ba Hausawa ba. A nan ne za a ga yarinya ta ci ado, idan aka gan ta a cikin bidiyo za a zaci Ba’indiya ko Balaraba ko Baturiya idan aka yi la’akari da tufafin da ta sanya. Idan aka bincika za a tarar Bahaushiya ce wata Ƙila ma ta Kebbi ko Kano ko Katsina. Mai son gane wa idonsa ya je wuraren da aka ambata a sama a lokacin bikin aure zai tabbatar da cewa baƘin al’adu sun Ƙara wa Borno dawaki ta fuskar al’adun aure Hausawa.
Haka kuma, idan aka dubi gida Nijeriya za a ga irin saka/sanya wannan sutura ta wasu Ƙabilu ta yi naso a cikin al’adun Hausawa na aure musamman Yarbawa da Inyamurai, duk da ba nasu kaďai suka yi nason ba. Hausawanmu sun ďauki al’adar Yarbawa ta ďinka tufafi iri ďaya ba tare da samun bambanci ba a lokacin bikin aure. Yarbawa na kiran wannan Oshobe ko Anko. Bayan wannan ma abin haushi shi ne ďunkin lalaci ban a mutunci ba. Akwai wani ďunki da ake yi wa yara mata budare mai suna sakaďa-hannunka–masoyi a inda za a iya ganin hamutar yarinya ko da daga nesa bale kusa. Akwai a matse Ƙugu. Akwai irin waďannan ďunkuna da yawa Ba wannan kaďai ba. Zamani ya yi sanadiyar canje-canje masu yawan gaske a cikin al’adun Hausawa na ta fuskar aure. Haka kuma, al’adar Ƃarnar kuďi a Ƃangaren ďunka tufafi a lokacin bikin aure ya zan yayi. Kai! Kitson da ‘yan mata ke yi ma ba na Hausawa ba ne a lokacin bukukuwan aure. Ko dai ya kasance na Yarbawa ko na Ibo ko wasu Ƙabilu na daban, kuma kowane da nasa suna. Duk abin da aka faďi a Ƃangaren mata ana samun wani abu a na maza sai dai, abubuwan sun fi naso a Ƃangaren dangin Shaiďan (mata). Haka kuma a Katsina akwai wata fita da ake kira Arabian night inda ake yin fitar Larabawa a lokacin bikin aure. A Ƃangaren maza jallabiya fara suke sanyawa mata kuwa baƘa suke sanyawa. Don gudun faruwar wannan ne Sarkin taushin Katsina ya yi wata waƘa ta ‘FESTAC 77’ inda yake horon Hausawa yara da manya yana cewa:

Jagora:Yara-yara ‘yan makaranta,
: Manya da ƘanƘananku ku ďau horona
‘Y/Amshi: Ku kama al’adu na iyayenku
: Kar ku yarda da aikin banza
Jagora: Sai ku kama al’adu na iyayenku,
‘Y/Amshi: Kar ku yarda da aikin banza
Gindin WaƘa: Nufinta ne wasan gargajiya,
:Ta sa mu Ƙara fahintar juna. Wannan mawaƘiya yi horo ga dukkan al’ummar Hausawa tare da jan hankalinsu domin su riƘe al’adunsu da hannu biyu ba tare da sanya wasa ko abin da zai aibata al’adun ba kuma, kar su aminta da wasu baƘin al’adu bale ma su fifita su a kan nasu. Ga abin da ya Ƙara faďi dangane da wannan:
Jagora:Gwannati tana da yawa jama’a,
: Gargaďi ga babba da yaro,
‘Y/Amshi: Kowa ya kama al’adunshi,
:Akwai waďansu mutane,
:Sun yada nasu sun bi na ‘yan cirani.

Tabbas gaskiya ce makaďa ya faďa domin akwai waďanda suka fifita al’adun wasu a kan nasu ba tare da yin la’akari da aibin watsi da nasu ba, ta hanyar rungumar na wasu. Allah Ya sawwaƘa!

5.3 NASON AL’ADUN KIƊA DA WAƘA


Wannan ma ba abin musu ba ne domin ya zama ruwan dare game duniya a Ƙasar Hausa. A wannan zamani nason baƘin al’adu na kaďe-kaďe da waƘe-waƘe sun yi naso sosai a cikin al’adun auren Hausawa kuma ba mai tada hannu ya ce ba haka abin yake ba. A taƘaice, sanin kowa ne cewa mafi yawan Hausawa sun yi watsi da kaďe-kaďen gargajiya da raye-rayensu suka cirata zuwa ga na baƘi. Mafi yawan kayan kiďan Hausawa an fara watsi da su domin sun zama tsohon yayi, aka rungumi waďanda ba su kai su daraja ba kamar yadda Sarkin Taushin Sarkin Katsina ya yi bayani. A zamanin da ake ciki an yi jana’izar mafi yawa daga cikin kayan kiďan Hausawa da suka haďa da kalangu da ganga da duma da Ƙaho da kuge da kurya da kotso da dundufa da taushi da sauransu sai dai kaďan da ba a rasa ba. Ko su ma domin kada a rasa wuta ne a maƘera ko kada a rasa nono ruga. Ba shakka an koma ga kayan kiďan zamani irin jita da fiyano da gangunan bigala da sauran irinsu. Har ta kai ga ba a gayyatar makaďin da ke amfani da kayan kiďan gargajiya zalla sai can ba a rasa ba ko shi a Ƙauyuka da kaďan a cikin birane domin Ƙauyawan da suka kwararo ciki. Mafi yawa idan aka saurari makaďan Hausa tare da yin la’akari da kayan kiďansu za a tarar sun saka kayan kiďan zamani cikin kiďan da suke yi. Misali, Ɗandago da Mai Asharalle a Katsina da sarkin Ɗori a Sakkwato da wasu da dama. Mafi yawan kaďe-kaďen da ake yi a cikin waƘoƘin bikin auren Hausawa sigar waƘoƘin baƘi suke ďauke da su.
Idan aka yi zancen waƘe-waƘe kuwa, ba sai an yi dogon bayani ba domin abubuwa ne da aka shedar a wannan zamani. Maimakon waƘar gargajiya da sautin gargajiya, sai aka musanya da na baƘi inda za a ji muryar Turawa ko Indiyawa ko Larabawa da sauran ‘yan Ƙasa maƘwabta irin Yarbawa da Ibo da sauransu. Idan aka yi zancen rawa ma haka abin yake kamar sauran bayanan da suka gabata a Ƃangaren kiďa da waƘa a cikin bikin auren Hausawa.

5.4 NASON FATI DA FIKINIK


A da, ba fati ko fikinik Hausawa ke yi ba. Abin da suke yi shi ne ‘Ajo’ domin taimaka wa ango domin samun abin tarbon amaryarsa. Maimakon wannan sai aka sami nason baƘin al’adu na yin fati da fikinik a lokacin bikin auren Hausawa. Fikinik ba komai ba ne sai iskancin da ake yi a cikin daji da Hausawa suka ara suka yafa domin ganin an yi da su ba tare da an bar su a baya ba, kuma ba tare da sanin manufarsa ba. Ba komi ya haddasa wannan ba sai kalle-kallen fina-finan da ake yi na zamani. Wani abin da ya kamata a sani a nan shi ne, babu Ƃarnar da ba a yi a wajen fati da fikinik. A daji ake yin fikinik. Fati kuwa, a cikin gari ake yin sa. Sai dai saboda ci gaban mai gainar rijiya da ya Hausawa suka samu na Ƃatar basira, an fara barin garin da ake bikin aure a je wani gari a yi hayar otel domin a yi fati can. A can ne mafi yawan samari da ‘yan mata ke kinkan da zina, abin da ke sanadiyar gurƂatar tarbiyyar al’umma baki ďaya. Za a fahimci cewa waďannan al’adu na waje ne ba na gida ba, sun yi nason gaske a cikin na Hausawa musamman a bukukuwan aure.

5.5 NASON SHAYE-SHAYE


Shaye-shaye kala-kala ne. Akwai na ruwa da kuma sandararre. Ban ce Hausawa ba su shaye-shaye ba sai dai baƘin al’adun shaye-shayen wasu al’ummu sun yi naso sosai ga rayuwarsu a lokutan bukukuwan aure. Ya dace a san da cewa, shaye-shayen da Hausawa ke yi ba domin bukin aure ne ko wani abu da ya yi kama da haka nan ba. Suna sha ne saboda wata buƘata ta daban musamman wani aiki da ya kai wa mai shi gaya. Su kuma baƘin na yin shaye-shaye ne da nufin jin daďin rayuwa da kuma nuna wayewa. Idan aka dubi mawaƘan waje irin Bob Marley da Michael Jackson da sauransu, suna sha ne domin jin daďin gudanar da aikinsu na waƘa. Sai dai kayya! Ganin wannan a cikin na’urorin kallo ya sanya wasu Hausawa rungumar sa ba tare da wata fargaba ba. Sanin kowa ne cewa shaye-shaye aibi ne. Wasu na yin shaye-shaye ne domin samun raguwar damuwar rayuwa, suka manta da naƘasar rayuwarsu da suka samu. Idan aka yi la’akari da cikin gida Nijeriya za a ga cewa Hausawa sun sami nason al’adun baƘin da ake tare da su kamar Yrbawa da Ibo da sauran Ƙabilun da ake gwagwarmayar rayuwa tare das u. Nason baƘin al’adu ya sa shahararren makaďin nan Marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina, a waƘarsa mai suna ‘A shs ruwa’ yake nuna irin holewar da aka saba da ita sanadiyar mu’amala da baƘi. Ga kaďan daga cikin waƘar:
Jagora: Ya bisimil ilahi,
‘Y/amshi:Jalla ubangiji, sha ruwa,
Jagora: Ka ji karatun masu bugun ruwa,
Wa’anda ke zikiri a kuloniyal,
‘Y/Amshi: Sha ruwa ba lahani ba ne,
Jagora: A nan muke sallarmu ta jumma’a,
‘Y/Amshi: A sha ruwa ba lahani ba ne
……………………………………..

Allah Ya jiƘan rai! Wannan ya nuna ken an waďannan abubuwa sun faru ne sanadiyar nason baƘin al’adu, kuma yakan iya faruwa ga kowa domin tsaka mai wuyar sani ce.

5.6 NASON RASHIN TARBIYYA


Na yi Ƙudurin bayyana irin alaƘar da ke tsakanin miji da matarsa da kuma iyayen miji da matar. A da, ba yadda za a yi a sami rashin kirki tsakanin surukai da sarukarsu, wato matar ďansu, a bayyane kuma da gangan said a aka fara samun nason baƘin al’adu. Idan aka yi la’akari da wannan alaƘa a wannan zamani za a ga bambancin da ke akwai ba kaďan ba ne. WulaƘanta iyaye al’adar mutanen banza ce. Haka kuma Turawa na daga cikin waďanda ke wulaƘanta iyayensu musamman idan sun cimma shekarun tsufa. Sai ga shi wannan al’ada ta yi naso cikin al’adun Hausawa na aure inda za a sami matar yaro ba ta san girman iyayen mijinta ba bale ta girmama su. Ko miji ya tarar da matarsa ta ci mutuncin iyayensa, ba zai yi wani bincike ba, sai ya faďa iyayensa da faďa wai su ke da laifi musamman wasu ‘yan boko da ke barin iyayensu a Ƙauyuka su koma birni suna kece raini da jin daďi iri-iri. An sha samun matsalar rashin ďa’a da matar miji ke yi wa iyayensa, wani lokaci ma har kotu matar ďa ke kai iyayensa domin ganin sun kula mata kuma, suna damuwarta. A fahimtata ďan ne ya wulaƘantar da iyayensa ba matar ba. Ita kuma matar halin da ta nuna a gidan surukai ya tabbatar wa al’umma cewa ba a koyar da ita tarbiyyar kirki ba a gidansu. Duk waďannan halaye da ake samu sun faru ne sanadiyar nason baƘin al’adu a cikin al’adun Hausawa na aure. A taƘaice dai, duk zama ne da maďauki kanwa ya sa kai ya yi fari.

6. KAMMALAWA


Gaskiya dokin Ƙarfe! Yadda yanayin zamantakewa yake shi ne duk lokacin da mutum ya yi sake babu abin da za a yi masa face sakiya. RiƘon kirki ga abin da yake naka na sa shakku a zuciyar mai laƂaƂen ya canza maka naka tare da fargaba, duk da yake an san da cewa ďabi’a na satar ďabi’a. Wasu baƘin al’adu sun zama tarnaƘi ga ďorewar na Hausawa saboda nason da suka yi mai muni a cikinsu. Da ma Hausawa sun ce “Bala’i maganinka roƘon Allah”. Wannan ya yi daidai da maganar da Sani Sabulu na Kanoma ke faďi cewa:
Jagora: A zuba zuwa ya ishi mai hankali
………………………………......

Ba shakka na gaba idon na baya ne. Kuma in kunne ya ji, jiki ya tsira.
BaƘin al’adu sun yi wa Hausawa babbar Ƃarna saboda nason da suka yi a cikin al’adun aurensu har suka kai ga taƂarƂarewa. Don haka a fahimtata baƘin al’adun da suka yi naso a cikin al’adun Hausawa na aure sun kasance kamar abin da Sani Sabulu ya faďa a cikin waƘarsa inda yake cewa:
Jagora: Reza nike mai kaifin baki,
: Kowa ya hau ni karkace ya faďi,
:Kafin ya farga rainai ya Ƃaci.

Dangane da haka ana iya cewa nason baƘin al’adu cikin al’adun Hausawa na aure ya zama ma Hausawa reza yanke baƘauye. Don haka ina mafita?

Duba wannan:

https://www.amsoshi.com/2017/07/19/tsiya-adon-yan-tauri-nazarin-ayukkan-%c6%99ungiyoyin-banga-ga-tsaron-%c6%99asa-wasu-sassan-adabin-hausa/

MANAZARTA


Adamu M (1977) “Towards a Definition of Culture in West African Context”, a seminar paper presented at Centre for Nigerian Cultural Studies, A.B.U. Zaria, April 1977.
Alhassan da wasu (1988) Zaman Hausawa Bugu na Biyu. Lagos Islamic Publication Bureau,
Bunza A.M. (2006) Gadon Feďe Al’ada. Lagos Tiwal Nigeria LTD.
Bunza A.M. (2011) “Al’adun Hausawa Jiya Da Yau: Cigaba Ko Lalacewa?” MuƘala: KADA, Journal Of Liberal Arts, Kaduna. Kaduna State University, Nigeria.
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya (2006) Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano. Jami’ar Bayero.
Gusau S.M. (1996) Makaďa Da MawaƘan Hausa Kano. Usman Al-Amin Publishing Company.
Gusau S.M. (2008) WaƘoƘin Baka A Ƙasar Hausa: Yanye-Yanayensu Da Sigoginsu, Kano Benchmark Publishers Limited.
Gusau S.M. (2009) Diwanin WaƘoƘin Baka: ZaƂaƂƂun Matanoni Na WaƘoƘin Baka Na Hausa, Kano. Century Research and Publishing Limited.
Gusau G.U. (2012) Bukukuwan Hausawa, Gusau. Ol-Faith Publishers.
Zagga N.M. (1985) “ Salo Da Jigo Da Tsarin Al’adun Hausawa A Wasan Idon Matambayi (Na Gidan Talabijin Sakkwato”. Jarrabawar Digirin Farko, Sakkwato. Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Sakkwato.